المجادلة

Al-Mujaadila

The Pleading Woman · Surah 58 · Ayahs: 22 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. قَدۡ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوۡلَ ٱلَّتِي تُجَٰدِلُكَ فِي زَوۡجِهَا وَتَشۡتَكِيٓ إِلَى ٱللَّهِ وَٱللَّهُ يَسۡمَعُ تَحَاوُرَكُمَآۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٌ

    Open ayah 58:1

    Haƙiƙa Allah ya ji zancen wadda take muhawara da kai game da (lamarin) mijinta, tana kuma kai ƙara zuwa ga Allah, Allah kuma Yana jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.

  2. ٱلَّذِينَ يُظَٰهِرُونَ مِنكُم مِّن نِّسَآئِهِم مَّا هُنَّ أُمَّهَٰتِهِمۡۖ إِنۡ أُمَّهَٰتُهُمۡ إِلَّا ٱلَّٰٓـِٔي وَلَدۡنَهُمۡۚ وَإِنَّهُمۡ لَيَقُولُونَ مُنكَرٗا مِّنَ ٱلۡقَوۡلِ وَزُورٗاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٞ

    Open ayah 58:2

    Waɗanda suke yin zihari daga cikinku ga matansu, su ba iyayensu mata ba ne; iyayensu mata su ne waɗanda kawai suka haife su. Lalle kuma su tabbas suna faɗar muguwar magana ne da tsagwaron ƙarya. Kuma lalle Allah tabbas Mai afuwa ne, Mai gafara.

  3. وَٱلَّذِينَ يُظَٰهِرُونَ مِن نِّسَآئِهِمۡ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا قَالُواْ فَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مِّن قَبۡلِ أَن يَتَمَآسَّاۚ ذَٰلِكُمۡ تُوعَظُونَ بِهِۦۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

    Open ayah 58:3

    Waɗanda kuwa suke yin zihari ga matansu sannan suka yi niyyar janye abin da suka faɗa, to sai su ‘yanta wuyaye (bawa namiji ko mace), tun kafin su sadu. Wannan (shi ne abin da) ake yi muku wa’azi da shi. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne.

  4. فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ شَهۡرَيۡنِ مُتَتَابِعَيۡنِ مِن قَبۡلِ أَن يَتَمَآسَّاۖ فَمَن لَّمۡ يَسۡتَطِعۡ فَإِطۡعَامُ سِتِّينَ مِسۡكِينٗاۚ ذَٰلِكَ لِتُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۚ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۗ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٌ

    Open ayah 58:4

    Sannan wanda bai samu ba, to sai ya yi azumin wata biyu a jere tun kafin su sadu; sannan wanda bai sami iko ba sai ya ciyar da miskini sittin. Wannan kuwa don ku yi imani da Allah da Manzonsa. Waɗannan kuma su ne iyakokin Allah. Kafirai kuma suna da azaba mai raɗaɗi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da labarin wata mace mai suna Khaulatu ‘yar Sa’alaba wadda mijinta ya kwatanta ta da mahaifiyarsa, watau ya ce mata: “Ke a wurina kamar bayan mahaifiyata ne.” A zamanin jahiliyya idan mutum ya faɗa wa matarsa irin wannan maganar, to ta haramta a gare shi har abada. Sai Khaulatu ta kawo kukanta wurin Manzon Allah (ﷺ) game da abin da mijinta Ausu ɗan Samit ya yi mata, bayan ga shi ta tsufa suna kuma da ‘ya’ya a tsakaninsu, don haka tana neman ta ji hukuncin Allah a kai, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyi yana tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa lalle ya ji maganar matar nan da take muhawara da shi game da lamarin mijinta Ausu wanda ya yi mata zihari, tana kai kukanta zuwa ga Allah, kuma Allah yana jin muhawararsu da tattaunawarsu, domin yana jin dukkan maganganun bayinsa, yana kuma ganin dukkan ayyukansu, babu abin da yake ɓuya gare shi. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Yabo da godiya sun tabbata ga wanda jinsa ya yalwaci dukkan sautuka. Matar nan mai jayayya ta zo wa Annabi (ﷺ) tana yi masa magana, ni kuma ina wani ɓangare na wannan gida amma ba na jin abin da take faɗa, sai ga shi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “Haƙiƙa Allah ya ji zancen wadda take jayayya da kai game da lamarin mijinta....” har zuwa ƙarshen aya.” [Ahmad #24195 da Nasa’i #3460 da Ibni Maja #188]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mazajen da suka yi zihari ga matayensu har ɗayansu ya ce wa matarsa: “Ke a wurina kamar bayan mahaifiyata ne”, wannan maganar ƙarya ce, domin matayensu ba iyayensu ne ba, iyayensu su ne kawai waɗanda suka tsuguna suka haife su, kuma wannan maganar da suke faɗa mummunar magana ce kuma ƙarya ce tsagwaranta suke shararawa. Don haka masu irin wannan magana su gaggauta tuba zuwa ga Allah, lalle Allah mai afuwa ne mai gafara, don haka ne ma ya shar’anta musu yadda za su yi kaffara don su tsarkake kawunansu daga zunubi. Sannan Allah ya bayyana musu hanayar kaffarar warware abin da suka yi na zihari, watau shi ne su sani cewa bai halatta su koma zuwa ga saduwa da matansu ba har sai sun ‘yanta bawa ko baiwa. Allah ya bayyana cewa, an umarce su ne da wannan hukunci don ya zama tsawatarwa a gare su game da aikata zihari nan gaba, kuma Allah masanin abin da suke aikatawa ne, babu wani aikinsu da bai sani ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, wanda bai samu baiwa ko bawan da zai ‘yanta ba, to sai ya yi azumin wata biyu a jere kafin ya koma ga saduwa da matarsa da ya yi wa zihari. Wanda kuma ya kasa yin azumin, to sai ya ciyar da miskini sittin. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu wannan hukunci ne don su yi imani da cewa Allah ne ya shar’anta musu shi, don haka dole ne su bi umarninsa, su kuma sani cewa duk waɗannan hukunce-hukunce iyakokin Allah ne da ya shata wa bayinsa, ya kuma hana su tsallake su, duk kuma waɗanda suka kafirce wa dokokinsa da hukunce-hukuncensa suna da azaba mai raɗaɗi. An karɓo daga Khaulatu ‘yar Sa’alaba, (Allah ya kara mata yarda), ta ce: “Wallahi a kaina, ni da mijina Ausu ɗan Samit Allah ya saukar da ayoyin farko na ‘Suratul Mujadila ’.” Ta ce: “Na kasance a ƙarƙashinsa, shi kuma ya kasance tsoho mai shekaru har rikicin tsufa ya kama shi; sai wata rana ya shigo gida, sai ya yi wata magana ni kuma na yi masa musu, sai ya yi fushi ya ce mini: “Ke a wurina kamar bayan mahaifiyata kike.” Sai ya fita ya je majalisar abokansa sannan ya dawo gida yana son in amince da shi, ni kuwa na ce sam ba zan amince da shi ba, na rantse masa da cewa hannunsa ba zai ƙara taɓa jikina ba bayan ya faɗi maganar da ya faɗa har sai Allah da Manzonsa (ﷺ) sun yi hukunci a tsakaninmu. Sai na je na samu Manzon Allah na kwashe labarin abin da ya faru tsakanina da mijina na gaya masa. Ban bar wajensa ba har sai da Alƙur’ani ya sauko. Gumi da yake lulluɓe Manzon Allah idan za a yi masa wahayi sai ya lulluɓe shi. Sannan da aka yaye masa, sai ya ce mini: “Ya ke Khaulatu, lalle Allah ya saukar da ayoyin Alƙur’ani game da ke da mutuminki.” Sai ya karanta mini ayoyi huɗu na farkon Surar, sai ya ce mini: “Ki umarce shi ya ‘yanta wuyaye.” (Watau bawa ko baiwa). Sai na ce: “Ya Manzon Allah ba ya da abin da zai ‘yanta.” Sai ya ce: “To ya yi azumin wata biyu a jere.” Sai na ce: “Wallahi ya tsufa tukuf ba zai iya yin azumi ba.” Sai ya ce: “To ya ciyar da miskini sittin sa’i sittin na dabino.” Sai na ce: “Wallahi ba ya da shi.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “To mu za mu taimaka masa da kwandon dabino ɗaya.” Sai na ce: “Ni ma zan taimaka masa da kwando ɗaya na dabino.” Sai ya ce: “Kin yi daidai kuma kin kyauta, ki tafi ki yi sadaka da shi a madadinsa, sannan ki yi wa ɗan baffanki wasiyya da alheri.” Sai ta ce: “Zan yi hakan.” [Ahmad #27319 da Abu Dawud #2214 da 2215, da Ibn Hibban #4279].

  5. إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحَآدُّونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ كُبِتُواْ كَمَا كُبِتَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ وَقَدۡ أَنزَلۡنَآ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖۚ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٞ مُّهِينٞ

    Open ayah 58:5

    Lalle waɗanda suke saɓa wa Allah da Manzonsa an ƙasƙantar da su kamar yadda aka ƙasƙantar da waɗanda suke gabaninsu. Kuma haƙiƙa Mun saukar da ayoyi bayyanannu. Kafirai kuma suna da azaba mai wulaƙantarwa.

