النجم
An-Najm
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلنَّجۡمِ إِذَا هَوَىٰ
Open ayah 53:1Na rantse da tauraro yayin da ya faɗi.
مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمۡ وَمَا غَوَىٰ
Open ayah 53:2Mutumin naku bai ɓata ba, kuma bai kauce hanya ba.
وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلۡهَوَىٰٓ
Open ayah 53:3Kuma ba ya yin magana bisa son rai.
إِنۡ هُوَ إِلَّا وَحۡيٞ يُوحَىٰ
Open ayah 53:4Shi (Alƙur\'ani) ba wani abu ne ba in ban da wahayi da ake yiwo (masa).
عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلۡقُوَىٰ
Open ayah 53:5Mai tsananin ƙarfi ne (watau Jibrilu) ya koyar da shi.
ذُو مِرَّةٖ فَٱسۡتَوَىٰ
Open ayah 53:6Mai kyawawan halitta ne, sai ya daidaita.
وَهُوَ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡأَعۡلَىٰ
Open ayah 53:7Alhali kuwa shi yana a sassa na can sama.
ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ
Open ayah 53:8Sannan sai ya kusanto, sai ya ƙara matsawa.
فَكَانَ قَابَ قَوۡسَيۡنِ أَوۡ أَدۡنَىٰ
Open ayah 53:9Sai ya kasance kamar kusancin kamu biyu ko ƙasa da haka.
فَأَوۡحَىٰٓ إِلَىٰ عَبۡدِهِۦ مَآ أَوۡحَىٰ
Open ayah 53:10Sannan (Allah) Ya yiyo wahayin abin da Ya yi wahayi zuwa ga Bawansa (Ma’aiki).
مَا كَذَبَ ٱلۡفُؤَادُ مَا رَأَىٰٓ
Open ayah 53:11Zuciyar (ta Ma’aiki) ba ta yi ƙaryar abin da ta gani ba.
أَفَتُمَٰرُونَهُۥ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ
Open ayah 53:12Yanzu kwa riƙa jayayya da shi kan abin da yake gani?
وَلَقَدۡ رَءَاهُ نَزۡلَةً أُخۡرَىٰ
Open ayah 53:13Haƙiƙa ya gan shi (Jibrilu) a wani karon ma.
عِندَ سِدۡرَةِ ٱلۡمُنتَهَىٰ
Open ayah 53:14A wurin Magaryar tuƙewa.
عِندَهَا جَنَّةُ ٱلۡمَأۡوَىٰٓ
Open ayah 53:15A wurinta ne Aljannar makoma take.
إِذۡ يَغۡشَى ٱلسِّدۡرَةَ مَا يَغۡشَىٰ
Open ayah 53:16A yayin da abin da ya lulluɓe Magaryar (na ban mamaki) ya lulluɓe ta.
مَا زَاغَ ٱلۡبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ
Open ayah 53:17Ganin (nasa) bai karkace ba, kuma bai zarme ba.
لَقَدۡ رَأَىٰ مِنۡ ءَايَٰتِ رَبِّهِ ٱلۡكُبۡرَىٰٓ
Open ayah 53:18Haƙiƙa ya ga wasu ayoyin Ubangijinsa manya-manya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa da tauraro yayin da ya faɗi a ƙarshen dare, domin ya tabbatar wa mushirikai cewa mutuminsu, watau Annabi Muhammadu (ﷺ) bai ɓata ya kauce wa hanyar gaskiya ba, bai kuma zama mai sani ya take saninsa ba. Shi mutum ne da yake kan hanyar gaskiya kuma yana aiki da ita. Kuma ba ya magana ta son zuciya. Duk abin da yake karanta musu na Alƙur’ani da wanda yake sanar da su na shari’a ba wani abu ne ba illa wahayi daga Allah, Mala’ika mai tsananin ƙarfi ne ya koyar da shi, watau Jibirilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta Jibirilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa shi mai kyakkyawar halitta ne, kuma ya daidaita a zahiri a cikin surarsa da Allah ya halicce shi da ita ta mala’ika a lokacin yana can a cikin sassa na sama sosai. Sannan sai ya kusanto Annabi (ﷺ) ya sake matsowa kusa da shi, har sai da kusancinsa da shi ya zamanto kamar kusancin kamu biyu ko ma ƙasa da haka. Sai Jibirilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wahayi zuwa ga bawan Allah Annabi Muhammadu (ﷺ) na abin da ya yi masa wahayi da shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, zuciyar Manzon Allah (ﷺ) ba ta yi ƙaryar abin da idanunsa suka gani ba, watau jinsa da ganinsa da zuciyarsa duk sun haɗu a kan tabbatar da abu ɗaya na wahayi da Jibirilu ya yi masa ba su sassaɓa wa juna ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi mushirikai cewa, to yanzu su suna jayayya da Annabi ne (ﷺ) game da abin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna masa a daren Isra’i na manya-manyan ayoyinsa? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ga Mala’ika Jibirilu a surarsa ta mala\'ika da Allah ya halicce shi da ita a wani karo na daban, watau a daren Isra’i a wurin Magaryar tuƙewa, wata bishiya ce babba da ke saman sama ta bakwai, inda duk wani abu da ya hau sama yake tuƙewa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a wurin wannan bishiyar Aljannar makoma take. Kuma wani babban al’amari na Allah ne yake lulluɓe ta wanda babu mai iya siffanta shi sai Allah. Sai kuma ya bayyana cikar ladabin Manzon Allah (ﷺ) da nutsuwarsa lokacin da Allah ya tsayar da shi wannan matsayi, ganinsa bai karkata dama ko hagu ba, bai kuma ƙetare iyakar da ya shata masa ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda), yana cewa: “Manzon Allah (ﷺ) ya ga Ubangijinsa da zuciyarsa sau biyu.” [Muslim #171 da Ahmad #1958]. An karɓo daga Masruƙ ya ce: A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce masa: “Ya kai baban A’isha, duk wanda ya riya cewa Muhammadu ya ga Ubangijinsa, to ya yi wa Allah babbar ƙarya.” Ya ce: Na kasance ina kishingiɗe sai na miƙe zaune na ce: “Ya Uwar Muminai, ki saurara mini kada ki yi mini gaggawa, me za ki ce game da faɗar Allah: “Haƙiƙa ya gan shi a wani karon ma”, da kuma faɗarsa: “Haƙiƙa ya gan shi a sararin (samaniya) mabayyani”? Sai ta ce: “Wannan Jibrilu ne; ya gan shi a wani lokaci a surarsa da aka halicce shi da ita; ya sake ganin sa a wani lokaci na biyu yayin da yake sauka daga sama zuwa ƙasa, girman halittarsa ta cika sama da ƙasa.” Ta ce: “Ni ce farkon wanda na yi wa Manzon Allah (ﷺ) tambaya game da wannan ayar, sai ya ce: “Ai Jibrilu ne.” [Bukhari #3235 da Muslim #177]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “An nuna mini Magaryar tuƙewa a sama ta bakwai, ‘ya’yanta kamar kulolin Hajar, ganyenta kuwa kamar kunnuwan giwaye. Daga kututturan itacenta wasu ƙoramu suna fita, biyu a waje, biyu kuma a ciki, sai na ce: “Ya Jibrilu mene ne waɗannan?” Sai ya ce: Ƙoramu biyu na ciki daga Aljanna ne, amma na waje su ne Nilu da Furata.” [Ahmad #12673, Dubi Bukhari #3207 da Muslim #173]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lokacin da na isa wajen Magaryar tuƙewa, sai na ga ganyenta kamar kunnuwan giwaye, ‘ya’yanta kuwa kamar tuluna. Yayin da abin da ya lulluɓe ta daga al’amarin Allah ya lulluɓe ta sai ta rikiɗa ta zama yaƙutu da zumarradu da kwatankwacinsu.” [Ahmad #12301 da Ibn Jarir, Tafsiri, Juzu’i na 22 shafi na 36]. A wata ruwayar ya ce: “Yayin da abin da ya lulluɓe ta na al’amarin Allah ya lulluɓe ta sai ta rikiɗa, babu wanda zai iya siffanta ta saboda kyanta.” [Muslim #162]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, a daren Mi’iraji Annabi Muhammadu (ﷺ) ya ga manya-manyan ayoyin Ubangijinsa masu nuna cikar Ƙudurarsa, ya ga Aljanna ya kuma ga wuta da abubuwan ban mamaki da dama.
