الرحمن
Ar-Rahmaan
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلرَّحۡمَٰنُ
Open ayah 55:1(Allah) Mai rahama.
عَلَّمَ ٱلۡقُرۡءَانَ
Open ayah 55:2Shi Ya koyar da Alƙur’ani.
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ
Open ayah 55:3Ya halicci mutum.
عَلَّمَهُ ٱلۡبَيَانَ
Open ayah 55:4Ya koyar da shi bayani.
ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ بِحُسۡبَانٖ
Open ayah 55:5Rana da wata (suna tafiya) a tsare.
وَٱلنَّجۡمُ وَٱلشَّجَرُ يَسۡجُدَانِ
Open ayah 55:6Tsirrai da bishiyoyi suna yin sujjada.
وَٱلسَّمَآءَ رَفَعَهَا وَوَضَعَ ٱلۡمِيزَانَ
Open ayah 55:7Sama kuma Ya ɗaga ta, Ya kuma kafa adalci.
أَلَّا تَطۡغَوۡاْ فِي ٱلۡمِيزَانِ
Open ayah 55:8Don kada ku yi zalunci a abin awo.
وَأَقِيمُواْ ٱلۡوَزۡنَ بِٱلۡقِسۡطِ وَلَا تُخۡسِرُواْ ٱلۡمِيزَانَ
Open ayah 55:9Kuma ku tabbatar da awo da adalci kada kuma ku tauye abin awo.
وَٱلۡأَرۡضَ وَضَعَهَا لِلۡأَنَامِ
Open ayah 55:10Ƙasa kuma Ya yi ta saboda talikai.
فِيهَا فَٰكِهَةٞ وَٱلنَّخۡلُ ذَاتُ ٱلۡأَكۡمَامِ
Open ayah 55:11A cikinta akwai abin marmari da dabinai ma’abota kwasfa.
وَٱلۡحَبُّ ذُو ٱلۡعَصۡفِ وَٱلرَّيۡحَانُ
Open ayah 55:12Da ƙwayoyi ma’abota ƙaiƙayi da kuma ganyaye masu ƙanshi.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:13To da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da ambaton sunansa \'Mai rahma\' wanda yake nuna yalwatacciyar rahamarsa da ta game kowa da komai a nan duniya. Sannan ya bayyana cewa, shi ne ya koyar da karatun Alƙur’ani, ya sauƙaƙe haddarsa da fahimtar ma’anoninsa. Ya kuma kyautata halittar ɗan’adam, ya koyar da shi yadda zai yi bayanin abin da ke cikin zuciyarsa ta hanyar furuci ko rubutu. Sai kuma ya bayyana cikar Ƙudurarsa da ɗa’ar halittu a gare shi da cewa, shi ne ya halicci rana da wata ya kuma tsara tafiyarsu a cikin sararin samaniya a kan wani lissafaffen tsari, domin mutane su riƙa sanin adadin shekaru da lissafin kwanakin wata. Sannan ya bayyana cewa, tsirrai waɗanda ba sa tashi tsaye da bishiyoyi masu tsayawa a kan sandunansu, dukkansu suna yi masa sujjada suna miƙa wuya a gare shi. Sai kuma ya bayyana cewa, shi ne ya halicci sama ya ɗaga ta domin ta zama kamar rufi ga halittunsa na ƙasa, ya kuma kafa adalci a bayan ƙasa ya kuma umarci bayinsa su tsayar da shi a tsakaninsu. Ya yi musu haka ne domin kada su yi zalunci su tsauye sikeli ko mudu, don haka ya jaddada musu cewa lalle su tsayar da sikeli a tsakaninsu da adalci, kada su kuskura su yi ƙwange wajen yin awo. Sai kuma ya bayyana ni\'imar da ya yi wa bayinsa da ya halicci ƙasa ya yi ta yadda ta dace da rayuwar halittunsa a kanta, ya kuma saka mata kayayyakin rayuwa iri-iri, kamar kayan marmari da dabinai masu kwasfa da ke ɗauke da ‘ya’yan dabinan da kuma ƙwayoyi masu ƙaiƙayi, kamar alkama da sha’iri da kuma ganyaye masu ƙanshi. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gama lissafa waɗannan dangogin ni’ima da ya yi wa ɗan’adam da aljan a nan duniya sai ya tambaye su cewa, da wacce ni’ima ce daga cikin ni’imomin Ubangijinsu masu yawa suke ƙaryatawa? An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce : Manzon Allah (ﷺ) ya fita wajen sahabbansa, sai ya karanta musu ‘Suratur Rahman ’ daga farkonta har ƙarshenta, sai suka yi shiru suna sauraron sa, sai ya ce: “Me ya sa na ga kun yi shiru? Haƙiƙa na karanta wa aljannu wannan Surar a daren haɗuwata da su, sai ya zamanto sun fi ku iya bayar da amsa; duk sanda na karanta musu faɗar Allah: “To da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa ?” Sai su ce: \'Babu wani abu daga cikin ni’imominka da muke ƙaryatawa ya Ubangijinmu, yabo da godiya sun tabbata a gare ka\'.” [Tirmizi #3575].
