الواقعة
Al-Waaqia
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
إِذَا وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ
Open ayah 56:1Idan mai afkowa ta afku (watau alƙiyama).
لَيۡسَ لِوَقۡعَتِهَا كَاذِبَةٌ
Open ayah 56:2Babu wani (rai) mai ƙaryata aukuwarta.
خَافِضَةٞ رَّافِعَةٌ
Open ayah 56:3Mai ƙasƙantarwa ce mai ɗaukakawa.
إِذَا رُجَّتِ ٱلۡأَرۡضُ رَجّٗا
Open ayah 56:4Idan aka girgiza ƙasa girgizawa.
وَبُسَّتِ ٱلۡجِبَالُ بَسّٗا
Open ayah 56:5Aka kuma dandaƙe duwatsu dandaƙewa.
فَكَانَتۡ هَبَآءٗ مُّنۢبَثّٗا
Open ayah 56:6Suka zama ƙura abar sheƙewa.
وَكُنتُمۡ أَزۡوَٰجٗا ثَلَٰثَةٗ
Open ayah 56:7Kuka kuma kasance dangogi guda uku.
فَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ
Open ayah 56:8To ma’abota dama fa, mamakin darajar ma’abota dama!
وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ
Open ayah 56:9Da kuma ma’abota hagu, mamakin wulaƙantar ma’abota hagu!
وَٱلسَّٰبِقُونَ ٱلسَّٰبِقُونَ
Open ayah 56:10Da kuma masu rige-rige (zuwa alheri).
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلۡمُقَرَّبُونَ
Open ayah 56:11Waɗannan su ne makusanta.
فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Open ayah 56:12A cikin gidajen Aljanna na ni’ima. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tabbatar da aukuwar tashin alƙiyama idan lokacinta ya yi, kuma idan ta auku babu wani rai da zai iya ƙaryata ta, kamar yadda yake faruwa a nan gidan duniya, inda wasu kafirai suke cewa ƙarya ne babu ita. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta ranar alƙiyama da cewa rana ce da za ta ƙasƙantar da kafirai, domin kuwa za a jefa su cikin wuta kowa yana gani, ta kuma ɗaga likkafar muminai masu tsoron Allah, yayin da za a shigar da su gidajen Aljanna kowa yana gani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lokacin aukuwar ranar alƙiyama ƙasa za ta yi wata babbar girgiza da ba ta taɓa yin irinta ba, za kuma a yi fata-fata da duwarwatsu su zama kamar ƙura abar sheƙewa, watau ƙasa ta dawo fili fetal babu tudu ko kwari, kuma babu komai a kanta. A ranar mutane za su kasu gida uku: <b>Na farko </b>, ma’abota hannun dama, waɗanda za su karɓi littattafan ayyukansu da hannayensu na dama. Waɗannan suna da babban matsayi. <b>Na biyu </b>, ma’abota hannun hagu, watau waɗanda za su karɓi littattafansu na ayyuka a hannayensu na hagu. Waɗannan kam matsayinsu ya munana ainun. <b>Na uku </b>, masu rige-rige wajen ayyukan alheri a duniya, to waɗannan su ne za su riga kowa shiga Aljanna a lahira, kuma su ne makusantan Allah (Mai tsarki da daukaka) waɗanda zai sanya su a cikin gidajen Aljanna na ni’ima, su yi rayuwar jin daɗi a cikinsu babu yankewa.
ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 56:13Su jama’a ne (masu yawa) daga (al’ummun) farko.
وَقَلِيلٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 56:14Kuma kaɗan ne daga (al’ummun) ƙarshe.
عَلَىٰ سُرُرٖ مَّوۡضُونَةٖ
Open ayah 56:15Suna kan gadaje masu adon zinari.
مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيۡهَا مُتَقَٰبِلِينَ
Open ayah 56:16Suna kishingiɗe a kansu suna fuskantar juna.
يَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٞ مُّخَلَّدُونَ
Open ayah 56:17Yara samari dawwamammu (masu hidima) za su riƙa zagaya su.
بِأَكۡوَابٖ وَأَبَارِيقَ وَكَأۡسٖ مِّن مَّعِينٖ
Open ayah 56:18Da kofuna (marasa mariƙai) da butoci masu hannaye da kuma ƙoƙuna na giya.