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱللَّٰتَ وَٱلۡعُزَّىٰ
Open ayah 53:19Ku ba ni labarin (gumakan) Lata da Uzza.
وَمَنَوٰةَ ٱلثَّالِثَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ
Open ayah 53:20Da Manata cikon ta ukunsu.
أَلَكُمُ ٱلذَّكَرُ وَلَهُ ٱلۡأُنثَىٰ
Open ayah 53:21Yanzu ɗa namiji zai zama naku, Shi kuma Ya tashi da \'ya mace?
تِلۡكَ إِذٗا قِسۡمَةٞ ضِيزَىٰٓ
Open ayah 53:22Idan haka ne wannan rabon na zalunci ne.
إِنۡ هِيَ إِلَّآ أَسۡمَآءٞ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهۡوَى ٱلۡأَنفُسُۖ وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلۡهُدَىٰٓ
Open ayah 53:23Su ba komai ba ne face sunaye da kuka sa musu, ku da iyayenku, Allah bai saukar muku da wata hujja ba game da su. Ba abin da suke bi sai zato da son zuciya. Haƙiƙa kuwa shiriya ta zo musu daga Ubangijinsu.
أَمۡ لِلۡإِنسَٰنِ مَا تَمَنَّىٰ
Open ayah 53:24Ko kuwa sai mutum ya sami abin da yake buri ne?
فَلِلَّهِ ٱلۡأٓخِرَةُ وَٱلۡأُولَىٰ
Open ayah 53:25To lahira da duniya duka na Allah ne.
۞وَكَم مِّن مَّلَكٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ لَا تُغۡنِي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ أَن يَأۡذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرۡضَىٰٓ
Open ayah 53:26Mala’iku nawa ne a cikin sammai cetonsu ba ya amfanar da komai sai da izinin Allah ga waɗanda Ya ga dama Ya kuma yarda (da shi)? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rushewar addinin mushirikai masu bautar gumaka ba Allah ba waɗanda ba za su amfane su ko su cutar da su ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su game da gumakansu: Lata da Uzza da Manata ta cikon ukunsu, shin suna yi masu wani amfani ne ko suna iya cutar da su da wani abu? Sun tabbata ba sa iya yi musu komai daga cikin waɗannan abubuwa biyu, to wane rashin hankali ne ya kai su ga bauta musu da ba su matsayin Allah (Mai tsarki da daukaka)? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rashin ladabinsu gare shi, da tsabar zalunci da suke nunawa game da sha’aninsa, domin suna jingina masa ‘ya’ya mata suna cewa su ne mala’iku. Su kuma suna zaɓa wa kawunansu ‘ya’ya maza suna fifita su a kan mata. Allah ya tabbatar musu cewa, da abin haka yake, to da wannan rabo nasu ya zama rabon zalunci, domin yana ƙunshe da fifita mahaluƙi a kan Mahalicci Allah. Kuma su gumakan da suke bauta ba Allah ba ba komai ba ne sai sunayen banza da suka ƙirƙira su da iyayensu suka laƙaba wa gumakan, amma ko kaɗan ba su cancanci a bauta musu ba, domin babu wata hujja da Allah ya saukar a kan haka. Mushirikai ba su gina addininsu a kan komai ba sai zunzurutun zato marar tushe da abin da soye-soyen zukatansu da shaiɗanunsu suke ƙawata musu suna bi suna aiki da shi, alhali sun yi watsi da shiriyar Allah, ga ta kuma tabbas Manzo ya zo musu da ita daga Ubangijinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk da wannan ɓata da rashin hankalin da kafirai suke ciki da sunan addini, wai amma suna burin samun wani tagomashi a cikinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, abin da suke buri na samun ceton gumakansu ba mai samuwa ba ne, domin kuwa ba duk abin da mutum yake buri yake samu ba, domin al\'amura ba a hannunsa suke ba, komai yana ƙarƙashin mulkin Allah, don shi ne mai mulkin lahira da duniya duka, don haka yana ba wa wanda ya ga dama abin da ya ga dama a cikinsu, yana kuma hana wanda ya ga damar hanawa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya soki bautar mala’iku da wasu suke yi suna tsammanin za su cece su a wurin Allah a ranar alƙiyama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, mala’iku da dama a cikin sammai cetonsu ba zai amfanar da komai ba sai bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba su izinin yin ceto ga wanda ya ga damar su ceta ya kuma yarda da shi. Don haka mushirikai su san da cewa, Allah ba zai taɓa ba da izinin a ceci wanda yake yi masa shirka ba.
إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ لَيُسَمُّونَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ تَسۡمِيَةَ ٱلۡأُنثَىٰ
Open ayah 53:27Lalle waɗanda ba sa yin imani da ranar lahira suna kiran mala’iku da sunan mata.
وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّۖ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغۡنِي مِنَ ٱلۡحَقِّ شَيۡـٔٗا
Open ayah 53:28Kuma ba su da wani ilimi game da haka; ba abin da suke bi sai zato; shi kuma zato, lalle ba ya wadatar da komai game da gaskiya.
فَأَعۡرِضۡ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكۡرِنَا وَلَمۡ يُرِدۡ إِلَّا ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا
Open ayah 53:29Sai ka kau da kai daga duk wanda ya ba da baya daga ambatonmu, bai kuma yi nufin komai ba sai rayuwar duniya..
ذَٰلِكَ مَبۡلَغُهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱهۡتَدَىٰ
Open ayah 53:30Wannan ne maƙurar iliminsu. Lalle Ubangijinka Shi ne Ya fi sanin wanda ya ɓace daga hanyarsa kuma Shi Ya fi sanin wanda ya shiriya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mushirikai waɗanda ba su yi imani da ranar lahira ba suna kiran mala’iku da sunan mata, domin a cewarsu su ‘ya’yan Allah ne mata, alhalin ba haka abin yake ba, suna faɗar waɗannan maganganun ne da jahilci ba da wani ilimi da suka dogara da shi ba sai shaci-faɗi da tsantsar zato, zato kuwa ba ya wadatar da komai game da gaskiya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa ya yi watsi da duk wanda ya bijire wa ambaton Allah ya zamanto ba gaskiya ce a gabansa ba, ba ya da wata manufa sai son rayuwar duniya kaɗai; ba wani aiki da yake yi don lahirarsa, domin bai yi imani da ita ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, duk irin waɗancan munanan maganganun da mushirikai suke yi na kiran mala’iku da sunan mata da sanya duniya a gaba da mantawa da lahira su ne ƙololuwar iliminsu, wanda ya kasa kai su ga samun yaƙini da gano gaskiya da aiki da ita. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa cewa shi ne mafi sanin wanda ya ɓace ya bar hanyar gaskiya. Shi kuma ne ya fi kowa sanin wanda ya shirya ya kama hanyarsa.
وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ أَسَٰٓـُٔواْ بِمَا عَمِلُواْ وَيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ بِٱلۡحُسۡنَى
Open ayah 53:31Kuma abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa na Allah ne, don Ya saka wa waɗanda suka munana da irin abin da suka aikata, Ya kuma saka wa waɗanda suka kyautata da mafi kyan sakamako.
