الطور

At-Tur

The Mount · Surah 52 · Ayahs: 49 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. وَٱلطُّورِ

    Open ayah 52:1

    Na rantse da dutsen Ɗuri.

  2. وَكِتَٰبٖ مَّسۡطُورٖ

    Open ayah 52:2

    Da kuma rubutaccen littafi.

  3. فِي رَقّٖ مَّنشُورٖ

    Open ayah 52:3

    Cikin buɗaɗɗiyar takardar fata.

  4. وَٱلۡبَيۡتِ ٱلۡمَعۡمُورِ

    Open ayah 52:4

    Da kuma Al-Baitul-Ma’amur .

  5. وَٱلسَّقۡفِ ٱلۡمَرۡفُوعِ

    Open ayah 52:5

    Da kuma rufi abin ɗaukakawa.

  6. وَٱلۡبَحۡرِ ٱلۡمَسۡجُورِ

    Open ayah 52:6

    Da kuma kogi cikakke maƙil.

  7. إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَٰقِعٞ

    Open ayah 52:7

    Lalle azabar Ubangijinka tabbas mai aukuwa ce.

  8. مَّا لَهُۥ مِن دَافِعٖ

    Open ayah 52:8

    Ba wani mai ingije ta.

  9. يَوۡمَ تَمُورُ ٱلسَّمَآءُ مَوۡرٗا

    Open ayah 52:9

    A ranar da sama za ta yi matsananciyar jujjuyawa.

  10. وَتَسِيرُ ٱلۡجِبَالُ سَيۡرٗا 

    Open ayah 52:10

    Duwatsu kuma su riƙa tafiya (suna barin wurarensu).

  11. فَوَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

    Open ayah 52:11

    To tsananin azaba a wanan ranar ya tabbata ga masu ƙaryatawa.

  12. ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي خَوۡضٖ يَلۡعَبُونَ

    Open ayah 52:12

    Waɗanda suke wasanni cikin ɓarna.

  13. يَوۡمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّا

    Open ayah 52:13

    A ranar da za a ingiza su zuwa ga wutar Jahannama ingizawa.

  14. هَٰذِهِ ٱلنَّارُ ٱلَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ

    Open ayah 52:14

    (Za a ce da su): “Wannan ita ce wutar da kuka kasance kuna ƙaryatawa.

  15. أَفَسِحۡرٌ هَٰذَآ أَمۡ أَنتُمۡ لَا تُبۡصِرُونَ

    Open ayah 52:15

    “Yanzu sihiri ne wannan ko kuwa ku ne ba kwa gani?

  16. ٱصۡلَوۡهَا فَٱصۡبِرُوٓاْ أَوۡ لَا تَصۡبِرُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡكُمۡۖ إِنَّمَا تُجۡزَوۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 52:16

    “To ku shige ta, sai ku yi haƙuri ko kada ku yi haƙuri duk ɗaya ne; ana saka muku ne kawai da abin da kuka kasance kuna aikatawa.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da rantsuwa da wasu manyan abubuwa guda biyar, su ne: <b>Na farko </b>, ya rantse da dutsen Ɗuri, shi ne dutsen da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi magana da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a gefensa, ya kuma ba shi littafin Attaura a nan wurin. <b>Na biyu </b>, ya yi rantsuwa da rubutaccen littafi, wasu malamai sun ce ana nufin littafin Lauhul Mahfuzu wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rubuta komai a cikinsa. Wasu kuma sun ce shi ne littafin Attaura da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a rubuce a cikin alluna. Wasu kuma suka ce shi ne duk wani littafi da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa manzanninsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta wannan littafin rubutacce da cewa, an rubuta shi a cikin fata mai taushi abar buɗewa. <b>Na uku </b>, ya yi rantsuwa da ‘Al-Baitul Ma’amur’ , shi ne ɗakin da ke a sama ta bakwai, wanda a koyaushe mala’iku suke raya shi da bautar Allah (Mai tsarki da daukaka). An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Al-Baitul Ma’amuru yana sama ta bakwai, kullum mala’iku dubu saba’in ne suke shiga cikinsa sannan ba za su sake komawa cikinsa ba har alƙiyama ta tashi.” [Ahmad #12558 da Hakim #3742]. Ya zo a cikin dogon hadisin Isra’in Manzon Allah (ﷺ) da Mi’irajinsa wanda Malik ɗan Sa’asa’a (Allah ya kara masa yarda) ya ruwaito, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “....Sannan aka ɗage min sai na ga Al-Baitul Ma’amur , sai na tambayi Jibrilu game da shi, sai ya ce mini: “Wannan ne Baitul Ma’amur , a kullum mala’ika dubu saba’in ne suke yin salla a cikinsa, idan sun fita dukkansu ba za su sake komowa cikinsa ba har abada.” [Bukhari #3207 da Muslim #164]. <b>Na huɗu </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da sama abar ɗaukakawa kamar rufi ga ƙasa. <b>Na biyar </b>, ya rantse da kogi wanda yake cike da ruwa maƙil, amma Allah ya hana shi ya yi ambaliya ya mamaye bayan ƙasa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin waɗannan rantse-rantse, watau shi ne tabbatar da aukuwar azabar Allah ga kafirai masu musunta tashin alƙiyama, masu jayayya da Manzon Allah (ﷺ). Idan kuma azabarsa ta auku to babu mai iya ture ta, domin babu mai iya ja da ikon Allah, babu kuma mai iya tsere masa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta ranar aukuwar wannan azaba, da cewa, ita ce ranar da sama za ta girgiza sosai, duwatsu kuma a gusar da su daga wurarensu su riƙa tashi sama bayan an niƙe su tilis sun zama kamar ƙura. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, tsananin azaba a wannan ranar ya tabbata ga masu ƙaryata alƙawarin Allah da tashin alƙiyama. Waɗanda suka rayu a duniya cikin kutse a cikin ƙarya da ɓarna suna ta wasanninsu sun gafala daga tuna Allah da ranar alƙiyama. A ranar za a zo da su ana ingiza su cikin wutar Jahannama da ƙarfi, ana faɗa musu cikin izgili da zargi cewa, wannan ita ce wutar da suka kasance kuna ƙaryatawa a duk sanda manzanninsu suka yi muku wa’azi suka tsoratar da su ita. Ana kuma tambayar su cewa, to yanzu wannan ma da suke gani shi ma sihiri ne, ko kuma ma babu abin da idanunsu suke gane musu? Don haka sai a ci gaba da cewa su ɗanɗani azabar wuta, haƙurinsu da rashin haƙurinsu a yau duk ɗaya ne, domin babu abin da zai amfana musu, kuma munanan ayyukansu ne suka jawo musu wannan mummunan sakamakon, babu wanda ya zalunce su.

  17. إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّٰتٖ وَنَعِيمٖ

    Open ayah 52:17

    Lalle masu tsoron Allah suna cikin gidajen Aljanna da ni’ima.

  18. فَٰكِهِينَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡ وَوَقَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ

    Open ayah 52:18

    Suna masu more abin da Ubangijisu Ya ba su, Ubangijinsu kuma Ya tserar da su daga azabar Jahima.

  19. كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 52:19

    Ku ci ku sha cikin jin ɗaɗi saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.

  20. مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ سُرُرٖ مَّصۡفُوفَةٖۖ وَزَوَّجۡنَٰهُم بِحُورٍ عِينٖ 

    Open ayah 52:20

    Kuna masu kishingiɗa a kan gadaje waɗanda aka jera su sahu-sahu; Muka kuma aura musu ‘yan matan Hurul-Ini. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon masu taƙawa, watau masu kiyaye dokokinsa; suna bin umarninsa suna kuma guje wa haninsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, a lahira za a kai su gidan Aljanna cikin wata ni’ima mai girma marar yankewa har abada, suna gidajensu na Aljanna suna morewa da kayayyakin jin daɗi da Allah Ubangijinsu ya tanadar musu na ci da na sha da auratayya, ya kuma tserar da su daga azabar wutar Jahimu. Watau dai ya ba su duk abin da suke so, ya kuma kare su daga abin da suke ƙi, saboda sun aikata abin da yake so, sun guji abin da yake ƙi. Bayan wannan ma, za kuma su riƙa jin maganganu masu daɗi na girmamawa, a riƙa ce musu, su ci su sha duk abin da ransu yake sha’awa cikin marmari da raha, hankalinsu kwance ba tare da suna fargabar wani abu zai cutar da su ba. Ana kuma tabbatar musu da cewa, wannan duka sakamakon kyawawan ayyukansu ne da suka kasance suna aikatawa a duniya. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani yanayi na jin daɗi da suke ciki, watau suna kishingiɗe a kan gadaje masu kwalliya waɗanda aka jera sahu-sahu, wasu na fuskantar wasu a jere da juna, kuma ƙari a kan haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aura musu matan Hurul-Ini, watau mata masu fararen idanuwa manya-manya, suna tare da su koyaushe suna ɗebe musu kewa.

