الحديد
Al-Hadid
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 57:1Abin da yake cikin sammai da ƙasa ya yi tasbihi ga Allah; Shi ne kuma Mabuwayi, Mai hikima.
لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Open ayah 57:2Mulkin sammai da ƙasa nasa ne; Yana rayawa, Yana kuma kashewa; kuma Shi Mai iko ne a kan komai.
هُوَ ٱلۡأَوَّلُ وَٱلۡأٓخِرُ وَٱلظَّٰهِرُ وَٱلۡبَاطِنُۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ
Open ayah 57:3Shi ne Na farko kuma Na ƙarshe, kuma Bayyananne kuma Ɓoyayye; Shi kuma Masanin komai ne.
هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يَعۡلَمُ مَا يَلِجُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا يَخۡرُجُ مِنۡهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا يَعۡرُجُ فِيهَاۖ وَهُوَ مَعَكُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Open ayah 57:4Shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa cikin kwana shida, sannan Ya daidaitu a kan Al’arshi. Yana sane da abin da yake shiga cikin ƙasa da abin da yake fitowa daga cikinta, da kuma abin da yake saukowa daga sama da abin da yake hawa cikinta; kuma Shi Yana tare da ku a duk inda kuka kasance. Allah kuwa Mai ganin duk abin da kuke aikatawa ne.
لَّهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ
Open ayah 57:5Mulkin sammai da ƙasa nasa ne. Kuma ga Allah ake mayar da al’amura.
يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِۚ وَهُوَ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Open ayah 57:6Yana shigar da dare cikin rana, Yana kuma shigar da rana cikin dare. Kuma Shi Masanin abubuwan da suke cikin ƙiraza ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da sanar da bayinsa cewa, duk abubuwan da suke cikin sammai da na ƙasa sun tsarkake shi da yi masa tasbihi, kuma shi ne Mabuwayi wanda babu mai iya ja da shi, mai hikima a cikin halittarsa da shari’arsa da ƙaddararsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mulkin sammai da ƙasa duka nasa ne, shi ne yake raya wanda ya ga damar rayawa, yake kuma kashe duk wanda ya ga damar kashewa, babu mai iya hana shi aikata abin da ya so, kuma shi mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi. Sai kuma ya bayyana cewa, shi ne na farko, watau babu wani abu gabaninsa, shi ne kuma na ƙarshe, watau babu wani abu bayansa, shi ne kuma bayyananne, watau babu wani abu sama da shi, kuma shi ne ɓoyayye, watau babu wani abu da ya fi shi ɓuya, kuma shi masanin komai ne na sarari da na ɓoye. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Faɗima (Allah ya kara mata yarda), ta zo wajen Manzon Allah (ﷺ) tana roƙon sa ya ba ta hadima, sai ya ce mata: “Ki ce: Ya Allah, Ubangijin sammai bakwai, kuma Ubangijin Al’arshi mai girma, kuma Ubangijinmu, kuma Ubangijin komai, wanda ya saukar da Attaura da Linjila da Alƙur’ani, wanda ya fitar da ƙwaya da ƙwallon dabino, ina neman tsarinka daga sharrin duk wani abu wanda kai ne kake riƙe da makwarkwaɗarsa. Kai ne na farko babu wani abu gabaninka, kuma kai ne na ƙarshe babu wani abu bayanka, kai ne kuma bayyananne babu wani abu sama da kai, kai ne kuma ɓoyayye babu wani abu da ya fi ka ɓuya, ka biya mana bashi, ka kuma raba mu da talauci.” [Muslim #2713]. A wata ruwayar: Annabi (ﷺ) ya kasance yana karanta wannan addu’ar yayin da ya zo kwantawa barci. [Muslim #2713]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi ne ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, ya fara ranar Lahadi ya kuma ƙare ranar Juma’a, duk kuwa da cewa yana da ikon halittar su cikin ƙasa da ƙiftawar ido. Sannan ya daidaita a kan Al’arshi daidaiton da ya dace da shi. Yana sane da duk abin da yake shiga cikin ƙasa na ruwan sama da irin shuka da makamantansu, yana kuma sane da abin da yake fita daga cikin ƙasa, kamar tsirrai da ma’adanai da makamantansu. Yana kuma sane da duk abin da yake saukowa daga sama, kamar ruwa da wahayi da sauransu, yana kuma sane da abin da yake hawa zuwa sama, kamar mala’iku da ayyukan bayinsa da rayukansu. Ya tabbatar wa da bayinsa cewa yana tare da su a duk inda suke, watau da iliminsa, babu wani abu da yake ɓuya a gare shi, yana kuma ganin duk abin da suke aikatawa, zai kuma yi musu sakayya a kansa, domin kuwa duk mulkin sammai da ƙasa nasa ne shi kaɗai, kuma zuwa gare shi ne za a mayar da duk al’amura, inda zai yi wa bayinsa hisabi a ranar alƙiyama, ya saka wa kowa gwargwadon aikinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sake tabbatar da cikar Ƙudurarsa da yalwar iliminsa, da cewa shi ne yake shigar da dare cikin yini don tsawonsa ya ragu shi kuma yini ya ƙara tsawo, wani lokaci kuma ya shigar da yini cikin dare domin tsawonsa ya ragu shi kuma dare ya ƙaru. Allah masanin abin da yake cikin ƙirazan bayinsa ne, babu abin da za su iya ɓoye masa.
ءَامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَأَنفِقُواْ مِمَّا جَعَلَكُم مُّسۡتَخۡلَفِينَ فِيهِۖ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡ وَأَنفَقُواْ لَهُمۡ أَجۡرٞ كَبِيرٞ
Open ayah 57:7Ku yi imani da Allah da kuma Manzonsa, ku kuma ciyar daga abin da ya sanya ku wakilai a kansa, to waɗanda suka yi imani daga cikinku, suka kuma ciyar suna da lada mai girma.
وَمَا لَكُمۡ لَا تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلرَّسُولُ يَدۡعُوكُمۡ لِتُؤۡمِنُواْ بِرَبِّكُمۡ وَقَدۡ أَخَذَ مِيثَٰقَكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 57:8Kuma me ya same ku ne ba kwa yin imani da Allah, alhali kuwa Manzo yana kiran ku don ku yi imani da Ubangijinku, haƙiƙa kuma kun yi masa alƙawari, in dai kun kasance muminai.
هُوَ ٱلَّذِي يُنَزِّلُ عَلَىٰ عَبۡدِهِۦٓ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖ لِّيُخۡرِجَكُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ بِكُمۡ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 57:9Shi ne Wanda Yake saukar da ayoyi bayyanannu ga Bawansa don Ya fitar da ku daga duffai zuwa haske. Kuma lalle Allah Mai tausayi ne, Mai rahama a gare ku.
وَمَا لَكُمۡ أَلَّا تُنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلِلَّهِ مِيرَٰثُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَا يَسۡتَوِي مِنكُم مَّنۡ أَنفَقَ مِن قَبۡلِ ٱلۡفَتۡحِ وَقَٰتَلَۚ أُوْلَٰٓئِكَ أَعۡظَمُ دَرَجَةٗ مِّنَ ٱلَّذِينَ أَنفَقُواْ مِنۢ بَعۡدُ وَقَٰتَلُواْۚ وَكُلّٗا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ
Open ayah 57:10Kuma me ya same ku ne da ba za ku ciyar saboda Allah ba, alhali kuwa gadon sammai da ƙasa na Allah ne? Wanda ya ciyar daga cikinku tun kafin buɗe (Makka) ya kuma yi yaƙi, ba zai zama daidai (da wanda bai yi) ba. Waɗannan su suka fi girman daraja a kan waɗanda suka ciyar daga bisani, suka kuma yi yaƙi. Amma kuma kowannensu Allah Ya yi masa alƙawarin Aljanna. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne.
مَّن ذَا ٱلَّذِي يُقۡرِضُ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا فَيُضَٰعِفَهُۥ لَهُۥ وَلَهُۥٓ أَجۡرٞ كَرِيمٞ
Open ayah 57:11Wane ne wanda zai bai wa Allah rance kyakkyawan rance, sai Ya ninka masa shi, alhali yana kuma da lada mai girma? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su yi imani da shi su kuma yi imani da Manzonsa, su kuma ciyar daga dukiyar da ya sanya su masu kula da ita, watau kamar wakilai da ya umarce su su juya ta yadda ya dace da shari’arsa. Sannan ya sanar da su cewa duk waɗanda a cikinsu suka yi imani da shi, suka kuma bayar da dukiyoyinsu saboda shi, to suna da gwaggwaɓan lada a wurinsa, watau gidan Aljanna. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su cewa me ya hana su su yi imani da Allah alhalin ga Manzonsa ya aiko musu yana kiran su zuwa gare shi, don su yi imani da Ubangijinsu (Mai tsarki da daukaka), ga shi kuma ya yi alƙawari da su lokacin da ya fito da su daga tsatson iyayensu cewa za su yi imani, don haka su yi imani mana idan har su muminai ne da gaske. Wannan shi ne tafisirin Mujahid alamajirin Ibn Abbas, kuma shi ne zaɓin Ibn Jarir. Ibnu Kasir kuwa yana ganin ma\'anar alƙawari da su a nan shi ne mubaya\'a da suka yi wa Manzon Allah (ﷺ) cewa za su ji maganarsa su yi masa ɗa\'a. Don haka a nan ana nufin tunatar da su wannan alƙawari ne da suka ɗauka, da nuna musu lalle su ci gaba da riƙe shi da bin sa sau-da-ƙafa. Sai kuma ya bayyana