  6. يَوۡمَ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوٓاْۚ أَحۡصَىٰهُ ٱللَّهُ وَنَسُوهُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ

    Open ayah 58:6

    A ranar da Allah zai tashe su gaba ɗaya, sannan Ya ba su labarin abin da suka aikata. Allah Ya ƙididdige shi, su kuwa sun manta shi. Allah kuwa Mai ganin kowane abu ne.

  7. أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ مَا يَكُونُ مِن نَّجۡوَىٰ ثَلَٰثَةٍ إِلَّا هُوَ رَابِعُهُمۡ وَلَا خَمۡسَةٍ إِلَّا هُوَ سَادِسُهُمۡ وَلَآ أَدۡنَىٰ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكۡثَرَ إِلَّا هُوَ مَعَهُمۡ أَيۡنَ مَا كَانُواْۖ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُواْ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ

    Open ayah 58:7

    Shin ba ka sani ba ne cewa Allah Ya san abin da yake cikin sammai da abi da yake cikin ƙasa? Babu wata ganawa tsakanin mutum uku da za ta faru sai Shi ne na huɗunsu, da kuma (tsakanin mutum) biyar sai Shi ne na shidansu, da kuma abin da ya kasa (haka) ko ya fi, sai Shi (Allah) Yana tare da su a duk inda suke; sannan Ya ba su labarin abin da suka aikata a ranar alƙiyama. Lalle Allah Masanin komai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan sakamakon waɗanda suke ƙin Allah da Manzonsa (ﷺ), da cewa an ƙasƙantar da su kamar yadda aka ƙasƙantar da al’ummun da suka gabata waɗanda suka nuna ƙiyayyarsu ga Allah da manzanninsa, tare da cewa ba su da wani uzuri na yin hakan. Domin ya saukar da ayoyi bayyanannu ga Manzonsa (ﷺ) amma duk da haka suka kafirce musu, to suna da azaba mai raɗaɗi a ranar alƙiyama, ranar da Allah zai tashe su gaba ɗaya, ba tare da ya bar ko ɗaya daga cikinsu ba, don yi musu sakayya game da ayyukansu, sai ya ba su labarin duk munanan ayyukansu a duniya, ya riga ya ƙididdige musu su, su kuwa sun manta, sai kwatsam su gan su a rubuce a cikin takardun ayyukansu waɗanda ba sa barin aiki ƙarami ko babba sai sun lissafa shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi haka ne domin shi masanin komai ne na ayyukansu, babu abin da zai ɓuya a gare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yalwar iliminsa wanda ya kewaye duk abubuwan da suke cikin sammai da ƙasa, na sarari da na ɓoye, inda ya ja hankalin Manzonsa (ﷺ) da cewa, bai lura da cewa shi Allah yana sane da duk abin da yake cikin sammai da wanda yake ƙasa babba da ƙarami ba, kuma babu mutum uku da za su keɓe suna ganawa face shi ne na huɗunsu da iliminsa; ko mutum biyar face shi ne na shidansu; ko adadinsu ya kasa haka ko ma ya fi haka, face yana tare da su da saninsa a duk inda suke, yana jin maganganunsu, sannan a ranar alƙiyama ya ba su labarin duk abin da suka aikata a duniya, domin shi masanin komai ne. An karɓo daga Abu Musa Al’Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Yayin da Manzon Allah (ﷺ) yake tafiya zuwa yaƙin Khaibara sai mutane suka tsinkayo wani kwazazzabo sai suka ɗaga muryoyinsu suna kabbara suna cewa: “Allahu Akbar La’ilaha Illallahu.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce musu: “Ku sassauta wa kawunanku, domin ba kurma kuke kira ba ko wanda ba ya nan, domin kuna kiran mai ji ne, makusanci, yana nan tare da ku....” [Bukhari #4205 da 2704].

  8. أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ نُهُواْ عَنِ ٱلنَّجۡوَىٰ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا نُهُواْ عَنۡهُ وَيَتَنَٰجَوۡنَ بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَمَعۡصِيَتِ ٱلرَّسُولِۖ وَإِذَا جَآءُوكَ حَيَّوۡكَ بِمَا لَمۡ يُحَيِّكَ بِهِ ٱللَّهُ وَيَقُولُونَ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ لَوۡلَا يُعَذِّبُنَا ٱللَّهُ بِمَا نَقُولُۚ حَسۡبُهُمۡ جَهَنَّمُ يَصۡلَوۡنَهَاۖ فَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 58:8

    Shin ba ka ga waɗanda aka hana su ganawa ba, sannan suke koma wa abin da aka hane su yinsa, suke kuma ganawa a kan saɓo da ta\'addanci, da kuma saɓa wa Manzo? Idan kuma suka zo wurinka sai su gaishe ka da lafazin da Allah bai gaishe ka da shi ba, su riƙa cewa a ransu: “Me ya hana Allah Ya azabtar da mu saboda abin da muka faɗa?” Jahannama ta ishe su, za su shige ta; saboda haka makoma ta munana.