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِن صَلۡصَٰلٖ كَٱلۡفَخَّارِ
Open ayah 55:14Ya halicci mutum daga busasshen taɓo kamar kasko.
وَخَلَقَ ٱلۡجَآنَّ مِن مَّارِجٖ مِّن نَّارٖ
Open ayah 55:15Ya kuma halicci aljani daga harshen wuta.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:16Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقَيۡنِ وَرَبُّ ٱلۡمَغۡرِبَيۡنِ
Open ayah 55:17Ubangijin mahudar rana biyu da mafaɗarta biyu.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:18Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
مَرَجَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ يَلۡتَقِيَانِ
Open ayah 55:19Ya gudanar da koguna guda biyu suna haɗuwa (da juna).
بَيۡنَهُمَا بَرۡزَخٞ لَّا يَبۡغِيَانِ
Open ayah 55:20A tsakaninsu (kuma) akwai wani shamaki da ya hana su shiga juna.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:21Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
يَخۡرُجُ مِنۡهُمَا ٱللُّؤۡلُؤُ وَٱلۡمَرۡجَانُ
Open ayah 55:22Lu’ulu’u da murjani suna fita daga cikinsu.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:23Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
وَلَهُ ٱلۡجَوَارِ ٱلۡمُنشَـَٔاتُ فِي ٱلۡبَحۡرِ كَٱلۡأَعۡلَٰمِ
Open ayah 55:24Jiragen ruwa kuma da aka yi su suna gudu a cikin kogi kamar manya-manyan duwatsu nasa ne.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:25Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu alamomi na Ƙudurarsa da cikar ikonsa, inda ya bayyana cewa, ya halicci mutum, watau Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga busasshen taɓo mai amo kamar kasko, watau bayan taɓon ya bushe sai ya riƙa yin ƙara idan an ƙwanƙwasa shi, kamar ana ƙwanƙwasa kasko. Ya kuma halicci uban aljannu, watau Iblis daga tsantsar harshen wuta. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “An halicci mala’iku daga haske, an kuma halicci aljani daga wuta, an kuma halicci Adamu daga abin da aka siffanta muku.” [Muslim #2996 da Ahmad #12303]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi mutane da aljannu cewa, da wacce ni’imar ce daga cikin ni’imominsa masu yawa suke ƙaryatawa? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, shi ne Ubangijin mahudar rana biyu da mafaɗarta biyu, watau a lokacin sanyi da lokacin zafi, shi kaɗai ne mai gudanar da su, dukkansu kuma suna ƙarƙashin ikonsa ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikar Ƙudurarsa dangane da koguna, yayin da ya gauraya ruwan koguna biyu, mai daɗi da mai zartsi, watau a ido ana ganin su suna haɗuwa da juna, amma a tsakaninsu akwai wani shamaki wanda yake hana su gauraya da juna, don haka mai daɗi zai ci gaba da kasancewa mai daɗi, mai zartsi shi ma zai ci gaba da zama mai zartsi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi mutane da aljannu cewa da waɗanne ni’imominsa ne suke ƙaryatawa? Waɗannan koguna biyu kuma ana fitar da lu’ulu’u da murjani, watau ana nufin cewa suna fita daga cikin kogi mai zartsi wanda yake tare da mai daɗi wuri guda. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi kaɗai ne yake da ikon gudanar da manya-manyan jiragen ruwa a cikin kogi, suna tafiya kamar manyan duwatsu, mutane suna hawan su tare da kayayyakinsu masu nauyi su yi ta zirga-zirga da su ƙasa-ƙasa. Babu shakka wannan babbar ni’ima ce daga ni’imomin Allah masu yawa, don haka ya sake tambayar mutane da aljannu cewa da wacce ni’imar ce suke ƙaryatawa?