  21. وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱتَّبَعَتۡهُمۡ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَٰنٍ أَلۡحَقۡنَا بِهِمۡ ذُرِّيَّتَهُمۡ وَمَآ أَلَتۡنَٰهُم مِّنۡ عَمَلِهِم مِّن شَيۡءٖۚ كُلُّ ٱمۡرِيِٕۭ بِمَا كَسَبَ رَهِينٞ

    Open ayah 52:21

    Waɗanda kuwa suka yi imani, zuriyarsu kuma suka bi su a imani, za Mu haɗa su da zuriyarsu, ba kuma za Mu tauye musu komai ba na aikinsu. Kowane mutum jingina ne ga abin da ya tsuwurwurta.

  22. وَأَمۡدَدۡنَٰهُم بِفَٰكِهَةٖ وَلَحۡمٖ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ

    Open ayah 52:22

    Muka kuma daɗe su da abin marmari da nama irin wanda suke sha’awa.

  23. يَتَنَٰزَعُونَ فِيهَا كَأۡسٗا لَّا لَغۡوٞ فِيهَا وَلَا تَأۡثِيمٞ

    Open ayah 52:23

    A cikinta (Aljannar) suna musayan kofuna na giya da babu wani zancen banza game da ita, kuma babu wani zunubi.

  24. ۞وَيَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ غِلۡمَانٞ لَّهُمۡ كَأَنَّهُمۡ لُؤۡلُؤٞ مَّكۡنُونٞ

    Open ayah 52:24

    Wasu yara nasu kuma waɗanda suke kamar lu’u-lu’un da yake cikin kwasfa suna kaiwa da komowa a kansu.

  25. وَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ

    Open ayah 52:25

    Kuma shashinsu ya fuskanci shashi suna tambayar juna.

  26. قَالُوٓاْ إِنَّا كُنَّا قَبۡلُ فِيٓ أَهۡلِنَا مُشۡفِقِينَ

    Open ayah 52:26

    Suka ce: “Lalle sanda muke cikin iyalinmu (a duniya) kafin wannan, mun kasance masu tsoron azabar Allah.

  27. فَمَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡنَا وَوَقَىٰنَا عَذَابَ ٱلسَّمُومِ

    Open ayah 52:27

    “Sai Allah Ya yi mana baiwa ya kiyaye mu azabar wuta.

  28. إِنَّا كُنَّا مِن قَبۡلُ نَدۡعُوهُۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡبَرُّ ٱلرَّحِيمُ