لَّا يُصَدَّعُونَ عَنۡهَا وَلَا يُنزِفُونَ
Open ayah 56:19Ba sa ciwon kai saboda ita, kuma ba sa buguwa.
وَفَٰكِهَةٖ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ
Open ayah 56:20Da kuma ababan marmari na abin da suke so su zaɓa.
وَلَحۡمِ طَيۡرٖ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ
Open ayah 56:21Da kuma naman tsuntsaye na abin da suke sha’awa.
وَحُورٌ عِينٞ
Open ayah 56:22Da kuma matan Hurul-Ini.
كَأَمۡثَٰلِ ٱللُّؤۡلُوِٕ ٱلۡمَكۡنُونِ
Open ayah 56:23Kamar misalin lu’ulu’u da yake cikin kwasfa.
جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 56:24Sakamako ne na abin da suka kasance suna aikatawa.
لَا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا تَأۡثِيمًا
Open ayah 56:25Ba sa kuma jin wani zancen banza da mai sa zunubi a cikinta.
إِلَّا قِيلٗا سَلَٰمٗا سَلَٰمٗا
Open ayah 56:26Sai dai faɗar salamun-salamun. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, rukunin muminai masu rige-rige zuwa aikata alheri jama’a ne masu yawa a cikin al’ummun farko, watau al’ummun annabawa da manzannin da suka gabaci wannan al’umma ta Musulmi, kuma \'yan kaɗan ne a cikin wannan al’umma ta ƙarshe, watau al’ummar Annabi Muhammad (ﷺ). Ko kuma ana nufin wannan rukuni na bayin Allah jama’a ne masu yawa a cikin al’ummun farko na wannan al’umma da kuma al’ummun da suka gabace ta, kuma kaɗan ne a cikin al’ummun ƙarshe na wannan al’umma. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakonsu da cewa, su a gidan Aljanna suna kan wasu gadaje ne na alfarma waɗanda aka yi wa ado da zinare, suna kishingiɗe a kansu cikin natsuwa da jin daɗi, suna fuskantar juna cike da soyayya da ƙaunar juna, babu mai juya wa ɗan’uwansa baya. Kuma ga yara ƙanana masu yi musu hidima waɗanda za su dawwama a cikin kamanni ɗaya ba tare da sun tsufa ba ko sun tagayyara, suna kai-komo a kansu ɗauke da kofunan giya marasa mariƙai da butoci masu hannaye da ƙoƙuna cike da giyar Aljanna wadda ba ta yankewa, sannan idan sun sha ta ba ta sa musu ciwon kai kamar giyar duniya, ba kuma ta sa su buguwa ta tafiyar musu da hankulansu har su riƙa yin wasu sumbatu da surutai na banza. Bayan waɗannan kuma su yaran hadimai za su riƙa kewaya su da kayan marmari wanda suka zaɓa suka nuna suna so, da kuma naman tsuntsaye waɗanda ransu yake sha’awa. Bayan an ba su kayan shaye-shaye da ciye-ciye, sannan kuma suna da matan Hurul-Ini waɗanda aka bayyana kyansu da haskensu da cewa kamar misalin lu’ulu’u ne da yake cikin kwasfansa, iska ko rana ba sa dukan sa sannan babu mai ganin sa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk waɗannan abubuwa da ya tanadar musu sakamako ne a gare su saboda kyawawan ayyukansu da suka kasance suna aikatawa a duniya. Su kuma ‘yan Aljanna ba abin da za su ji na maganganun banza ko na saɓon Allah, sai dai su riƙa jin sallamar mala’iku a gare su da wadda za su riƙa yi wa junansu.
وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 56:27Ma’abota hannun dama kuwa, mamakin darajar ma’abota hannun dama!
فِي سِدۡرٖ مَّخۡضُودٖ
Open ayah 56:28Suna cikin ‘ya’yan itacen magarya marasa ƙaya.
وَطَلۡحٖ مَّنضُودٖ
Open ayah 56:29Da kuma ayaba mai ‘ya’ya daɓa-daɓa.
وَظِلّٖ مَّمۡدُودٖ
Open ayah 56:30Da inuwa madawwamiya.
وَمَآءٖ مَّسۡكُوبٖ
Open ayah 56:31Da kuma ruwa mai kwarara.