كُلُّ مَنۡ عَلَيۡهَا فَانٖ
Open ayah 55:26Dukkan wanda yake kanta (ƙasar) ƙararre ne.
وَيَبۡقَىٰ وَجۡهُ رَبِّكَ ذُو ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ
Open ayah 55:27Fuskar Ubangijinka kuwa Ma’abocin girma da karamci ne kawai take wanzuwa.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:28Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
يَسۡـَٔلُهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ كُلَّ يَوۡمٍ هُوَ فِي شَأۡنٖ
Open ayah 55:29Duk wanda yake cikin sammai da ƙasa yana roƙon Sa. Kowane lokacin Shi a cikin wani sha’ani yake.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:30Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa mutum da aljani cewa, su sani duk wani abu da yake bayan ƙasa, na mutane da aljannu da dabbobi da sauran halittu na ruwa da na tudu, dukansu masu ƙarewa ne, su gushe kamar ba a yi su ba, babu wanda zai wanzu sai Allah (Mai tsarki da daukaka) Ma’abocin girma da karamci ga bayinsa, shi kam yana nan har abada, gushewa ba za ta riske shi ba balle ƙarewa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tambayar mutane da aljannu cewa, da waɗanne ni’imomin Ubangijinsu ne suke ƙaryatawa? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tsananin buƙatuwar halittunsa na sama da na ƙasa gare shi, domin cikar wadatarsa da kyautayinsu. Mala’iku a cikin sammai da mutane da aljannu a ƙasa dukkansu suna roƙon sa ya biya musu buƙatunsu babu ƙaƙƙautawa. Shi kuwa a kowane lokaci yana cikin wani al’amari da ya shafi al’amuran bayinsa, wanda ya danganci rayawa da kashewa da arzutawa da talautawa da sauransu. Sai kuma ya maimaita tambayarsa ga mutane da aljannu game da ni’imomin Ubangijinsu da suke ƙaryatawa?
سَنَفۡرُغُ لَكُمۡ أَيُّهَ ٱلثَّقَلَانِ
Open ayah 55:31Ba da daɗewa ba za Mu dawo kanku ya ku mutane da aljannu.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:32Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ إِنِ ٱسۡتَطَعۡتُمۡ أَن تَنفُذُواْ مِنۡ أَقۡطَارِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ فَٱنفُذُواْۚ لَا تَنفُذُونَ إِلَّا بِسُلۡطَٰنٖ
Open ayah 55:33Ya ku jama’ar aljannu da mutane, idan kun sami ikon ficewa daga cikin sassan sammai da ƙasa to ku fice. Ba za ku fice ba sai da samun wani ƙarfi.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:34Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
يُرۡسَلُ عَلَيۡكُمَا شُوَاظٞ مِّن نَّارٖ وَنُحَاسٞ فَلَا تَنتَصِرَانِ
Open ayah 55:35Za a aiko muku (ku mutane da aljannu) da balbalin wuta da kuma hayaƙi, saboda haka ba za ku iya kare kanku (daga gare shi) ba.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:36Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da bayinsa mutane da aljannu da cewa, ba da jimawa ba zai dawo kansu, watau a ranar alƙiyama domin yi musu hisabi a kan ayyukansu kyawawa da munana, zai kuma saka wa kowa gwargwadon aikinsa. Don haka ya sake jan hankalinsu game da ƙaryata wata ni’ima daga cikin ni’imominsa gare su. Sannan ya sanar da su cewa, a ranar alƙiyama idan ya tattara mutane da aljannu zai umarce su da cewa, idan har suna da iko kuma sun isa to su fice daga sassan sammai da na ƙasa, su guje wa damƙarsa. Ya tabbatar musu da cewa, tabbas ba za su iya samun wata mafita ba da za su kuɓuce wa Allah sai idan suna da wata hujja ko wani ƙarfi, wanda kuwa su ma sun tabbata ba su da shi. Sai ya sake jan kunnensu game da ƙaryata wata ni’ima daga cikin ni’imominsa gare su. Sai kuma ya bayyana musu abin da zai faru da su a wannan rana ta alƙiyama inda zai aiko musu da balbalin wuta marar hayaƙi da kuma hayaƙi marar balbali, saboda haka ba za su iya kare kansu daga gare shi ba, ba kuma za su iya taimaka wa junansu ba. To wannan tsoratarwar da yake yi musu ita kanta wata ni’ima ce a gare su, don haka ya sake jan kunnensu ta hanyar tambayar su game da ni’imarsa da suke ƙaryatawa.
فَإِذَا ٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ وَرۡدَةٗ كَٱلدِّهَانِ
Open ayah 55:37Sannan idan sama ta kekkece ta zama jajir kamar jar fata.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:38Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
فَيَوۡمَئِذٖ لَّا يُسۡـَٔلُ عَن ذَنۢبِهِۦٓ إِنسٞ وَلَا جَآنّٞ
Open ayah 55:39Sannan a wannan rana ba a tambayar mutum ko aljan laifinsa.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:40Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
يُعۡرَفُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ بِسِيمَٰهُمۡ فَيُؤۡخَذُ بِٱلنَّوَٰصِي وَٱلۡأَقۡدَامِ
Open ayah 55:41Ana gane manyan masu laifi da alamominsu, sai a kama su ta makwarkwaɗa da dugadugai.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:42Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
هَٰذِهِۦ جَهَنَّمُ ٱلَّتِي يُكَذِّبُ بِهَا ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Open ayah 55:43(Za a ce da su): Wannan ita ce Jahannamar da manyan masu laifi suke ƙaryatawa.
يَطُوفُونَ بَيۡنَهَا وَبَيۡنَ حَمِيمٍ ءَانٖ
Open ayah 55:44Za su riƙa kai-kawo tsakaninta da tafasasshen ruwa mai tsananin zafi.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:45Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda a ranar alƙiyama sama za ta tsattsage ta zama ja kamar jan fure ko jar fata, saboda an gusar da hasken taurarinta gaba ɗaya, domin wani babban sauyi da Allah ya samar a sammai da ƙasa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya maimaita tambayar ga mutane da aljannu cewa da waɗanne ni’imomin Ubangijinsu ne suke ƙaryatawa? Sai ya ci gaba da bayanin cewa, a wannan ranar ta alƙiyama ba za a tsaya tambayar wani mutum ko aljani game da laifin da ya aikata ba, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya riga ya san komai na ayyukansa ba ya kokwanto a kan abin da kowa ya aikata, domin kuwa duk wasu masu miyagun laifuka za a gane su da alamominsu, saboda fuskokinsu za su yi baƙi ƙirin, idanuwansu kuma za su zama jajaye jawur, daga nan sai a damƙe su ta makwarkwaɗarsu tare da dugadugansu a watsa su cikin wutar Jahannama. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tambayar mutane da aljannu cewa da waɗanne ni’imomin Ubangijinsu ne suke ƙaryatawa? Sannan bayan mala’iku sun jefa kafirai cikin wutar Jahannama sai su riƙa faɗa musu cewa, wannan fa ita ce Jahannamar da suke ƙarayatawa a duniya, ga su nan yau a cikinta tsundum babu sauran maganar ƙaryatawa kuma, domin kuwa a cikinta ne za su yi ta kai-kawo tsakaninta da tafasasshen ruwa mai tsananin zafi. To da waɗanne ni’imomin Ubangijinsu ne suke ƙaryatawa?
وَلِمَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ جَنَّتَانِ
Open ayah 55:46Duk wanda kuwa ya ji tsoron tsayuwa (gaban) Ubangijinsa yana da Aljanna biyu.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:47Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
ذَوَاتَآ أَفۡنَانٖ
Open ayah 55:48Ma’abota rassan bishiyoyi.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:49Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
فِيهِمَا عَيۡنَانِ تَجۡرِيَانِ
Open ayah 55:50A cikinsu akwai idanuwa (na ruwa) guda biyu masu gudana.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:51Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
فِيهِمَا مِن كُلِّ فَٰكِهَةٖ زَوۡجَانِ
Open ayah 55:52A cikinsu akwai (dangi) biyu na kowane abin marmari.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:53Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ فُرُشِۭ بَطَآئِنُهَا مِنۡ إِسۡتَبۡرَقٖۚ وَجَنَى ٱلۡجَنَّتَيۡنِ دَانٖ
Open ayah 55:54Suna kishingiɗe a kan shimfiɗu da shafin cikinsu na kakkauran alhariri ne. Kuma ‘ya’yan bishiyoyin Aljannatai biyun kusa suke (da kowa).