ٱلَّذِينَ يَجۡتَنِبُونَ كَبَٰٓئِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَۚ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلۡمَغۡفِرَةِۚ هُوَ أَعۡلَمُ بِكُمۡ إِذۡ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ وَإِذۡ أَنتُمۡ أَجِنَّةٞ فِي بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡۖ فَلَا تُزَكُّوٓاْ أَنفُسَكُمۡۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ
Open ayah 53:32(Su ne) waɗanda suke nisantar manya-manyan zunubai da munanan ayyukan saɓo, sai dai ‘yan ƙananan zunubai. Lalle Ubangijinka Mayalwacin gafara ne. Shi ne Ya fi sanin ku, tun sanda Ya halicce ku daga ƙasa, sai ga ku kun zama ‘yan tayi a cikin cikin iyayenku mata; to kada ku tsarkake kanku; Shi ne Ya fi sanin wanda ya fi taƙawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi kaɗai ne mamallakin duk abin da yake cikin sammai da ƙasa, domin dukkansu halittarsa ne kuma bayinsa ne, shi ne kuma mai gudanar da su yadda ya ga dama. Yana zartar musu da ƙaddararsa da hukuncinsa da shari’arsa, yana umartar su ya hana su, don ya saka wa waɗanda suka munana ayyukansu da irin abin da suka cancanta na azaba, ya kuma saka wa muminai waɗanda suka kyautata ayyukansu da mafi kyan sakamako, shi ne gidan Aljanna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta muminai masu kyawawan ayyuka da cewa su ne waɗanda suke nisantar manya-manyan zunubai da munanan ayyukan saɓo, sai ‘yan ƙananan zunubai waɗanda suke samun gafara a kansu, saboda sun kauce wa manyan laifuka sun kuma yawaita ayyukan ɗa’a; Allah yana yi musu gafarar ne saboda shi mai yalwar gafara ne, ba don haka ba da ya azabtar da mutane da yawa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ban ga wani abu mai kama da ‘lamamu’ ba kamar abin da Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah ya rubuta wa ɗan’adam rabonsa daga zina zai riske shi babu makawa; zinar ido shi ne kallo; zinar harshe kuma furuci; rai kuma sai ya yi buri ya yi sha’awa; farji kuma sai ya gaskata hakan ko ya ƙaryata shi.” [Bukhari #5243 da Muslim #2657]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa ‘yan’adam cewa, ya fi su sanin kawunansu da halayensu da abin da za su iya da wanda ba za su iya ba da ƙarfinsu da rauninsu, domin shi ne ya halicci babansu Annabi Adamu daga ƙasa, da kuma lokacin da suke ‘yan tayi a cikin cikkunan iyayensu mata, sannan aka riƙa halittar su mataki-mataki, babu abin da bai sani ba game da su a waɗannan lokuta, don haka bai dace da su ba su riƙa tsarkake kawunansu suna siffanta kansu da taƙawa da tsoron Allah, domin shi Allah shi ne ya fi sanin mai taƙawa a cikin bayinsa. An karɓo daga Zainab ‘yar Ummu Salama (Allah ya kara mata yarda) cewa, an sa mata suna Barra (watau mai biyayya) sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ku tsarkake kawunanku, Allah shi ne ya fi sanin masu biyayya daga cikinku.” [Muslim #2142]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Sunan Juwairiyya na farko Barra, sai Manzon Allah (ﷺ) ya canza mata shi zuwa Juwairiyya. Ba ya so ya ji ana cewa ya fito daga wajen Barra.” [Muslim #2140].
أَفَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي تَوَلَّىٰ
Open ayah 53:33Ka ba ni labarin wanda ya ba da baya.
وَأَعۡطَىٰ قَلِيلٗا وَأَكۡدَىٰٓ
Open ayah 53:34Ya kuma bayar da dukiya kaɗan kuma ya yi rowa.
أَعِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلۡغَيۡبِ فَهُوَ يَرَىٰٓ
Open ayah 53:35Shin yana da ilimin gaibu ne don haka yana ganin (komai)?
أَمۡ لَمۡ يُنَبَّأۡ بِمَا فِي صُحُفِ مُوسَىٰ
Open ayah 53:36Ko ba a ba shi labarin abin da yake cikin takardun Musa ba ne?
وَإِبۡرَٰهِيمَ ٱلَّذِي وَفَّىٰٓ
Open ayah 53:37Da kuma Ibrahimu wanda ya cika alƙawari?
أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰ
Open ayah 53:38Cewa: “Wani rai ba ya ɗaukar nauyin laifin wani.
وَأَن لَّيۡسَ لِلۡإِنسَٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ
Open ayah 53:39“Kuma mutum bai mallaki wani sakamako ba sai na abin da ya aikata.
وَأَنَّ سَعۡيَهُۥ سَوۡفَ يُرَىٰ
Open ayah 53:40“Kuma lalle aikin nasa ba da daɗewa ba za a gan shi.
ثُمَّ يُجۡزَىٰهُ ٱلۡجَزَآءَ ٱلۡأَوۡفَىٰ
Open ayah 53:41“Sannan a saka masa da cikakken sakamako.
وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلۡمُنتَهَىٰ
Open ayah 53:42“Lalle kuma zuwa ga Ubangijinka ne makoma.
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضۡحَكَ وَأَبۡكَىٰ
Open ayah 53:43“Kuma lalle Shi ne Ya sa a yi dariya, kuma Ya sa a yi kuka.
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحۡيَا
Open ayah 53:44“Kuma lalle Shi ne Ya kashe kuma Ya raya.
وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰ
Open ayah 53:45“Kuma lalle Shi ne Ya halicci dangi biyu namiji da mace.
مِن نُّطۡفَةٍ إِذَا تُمۡنَىٰ
Open ayah 53:46“Daga maniyyi yayin da ake zuba shi.
وَأَنَّ عَلَيۡهِ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰ
Open ayah 53:47“Kuma lalle Ya ɗora wa kansa sake tashin matattu.
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغۡنَىٰ وَأَقۡنَىٰ
Open ayah 53:48“Lalle kuma Shi ne Ya wadata, Ya kuma yalwata.
وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعۡرَىٰ
Open ayah 53:49“Kuma lalle Shi ne Ubangijin tauraron nan Shi’ira .
وَأَنَّهُۥٓ أَهۡلَكَ عَادًا ٱلۡأُولَىٰ
Open ayah 53:50“Lalle kuma Ya hallakar da Adawa na farko.
وَثَمُودَاْ فَمَآ أَبۡقَىٰ
Open ayah 53:51“Da kuma Samudawa, don haka bai bar saura ba.
وَقَوۡمَ نُوحٖ مِّن قَبۡلُۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ هُمۡ أَظۡلَمَ وَأَطۡغَىٰ
Open ayah 53:52“Da mutanen Nuhu tun kafin su; lalle su sun kasance su ne mafiya zalunci kuma mafiya ɗagawa.
وَٱلۡمُؤۡتَفِكَةَ أَهۡوَىٰ
Open ayah 53:53“Da waɗanda aka kife (mutanen Luɗu, Allah) ya ƙasƙanta su.
فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ
Open ayah 53:54“Sannan abin da ya lulluɓe su (na azaba) ya lulluɓe su.”
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ
Open ayah 53:55To (kai ɗan’adam) da waɗanne ni’imomin Ubangijinka kake jayayya? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan halin wanda ake umartar sa da kaɗaita Allah da bautar sa amma sai ya bijire bayan da ya nuna kusantar sa. Abdurrahman ɗan Zaid yana cewa: Wannan ayar ta sauka ne game da wani mutum da ya musulunta sai wani kafiri ya riƙa aibanta shi yana cewa, ya tabka abin kunya, domin ya yarda ya bar addininsa na iyaye da kakanni ya dawo yana sukan su, yana ganin su ‘yan wuta. Sai wannan mutum ya nuna wa wannan kafiri cewa shi fa yana jin tsoron azabar Allah. Sai kafirin ya ce: “Ka ba ni wasu maƙudan kuɗi ni kuma zan ɗauke maka duk wata azaba da za ta hau kanka.” Sai ya ba shi wani abu na dukiya, sai ya nemi ya ƙara masa, amma sai ya ji nauyin ya ƙara masa, sannan ya ɗan ƙara masa kaɗan. Sai kafirin ya rubuta game da shi ya kafa shaidu a kai. [Ibn Jariri, Tafsir Juzu’i na 22, shafi na 72]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyi yake faɗa wa Manzon Allah wannan mummunan hali da wannan mutum ya faɗa cikinsa wanda har ya kai shi ga ƙara bijire wa Musulunci bayan da farko ya ɗan kusance shi. Ya yi alƙawarin zai bayar da wani abu na dukiyarsa don wani ya ɗauke masa azabar Allah a ranar alƙiyama, sai daga baya kuma ya hana. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalanci wannan kafirin da cewa, ya san gaibu ne da har yake faɗar zai iya ɗauke wa wani azabar Allah? Ko kuma dai ƙarya ce kawai yake yi wa Allah? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalinsa da cewa, shin ba a sanar da shi dokar Allah da ya saukar a cikin littattafan farko ba? Dokar da ya saukar wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da wadda take cikin littattafan Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya cika duk wani umarni na Allah? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana waɗannan dokoki nasa da cewa: <b>Na farko </b>, wani rai ba ya ɗaukar laifin wani. Kowa za a hukunta shi da abin da ya aikata ba abin da wani ya aikata ba. An karɓo daga Abu Risma (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mun tafi tare da babana wurin Manzon Allah (ﷺ) sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce wa babana: “Wannan ɗanka ne?” Sai ya ce: “E, na rantse da Ubangijin Ka’aba.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ka tabbatar?” Sai ya ce: “Ka zama shaida a kan haka.” Ya ce: Sai Manzon Allah (ﷺ) ya yi murmushi saboda yadda nake da tsananin kama da mahaifina amma duk da haka yana rantsuwa a kan ni ɗansa ne. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “To ka sani lalle ba za a kama shi da laifinka ba, kai ma ba za a kama ka da laifinsa ba.” Sannan Manzon Allah (ﷺ) ya karanta faɗar Allah: “Wani rai ba zai ɗauki laifin wani ba.” [Dubi, Ahmad #7109 da Abu Dawud #4495]. <b>Na biyu </b>, mutum ba shi da wani sakamako sai na aikinsa da ya yi. Watau bai cancanci ya nemi a ba shi sakamako ba sai a kan aikinsa. Wannan ba ya hana ya amfana da addu’ar wani gare shi ko sadakar ‘ya’yansa da za su yi masa da sauran abubuwan da nassoshi suka zo da su. [Dubi, Al-Ƙinnauji, Fathul Bayan , Juzu’i na 13, shafi na 271-273]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan mutum ya mutu to aikinsa ya yanke sai na abubuwa uku, sadaka mai gudana, ko ilimin da ake amfana da shi, ko wani yaro nagari da zai riƙa yi masa addu’a.” [Muslim #1631]. <b>Na uku </b>, lalle za a nuna wa mutum aikinsa a ranar alƙiyama, ya gan shi a rubuce a cikin takardun ayyukansa. <b>Na huɗu </b>, lalle za a yi masa cikakken sakamako a kan dukkan ayyukansa ba tare da an tauye masa komai ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa makomar bayinsa duka bayan mutuwarsu zuwa gare shi ne, don haka duk tafiyar kowa da komai zuwa wurinsa za ta tuƙe ta ƙare. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake jan hankalin ɗan’adam a kan ya lura da wasu al’amura da suke wakana a rayuwarsa waɗanda dukkansu aikin Allah ne shi kaɗai: <b>Na farko </b>, shi ne wanda ya sa a yi dariya ya kuma sa a yi kuka, watau shi ne yake kimsa farin ciki ga wanda ya ga dama har ya sa shi darawa saboda murna; shi kuma ne yake jefa baƙin ciki ga wanda ya ga dama har ya sa shi kuka. <b>Na biyu </b>, shi ne mai kashe masu rai a nan duniya, ya kuma tashe su a lahira domin yi musu hisabi, kamar yadda shi ne ya samar da duk wani mai rai daga babu ya busa masa rai, sannan yake karɓar ransa bayan ajalinsa ya zo. <b>Na uku </b>, shi ne ya halicci mutum nau’i biyu, namiji da mace daga maniyyi da ake zuba shi a mahaifa. Wannan duka yana nuna cikar Ƙudurarsa da Kaɗaitakarsa, don haka babu abin da yake gagararsa, saboda haka ya tabbatar da cewa, shi ne mai ikon sake dawo da halittu bayan mutuwa domin yi musu hisabi da sakamako. <b>Na huɗu </b>, shi ne ya ba wa wanda ya ga dama wadata, ya mallaka masa dukiya irin wadda ya ga dama, ya kuma yalwata wa bayinsa dukiyoyi iri-iri waɗanda suke mallaka domin amfaninsu na yau da kullum. <b>Na biyar </b>, shi ne Ubangijin tauraron Shi’ira . Wannan wani tauraro ne mai tsananin haske da ke cikin taurarin burujin Jauza’u . Wasu ƙabilu na Larabawa a jahiliyya, kamar ƙabilar Khuza’atu sun riƙa bauta masa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, taurari ba su da wani tasiri, su ma bayin Allah ne, Mahaliccinsu shi ne Allah, shi kaɗai ya cancanta a bauta masa. <b>Na shida </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, shi