musu wata babbar ni\'ima da ya yi musu da cewa, shi ne ya saukar wa Bawansa Muhammadu (ﷺ) ayoyi bayyanannu, domin ya fitar da su daga duffan kafirci da jahilci da son zuciya, zuwa ga hasken imani da ilimi da shiriya. Kuma lalle shi mai tausayi ne da rahama gare su yayin da ya yi musu tagomashin aiko musu da Manzo don ya zama mai kira da shiryarwa a gare su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake nuna musu cewa, ba su da wata hujja da za ta hana su taimaka wa addininsa da dukikoyinsu, domin saninsu ne cewa, duk wata dukiya da suke taƙama da ita tasa ce, domin duk abin da yake sammai da na ƙasa gadonsa ne, watau mallakarsa ne duka, su kawai ajiya ce ya ba su ta ɗan lokaci daga baya za su dawo gare shi baki ɗaya. Sai kuma ya bayyana musu falalar ciyar da dukiya lokacin tsananin buƙata a kan ciyar da ita lokacin ƙarancin buƙata. Ya tabbatar musu cewa, sahabban da suka yi imani tun farko suka ciyar da dukiyoyinsu suka yi yaƙi tare da Manzonsa (ﷺ) tun kafin a yi Fat’hu Makka, watau a shekara ta takwas, sun fi waɗanda suka yi imani daga bayan Fat’hu Makka suka yi yaƙi tare da Manzon Allah (ﷺ), amma dukkansu Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu alƙawarin gidan Aljanna, kuma shi masanin abin da suke aikatawa ne, zai yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa mai kyau ko mummuna. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake kwaɗaitar da su a kan ciyar da dukiyoyinsu don taimakon Musulunci da Musulmi, ya kira su a kan su ba shi rance mai kyau shi kuma zai ninninka musu sakamako, kuma a ranar alƙiyama suna da wani sakamako mai girma, watau Aljanna.
يَوۡمَ تَرَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ يَسۡعَىٰ نُورُهُم بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَبِأَيۡمَٰنِهِمۖ بُشۡرَىٰكُمُ ٱلۡيَوۡمَ جَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 57:12(Ka tuna) ranar da za ka ga muminai maza da muminai mata haskensu yana tafiya ta gabansu da ta damansu, (ana cewa da su): “Albishirinku a wannan rana (su ne) gidajen Aljanna da ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, kuna masu dawwama a cikinsu. Wannan shi ne rabo mai girma.”
يَوۡمَ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتُ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱنظُرُونَا نَقۡتَبِسۡ مِن نُّورِكُمۡ قِيلَ ٱرۡجِعُواْ وَرَآءَكُمۡ فَٱلۡتَمِسُواْ نُورٗاۖ فَضُرِبَ بَيۡنَهُم بِسُورٖ لَّهُۥ بَابُۢ بَاطِنُهُۥ فِيهِ ٱلرَّحۡمَةُ وَظَٰهِرُهُۥ مِن قِبَلِهِ ٱلۡعَذَابُ
Open ayah 57:13A ranar da munafukai maza da munafukai mata za su riƙa cewa da waɗanda suka yi imani: “Ku saurara mana mu ɗan ɗosani haskenku.” Aka ce (da su): “Ku koma bayanku (watau duniya) sai ku nemi haske.” sai aka raba tsakaninsu da katanga wadda take da wata ƙofa, daga cikinta akwai rahama, bayanta kuma azaba ce (take bugowa) daga gare ta.
يُنَادُونَهُمۡ أَلَمۡ نَكُن مَّعَكُمۡۖ قَالُواْ بَلَىٰ وَلَٰكِنَّكُمۡ فَتَنتُمۡ أَنفُسَكُمۡ وَتَرَبَّصۡتُمۡ وَٱرۡتَبۡتُمۡ وَغَرَّتۡكُمُ ٱلۡأَمَانِيُّ حَتَّىٰ جَآءَ أَمۡرُ ٱللَّهِ وَغَرَّكُم بِٱللَّهِ ٱلۡغَرُورُ
Open ayah 57:14(Munafukan) suna kiran su cewa: “Yanzu ba mu kasance a tare da ku ba ne?” Suka ce: “Haka ne, sai dai ku kuma kun fitini kanku (da munafunci) kuka kuma saurari (aukuwar mummunan abu ga muminai), kuka kuma yi shakka (game da addini), burace-burace kuma suka ruɗe ku har mutuwa ta zo, Shaiɗan kuma ya ruɗe ku game da Allah.