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:55Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
فِيهِنَّ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ لَمۡ يَطۡمِثۡهُنَّ إِنسٞ قَبۡلَهُمۡ وَلَا جَآنّٞ
Open ayah 55:56A cikinsu akwai (mata) masu taƙaita kallo (ga mazajensu, waɗanda) wani mutum ko aljan bai taɓa shafar su ba a gabaninsu.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:57Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
كَأَنَّهُنَّ ٱلۡيَاقُوتُ وَٱلۡمَرۡجَانُ
Open ayah 55:58Kai ka ce su yaƙutu ne da murjani.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:59Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
هَلۡ جَزَآءُ ٱلۡإِحۡسَٰنِ إِلَّا ٱلۡإِحۡسَٰنُ
Open ayah 55:60Shin akwai wani sakamako na kyautatawa in ba kyautatawa ba?
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:61Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu ni’imomin Aljanna da zai saka wa muminai masu tsoron sa da su, inda ya ce, duk wani muminin da ya ji tsoron tsayawa gaban Ubangijinsa a ranar alƙiyama ya kuma yi aiki nagari, to yana da aljannatai guda biyu waɗanda ya bayyana siffofinsu har guda shida: <b>Na ɗaya </b>, suna da rassan bishiyoyi masu yawa da girma da inuwoyi luf-luf. <b>Na biyu </b>, a cikinsu kuma akwai idanuwan ruwa masu gudana ko’ina suna shayar da bishiyoyi da shuke-shuken cikinsu. <b>Na uku </b>, kowane nau’i na kayan marmari a cikinsu ana kawo musu bibbiyu ne, watau ɗanye da busasshe, kowanne cikinsu yana da launinsa da ɗanɗanonsa na daban, fari da ja da mai zaƙi da mai tsami. <b>Na huɗu </b>, akwai shimfiɗu na alfarma da ‘yan Aljannar za su riƙa kishingiɗa a kansu, ƙasansu na alhariri ne mai kauri mai ban sha’awa, ballanta kuma samansu inda suke kwanciya a kai ko zama, abin sai dai wanda ya gani kawai. <b>Na biyar </b>, ‘ya’yan itatuwan waɗannan aljannatai biyu kusa-kusa suke ta yadda ɗan Aljanna ko yana kishingiɗe zai iya miƙa hannunsa ya tsinko. <b>Na shida </b>, a cikinsu kuma akwai matan Hurul-Ini waɗanda ba sa kallon kowa sai mazajensu, waɗanda kuma babu wani mahaluƙi mutum ko aljani da ya taɓa taɓa su sai mazajensu. Allah ya yi musu tsalelen kyau da haske, idan ka gan su sai ka ga suna haske da sheƙi kamar yaƙutu da murjani. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (() ya ce: “Farkon ayarin da za su shiga Aljanna za su shige ta ne suna masu haske kamar wata daren goma sha huɗu, waɗanda za su biyo bayansu kuwa suna haske kamar tauraron da ya fi kowanne tauraro haske. Zukatansu kamar zuciyar mutum ɗaya, babu saɓani ko ƙyamar juna a tsakaninsu. Duk mutum ɗaya daga cikinsu yana da mata biyu, kowace ɗaya daga cikinsu ana gano ɓargon ƙwaurinta ta bayan tsokar nama saboda tsananin kyau. Suna yi wa Allah tasbihi suna tsarkake shi safe da yamma. Ba sa rashin lafiya ba sa face majina ko tofar da yawu. Kwanukansu na zinariya ne da azurfa, matajan kansu kuwa na zinariya ne, makamashin turaren wutarsu shi ne Al-ud , guminsu kuwa ƙamshin almiski yake.” [Bukhari #2346 da Muslim #2834]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, babu wani sakamako ga duk wanda ya kyautata biyayya gare shi sai dai kyakkyawan sakamako da zai samu daga Ubangijinsa. To yanzu da waɗannen ni’imomin Ubangiji ne mutane da aljannu suke ƙaryatawa?
وَمِن دُونِهِمَا جَنَّتَانِ
Open ayah 55:62A ƙasa da su kuma akwai wasu aljannatai guda biyu.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:63Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
مُدۡهَآمَّتَانِ
Open ayah 55:64Masu tsananin kore.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:65Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
فِيهِمَا عَيۡنَانِ نَضَّاخَتَانِ
Open ayah 55:66A cikinsu (kuma) akwai idanuwan (ruwa) guda biyu masu feshi.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:67Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
فِيهِمَا فَٰكِهَةٞ وَنَخۡلٞ وَرُمَّانٞ
Open ayah 55:68A cikinsu (kuma) akwai abin marmari da dabino da ruman.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:69Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
فِيهِنَّ خَيۡرَٰتٌ حِسَانٞ
Open ayah 55:70A cikinsu (watau gidajen Aljannar) akwai mata nagartattu kyawawa.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:71Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
حُورٞ مَّقۡصُورَٰتٞ فِي ٱلۡخِيَامِ
Open ayah 55:72(Matayen) masu fari da baƙin ido ne, suna kawwame cikin tantuna.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:73Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
لَمۡ يَطۡمِثۡهُنَّ إِنسٞ قَبۡلَهُمۡ وَلَا جَآنّٞ
Open ayah 55:74Wani mutum ko aljan bai taɓa shafar su ba a gabaninsu.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:75Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ رَفۡرَفٍ خُضۡرٖ وَعَبۡقَرِيٍّ حِسَانٖ
Open ayah 55:76Suna kishingiɗe a kan matasan kai koraye, da kuma kilisai kyawawa.
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Open ayah 55:77Da waɗanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke ƙaryatawa?
تَبَٰرَكَ ٱسۡمُ رَبِّكَ ذِي ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ
Open ayah 55:78Albarkatun sunan Ubangijinka Ma’abocin girma da ɗaukaka sun yawaita. A waɗannan ayoyi kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, akwai wasu aljannatai biyu ƙasa da waɗanda aka ambata da farko waɗanda su ma ya siffanta su da siffofi biyar, su ne: <b>Na ɗaya </b>, bishiyoyinsu da shuke-shukensu koraye ne shar masu matuƙar ban sha’awa. <b>Na biyu </b>, a cikinsu akwai wasu idanuwan ruwa biyu masu feshin ruwa da ƙarfi ba ƙaƙƙautawa. <b>Na uku </b>, a cikinsu akwai kayan marmari masu yawa da itatuwan dabino manya-manya da kuma rumman, waɗanda koyaushe ake samu ba sa yankewa. <b>Na huɗu </b>, a cikinsu har ila yau akwai mata masu kyawawan halaye masu kyan sura da fari da baƙin ido, kawwamammu a cikin tantuna, babu mai ganin su su ma ba sa ganin kowa sai mazajensu, don haka ne ma babu wani mahaluƙi mutum ko aljani da ya taɓa kusantar su kafin mazajensu. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Tantin (‘yan Aljanna) wani kewayayyen lu’ulu’u ne, tsawonsa a sama mil talatin ne. A cikin kowane rukunin tantin mumini yana da iyali da sauran ba sa ganin su.” [Bukhari #3243 da Muslim #2838]. <b>Na biyar </b>, a cikinsu akwai matasan kai waɗanda aka naɗe su cikin korayen riguna da kuma shimfiɗu masu tsananin kyau, a kansu ne ‘yan Aljanna suke kishingiɗa suna morewa. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Akwai wasu aljannatai biyu na azurfa, kwanukansu da duk wani abu da yake cikinsu na azurfa ne. Da kuma wasu aljannatai biyu na zinari, duk wani abin da yake cikinsu shi ma na zinari ne. Babu wani abu da ya zama shamaki tsakaninsu da ganin Ubangijinsu sai gwadon ƙasaita da ke kan fuskarsa, suna cikin Aljannar dawwama.” [Bukhari #4878 da Muslim #180]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nanata tambayarsa ga mutane da aljannu cewa da waɗanne ni’imominsa ne suke ƙaryatawa? Allah kuma a ƙarshen Surar ya yabi kansa da cewa albarkatun sunansa sun yawaita ya kuma girmama, shi ne ma’abocin girma da karamci ga bayinsa. An karɓo daga Rabi’a ɗan Amir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku lizimci faɗar: “Ya Zal-Jalali Wal Ikram ”. [Ahmad #17596 da Hakim #1836]. An karɓo daga Sauban (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance da zarar ya gama salla sai ya ce: “Allahumma Antas Salamu Wa Minkas Salamu Tabarakta Ya Zal Jalali Wal Ikram .” [Muslim #591]