  9. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا تَنَٰجَيۡتُمۡ فَلَا تَتَنَٰجَوۡاْ بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَمَعۡصِيَتِ ٱلرَّسُولِ وَتَنَٰجَوۡاْ بِٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

    Open ayah 58:9

    Ya ku waɗanda suka yi imani, idan za ku gana to kada ku yi ganawar saɓo da ta\'addanci da kuma saɓa wa Manzo. (A maimakon haka) ku gana a kan ayyukan alheri da taƙawa; kuma ku kiyaye dokokin Allah wanda zuwa gare Shi ne za a tattaro ku.

  10. إِنَّمَا ٱلنَّجۡوَىٰ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ لِيَحۡزُنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَيۡسَ بِضَآرِّهِمۡ شَيۡـًٔا إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ 

    Open ayah 58:10

    Ganawar (tasu) kawai daga Shaiɗan take, don ya baƙanta ran waɗanda suka yi imani, ba kuwa zai cuce su da komai ba sai da izinin Allah. Ga Allah ne kuma muminai za su dogara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin Manzonsa (ﷺ) game da mummunar ɗabi’ar Yahudawa ta ganawa da junansu, watau idan sun hango mumini sai su keɓe wuri ɗaya su riƙa yin ƙus-ƙus a tsakaninsu don su jefa masa damuwa a ransa, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana su aikata haka, amma kuma sai suka koma suka ci gaba da aikatawa, sukan kuma gana a tsakaninsu ne da maganganu da suke tattare da saɓon Allah, kamar giba, watau cin naman muminai, ko kuma shirya wani ta’addanci a kan muminai, ko saɓa wa Manzon Allah (ﷺ). Sannan kuma idan sun je wajen Manzon Allah (ﷺ) sai su riƙa gaishe shi da gaisuwar da Allah bai yi masa irinta ba, watau suna ce masa: “Assamu Alaika” ma\'ana: ‘Mutuwa ta tabbata a kanka’, don su nuna cewa Annabi ba gaskiya yake faɗa ba da yake cewa shi Manzon Allah ne, har ma suna cika baki suna tutiya da cewa idan da gaske shi Annabi ne me ya hana Allah ya azabtar da su a kan maganar da suke faɗa masa? To tun da sun faɗa babu kuma abin da ya same su, wannan shi ya tabbatar musu cewa, shi ba Manzon Allah ne ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa, ai talala ce yake yi musu ba ƙyale su ya yi ba, domin wutar Jahannama tana nan tana jiran su, kuma azabarta ta ishe su a kan mummunar kalmar da suke faɗa wa Manzonsa (ﷺ), za su ƙuna da zafinta, to tir da wannan makoma ta wutar Jahannama. An karɓo daga A’isha, (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Wasu Yahudawa sun shigo wajen Annabi (ﷺ) sai suka ce masa: “Assamu Alaika ya baban Alƙasim!” Sai A’isha ta mayar musu da cewa: “Wa Alaikumus Sam!” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce mata: “Ya A’isha, Allah ba ya son alfasha da ƙaƙalo alfasha.” Sai A’isha ta ce: “Ba ka ji su suna cewa: ‘Assamu Alaika’ ba?”Sai ya ce: “Ni ba ki ji abin da nake faɗa ba: ‘Wa Alaikum’ , watau a kanku dai. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar.” [Ibni Abi Hatim, dubi, Suyuɗi, Ad-Durrul Mansur , Juzu’i na 14, shafi na 319 da Bukhari #6024 da Muslim #2165]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Yahudawa suna ce wa Manzon Allah: “Samun Alaika” suna nufin zaginsa, sannan sai su riƙa faɗa a ransu cewa: “Me ya hana Allah ya yi mana azaba saboda abin da muke faɗa?” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar.” [Ahmad #6589 da 7061]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ga muminai waɗanda suka yi imani da shi da kuma Manzonsa (ﷺ) tare da riƙe shari’arsa, ya hana su su kwaikwayi irin ɗabi’ar Yahudawa, watau kada su riƙa ganawa a tsakaninsu da abin da yake saɓon Allah ne ko shirin ta’addanci da saɓa wa Manzonsa (ﷺ); idan har za su yi wata ganawa a tsakaninsu, to su yi ta a kan aikin alheri da taƙawa, watau kiyaye dokokin Allah (Mai tsarki da daukaka), shi ne su bi umarninsa su kuma guji haninsa, domin sun san zuwa gare shi za a tattara su ranar alƙiyama, don ya yi musu hisabi da sakamako a kan ayyukansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wata ganawa wadda ta ƙunshi saