القمر
Al-Qamar
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱقۡتَرَبَتِ ٱلسَّاعَةُ وَٱنشَقَّ ٱلۡقَمَرُ
Open ayah 54:1Alƙiyama ta kusanto, wata kuma ya tsage.
وَإِن يَرَوۡاْ ءَايَةٗ يُعۡرِضُواْ وَيَقُولُواْ سِحۡرٞ مُّسۡتَمِرّٞ
Open ayah 54:2Idan kuma suka ga wata aya sai su kau da kai kuma su ce: “Wannan sihiri ne ƙaƙƙarfa.”
وَكَذَّبُواْ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَكُلُّ أَمۡرٖ مُّسۡتَقِرّٞ
Open ayah 54:3Suka kuma ƙaryata, suka bi soye-soyen zukatansu. Kowane al’amari kuwa (na alheri ko na sharri) mai tabbata ne.
وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّنَ ٱلۡأَنۢبَآءِ مَا فِيهِ مُزۡدَجَرٌ
Open ayah 54:4Haƙiƙa kuma wasu labarai waɗanda tsawatarwa take cikinsu sun zo musu.
حِكۡمَةُۢ بَٰلِغَةٞۖ فَمَا تُغۡنِ ٱلنُّذُرُ
Open ayah 54:5Hikima ce mai kaiwa matuƙa, sai dai kuma gargaɗin ba ya amfanarwa.
فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡۘ يَوۡمَ يَدۡعُ ٱلدَّاعِ إِلَىٰ شَيۡءٖ نُّكُرٍ
Open ayah 54:6Saboda haka ka rabu da su. A ranar da mai kira zai yi kira zuwa ga wani abu na ƙi a rai.
خُشَّعًا أَبۡصَٰرُهُمۡ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ كَأَنَّهُمۡ جَرَادٞ مُّنتَشِرٞ
Open ayah 54:7Idanuwansu suna a ƙasƙance suna fitowa daga ƙaburbura, kai ka ce su farin ɗango ne masu bazuwa.
مُّهۡطِعِينَ إِلَى ٱلدَّاعِۖ يَقُولُ ٱلۡكَٰفِرُونَ هَٰذَا يَوۡمٌ عَسِرٞ
Open ayah 54:8Suna gaggawa zuwa ga mai kiran; kafirai za su riƙa cewa: “Wannan rana ce mai tsanani.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tsoratarwa cewa alƙiyama ta kusanto, wata kuma ya tsage, watau a zamanin Manzon Allah (ﷺ) wanda mushirikai suka gane wa idanunsu, amma sai suka yi ƙememe suka ƙi yarda da gaskiyar Annabi (ﷺ), suka ma tuhume shi da cewa, sihiri ne ya yi musu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, su waɗannan mushirikai ba gaskiya suke nema ba, jayayya kawai suke so, domin kuwa da a ce za su ga kowace aya da dalili mai ƙarfi a kan gaskiyar Manzon Allah (ﷺ), to da sun bijire sun ƙi yarda da shi har ma su ce, ai abin da suka gani wani ƙaƙƙarfan sihiri ne kuma zai gushe ba da jimawa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan mushirikan manufarsu ba ita ce ganin gaskiya su bi ta ba, a’a, buƙatarsu kawai ita ce su ƙaryata duk abin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo musu da shi na gaskiya, su bi son zuciyarsu, domin da gaskiya suke so da sun yi imani bayan sun ga ƙarfafan dalilai da idanuwansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da su cewa kowane al’amari na alheri ko na sharri mai tabbata ne a ranar alƙiyama inda kowa zai ga abin da ya kasance a kansa na gaskiya ko na ƙarya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, waɗannan mutane ba neman gaskiya suke yi ba, domin kuwa labaran al’ummun da suka gabata waɗanda Allah ya hallaka su saboda kafircinsu da zaluncinsu ya zo musu, to da gaskiya ce a gabansu da wannan ya ishe su wa’azi da tsoratarwa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, abin da ya zo musu cikakkiyar hikima ce don kafa musu hujja da janyo hankulansu, to amma gargaɗi ba ya amfanar da mutanen da ba su yi imani da Allah da ranar lahira ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa da cewa idan waɗannan mutane sun ƙi su shiriya, to ya yi watsi da su ya jira zuwan ranar da mala’ika mai busa a ƙaho zai yi kira zuwa ga wani mummunan al’amari wanda halittu ba su taɓa ganin irinsa ba, watau lokacin da matattu za su fito daga ƙaburburansu, idanunsu a ƙasƙance, su nufi wurin tsayuwa da gaggawa a kuma warwatsu kamar farin ɗango saboda yawansu. Za su yi ta gaggawa zuwa ga mai kiran don amsa kiransa, a nan ne kafirai za su ga gaskiyar abin da ake tsoratar da su shi, za su tabbatar da cewa, wannan rana ce mai tsanani da wahala a gare su, saboda sun san abin da suka shuka ba mai kyau ba ne.
۞كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ فَكَذَّبُواْ عَبۡدَنَا وَقَالُواْ مَجۡنُونٞ وَٱزۡدُجِرَ
Open ayah 54:9Mutanen Nuhu sun ƙaryata kafin su (Ƙuraishawa), sai suka ƙaryata Bawanmu suka kuma ce, mahaukaci ne, aka kuma kyare (shi).
فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَغۡلُوبٞ فَٱنتَصِرۡ
Open ayah 54:10Sai ya roƙi Ubangijinsa (cewa): “Lalle an fi ƙarfina, sai Ka taimaka.”
فَفَتَحۡنَآ أَبۡوَٰبَ ٱلسَّمَآءِ بِمَآءٖ مُّنۡهَمِرٖ
Open ayah 54:11Sai Muka buɗe ƙofofin sama da ruwa mai kwararowa.
وَفَجَّرۡنَا ٱلۡأَرۡضَ عُيُونٗا فَٱلۡتَقَى ٱلۡمَآءُ عَلَىٰٓ أَمۡرٖ قَدۡ قُدِرَ
Open ayah 54:12Muka kuma ɓuɓɓugar da idanuwan ruwa daga ƙasa, sai ruwayen suka haɗu a bisa al’amarin da aka riga aka ƙaddara.
وَحَمَلۡنَٰهُ عَلَىٰ ذَاتِ أَلۡوَٰحٖ وَدُسُرٖ
Open ayah 54:13Muka kuma ɗauke shi a kan (jirgin ruwa) mai alluna da ƙusoshi.
تَجۡرِي بِأَعۡيُنِنَا جَزَآءٗ لِّمَن كَانَ كُفِرَ
Open ayah 54:14Yana gudu a kan idonmu, don ya zama sakayya ga wanda aka kafirce wa (watau Nuhu).
وَلَقَد تَّرَكۡنَٰهَآ ءَايَةٗ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Open ayah 54:15Haƙiƙa kuma Mun bar (abin da ya faru) ya zama aya, to ko akwai mai wa’azantuwa?
فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
Open ayah 54:16To ƙaƙa azabata da gargaɗina suka kasance?
وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Open ayah 54:17Haƙiƙa kuma Mun sauƙaƙe Alƙur’ani don tunasarwa da hadda, to ko akwai mai wa’azantuwa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) ne game da ƙaryata shi da mutanensa suke yi, da cewa al’ummun da suka gabace su ma sun ƙaryata manzanninsu kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fara lissafa manzannin da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yayin da mutanensa suka ƙaryata shi, lokacin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aike shi gare su, har ma suka kira shi da mahaukaci, suka riƙa yi masa tsawa da cin zarafi iri-iri, har ta kai su ga yi masa barazanar kisa idan bai bar da’awarsa ba. Daga nan ne shi kuma ya roƙi Ubangijinsa cewa ya kawo masa ɗauki, domin mutanensa sun fi ƙarfinsa, sun ƙi yin imani da shi bayan ya shafe shekara dubu ba hamsin a cikinsu yana yi musu wa’azi. Ya roƙi Allah ya saukar musu da azabarsa wadda za ta hallaka su ba za ta bar ko mutum guda daga cikinsu ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa ya karɓi addu’arsa, don haka ya buɗe ƙofofin sama ruwa ya yi ta kwararowa babu ƙaƙƙautawa, Ya kuma ɓuɓɓugo da idanuwan ruwa ta ƙasa ta ko’ina, sai ruwan sama da na ƙasa suka haɗe suka gama duniya bisa umarnin Allah da ya riga ya ƙaddara shi tun fil azal. Allah ya hallakar da mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ruwan Ɗufana gaba ɗayansu tare da dabbobinsu da dukiyoyinsu sai fa wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tserar. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya ɗauki Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwa wanda aka ƙera da alluna da ƙusoshi, yana gudu a kan ruwa tare da kulawar Allah da lurarsa, domin wannan ya zamanto sakayya ga Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda mutanensa suka ƙaryata shi, suka kuma kafirce wa abin da ya zo musu da shi daga Allah. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan azaba da ya yi wa mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bar ta don ta zama aya da izina ga duk wani mai wa’azantuwa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin mushirikai a kan su lura su ga yadda azabarsa da gargaɗinsa ga mutanen Annabi Nuhu suka kasance. Sai kuma Allah ya tabbatar da cewa, ya sauƙaƙe Alƙur’ani don a karanta shi a haddace shi a fahimce shi, domin ya zama wa’azi da tunatarwa, to shin ko akwai mai wa’azantuwa?
كَذَّبَتۡ عَادٞ فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
Open ayah 54:18Adawa sun ƙaryata (Annabinsu), to ƙaƙa azabata da gargaɗina suka kasance?
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا صَرۡصَرٗا فِي يَوۡمِ نَحۡسٖ مُّسۡتَمِرّٖ
Open ayah 54:19Lalle Mu Mun aiko musu da iska mai ƙarfi a ranar shu’umci mai zarcewa.
تَنزِعُ ٱلنَّاسَ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٖ مُّنقَعِرٖ
Open ayah 54:20Tana tumɓuko mutane ta kayar su, kai ka ce su kututturan dabinai ne da aka tuttunɓuke.
فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
Open ayah 54:21To ƙaƙa azabata da gargaɗina suka kasance?
وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Open ayah 54:22Kuma haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur’ani don tunatarwa, to ko akwai mai wa’azantuwa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake jan hankalin Larabawa mushirikai a kan su yi la’akari da azabarsa da gargaɗinsa ga Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da suka ƙaryata shi suka doge a kan kafircinsu, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu wata iska mai tsananin sanyi a wani yini mai shu’umancin gaske wanda shu\'umcinsa ba iya nan duniya ya tsaya ba; zai zarce ne yana bin su har zuwa lokacin shigarsu wutar Jahannama a ranar alƙiyama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan iskar da ya aika wa Adawa ta riƙa tumɓuke mutane daga doron ƙasa ta yi sama da su sannan ta kifo da su ta kawunansu su faɗo ƙasa a mace, idan mutum ya gan su kwankwance a ƙasa sai ya ga kamar kututturan dabino ne da aka daddatse su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartar mushirikai da su yi la’akari da tunani game da azabarsa da ya saukar wa Adawa da kuma gargaɗinsa da yake yi wa wasunsu na su ɗauki izina daga waɗancan mutane. Sai kuma ya tabbatar da cewa, ya sauƙaƙe Alƙur’ani wajen karatunsa da haddarsa da fahimtarsa don wa’azantuwa, to shin ko akwai mai wa’azantuwa?
كَذَّبَتۡ ثَمُودُ بِٱلنُّذُرِ
Open ayah 54:23Samudawa sun ƙaryata gargaɗi.
فَقَالُوٓاْ أَبَشَرٗا مِّنَّا وَٰحِدٗا نَّتَّبِعُهُۥٓ إِنَّآ إِذٗا لَّفِي ضَلَٰلٖ وَسُعُرٍ
Open ayah 54:24Sannan suka ce: “Yanzu mutum ɗaya daga cikinmu ne za mu bi? To lalle idan mun yi haka, mun tabbata cikin ɓata da hauka.
أَءُلۡقِيَ ٱلذِّكۡرُ عَلَيۡهِ مِنۢ بَيۡنِنَا بَلۡ هُوَ كَذَّابٌ أَشِرٞ
Open ayah 54:25“Yanzu (zai yiwu) a saukar masa da wahayi a tsakaninmu? A’a, shi dai maƙaryaci ne mai tsananin girman kai.”
سَيَعۡلَمُونَ غَدٗا مَّنِ ٱلۡكَذَّابُ ٱلۡأَشِرُ
Open ayah 54:26A gobe lalle za su san wane ne maƙaryacin mai girman kai.
إِنَّا مُرۡسِلُواْ ٱلنَّاقَةِ فِتۡنَةٗ لَّهُمۡ فَٱرۡتَقِبۡهُمۡ وَٱصۡطَبِرۡ
Open ayah 54:27Lalle Mu Masu aiko taguwa ne don ta zama fitina a gare su, saboda haka ka saurara musu, kuma ka jure.
وَنَبِّئۡهُمۡ أَنَّ ٱلۡمَآءَ قِسۡمَةُۢ بَيۡنَهُمۡۖ كُلُّ شِرۡبٖ مُّحۡتَضَرٞ
Open ayah 54:28Kuma ka ba su labarin cewa ruwan sha an raba ne tsakaninsu (da ita taguwar); kowane akwai ranar shansa.
فَنَادَوۡاْ صَاحِبَهُمۡ فَتَعَاطَىٰ فَعَقَرَ
Open ayah 54:29Sai suka kirawo (shaƙiyin) abokin nasu sai ya ɗauki (abin sara) sai ya sare ta.
فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
Open ayah 54:30To ƙaƙa azabata da gargaɗina suka kasance?
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَكَانُواْ كَهَشِيمِ ٱلۡمُحۡتَظِرِ
Open ayah 54:31Lalle Mun aika musu da tsawa guda ɗaya, sai suka zamo kamar duddugar ciyawa a garken makiyayi.
وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Open ayah 54:32Haƙiƙa kuma Mun sauƙaƙe Alƙur’ani don tunatarwa, to ko akwai mai wa’azantuwa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Ƙuraishawa cewa, Samudawa mutanen Annabi Salihu sun ƙaryata gargaɗin da Annabinsu ya yi musu, domin wai suna ganin cewa ta ƙaƙa za su bi wani mutum guda ɗaya irinsu wanda bai fi su da komai ba, suka tabbatar masa da cewa, lalle su har in sun yarda sun bi shi a haka, to tabbas sun tabka babban kuskure a rayuwarsu, sun kuma jefa kansu cikin hauka. Sannan suna mamakin cewa, ta yaya za a ware shi shi kaɗai a yi masa wahayi, su kuma ba a yi musu ba? Don haka suka yanke hukuncin cewa Annabi Salihu babban maƙaryaci ne mai girman kai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa, ba da jimawa ba gobe za su san wane ne babban maƙaryaci mai girman kai tsakanin shi da su? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya fito wa da Samudawa taguwa daga wani falalen dutse kamar yadda suka nema, don ta zama jarraba a gare su, ya kuma umarci Annabinsa Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya saurara ya ga yadda za su yi wa wannan taguwa, su kuma ya ga yadda Allah zai yi da su, shi kuma ya ci gaba da haƙuri a kan cutarwarsu gare shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya faɗa wa mutanensa cewa ruwan rijiyarsu na sha an raba musu shi ne tsakaninsu da wannan taguwar, kowannensu akwai ranarsa da zai sha ruwanta, watau yau gare su gobe ga taguwar, ba wanda zai halarci ranar wani tsakaninsu da ita. To amma sai Samudawa suka kasa kiyaye wannan doka, har ma wasu daga cikinsu suka gana da junansu suka yanke shawarar su kashe taguwar Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kowa ya huta, don haka sai suka kirawo shaƙiyyunsu suka umarce shi da wannan mugun aiki, shi kuma ya ɗauki takobinsa ya sare wannan taguwa, ya cika umarnin shugabanninsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mutanen Makka da su lura da yadda azabar Allah ta kasance ga mutanen Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da gargaɗinsa ga na bayansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ya aika musu wata tsawa guda ɗaya wadda ta hallaka su gaba ɗayansu, suka wayi gari kamar duddugar ciyawa busassa a garken dabbobi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya sauƙaƙe Alƙur’ani wajen karatunsa da haddarsa da fahimtarsa don tunatarwa da wa’azi, to ko akwai mai wa’azantuwa?
كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطِۭ بِٱلنُّذُرِ
Open ayah 54:33Mutanen Luɗu sun ƙaryata gargaɗi.
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ حَاصِبًا إِلَّآ ءَالَ لُوطٖۖ نَّجَّيۡنَٰهُم بِسَحَرٖ
Open ayah 54:34Lalle Mun aika musu da iska cike da duwatsu (ta hallaka su), sai dai iyalin Luɗu kaɗai Muka tserar da su a lokacin asuba.
نِّعۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَاۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي مَن شَكَرَ
Open ayah 54:35(Wannan) ni’ima ce daga wurinmu. Kamar haka Muke saka wa wanda ya yi godiya.
وَلَقَدۡ أَنذَرَهُم بَطۡشَتَنَا فَتَمَارَوۡاْ بِٱلنُّذُرِ
Open ayah 54:36Kuma haƙiƙa ya tsoratar da su irin damƙarmu, sai suka yi jayayya da gargaɗin (da ya yi musu).
وَلَقَدۡ رَٰوَدُوهُ عَن ضَيۡفِهِۦ فَطَمَسۡنَآ أَعۡيُنَهُمۡ فَذُوقُواْ عَذَابِي وَنُذُرِ
Open ayah 54:37Haƙiƙa kuma sun nemi baƙinsa da lalata, sai Muka shafe idanuwansu, (Muka ce da su): “Sai ku ɗanɗani azabata da gargaɗina.”
وَلَقَدۡ صَبَّحَهُم بُكۡرَةً عَذَابٞ مُّسۡتَقِرّٞ
Open ayah 54:38Haƙiƙa kuma azaba matabbaciya ta yi musu sammako da asuba.
فَذُوقُواْ عَذَابِي وَنُذُرِ
Open ayah 54:39Saboda haka ku ɗanɗani azabata da gargaɗina.”
وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Open ayah 54:40Haƙiƙa kuma Mun sauƙaƙe Alƙur’ani don tunatarwa, to ko akwai mai wa’azantuwa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya labarta wa mushirikai cewa mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ƙaryata abin da Manzonsu Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi musu gargaɗi da shi, yayin da ya kira su zuwa ga bautar Allah shi kaɗai, ya yi musu kashedi da aikata shirka da mummunar alfasha ta neman maza, to amma sai suka ƙaryata shi, suka ci gaba da laifukan da suke yi, har zuwa lokacin da mala’iku suka baƙunci Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a gidansa a cikin kamannin mazaje. Mutanen Annabi Luɗu kuwa suka yunƙuro da nufin aikata alfasha da su. A nan ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci waɗannan mala’iku da su hallaka su gaba ɗayansu in ban da Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da waɗanda suka yi imani da shi daga cikin ahlinsa, amma ban da matarsa wadda ita kam tana cikin kafirai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya aiko musu da iska mai cike da duwatsu waɗanda suka yi ta sauka a kansu bayan an kifar da garuruwansu, inda ilahirinsu suka hallaka sai dai iyalan Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kaɗai, su ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tserar da su lokacin da ya umarce shi da ya fita da su tun kafin saukar wannan azabar a ƙarshen dare. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya kuɓutar da Annabi Luɗu da iyalansa daga azaba ne don yin ni’ima a gare su, kuma kamar haka ne yake sakayya ga duk wanda ya gode wa ni’imarsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi ta gargaɗin mutanensa game da wannan azabar ta Ubangiji, to amma sai suka ƙi ji, suka yi ta jayayya game da gargaɗin da yake yi musu suka ƙaryata shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin yadda rashin kunyar mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ta yi tsamari har sai da suka kai ga neman sa da ya ƙyale su su yi lalata da baƙinsa, watau mala’ikun da Allah ya aiko masa, suka yunƙuro da ƙarfinsu suna so su cim ma biyan buƙatarsu, sai Allah ya shafe idanuwansu suka makance, don haka suka kasa shiga wurinsu, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce musu, su ɗanɗani azabarsa da sakamakon bijire wa gargaɗinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ya hallaka su lokacin da tabbatacciyar azabarsa ta yi musu sammako daidai lokacin asuba, saboda haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce musu su ɗanɗani azabarsa sakamakon gargaɗinsa da suka bijire wa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa, ya sauƙaƙe Alƙur’ani wajen karatunsa da haddarsa da fahimtarsa don tunatarwa, to shin ko akwai mai wa’azantuwa?
وَلَقَدۡ جَآءَ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ ٱلنُّذُرُ
Open ayah 54:41Kuma haƙiƙa gargaɗi ya zo wa mutanen Fir’auna.
كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذۡنَٰهُمۡ أَخۡذَ عَزِيزٖ مُّقۡتَدِرٍ
Open ayah 54:42Suka ƙaryata ayoyinmu dukkaninsu, sai Muka kama su irin kamu na Mabuwayi, Mai iko. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, gargaɗi iri-iri ya zo wa Fir’auna da mutanensa lokacin da ya aika musu Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Haruna (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ba su ayoyi bayyanannu da ƙarfafan dalilai waɗanda suka nuna wa Fir’auna da jama’arsa, amma sai suka ƙaryata su baki ɗaya, suka sa ƙafa suka shure su, sai Allah ya kama su da azabarsa, irin kamu na mabuwayi wanda ya fi ƙarfin komai, mai iko a kan komai, babu abin da yake gagarar sa, watau ya nutsar da Fir’auna da rundunarsa a cikin ruwa suka hallaka gaba ɗayansu.
أَكُفَّارُكُمۡ خَيۡرٞ مِّنۡ أُوْلَٰٓئِكُمۡ أَمۡ لَكُم بَرَآءَةٞ فِي ٱلزُّبُرِ
Open ayah 54:43Yanzu kafiranku (ku mutanen Makka) su ne suka fi waɗancan alheri, ko kuwa kuna da wata hanya ta kuɓuta ne a cikin littattafan da aka saukar?
أَمۡ يَقُولُونَ نَحۡنُ جَمِيعٞ مُّنتَصِرٞ
Open ayah 54:44A’a, suna dai cewa ne: “Mu jama’a ce wadda za ta ci nasara.”
سَيُهۡزَمُ ٱلۡجَمۡعُ وَيُوَلُّونَ ٱلدُّبُرَ
Open ayah 54:45To ba da daɗewa ba za a karya jama’ar tasu, su kuma su ba da baya.
بَلِ ٱلسَّاعَةُ مَوۡعِدُهُمۡ وَٱلسَّاعَةُ أَدۡهَىٰ وَأَمَرُّ
Open ayah 54:46A’a, alƙiyama ita ce lokacin yi musu azaba, alƙiyama kuwa ita ta fi bala’i, ta kuma fi ɗaci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin kafirai masu ƙaryata Manzonsa (ﷺ) game da azabarsa da za ta iya sauka a kansu idan ba su yi imani ba, kamar yadda ta sauka a kan waɗancan al’ummu da ya ba su labarinsu. Domin bai kamata a ce suna zaton su sun fi ƙarfin azabar Allah ba, sai don in suna zaton ɗaya daga cikin abubuwa uku: <b>Na ɗaya </b>, ko dai suna ganin su sun fi waɗancan kafiran na farko, tare da cewa ga su sun ƙaryata mafi darajar manzannin Allah kuma shugabansu Annabi Muhammadu (ﷺ). To idan suna ganin sun fi su matsayi ne a wurin Allah, to tana iya yiwuwa su tsira. To amma su ma sun san abin ba haka yake ba, in dai ba su zama mafi sharrinsu ba, to ba za su kasa zama daidai da su ba. <b>Na biyu </b>, ko kuma ya zamanto Allah ya yi musu wani alƙawari ne a cikin littattafan da ya saukar wa annabawansa da cewa, su za su tsira daga azabarsa ko da kuwa sun ƙaryata Manzonsa. To su ma sun tabbatar da cewa, wannan bai faru ba. <b>Na uku </b>, ko kuma suna ganin cewa suna da wani ƙarfi ne wanda za su yi nasara a kan duk wata azaba da za ta doso su. Tabbas ba su da ƙarfin da za su kare kansu daga azabar Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba da jimawa ba zai tarwatsa taronsu ya karya lagon jama’arsu su juya a guje. Haka kuwa ya faru a yaƙin Badar inda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karya lagon kafiran Makka aka kashe manyansu da dama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, suna da wani lokaci da ya yi alƙawarin tattara su baki ɗaya don yi musu azaba, ita ce ranar alƙiyama, wadda rana ce mafi girman bala’i gare su kuma mafi tsanani, inda za su gamu da azabar da ta fi wadda suka gamu da ita a ranar Badar nesa ba kusa ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: A yaƙin Badar Manzon Allah (ﷺ) yana zaune a cikin wani ƙaramin tanti sai yake addu’a yana cewa: “Ya Allah, ina roƙon ka alƙawarin da ka yi min na cin nasara, ya Allah, in ka ga damar hallaka waɗannan muminan to ba za a sake bautar ka ba daga yau.” Sai Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya kama hannunsa yana ce masa: “Addu’ar ta isa hakanan ya Manzon Allah, ka nuna nacinka ga Ubangijinka.” Sai ya taso yana sanye da silkensa yana karanta faɗar Allah: “To ba da daɗewa ba za a karya jama’ar tasu, su kuma ba da baya. A’a, alƙiyama ita ce wa’adinsu, alƙiyama kuma ta fi bala’i kuma ta fi tsanani.” [Bukhari #2915].
إِنَّ ٱلۡمُجۡرِمِينَ فِي ضَلَٰلٖ وَسُعُرٖ
Open ayah 54:47Lalle masu manyan laifuka suna cikin ɓata da azabar wuta.
يَوۡمَ يُسۡحَبُونَ فِي ٱلنَّارِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ ذُوقُواْ مَسَّ سَقَرَ
Open ayah 54:48Ranar da za a ja su cikin wuta a kan fuskokinsu (a ce da su): “Ku ɗanɗani azabar wutar Saƙara.”
إِنَّا كُلَّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَٰهُ بِقَدَرٖ
Open ayah 54:49Lalle Mu, kowane abu Mun halitta shi da ƙaddara.
وَمَآ أَمۡرُنَآ إِلَّا وَٰحِدَةٞ كَلَمۡحِۭ بِٱلۡبَصَرِ
Open ayah 54:50Kuma al’amarinmu bai zamanto ba face kalma ɗaya kamar ƙiftawar ido.
وَلَقَدۡ أَهۡلَكۡنَآ أَشۡيَاعَكُمۡ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Open ayah 54:51Haƙiƙa kuma Mun hallakar da ire-irenku, to ko akwai mai wa’azantuwa?
وَكُلُّ شَيۡءٖ فَعَلُوهُ فِي ٱلزُّبُرِ
Open ayah 54:52Kuma kowane abu da suka aikata yana cikin littattafai.
وَكُلُّ صَغِيرٖ وَكَبِيرٖ مُّسۡتَطَرٌ
Open ayah 54:53Kowane ƙaramin abu da babba kuma suna nan a rubuce.
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّٰتٖ وَنَهَرٖ
Open ayah 54:54Lalle masu taƙawa suna cikin gidajen Aljanna da ƙoramu.
فِي مَقۡعَدِ صِدۡقٍ عِندَ مَلِيكٖ مُّقۡتَدِرِۭ
Open ayah 54:55A mazauni na gaskiya a wurin Mai mulki, Mai iko. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, masu aikata manyan laifuka kamar shirka da sauran ayyukan saɓon Allah, suna cikin ɓata da barin gaskiya a nan duniya, suna kuma cikin azaba da wahala a ranar lahira. Ranar da mala’iku za su yi ta jan su a kan fuskokinsu a cikin wuta, a nuna musu matuƙar wulaƙanci da ƙasƙanci ana kuma faɗa musu cewa su ɗanɗani azabar wutar Saƙara. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lalle komai a duniya ya halicce shi ne da ƙaddararsa wadda ta riga ta gabata, don ya san komai da komai, ya kuma rubuta shi a littafin Lauhul Mahfuzu, yana kuma faruwa ne da ganin damarsa da izininsa. Wannan kuwa aiki ne mai matuƙar sauƙi a wurinsa, don haka ya tabbatar da cewa, idan ya nufi faruwar wani abu to umarninsa kalma ɗaya ce kawai, watau ya ce wa abin nan ‘kasance’, kafin ƙiftawar ido kuwa ya kasance. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mushirikan Ƙuraishawa sun zo suna jayayya da Manzon Allah (ﷺ) game da ƙaddara, sai faɗar Allah (Mai tsarki da daukaka) ta sauka inda yake cewa: “Ranar da za a ja su cikin wuta a kan fuskokinsu (a ce da su) ku ɗanɗani azabar wutar Saƙara. Lalle mu kowane abu mun halicce shi da ƙaddara.” [Muslim #2656 da Tirmizi #3290 da Ahmad #9736]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake jan hankalin kafirai a kan su guji fushinsa (Mai tsarki da daukaka), da cewa ya hallaka wasu kafirai irinsu masu taurin kai, to shin wannan bai ishe su wa’azi ba, su ma su ji tsoron kada irin haka ya faru da su? Sannan ya kuma tabbatar da cewa, duk fa wani abu da bayinsa suke aikatawa yana nan a rubuce a cikin littattafan mala’iku masu tsaron su, babu abin da yake kuɓuce musu. Kuma duk wani aikinsu ko maganarsu ƙaramin abu da babba yana nan a rubuce a littattafansu na ayyuka da kuma Lauhul Mahfuzu, zai yi musu sakayya a kansu. Sai kuma a ƙarshen Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon masu taƙawa da kiyaye dokokinsa da cewa suna cikin gidajen Aljanna na jin daɗi da ƙoramu masu gudana, a wani majalisi na gaskiya wanda babu maganar banza ko laifi a cikinsa a wurin Sarki mamallakin komai mai cikakken iko da babu abin da yake gagarar sa, zai kuma yi musu goma ta arziki da babu mai iya bayyana girmanta da daɗinta sai dai wanda ya gani.