وَفَٰكِهَةٖ كَثِيرَةٖ
Open ayah 56:32Da ababen marmari masu yawa.
لَّا مَقۡطُوعَةٖ وَلَا مَمۡنُوعَةٖ
Open ayah 56:33Ba masu yankewa ba kuma ba ababen hanawa ba.
وَفُرُشٖ مَّرۡفُوعَةٍ
Open ayah 56:34Da shimfiɗu masu daraja.
إِنَّآ أَنشَأۡنَٰهُنَّ إِنشَآءٗ
Open ayah 56:35Lalle Mu ne Muka ƙage su (‘yan matan Aljanna) sabuwar ƙagowa.
فَجَعَلۡنَٰهُنَّ أَبۡكَارًا
Open ayah 56:36Sannan Muka sanya su budurwai.
عُرُبًا أَتۡرَابٗا
Open ayah 56:37Masu begen mazajensu, tsarekun juna.
لِّأَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 56:38Don ma’abota hannun dama.
ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 56:39Su jama’a ne (masu yawa) daga (al’ummun) farko.
وَثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 56:40Kuma jama’a ne (masu yawa) daga (al’ummar) ƙarshe. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon da ya tanadar wa ma’abota hannun dama masu girman daraja a wajensa, da cewa ya tanadar musu Aljanna mai cike da ‘ya’yan itacen magarya marar ƙaya wadda ba za su cutu da ita ba. An karɓo daga Sulaim ɗan Amir ya ce: Sahabban Manzon Allah sun kasance suna cewa: “Lalle Allah tabbas yakan amfanar da mu ta hanyar tambayoyin mutanen ƙauye.” Ya ce: “Wata rana wani mutumin ƙauye ya zo wurin Manzon Allah (ﷺ) ya ce: ‘Allah mai girma da buwaya ya ambaci wata bishiya mai cutarwa a gidan Aljanna, ni kuma ba na ganin ya dace a sami bishiyar da za ta riƙa cutar da mai ita.’ Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wacce bishiya ce?” Sai ya ce: “Magarya ce, domin kuwa tana da ƙaya mai cutarwa.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce da shi: “Ba Allah cewa ya yi ba: ‘A cikin ‘ya’yan itacen magarya marasa ƙaya’? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya cire mata ƙayoyinta, ya sanya ɗan itace a mahallin kowace ƙaya, lalle za ta fitar da ‘ya’yanta, kowane ɗaya kuwa zai fitar da launin abinci saba’in da biyu, wanda a cikinsu babu wani launi da ya yi kama da ɗan’uwansa.” [Ibn Abid Dunya, Sifatul Janna #105 da Hakim #3778]. Akwai kuma ayaba mai ‘ya’ya goyo-goyo, wasu kan wasu, da kuma inuwa wadda ba ta janyewa da ruwa mai kwarara, shi ne ruwan ƙoramun Aljanna, da kayan marmari masu yawa marasa iyaka, ba sa yankewa har abada, kuma ba su da wani ƙayyadajjen lokaci, babu kuma abin da ya hana a same su duk sanda aka buƙace su. Da kuma shimfuɗu waɗanda aka ɗaga su sama a kan gadaje. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata ni’imar daban da ya tanadar musu a Aljanna, watau matan Hurul-Ini waɗanda ya sake ƙagar halittarsu cikin kyakkyawar sura, ya sanya su ‘yan mata budurwai da babu wani namiji da ya taɓa kusantar su, sannan ya mayar da su ababan soyuwa ga mazajensu kuma tsarekun juna. Ya bayyana cewa, ya tanade su ne ga ma’abota dama waɗanda za su karɓi littattafansu na ayyuka a hannayensu na dama, waɗanda su jama’a ne daga cikin al’ummun annabawan da suka gabata da kuma jama’a daga cikin al’ummar Muhammadu (ﷺ) waɗanda su ne al’umma ta ƙarshe. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Manzon Allah (ﷺ) ya fito wajenmu sai ya ce: “An bijiro mini al’ummomi, sai wani annabi ya zo ya wuce da mutum ɗaya tare da shi, wani annabin kuma da mutum biyu, wani tare da tarin mutane. Wani annabin kuwa ba kowa tare da shi. Sai na hango wani dandazo mai yawa wanda ya tokare sararin sama, sai na yi fatan su zamanto al’ummata ce. Sai aka ce mini: Wannan Musa ne da mutanensa. Sannan aka ce min: Duba ka gani. Sai na ga wani dandazo wanda ya tokare sararin sama. Sai aka sake ce min: Duba can da can. Sai na ga dandazo mai yawa ya tokare sama. Sai aka ce min: Waɗannan al’ummarka ne. Tare da waɗannan kuma akwai mutum dubu saba’in da za su shiga Aljanna ba tare da hisabi ba....” [Bukhari #5752 da Muslim #220].
وَأَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ
Open ayah 56:41Ma’abota hannun hagu kuma, mamakin ƙasƙancin ma’abota hannun hagu!
فِي سَمُومٖ وَحَمِيمٖ
Open ayah 56:42Suna cikin iska mai tsananin zafi da kuma tafasasshen ruwa.
وَظِلّٖ مِّن يَحۡمُومٖ
Open ayah 56:43Da kuma inuwa ta turnuƙun hayaƙi.
لَّا بَارِدٖ وَلَا كَرِيمٍ
Open ayah 56:44Ba mai sanyi ba, kuma ba mai daraja ba.
إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُتۡرَفِينَ
Open ayah 56:45Lalle su sun kasance masu holewa ne kafin wannan.
وَكَانُواْ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلۡحِنثِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 56:46Sun kuma kasance suna dogewa a kan zunubi mai girma.
وَكَانُواْ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ
Open ayah 56:47Sun kuma kasance suna cewa: “Yanzu idan mun mutu, mun zama ƙasa da ƙasusuwa, yanzu lalle za a tashe mu?
أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ
Open ayah 56:48“Hakanan ma iyayenmu na farko?”
قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَوَّلِينَ وَٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 56:49Ka ce: “Lalle na farkon da na ƙarshen.
لَمَجۡمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ
Open ayah 56:50“Tabbas za a tattara su zuwa wani lokaci na rana sananniya.
ثُمَّ إِنَّكُمۡ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلۡمُكَذِّبُونَ
Open ayah 56:51“Sannan lalle ku kuma waɗannan ɓatattu masu ƙaryatawa.
لَأٓكِلُونَ مِن شَجَرٖ مِّن زَقُّومٖ
Open ayah 56:52“Tabbas za ku ci daga bishiyar Zaƙƙumu.
فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ
Open ayah 56:53“Sannan za ku cika cikunanku da ita.
فَشَٰرِبُونَ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡحَمِيمِ
Open ayah 56:54“Sannan za ku sha tafasasshen ruwa a kanta.
فَشَٰرِبُونَ شُرۡبَ ٱلۡهِيمِ
Open ayah 56:55“Sannan za ku sha irin shan raƙuma masu jin ƙishirwa.”
هَٰذَا نُزُلُهُمۡ يَوۡمَ ٱلدِّينِ
Open ayah 56:56Wannan ita ce gararsu a ranar sakamako. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan sakamakon ‘yan wuta ma’abota hagu, watau waɗanda za a ba su littattafan ayyukansu ta hannun hagu. A ranar lahira suna cikin wata iska mai tsananin zafi wadda za ta yi matuƙar addabar su, idan sun buƙaci ruwan sha kuwa sai dai su sha wani tafasasshen ruwa wanda yake tsittsinka musu ‘ya’yan hanji. Ba kuma za su sami wata inuwa ba sai inuwar wani turnuƙaƙƙen baƙin hayaƙi wanda ba ya da iska mai daɗi, ga shi kuma ba ya da kyan gani. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana abin da ya kai ‘yan wuta cikin wannan mummunar azabar da cewa su sun kasance a duniya suna rayuwa irin ta ta-more da sharholiya ba abin da suka sa a gaba sai biyan buƙatun sha’awarsu, kuma ga uwa-uba sun kasance masu dogewa a kan babban laifi na kafirci da bautar abin da ba Allah ba, ga shi kuma suna ƙaryata ranar alƙiyama suna cewa babu wata rayuwa bayan mutuwa, har ma suna mamakin cewa, ta yaya bayan sun riga sun mutu sun zama ƙasa da rududdugaggun ƙasusuwa a ce kuma za a tayar da su da ransu, kuma wai ba ma su ba har da iyayensu na farko waɗanda sun shafe shekaru aru-aru da mutuwa a ce su ma za a tashe su, don haka suna ganin wannan batu ba gaskiya ne ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) cewa, ya mayar musu da martani na cewa, lalle su sani duk mutanen farko da na ƙarshe gaba ɗayansu za a tashe su a tattara su wuri guda a ranar alƙiyama, ranar da Allah ya sanya mata wani lokaci ƙayyadadde da za ta zo a cikinsa, don ya yi musu hisabi da sakamako. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa waɗannan masu ƙaryata ranar alƙiyama irin mummunan sakamakon da za su gamu da shi a ranar yayin da za a jefa su wuta, abincinsu kuma ‘ya’yan itaciyar Zaƙƙum ne, bishiya mafi muni da sharri a wutar Jahannama, su ci har su take cikinsu da ita ba kuma tare da ta yi musu maganin yunwa ba. Sannan abin shansu shi ne tafasasshen ruwa, wanda za su yi ta kwankwaɗar sa kamar yadda raƙuma masu fama da cutar ƙishirwa suke kwankwaɗar ruwa, ba kuma tare da ya yi musu maganin ƙishi ba sai dai ya tsittsinka musu ‘yan hanji. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa wannan mummunan abinci da za su ci da tafasasshen ruwan da za su sha a ranar alƙiyama ita ce liyafar da aka tanadar musu. Wannan magana ce ta gatse da ba’a mai ƙara cusa musu haushi da baƙin ciki a ransu.
نَحۡنُ خَلَقۡنَٰكُمۡ فَلَوۡلَا تُصَدِّقُونَ
Open ayah 56:57Mu ne Muka halicce ku, me ya sa ba kwa gaskatawa?
أَفَرَءَيۡتُم مَّا تُمۡنُونَ
Open ayah 56:58Ba kwa ganin maniyyi da kuke zubawa.
ءَأَنتُمۡ تَخۡلُقُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡخَٰلِقُونَ
Open ayah 56:59Shin ku ne kuke halittar sa, ko kuwa Mu ne Masu halittar?
نَحۡنُ قَدَّرۡنَا بَيۡنَكُمُ ٱلۡمَوۡتَ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ
Open ayah 56:60Mu ne Muke ƙaddara mutuwa a tsakaninku, kuma Mu ba Masu gajiyawa ba ne.
عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمۡثَٰلَكُمۡ وَنُنشِئَكُمۡ فِي مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 56:61A kan Mu musanya irinku Mu kuma halitta ku cikin abin da ba ku sani ba.
وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُولَىٰ فَلَوۡلَا تَذَكَّرُونَ
Open ayah 56:62Haƙiƙa kuma ku kun san halitta ta farko, don me ba kwa wa’azantuwa?
أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَحۡرُثُونَ
Open ayah 56:63Ku ba Ni labarin abin da kuke nomawa?
ءَأَنتُمۡ تَزۡرَعُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلزَّٰرِعُونَ
Open ayah 56:64Shin ku ne kuke tsiro da shi, ko Mu ne Masu tsirarwar?
لَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَٰهُ حُطَٰمٗا فَظَلۡتُمۡ تَفَكَّهُونَ
Open ayah 56:65Idan da Mun ga dama tabbas da Mun mayar da shi karmami, sai ku wayi gari kuna mamaki.
إِنَّا لَمُغۡرَمُونَ
Open ayah 56:66(Kuna cewa): “Lalle mu an ɗora mana asara.”
بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ
Open ayah 56:67“A’a, mu dai an hana mu ne.”
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلۡمَآءَ ٱلَّذِي تَشۡرَبُونَ
Open ayah 56:68Ku ba Ni labarin ruwa wanda kuke sha.
ءَأَنتُمۡ أَنزَلۡتُمُوهُ مِنَ ٱلۡمُزۡنِ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنزِلُونَ
Open ayah 56:69Yanzu ku ne kuke sauko da shi daga girgije, ko kuwa Mu ne masu saukarwar?
لَوۡ نَشَآءُ جَعَلۡنَٰهُ أُجَاجٗا فَلَوۡلَا تَشۡكُرُونَ
Open ayah 56:70Da Mun ga dama da Mun mayar da shi (ruwa) mai zartsi, to don me ba kwa godewa?
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي تُورُونَ
Open ayah 56:71Ku ba Ni labarin wutar da kuke kunnawa.
ءَأَنتُمۡ أَنشَأۡتُمۡ شَجَرَتَهَآ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنشِـُٔونَ
Open ayah 56:72Yanzu ku ne kuka halicci bishiyarta, ko kuwa Mu ne Masu halittar?
نَحۡنُ جَعَلۡنَٰهَا تَذۡكِرَةٗ وَمَتَٰعٗا لِّلۡمُقۡوِينَ
Open ayah 56:73Mu ne Muka sanya ta wa’azi da kuma abin amfani ga matafiya.
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 56:74Saboda haka sai ka tsarkake Sunan Ubangijinka Mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mushirikai masu ƙaryata tashi bayan mutuwa ƙarfafan hujjoji da suke tabbatar da yiwuwar dawo da matattu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalinsu a kan abubuwa bakwai waɗanda suke tabbatar da cikar Ƙudurar Allah game da sake dawo da matattu. <b>Na farko </b>, Allah ya tabbatar musu cewa, shi ne ya samar da su daga babu, ya halicce su suka zama mutane, to me zai hana su su gaskata cewa zai iya dawo da halittarsu bayan mutuwarsu? <b>Na biyu </b>, su dubi ruwan maniyyi da suke sanyawa a mahaifar matansu wanda daga bisani ake halittar mutum da shi, shin su ne suka halicci wannan maniyyin ko kuwa Allah ne ya halicce shi? Babu shakka sun san ba su ne suka halicce shi ba, wannan aikin Allah ne shi kaɗai, to yanzu mai irin wannan Ƙudurar sai ya kasa dawo da matattu bayan sun zama ƙasa?! <b>Na uku </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, shi ne ya ƙaddara mutuwa a tsakaninsu, kowanne ɗaya daga cikinsu yana da ajalinsa wanda ba zai rigaye shi ba, ba kuma zai wuce shi ba. Idan har sun yarda shi ne yake da ikon karɓe rayuwarsu su mutu, to me zai hana su yarda zai iya dawo musu da rayukansu su sake tashi bayan sun mutu?! Don haka ba za su gagare shi ba a kan ya musanya tsarin halittarsu daga yadda suka san ta, ya sake halittar su a cikin wata surar da ba su sani ba. Yanzu wannan kaɗai ba zai sanya su su wa’azantu ba? <b>Na huɗu </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tabbatar musu cewa, sun riga sun san yadda ya halicce su a karon farko, to ashe ba za su ɗau izina ba a kan cewa wanda ya yi halitta a karon farko yana da cikakken ikon ya tashe su da rai bayan sun mutu? <b>Na biyar </b>, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalinsu zuwa ga lura da irin da suke shukawa a cikin ƙasa ya fito ya zama shuka, to shin su ne suke fito da wannan shukar ko kuma Allah ne yake fito da ita ta girma ta yi ‘ya’ya wanda shi ne suke girba su ci su kuma ciyar da dabbobinsu? Babu shakka Allah ne kawai mai yin wannan aiki, ba shi da abokin tarayya. To me zai hana shi ikon sake dawo da matattu ya busa musu rai su tashi, kamar yadda ya busa wa wannan iri rai ya fito ya zama shuka? Kuma da ya ga dama da ita kanta shukar bayan ta fito da sai ya mayar da ita duddugar karmami tun kafin ta nuna su girbi amfaninsu, sai kuma su wayi gari suna mamakin abin da ya faru da shukarsu, suna cewa sun tabka hasara, wasu kuma suna cewa, a’a an dai hana su ne su amfana da shukarsu. <b>Na shida </b>, ya ja hankalinsu zuwa ga ruwan da suke sha, ya tambaye su cewa, shin su ne suka saukar da shi daga girgije ko kuwa Allah ne ya saukar da shi? Babu shakka sun san yin haka aikin Allah ne shi kaɗai mai iko a kan komai. Da kuma ya ga dama sai ya mayar da ruwan ya zama na zartsi ya gagara shayuwa kuma ya ƙi amfani wajen ban-ruwa, to amma sai ya ni’imta su da ruwa mai daɗin kwankwaɗa mai amfani a gare su da kuma dabbobinsu da shuke-shukensu, to don me ba za su riƙa gode wa Allah ba, su yi imani da cikar Ƙudurarsa a kan komai har da tashin matattu don yi musu hisabi? <b>Na bakwai </b>, ya sake jan hankalinsu game da wutar da suke kunnawa domin buƙatunsu daban-daban, ya tambaye su, ko shin su ne suka halicci bishiyar da ake hura wutar da ita, ko kuma Allah ne ya tausaya musu ya fito musu da ita? Su dai sun tabbatar ba aikinsu ba ne, aikin Allah ne shi kaɗai, to me ya hana su gaskata Ƙudurarsa ta sake dawo da halittu bayan mutuwa? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, shi ne ya sanya wannan wutar ta duniya ta zama tunatarwa game da wutar lahira, kuma ta kasance mai amfani ga matafiya daga cikinsu a nan duniya. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wutarku ta duniya kaso ɗaya ne daga cikin kaso saba’in na wutar Jahannama, kuma sai da aka nutsar da ita a cikin kogi sau biyu, ba don haka ba da Allah bai sanya wani amfani a cikinta ga wani ba.” [Ahmad #7327]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa da ya tsarkake Ubangijinsa mai girma daga duk wani abu da bai dace da shi ba.
۞فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ
Open ayah 56:75To ina yin rantsuwa da mafaɗar taurari.
وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٞ لَّوۡ تَعۡلَمُونَ عَظِيمٌ
Open ayah 56:76Lalle ita kuwa rantsuwa ce mai girma, da kuna ganewa.
إِنَّهُۥ لَقُرۡءَانٞ كَرِيمٞ
Open ayah 56:77Lalle shi Alƙur’ani ne mai girma.
فِي كِتَٰبٖ مَّكۡنُونٖ
Open ayah 56:78A cikin littafi abin kiyayewa (daga wani sauyi).
لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُطَهَّرُونَ
Open ayah 56:79Babu mai taɓa shi sai tsarkakakku.
تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 56:80Saukakke ne daga Ubangijin talikai.
أَفَبِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَنتُم مُّدۡهِنُونَ
Open ayah 56:81Yanzu wannan zance kuke ƙaryatawa?
وَتَجۡعَلُونَ رِزۡقَكُمۡ أَنَّكُمۡ تُكَذِّبُونَ
Open ayah 56:82Kuke kuma sanya (godiyar) arzikinku shi ne ku riƙa ƙaryatawa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da kafirai cewa Alƙur’ani mai girma gaskiya ne, inda ya yi musu rantsuwa da wuraren taurari da mafaɗarsu. Ya tabbatar musu cewa, lalle wannan rantsuwa ce mai girma, domin taurari da tafiyarsu a sararin sama abu ne da ke cike da ayoyi da darussa masu ɗimbin yawa. Ya kuma yi wannan rantsuwa ne don ya tabbatar musu cewa, abin da suke ji ana karanta musu Alƙur’ani ne mai girma, domin ya ƙunshi alheri mai yawa, da ɗimbin ilimi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da shi da farko a cikin Lauhul Mahafuzu wanda aka kiyaye shi babu mai ganin sa. Babu kuma mai taɓa wannan Alƙur’ani sai mala’iku tsarkakakku, watau waɗanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsarkake su daga dukkan zunubai da aibubbuka. Alƙur\'ani saukakke ne daga Ubangijin halittu zuwa ga Annabi Muhammadu (ﷺ) Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi kafirai cewa, yanzu wannan Alƙur’ani shi suke ƙaryatawa suna faɗar maganganu marasa kyau a kansa? Sannan maimakon su gode wa Allah bisa arzikin da ya ba su sai su riƙa ƙaryata shi, suna danganta wasu ni’imominsa kamar ruwan sama, zuwa ga wasu halittunsa, kamar taurari, suna cewa tauraro kaza ne ya yi musu ruwa? An karɓo daga Zaid ɗan Khalid Al-Juhami (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya yi mana sallar asuba a Hudaibiyya bayan an kwana ana ruwa. Bayan ya gama salla sai ya fuskanto mutane ya ce musu: “Shin kun san abin da Ubangijinku ya faɗa?” Sai suka ce: “Allah da Manzonsa ne mafiya sani.” Sai ya ce: “Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce: “Daga cikin bayina wani ya wayi gari yana mai imani da ni wani kuma yana kafirce mini. Amma wanda ya ce: “An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarsa, to wannan mai imani ne da ni; wanda kuma ya ce: “An yi mana ruwa da tauraro kaza da kaza, to wannan ya kafirce mini, ya kuma yi imani da tauraro.” [Bukhari #846 da Muslim #17061].
فَلَوۡلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلۡحُلۡقُومَ
Open ayah 56:83Me ya hana idan (rai) ya isa maƙogwaro.
وَأَنتُمۡ حِينَئِذٖ تَنظُرُونَ
Open ayah 56:84Ku kuma a lokacin kuna kallo.
وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُبۡصِرُونَ
Open ayah 56:85Mu ne kuwa Muka fi ku kusanci da shi, sai dai kuma ba kwa gani.
فَلَوۡلَآ إِن كُنتُمۡ غَيۡرَ مَدِينِينَ
Open ayah 56:86Me ya hana idan da kun zamanto ba waɗanda za a tasa ba ne.
تَرۡجِعُونَهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 56:87Ku dawo da shi (ran) mana idan kun kasance masu gaskiya.
فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ
Open ayah 56:88Amma kuma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta.
فَرَوۡحٞ وَرَيۡحَانٞ وَجَنَّتُ نَعِيمٖ
Open ayah 56:89To (sakamakonsa) hutu ne da arziki mai daɗi, da kuma Aljannar ni’ima.
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 56:90Idan kuma ya kasance daga ma’abota hannun dama ne.
فَسَلَٰمٞ لَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 56:91To aminci ya tabbata a gare ka don zamanka na hannun dama.
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ
Open ayah 56:92Idan kuwa ya kasance daga masu ƙaryatawa ne ɓatattu.
فَنُزُلٞ مِّنۡ حَمِيمٖ
Open ayah 56:93To kaɓaki ne na tafasasshen ruwa (sakamakonsa).
وَتَصۡلِيَةُ جَحِيمٍ
Open ayah 56:94Da kuma shiga wutar Jahannama.
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلۡيَقِينِ
Open ayah 56:95Lalle wannan (bayani na cikin wannan Surar) shi ne haƙiƙanin gaskiya.
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 56:96To ka yi tasbihi da tsarkake sunan Ubangijinka mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalanci kafirai masu ƙaryata zuwan ranar alƙiyama da hisabi a kan ayyukan bayi, da cewa me ya hana su lokacin da suka ga ɗayansu yana kakarin mutuwa, ransa ya zo maƙoshi zai fita, me ya sa ba za su hana ran fita ba, su dawo da shi cikin jikin wannan ɗan’uwa nasu, idan har su masu gaskiya ne cewa, babu tashi bayan mutuwa, kuma babu hisabi? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, a lokacin ya fi su kusanci da wannan ɗan’uwa nasu da iliminsa da Ƙudurarsa da mala’ikunsa, kawai dai ba sa ganin mala’ikun ne. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda mutane za su kasu kashi uku yayin da suka zo mutuwa. <b>Na farko </b>, idan mamacin yana daga cikin bayin Allah ne masu rige-rige wajen aikin alheri, makusanta ga Allah, waɗanda suka aikata abubuwan da aka wajabta musu har da mustahabbi, suka guje wa abubuwan da aka hana su har ma da makaruhi, to waɗannan suna da sakamakon hutu babu wahala tare da su da kuma arziki mai daɗi da rahama da gidan Aljanna. Za su sami duk ni’imar da suke sha’awa a cikinta. <b>Na biyu </b>, idan kuwa mamacin yana daga ma’abota hannun dama ne, waɗanda suka aikata wajibi suka kuma guje wa haramun, amma suka samu gazawa a wasu al’amuransu na addini ko na rayuwa, to waɗannan za a riƙa faɗa wa ɗayansu cewa amincin ya tabbata a gare shi, yana cikin ma’abota hannun dama. <b>Na uku </b>, idan mamacin yana daga cikin masu ƙaryata abin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo da shi, watau ɓatattu waɗanda suka kauce wa tafarki madaidaici, to kaɓakin da za a tare shi da shi, shi ne tafasasshen ruwa da ƙonawa da wutar Jahannama. A ƙarshen Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa wannan labari da yake ba shi tabbas shi ne haƙiƙanin gaskiya da babu sofanen shakka a cikinta, don haka ya umarce shi da ya tsarkake sunan Ubangijinsa mai girma da yi masa tasbihi.