ne ya hallaka Adawa na farko, watau mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yayin da suka dage a kan kafircinsu, suka ƙaryata Manzonsu Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu da iska mai tsananin ƙarfi ta hallaka su baki ɗaya. Hakanan shi ne ya hallaka Samudawa mutanen Annabi Salihu, yayin da suka ƙaryata Manzonsu Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka soke taguwarsa, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su gaba ɗayansu bai bar ko mutum ɗaya ba. Hakanan shi ne ya hallaka mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) tun kafin zuwan Adawa da Samudawa. Mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuwa sun fi tsananin kafirci da ɗagawa a bayan ƙasa fiye da Adawa da Samudawa, domin sai da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zauna a cikinsu tsawon shekara dubu ba hamsin yana musu wa’azi amma sai ‘yan tsiraru ne suka yi imani da shi. Hakanan Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne wanda ya yi ƙoli-ƙoli da garuruwan mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sannan ya jefo su ƙasa ya kifar da su, ya bi su da ruwan duwatsu har azaba mai girma ta lulluɓe su ta ko’ina, suka hallaka baki ɗaya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana butulcin ɗan’adam kafiri mai jayayya da Ƙudurar Allah da Kaɗaitakarsa bayan ɗimbin ni’imomi da ya yi masa, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye shi da waɗanne ni’imomin ne na Ubangijinsa yake jayayya, ya ƙi ɗaukar izina da wa’azi?
هَٰذَا نَذِيرٞ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلۡأُولَىٰٓ
Open ayah 53:56Wannan mai gargaɗi ne daga irin masu gargaɗin farko.
أَزِفَتِ ٱلۡأٓزِفَةُ
Open ayah 53:57Mai kusantowa ta kusanto (watau alƙiyama).
لَيۡسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ
Open ayah 53:58Ba wani mai bayyana lokacinta in ban da Allah.
أَفَمِنۡ هَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ تَعۡجَبُونَ
Open ayah 53:59Yanzu game da wannan zancen ne kuke mamaki?
وَتَضۡحَكُونَ وَلَا تَبۡكُونَ
Open ayah 53:60Kuke kuma dariya ba kwa yin kuka?
وَأَنتُمۡ سَٰمِدُونَ
Open ayah 53:61Alhali kuna cikin gafala?
فَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ وَٱعۡبُدُواْ۩
Open ayah 53:62To ku yi sujjada ga Allah ku kuma bauta (masa). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mushirikai cewa Manzon Allah Muhammadu ɗan Abdullahi wanda ya aiko musu ɗaya ne daga cikin tarin manzanni na farko da ya aika zuwa ga mutanensu, don haka ba shi ne farau ba, abin da kuma ya zo da shi na gaskiya shi ne dai abin da sauran manzannin Allah suka zo wa mutanensu da shi, to don mene ne suke jayayya da shi a kan haka? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, alƙiyama ta kusanto, babu kuma mai iya bayanin lokacin zuwanta, ko mai iya kawar da abin da za ta zo da shi na narko ga kafirai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna kakabin irin yadda kafirai suke mamakin cewa Alƙur’ani daga Allah yake. Maimakon su yi imani da shi su wa’azantu lokacin da ake karanta musu ayoyinsa sai su riƙa dariya suna izgili da shi, ba sa kuka yayin jin wa’azuzzukansa, sukan ma shagalta ne su yi watsi da shi. Sai a ƙarshen wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su yi sujjada ga Allah shi kaɗai su bauta masa tare da tsarkake shi wajen bauta. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Annabi (ﷺ) ya karanta ‘Suratun Najmi’ ya yi sujjada, sai Musulmi da mushirikai da aljannu da sauran mutane duk suka yi sujjada tare da shi.” [Bukhari #6482 da Muslim #2283].