    Open ayah 52:28

    “Lalle mu mun kasance a da can muna bauta masa; lalle shi Mai kyautatawa ne, Mai jin ƙai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin cikakkiyar ni’imar da ya tanadar wa ‘yan Aljanna, da cewa, duk waɗanda suka yi imani a nan duniya suka yi ayyuka nagari, sannan ‘ya’yansu ma suka bi su a imani, to sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya haɗa su wuri guda a Aljanna, watau ya ɗaukaka darajar ‘ya’yansu don su haɗu wuri ɗaya, ko da kuwa ayyukan ‘ya’yan ba su kai na iyayen ba. Ya yi musu haka ne don ya cika musu farin cikinsu, ba kuma tare da ya tauye musu wani abu na ladansu ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah yana ɗaga zuriyar mumini zuwa gare shi har ya kai su zuwa ga matsayinsa, ko da kuwa ba su kai shi ba wajen aiki, don hakan ya faranta masa rai.” Sai ya karanta wannan ayar. [Al-Bazzar #2260. Dubi, Al-Al-Bani, As-Silsilatus Sahihah #2490]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikar adalcinsa ga bayinsa, inda ya tabbatar musu da cewa, kowane mutum ana tsare shi ga abin da ya aikata kaɗai, ba za a kama wani rai da laifin wani ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana ni’imomin ‘yan Aljanna, yayin da za a daɗa kawo musu kayan marmari iri-iri waɗanda ransu yake so, da kuma nama irin wanda suke sha’awa. Bugu da ƙari kuma za su riƙa musayan kofuna na giya a tsakaninsu, irin giyar da ba ta sanya mai shan ta wani zancen banza ko aikata wani laifi, kamar yadda yake faruwa ga wanda ya sha giyar duniya ya bugu. Sannan kuma ga wasu yara matasa masu yi musu hidima suna kaiwa da komowa a kansu, ga su da haske kamar lu’u-lu’u da yake cikin kwasfansa wani abu bai ɓata shi ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Kowane ɗan’adam yana da hadimi dubu, kowane hadimi yana da aikinsa ba irin na ɗan’uwansa ba.” [Ibn Jarir, At-Tafsir Juzu’i na 21, shafi na 641]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ‘yan Aljanna za su zauna suna tuna rayuwarsu ta duniya, yayin da wasu za su fuskanci juna suna tambayar junansu labaransu da yanayin rayuwarsu a duniya, sai su amsa wa juna da cewa a duniya suna cike da tsoron azabar Allah, wanda hakan ya sanya suka guji saɓa masa, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu baiwar shiriya zuwa ga Musulunci, ya tsare su daga matsananciyar azaba. Suka kuma tabbatar wa da juna cewa sun kasance a duniya suna bautar Allah, suna kuma roƙon sa ya tsare su daga azabar wuta, domin shi mai kyautata wa bayinsa ne mai jin ƙan su ne, don haka ne ya shiryar da su ga imani, ya shigar da su gidan Aljanna, ya tsare su daga shiga wutar Jahannama.

  29. فَذَكِّرۡ فَمَآ أَنتَ بِنِعۡمَتِ رَبِّكَ بِكَاهِنٖ وَلَا مَجۡنُونٍ

    Open ayah 52:29

    To ka yi wa’azi, don ba za ka zama boka ba ko mahaukaci saboda ni’imar Ubangijinka.

  30. أَمۡ يَقُولُونَ شَاعِرٞ نَّتَرَبَّصُ بِهِۦ رَيۡبَ ٱلۡمَنُونِ 

    Open ayah 52:30

    A’a, cewa dai suka yi: “Shi mawaƙi ne da muke saurara masa hanyar halaka.”

  31. قُلۡ تَرَبَّصُواْ فَإِنِّي مَعَكُم مِّنَ ٱلۡمُتَرَبِّصِينَ

    Open ayah 52:31

    Ka ce, “To ku saurara, ni ma lalle ina cikin masu sauraron.”

  32. أَمۡ تَأۡمُرُهُمۡ أَحۡلَٰمُهُم بِهَٰذَآۚ أَمۡ هُمۡ قَوۡمٞ طَاغُونَ

    Open ayah 52:32

    Ko kuwa hankullansu ne suke umartar su da wannan? A’a, su dai mutane ne masu tsaurin kai.

  33. أَمۡ يَقُولُونَ تَقَوَّلَهُۥۚ بَل لَّا يُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 52:33

    Ko kuwa suna cewa: “Ya ƙago shi?” A’a, su dai ba sa yin imani ne kawai.