فَٱلۡيَوۡمَ لَا يُؤۡخَذُ مِنكُمۡ فِدۡيَةٞ وَلَا مِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ مَأۡوَىٰكُمُ ٱلنَّارُۖ هِيَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ
Open ayah 57:15“To a yau ba za a karɓi wata fansa ba daga gare ku da kuma daga waɗanda suka kafirta. Makomarku wuta; ita ce ta kamace ku, makoma kuwa ta munana.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana falalar waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari da matsayinsu a ranar alƙiyama ranar da muminai maza da mata za su riƙa tafiya haske ya kewaye su ta gabansu da ta damansu, kowanne gwargwadon imaninsa da kyawawan ayyukansa, ana kuma yi musu albishir a wannan ranar da rabauta da gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, za su shige su kuma su dawwama a cikinsu har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa wannan shi ne babban rabo da babu kamarsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon munafukai maza da mata a wannan ranar yayin da za su riƙa roƙon waɗanda suka yi imani cewa, su ɗan saurara musu don su ɗosani wani abu na haskensu wanda zai taimaka musu su tsallake Siraɗi, domin kowannensu ya samu kansa a cikin duhu ƙirin saboda munanan ayyukansu da suka yi a duniya. To a nan ne za a ba su amsa mai cike da izgili da ban haushi, da cewa su koma can bayansu su nemo haskensu, tare da cewa sun sani ba wani haske da suka bari a baya. Sannan don a ƙara cire musu tsammanin samun biyan wata buƙata tasu sai a sanya shamaki na wata doguwar katanga tsakaninsu da muminai, don su ƙara tabbatar da cewa, abin da suke nema ba zai taɓa samuwa a gare su ba har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta wannan katangar da cewa tana da wata ƙofa daga cikinta, watau ɓangaren muminai rahama ce, bayanta kuma, watau ɓangaren munafukai matsananciyar azaba ce. A nan ne munafukai za su marairaice wa muminai suna yi musu magiya da cewa, ashe ba tare suke a duniya ba, watau su ma ai suna faɗar ‘La’ilaha illallahu ’ suna kuma yin salla suna yin azumi har ma akan fita jihadi tare da su, amma suka ƙyale su a cikin wannan azabar? Sai muminai su amsa musu da cewa, haka ne suna tare da su a duniya, amma kuma ai ba a nan take ba; akwai bambanci babba a tsakaninsu, domin su sun fitini kansu da munafurci sun hallaka, sannan kuma sun yi sauraron zuwan lokacin da za a cinye muminai da yaƙi don su kuma su fito sarari su bayyana kafircinsu. Hakanan kuma sun yi shakka game da samun nasarar muminai da kuma tashi bayan mutuwa; wannan shi ya jawo burace-buracen ƙarya suka ruɗe su, sai ga shi ba su ankara ba har mutuwa ta zo musu, Shaiɗan kuma ya yi nasara a kansu ya yaudare su da ruɗinsa dangane da sha’anin Allah. Muminai suka bayyana wa munafukai miyagun halayensu na duniya waɗanda suka jawo musu matsanancin halin da suka tsinci kansu a cikinsa a ranar alƙiyama. Suka kuma tabbatar musu cewa, a ranar babu wata fansa da za a karɓa daga wajensu ko daga wajen kafirai waɗanda suka bayyana kafircinsu a fili ballantana har su sami kuɓuta daga azabar Allah, don haka makomarsu su da kafiran sarari ita ce wutar Jahannama, kuma da man ita ce ta fi cancanta da su, to tir da wannan mummunar makoma da suka tsinci kawunansu a ciki.
۞أَلَمۡ يَأۡنِ لِلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَن تَخۡشَعَ قُلُوبُهُمۡ لِذِكۡرِ ٱللَّهِ وَمَا نَزَلَ مِنَ ٱلۡحَقِّ وَلَا يَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلُ فَطَالَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَمَدُ فَقَسَتۡ قُلُوبُهُمۡۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ
Open ayah 57:16Yanzu lokaci bai yi ba ga waɗanda suka yi imani zukatansu su yi taushi da zikirin Allah da kuma abin da Ya saukar na gaskiya, kuma kada su zama kamar waɗanda aka bai wa Littafi tun gabaninsu, sai lokaci ya tsawaita a gare su, sai zukatansu suka ƙeƙashe; mafiya yawa kuma daga cikinsu fasiƙai ne?
ٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ قَدۡ بَيَّنَّا لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
Open ayah 57:17Ku sani cewa Allah Yana raya ƙasa bayan mutuwarta. Haƙiƙa Mun bayyana muku ayoyi don ku hankalta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin muminai da tsawatar musu game da sakaci wajen ambaton sa, da cewa, ashe lokaci bai yi ba da ya kamata zukatansu su yi taushi su nutsu da ambaton Allah da ayoyin Alƙur’ani da suka sauka masu ɗauke da kyakkyawan alƙawari ko narkon azaba, kada kuma su yarda su zama kamar Yahudawa da aka ba wa littafin Attaura ko Nasara da aka ba wa littafin Linjila aka umarce su da yin aiki da su, amma kuma bayan ɗaukar tsawon lokaci da rabuwa da annabawansu sai suka yi watsi da waɗannan littattafai suka manta da ambaton Allah da shari’arsa, har zukatansu suka ƙeƙashe, yawancinsu suka wayi gari sun zama fasiƙai masu saɓa wa Allah (Mai tsarki da daukaka)? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu yadda sauraron wa’azi da karatun Alƙur’ani yake yin tasiri a zukata kamar yadda ruwan sama yake yin tasiri idan ya sauka a kan ƙeƙasasshiyar ƙasa, yake raya ta bayan ta mutu. To hakanan Alƙur’ani yake raya zukata bayan sun ƙeƙashe. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, yana bayyana musu ayoyinsa ne masu nuna cikar Ƙudurarsa da Kaɗaitakarsa don mutane su hankalta su ɗauki izina da darasi daga gare su.
إِنَّ ٱلۡمُصَّدِّقِينَ وَٱلۡمُصَّدِّقَٰتِ وَأَقۡرَضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا يُضَٰعَفُ لَهُمۡ وَلَهُمۡ أَجۡرٞ كَرِيمٞ
Open ayah 57:18Lalle masu yin sadaka maza da masu yin sadaka mata, suka kuma bai wa Allah kyakkyawan rance, to za a ninninka musu shi, suna kuma da wani ladan mai daraja.
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦٓ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلصِّدِّيقُونَۖ وَٱلشُّهَدَآءُ عِندَ رَبِّهِمۡ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ وَنُورُهُمۡۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 57:19Waɗanda kuma suka yi imani da Allah da manzanninsa, waɗannan su ne siddiƙai; shahidai kuma suna da ladansu da haskensu a wurin Ubangijinsu; waɗanda kuwa suka kafirta suke kuma ƙaryata ayoyinmu, to waɗannan su ne ‘yan (wutar) Jahimu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana falalar maza da mata masu yawan sadaka da dukiyoyinsu don Allah don taimakon addininsu da ‘yan’uwansu muminai, suka kuma ba wa Allah kyakkyawan rance, to Allah zai ninninka musu ladansu, kowanne kyakkyawan aiki ɗaya za a ninka shi goma irinsa, har zuwa ɗari bakwai, har zuwa ninkin da ba adadi, tare da haka kuma suna da wani lada na karamci a wurin Allah, watau gidan Aljanna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa gaba ɗayansu, to waɗannan su ne siddiƙai a wurin Allah, watau matsayinsu shi ne yake biye da matsayin annabawa. Su kuma shahidai, watau waɗanda suka yi mutuwar shahada wajen ɗaukaka kalmar Allah, to suna da ladansu na karramawa da Ubangijinsu ya tanadar musu, suna da kuma haskensu wanda zai riƙa tafiya ta gabansu da ta damansu a ranar alƙiyama. Waɗanda kuma suka kafirce wa Allah da Manzonsa, suka kuma ƙaryata ayoyin da ya saukar wa Manzonsa, to waɗannan su ne ‘yan wuta waɗanda za su shige ta ranar alƙiyama su kuma dawwama a cikinta har abada babu ranar fita.
ٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا لَعِبٞ وَلَهۡوٞ وَزِينَةٞ وَتَفَاخُرُۢ بَيۡنَكُمۡ وَتَكَاثُرٞ فِي ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَوۡلَٰدِۖ كَمَثَلِ غَيۡثٍ أَعۡجَبَ ٱلۡكُفَّارَ نَبَاتُهُۥ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَىٰهُ مُصۡفَرّٗا ثُمَّ يَكُونُ حُطَٰمٗاۖ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٞ شَدِيدٞ وَمَغۡفِرَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٞۚ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ
Open ayah 57:20Ku sani cewa, ita dai rayuwar duniya ba wata aba ba ce sai wasa da sharholiya da ƙyale-ƙyale da kuma fariya a tsakaninku da takara wajan nuna yawan dukiya da ‘ya’yaye; ta yi kama da ruwan saman da tsirransa suka bai wa manoma sha’awa, sannan duk ya bushe, sai ka gan shi fatsi-fatsi, sannan kuma ya zama dudduga; a lahira kuwa akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da kuma yarda. Rayuwar duniya ba komai ba ce sai jin daɗi mai ruɗi.
سَابِقُوٓاْ إِلَىٰ مَغۡفِرَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا كَعَرۡضِ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ أُعِدَّتۡ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۚ ذَٰلِكَ فَضۡلُ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 57:21Ku yi rige-rige zuwa neman gafara daga Ubangijinku da Aljanna wadda faɗinta kamar faɗin sammai da ƙasa yake, an tanade ta don waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa. Wannan falalar Allah ce da Yake ba da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuwa Ma’abocin falala ne, Mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana matsayin duniya ne da rayuwar mutanenta, inda ya nuna cewa, abin da yake cikinta bai wuce wasa da sharholiya ba waɗanda suke ɗauke hankalin mutum daga tunanin wani abu mai muhimmanci a rayuwarsa, kuma ado ce da mutanen cikinta suke kwalliya da ita, suke fama wajen ƙawata tufafinsu da abincinsu da abin shansu da ababan hawansu da gidajensu; kuma abar fariya ce a tsakanin mutanen cikinta wajen nuna isa da mulki da matsayi da jin daɗi; kuma takara ce a tsakaninsu wajen tara dukiya da ‘ya’ya. Waɗannan kuwa duk wasu abubuwa ne masu saurin ƙarewa, a wayi gari kamar ba a taɓa ganin su ba. Wannan ya yi kama da ruwan sama mamako da ya sauko ya mayar da ƙasa koriya shar da shuke-shukenta har tsirranta suka riƙa ba manoma sha’awa, to amma bayan ɗan lokaci ƙanƙani sai ga shi tsirran sun bushe sun yi fatsi-fatsi, sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar da su dudduga, duk kyansu ya gushe amfaninsu ya ƙare. To haka rayuwar duniya take, sai bayan ta haska wa mai neman ta ya hango ƙyale-ƙyalenta, ta buɗe masa ƙofofinta yana samun biyan buƙatunsu daga gare ta, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gusar da ita daga hannunsa ya aiko masa mutuwa ta ɗauke shi daga cikinta ɗungurungum ba abin da zai tsira da shi sai ƙyallen likkafani, don haka mene ne amfanin raja’a a kanta a manta da lahira wadda ta ƙunshi yanayi biyu kacal a cikinta ga duk wani ɗan’adam; ko dai azaba mai tsanani ta wutar Jahannama ga waɗanda suka kafirta ko suka zaɓi rayuwar munafurci, ko kuma gafarar zunubai daga Allah ga bayinsa muminai da samun yardarsa a gidan Aljanna. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, rayuwar duniya ba komai ba ce sai ɗan jin daɗi mai ruɗi wanda ba ya ɗorewa, don haka duk wanda ya zaɓi rayuwar duniya a kan ta lahira to wannan shi ne ya yi asara ya taɓe har abada. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mutane da yin rige-rige zuwa ga ayyuka na ƙwarai waɗanda da su ne za su sami gafarar zunubansu, sannan su samu Aljanna wadda faɗinta kamar faɗin sama da ƙasa ne, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tanade ta ne ga waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan falalarsa ce da yake bayar da ita ga wanda ya ga dama daga bayinsa kuma shi ma’abocin falala mai girma ne ga bayinsa muminai.
مَآ أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مِّن قَبۡلِ أَن نَّبۡرَأَهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ
Open ayah 57:22Babu wani abu da ya samu na musiba a bayan ƙasa, ko kuma ga kawunanku face yana cikin Littafin (Lauhul Mahafuzu) tun kafin Mu halicce ta (watau halittar). Lalle wannan (a wurin Allah) mai sauƙi ne.
لِّكَيۡلَا تَأۡسَوۡاْ عَلَىٰ مَا فَاتَكُمۡ وَلَا تَفۡرَحُواْ بِمَآ ءَاتَىٰكُمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخۡتَالٖ فَخُورٍ
Open ayah 57:23Don kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kada kuma ku yi fariya da abin da Ya ba ku, Allah kuwa ba Ya son duk wani mai taƙama, mai fariya.
ٱلَّذِينَ يَبۡخَلُونَ وَيَأۡمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلۡبُخۡلِۗ وَمَن يَتَوَلَّ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ
Open ayah 57:24(Su ne) waɗanda suke yin rowa, suke kuma umartar mutane da yin rowar. Wanda kuwa ya ba da baya, to lalle Allah Shi Mawadaci ne, Sha-Yabo. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kowane abu yana gudana ne bisa ƙaddararsa mai daɗi ne ko marar daɗi. Ya tabbatar da cewa, babu wata musiba da za ta samu mutane a bayan ƙasa, kamar fari, ko ta same su a kawunansu, kamar annobar rashin lafiya ko mace-mace, face wannan abu yana nan a rubuce tun farko a cikin Littafin Lauhul Mahfuzu tun ma kafin ya halicci halittu, kuma yin haka aiki ne mai sauƙi a wurinsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah ya rubuta abubuwan da ya ƙaddara wa halittunsa tun kafin ya halicci sammai da ƙasa da shekara dubu hamsin. Al’arshinsa kuma yana kan ruwa.” [Muslim #2653 da Ahmad #6579]. Kuma Allah ya bayyana cewa, ya yi haka ne saboda wata hikima, ita ce mutane su gane wannan ƙa’idar tasa, su gina komai nasu a kanta, su ɗora duk wani abu na alheri ko na sharri a kan ma’auninta, don haka ba za su yi baƙin ciki game da abin da ya kuɓuce musu ba, ba kuma za su riƙa fariya da girman kai a kan abin da Allah ya ga dama ya ba su ba, domin ba ya son duk wani mai girman kai mai nuna taƙama da fariya a kan wata ni’ima ta duniya da Allah ya ba shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda suke yin rowa ba sa bayar da haƙƙoƙin Allah daga dukiyar da ya ba su, har ma suna zuga mutane kan su yi rowar abin da yake hannunsu; ya tabbatar da cewa, waɗannan su ne asararru, domin duk wanda ya bijire wa ɗa’ar Allah ya juya wa umarninsa baya, to ba zai cutar da Allah da komai ba, sai dai kansa kawai ya cutar, domin Allah mai cikakkiyar wadata ne ba ya da buƙatar ɗa’ar bayinsa, kuma shi sha-yabo ne a kowanne hali.
لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَنزَلۡنَا مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَنزَلۡنَا ٱلۡحَدِيدَ فِيهِ بَأۡسٞ شَدِيدٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥ وَرُسُلَهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٞ
Open ayah 57:25Haƙiƙa Mun aiko manzanninmu da (ayoyi) mabayyana, Muka kuma saukar da littafi da ma’auni a tare da su (manzannin) don mutane su tsaya da adalci; Muka kuma saukar da baƙin ƙarfe wanda a tare da shi akwai tsananin ƙarfi da kuma amfani ga mutane, don kuma Allah Ya bayyanar da wanda yake taimakon Sa da manzanninsa a ɓoye. Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwayi. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ya aiko manzanninsa da hujjoji bayyanannu, ya kuma saukar musu da littattafai waɗanda suka ƙunshi shiriya da shari’a, ya kuma saukar musu da ma’auni don mutane su tsayar da adalci a tsakaninsu, a cikin maganganunsu da ayyukansu da mu’amalolinsu. Ya kuma saukar da baƙin ƙarfe wanda yake akwai tsananin ƙarfi tare da shi, domin da shi mutane suke yin makaman yaƙi, suke kuma amfani da shi a sauran sana’o’insu da ƙere-ƙerensu, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi haka ne don ya bayyana wanda yake taimakon sa shi da manzanninsa a ɓoye, sai ya bayyana shi kowa ya gan shi. Lalle Allah mai ƙarfi ne mabuwayi, babu mai iya karawa da shi ya kai labari.
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحٗا وَإِبۡرَٰهِيمَ وَجَعَلۡنَا فِي ذُرِّيَّتِهِمَا ٱلنُّبُوَّةَ وَٱلۡكِتَٰبَۖ فَمِنۡهُم مُّهۡتَدٖۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ
Open ayah 57:26Haƙiƙa kuma Mun aiko Nuhu da Ibrahimu, Muka kuma sanya annabta da littafi cikin zuriyarsu; To daga cikinsu akwai shiryayyu, masu yawa kuwa daga cikinsu fasiƙai ne.
ثُمَّ قَفَّيۡنَا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم بِرُسُلِنَا وَقَفَّيۡنَا بِعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡإِنجِيلَۖ وَجَعَلۡنَا فِي قُلُوبِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ رَأۡفَةٗ وَرَحۡمَةٗۚ وَرَهۡبَانِيَّةً ٱبۡتَدَعُوهَا مَا كَتَبۡنَٰهَا عَلَيۡهِمۡ إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ رِضۡوَٰنِ ٱللَّهِ فَمَا رَعَوۡهَا حَقَّ رِعَايَتِهَاۖ فَـَٔاتَيۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنۡهُمۡ أَجۡرَهُمۡۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ
Open ayah 57:27Sannan a bayansu Muka biyar da manzanninmu, Muka kuma biyar da Isa ɗan Maryamu Muka kuma ba shi Linjila, kuma Muka sanya jin ƙai da rahama a cikin zukatan waɗanda suka bi shi. Rahbaniyanci kuma su ne suka ƙago shi, ba Mu wajabta musu shi ba, sai dai (Mun wajabta musu) neman yardar Allah, amma ba su kiyaye shi ba kamar yadda ya kamata; sai Muka bai wa waɗanda suka yi imani daga cikinsu ladansu; da yawa kuwa fasiƙai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wasu manyan annabawansa waɗanda ya aiko ya kuma sanya sauran annabawansa suka fito daga zurriyarsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ya aiko Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda shi ne farkon manzannin Allah a bayan ƙasa, ya kuma aiko Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) uban annabawa. Waɗannan manzanni biyu ya zaɓe su ya kuma sanya annabci a cikin zurriyarsu, watau yawancin annabawan da suka zo duniya daga tsatsonsu suka fito. Hakanan kuma ya saukar musu da littattafai. To daga cikin zurriyar waɗannan annabawan biyu akwai wanda yake shiryayye ne yana bin tafarkin Allah miƙaƙƙe, amma kuma da dama daga cikinsu fasiƙai ne masu kauce wa hanya madaidaiciya. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya ci gaba da aiko manzanninsa ɗaya bayan ɗaya zuwa ga al’ummunsu suna yi musu wa’azi, har ya aiko da Annabi Isa ɗan Maryam (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a bayansu, shi ma ya ba shi littafin Linjila, ya kuma haɗa shi da mabiya waɗanda suka yi imani da shi, Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sanya jin tausayi da rahama a cikin zukatansu, suka zamanto masoya juna, masu tausayin juna, amma kuma daga baya sai suka ƙagi bidi’ar Rahbaniyanci a addininsu, suka ƙaurace wa aure da cin daɗaɗan abubuwa na halal, suka haramta wa kawunansu wasu abubuwa da Allah ya halatta musu, tare da cewa ba Allah ne ya nemi hakan daga gare su ba; su ne kawai suka lazimta wa kawunansu yin bidi’a a cikin addininsu. Abin da kawai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ɗora musu shi ne neman yardarsa ta hanyar riƙo da shari’arsa amma sai suka yi watsi da haka. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bai wa waɗanda suka yi imani daga cikinsu ladansu cikakke, amma yawancinsu fasiƙai ne, domin sun bijire wa ɗa’ar Allah sun kuma ƙaryata abin da Annabi Muhammadu (ﷺ) ya zo da shi na Musulunci.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَءَامِنُواْ بِرَسُولِهِۦ يُؤۡتِكُمۡ كِفۡلَيۡنِ مِن رَّحۡمَتِهِۦ وَيَجۡعَل لَّكُمۡ نُورٗا تَمۡشُونَ بِهِۦ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 57:28Ya ku waɗanda suka imani, ku kiyaye dokokin Allah, ku kuma yi imani da Manzonsa, zai ba ku riɓi biyu na rahamarsa, Ya kuma sanya muku haske da za ku riƙa tafiya da shi, kuma Ya gafarta muku. Domin kuwa Allah Mai gafara ne, Mai rahama.
لِّئَلَّا يَعۡلَمَ أَهۡلُ ٱلۡكِتَٰبِ أَلَّا يَقۡدِرُونَ عَلَىٰ شَيۡءٖ مِّن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلۡفَضۡلَ بِيَدِ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 57:29Don ma’abota littafi su san cewa ba su da hannu a falalar Allah, don ko lalle falala a hannun Allah take, Yana ba da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuma Ma’abocin babbar falala ne. A waɗannan ayoyi na ƙarshen Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin muminai waɗanda suka yi imani da Allah, suka kuma yi aiki da shari’arsa, da cewa su kiyaye dokokinsa, su aikata umarninsa, su guji haninsa, su kuma yi imani da Manzonsa (ﷺ); idan sun yi haka zai ninka ladansu kashi biyu; na farko na imaninsu da Annabi (ﷺ), na biyu kuma na imaninsu da manzannin da suka gabata. Sannan kuma zai ba su wani haske wanda zai haskaka musu hanyarsu a duniya su tafi bisa tafarki madaidaici, ya kuma haska musu Siraɗi a ranar alƙiyama, sannan kuma ya gafarta musu zunubbansu ya rufa musu asirinsu a lahira, domin shi mai yawan gafarta zunuban bayinsa ne, mai rahama gare su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ya bayyana wa mutane girman falalarsa da sakamakon da ya tanadar wa muminai riɓi biyu ko ma fiye da haka, don Yahudawa da Nasara su fahimci cewa falalar Allah ba a hannunsu take ba balle su ce za su ba wanda suka ga dama, su hana wanda suka ga dama; falala ta Allah ce, a hannunsa take, yana bayar da ita ga wanda ya ga dama daga cikin bayinsa, domin shi ne ma’abocin babbar falala, mai yin yadda ya ga dama da ita. An karɓo daga Abu Musa (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mutum uku ana ba su ladansu sau biyu; mutumin da ya yi imani da littafin farko ya kuma yi imani da littafin ƙarshe; da mutumin da yake da baiwa ya yi mata tarbiyya ya kuma kyautata tarbiyyarta, sannan ya ‘yanta ta ya aure ta; da bawa abin mallaka wanda ya kyautata bautar Ubangijinsa, ya kuma kyautata wa mai gidansa.” [Bukhari #3011 da Muslim #154].