  34. فَلۡيَأۡتُواْ بِحَدِيثٖ مِّثۡلِهِۦٓ إِن كَانُواْ صَٰدِقِينَ

    Open ayah 52:34

    To su zo da wani zance irinsa idan sun kasance masu gaskiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya ci gaba da yi wa mutane wa’azi da faɗakarwa, kada ya damu da masu ƙaryata shi, suna cutar da shi tare da mabiyansa, har suna jifan sa da miyagun maganganu da tuhumce-tuhumce na ƙarya, alhali kuwa sun san shi ciki da bai ba haka yake ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wanke shi daga duk wani aibi da suke liƙa masa, don haka shi ba boka ba ne ba kuma mahaukaci ba ne, domin Allah ya yi masa ni’imomi da dama, daga cikinsu har da kamalar hankali da guje wa shaiɗanu. To amma duk da wannan sai wani lokaci su ce masa shi mawaƙi ne ba manzo ne daga Allah ba, don haka suna saurara masa ne har mutuwa ta zo ta ɗauke shi kowa ya huta. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya mayar musu da martani da cewa su ci gaba da sauraron mutuwarsa, shi ma yana nan yana sauraron azabar da za ta zo ta auka musu saboda kafircinsu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su cewa, shin munanan maganganun da suke jifan Manzonsa da su, hankulansu ne suka faɗa musu haka, watau su kira shi boka da mahaukaci a lokaci guda, su haɗa masa abubuwan da ba za su haɗu wuri guda ba? Watau idan har haka hankulansu suke, to tir da irin waɗannan hankula nasu. Ko kuma dai ɗagawarsu ce ta jefa su cikin wannan harigido suna ƙazafi suna ƙetare duk wata iyaka, ba sa aiki da lura balle shari’a. Tabbas wannan shi ne dalilin taɓewarsu da yawan maganganunsu na ƙarya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wai suna zargin Annabi (ﷺ) da cewa shi ne ya ƙagi Alƙur’ani ba wahayinsa aka yi masa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da jawabi cewa ba haka ba ne, Manzon Allah (ﷺ) bai ƙagi Alƙur’ani ba, kawai dai saboda sun ƙi yin imani ne don girman kansu da bijirewarsu. Don haka sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalance su da cewa, tun da su ma Larabawa ne masu fasaha to su ƙago wani zance kamar na Alƙur’ani idan har su masu gaskiya ne game da abin da suke faɗa a kan Manzon Allah (ﷺ).

  35. أَمۡ خُلِقُواْ مِنۡ غَيۡرِ شَيۡءٍ أَمۡ هُمُ ٱلۡخَٰلِقُونَ

    Open ayah 52:35

    Ko kuwa an halicce su ne ba da wani mai halitta ba, ko kuwa su ne masu halittar (kansu)?

  36. أَمۡ خَلَقُواْ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ

    Open ayah 52:36

    Ko kuwa su suka halicci sammai da ƙasa? A’a, ba sa dai sakankancewa ne.

  37. أَمۡ عِندَهُمۡ خَزَآئِنُ رَبِّكَ أَمۡ هُمُ ٱلۡمُصَۜيۡطِرُونَ

    Open ayah 52:37

    Ko kuwa taskokin Ubangijinka suna wurinsu ne, ko kuwa su ne masu iko?

  38. أَمۡ لَهُمۡ سُلَّمٞ يَسۡتَمِعُونَ فِيهِۖ فَلۡيَأۡتِ مُسۡتَمِعُهُم بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ

    Open ayah 52:38

    Ko kuwa suna da wani tsani ne da suke jiyo (zancen Allah) ta kansa? To mai jiyowar tasu ya zo da wata hujja mabayyaniya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mushirikai masu musunta Kaɗaitakarsa wajen bauta da ƙaryata Manzonsa (ﷺ) da tashi bayan mutuwa wanda yake nuna rashin imaninsu da cikar Ƙudura da iko na Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jefa musu wasu tambayoyi da ba su da wata amsa da za su iya bayarwa sai dai yarda da sallama wa Ƙudurar Allah a kan komai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su cewa, shin haka kawai suka faɗo duniya ba tare da wani mahalicci ba, watau samuwa kawai suka yi ba tare da wani ya samar da su ba? Su kansu sun san wannan abu ba zai taɓa yiwuwa a hankali ba. Ko kuma su ne suka halicci kawunansu? Wannan ma sun san ba zai taɓa faruwa ba, domin kuwa sun san ba za a taɓa samun wani mahaluƙi ba tare da mahalicci ba, hakanan ba zai yiwu wani mahaluƙi ya yi halitta ba, to me ya hana su bauta wa mahaliccinsu Allah shi kaɗai? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tambayar su cewa, shin su ne suka halicci sammai da ƙasa, don haka suka zamanto suna tarayya da Allah wajen yin halittar? Wannan ma sun san ba haka ne ba, to me ya hana su bautar Allah shi kaɗai? Me kuma ya sanya suke ƙaryata tashi bayan mutuwa? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, musabbabin haka shi ne rashin yaƙini da sakankancewa da hujjojin da Allah ya bayyana musu shi ne ya kai su ga ƙaryata gaskiya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tambayar su game da taskokin arzukinsa da rahamarsa cewa, shin a hannunsu suke, suna zaɓar wanda suka ga dama su ba shi, su hana wanda suka ga damar hanawa, don haka suka ga damar hana wa Annabi (ﷺ) annabci, ko kuwa dai su ne masu iko da komai na halittar Allah, suna yin abin da suke so? Lalle sun tabbata ba haka abin yake ba, to me ya sanya su ƙaryata manzancin Annabi (ﷺ) har su riƙa jifan sa da tuhumce-tuhumce na banza? Sannan ya sake tambayar su game da dagewar da suke a kan cewa su ne masu gaskiya Annabi (ﷺ) maƙaryaci ne da cewa, shin suna da wani tsani ne da suke hawa sama da shi inda suka jiyo wahayi daga Allah na cewa lalle su ne masu gaskiya? To idan sun ce haka ne, to mai jiyo musu wahayin ya zo da wata hujja bayyananna da za ta gaskata su a kan da’awarsu. Sun tabbata haka ma ba mai yiwuwa ba ne.

  39. أَمۡ لَهُ ٱلۡبَنَٰتُ وَلَكُمُ ٱلۡبَنُونَ

    Open ayah 52:39

    Ko kuwa Shi ne zai zama mai ‘ya’ya mata, ku kuwa ku zamanto da ‘ya’ya maza?

  40. أَمۡ تَسۡـَٔلُهُمۡ أَجۡرٗا فَهُم مِّن مَّغۡرَمٖ مُّثۡقَلُونَ 

    Open ayah 52:40

    Ko kuwa kana tambayar su wani lada ne, saboda haka bashi ya yi musu nauyi?

  41. أَمۡ عِندَهُمُ ٱلۡغَيۡبُ فَهُمۡ يَكۡتُبُونَ

    Open ayah 52:41

    Ko kuwa sun san gaibu ne, saboda haka su ne suke rubutawa.

  42. أَمۡ يُرِيدُونَ كَيۡدٗاۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ هُمُ ٱلۡمَكِيدُونَ

    Open ayah 52:42

    Ko kuwa suna nufin (yi maka) makirci ne? To waɗanda suka kafirce su ne waɗanda makircinsu zai kama su.

  43. أَمۡ لَهُمۡ إِلَٰهٌ غَيۡرُ ٱللَّهِۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

    Open ayah 52:43

    Ko kuwa suna da wani abin bauta ne ba Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke tara (Shi da shi). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar wa da mushirikan Larabawa martani a kan da’awarsu ta cewa mala’iku ‘ya’yan Allah ne mata, inda ya nuna musu rashin adalcinsu har a cikin ƙaryar da suke yi, domin ta yaya za su danganta wa Allah ‘ya’ya mata alhalin su suna ƙin su, su kuma su zaɓa wa kansu ‘ya’ya maza? Don haka a nan sun haɗa munanan abubuwa biyu a tare, da farko sun jingina wa Allah ɗa, alhalin bai haifa ba, ba a haife shi ba. Na biyu kuma suka zaɓa masa ‘ya’ya mata waɗanda su ba sa son su, har ma suka ce su ne ‘ya’yan Allah. Yanzu akwai tauye haƙƙin da ya kai wannan? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi Manzonsa (ﷺ) game da bijirewar da mushirikai suke yi masa cewa, ko yana neman su riƙa ba shi wani lada ne game da saƙon da yake isar musu, su kuma suka kasa biyan sa, don haka suka ƙi ba da gaskiya da shi? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tambayar su cewa, ko suna da ilimin gaibu ne, don haka suna gano abubuwan da mutane ba su sani ba, sai suka riƙa rubuta su? Watau ta haka ne suka samo ilimin da ya fi wanda Annabi (ﷺ) ya zo musu da shi ko ya saɓa masa, saboda haka suka ƙi yin imani da shi. Lalle su ma sun tabbata ba haka abin yake ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, to idan duk abin ba haka yake ba, to su mushirikai masu sukan Manzon Allah suna ƙaryata shi, suna nufin yi masa makirci ne da niyyar su kuma cutar da shi su cutar da addininsa? To sai Allah ya umarci Manzon Allah (ﷺ) ya sami nutsuwa ya dogara ga Allah, waɗannan kafirai su ne makircin zai ci, ba zai shafe shi da komai ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tambayar su cewa, shin suna da wani abin bauta ne da gaskiya ba Allah ba, wanda yake amfanar da su ko ya cutar da su? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsarkake kansa daga duk wani abokin tarayya da suke danganta masa.

  44. وَإِن يَرَوۡاْ كِسۡفٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ سَاقِطٗا يَقُولُواْ سَحَابٞ مَّرۡكُومٞ

    Open ayah 52:44

    Da kuwa za su ga wani yanki na azaba mai faɗowa daga sama da sai su ce: “Hadari ne haɗaɗɗe.”

  45. فَذَرۡهُمۡ حَتَّىٰ يُلَٰقُواْ يَوۡمَهُمُ ٱلَّذِي فِيهِ يُصۡعَقُونَ

    Open ayah 52:45

    To ka rabu da su har sai sun haɗu da ranarsu wadda za a karɓi rayukansu a cikinta.

  46. يَوۡمَ لَا يُغۡنِي عَنۡهُمۡ كَيۡدُهُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ

    Open ayah 52:46

    Ranar da makircinsu ba zai maganta musu komai ba, kuma su ba za a taimake su ba.

  47. وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ عَذَابٗا دُونَ ذَٰلِكَ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 52:47

    Lalle kuma waɗanda suka yi zalunci suna da wata azabar daban ban da wannan (ta lahira), sai dai kuma mafi yawansu ba su sani ba.

  48. وَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعۡيُنِنَاۖ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ

    Open ayah 52:48

    Kuma ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijika, don ko lalle kana ƙarƙashin lurarmu; kuma ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka lokacin da za ka tashi (daga bacci).

  49. وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَسَبِّحۡهُ وَإِدۡبَٰرَ ٱلنُّجُومِ

    Open ayah 52:49

    Da daddare kuma sai ka tsarkake Shi da kuma lokacin da taurari suka ba da baya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tsananin taurin kan mushirikai da ƙaryata gaskiya bayan duk wasu dalilai sun tabbata, don haka ba abin da zai dace da su sai azabar Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, taurin kansu ya kai ta yadda ko da ma za su ga wani yanki na azaba ya taho gadan-gadan zai faɗo musu daga sama, to ba za su yarda da cewa azabar Allah ce ta zo musu ba, sai dai su riƙa cewa ai haɗari ne ya haɗo wani kan wani zai saukar musu da ruwa, don haka ba za su wa’azantu ba ballantana su yi imani. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya fita batunsu, ya ci gaba da wa’azinsa, domin sun kasance mutane ne da babu abin da zai yi maganin taurin kansu sai sun haɗu da ranar da za su gamu da azaba sun gan ta a fili babu sauran wani musu, watau ranar alƙiyama. A ranar duk wani makircinsu ba zai amfana musu komai ba, kuma ba su da waɗanda za su taimaka musu su kuɓutar da su daga azabar Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, waɗanda suka zalunci kawunansu da shirka da saɓon Allah suna da wata azaba ta daban tun kafin su haɗu da azabar lahira, watau a nan duniya za su iya gamuwa da azabar kisa a wurin yaƙi ko kamawa a matsayin ribatattun yaƙi, sannan idan sun mutu su haɗu da azabar ƙabari, to amma duk da irin wannan gargaɗi da ake yi musu Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, yawancinsu ba su san haka ba, don haka ba za su taɓa rabuwa da kafircinsu ba. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rugujewar duk abin da mushirikai suke kai na shirka da ƙaryata Manzon Allah da yi masa izgili, sai a ƙarshen wannan Surar ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya ci gaba da haƙuri da hukuncin Allah bisa duk abin da zai same shi marar daɗi, ya tabbatar masa cewa yana ƙarƙashin kulawarsa da kiyayewarsa, shi dai kawai ya ci gaba da bautar Allah Ubangijinsa yana tsarkake shi da tasbihi tare da gode masa duk lokacin da ya tashi daga barci. Hakanan da daddare ya tsarkake shi da yin tasbihi yayin sallolin dare, ya kuma sallaci sallar Asuba lokacin da taurari suka ba da baya yayin da hasken alfijir ya bayyana.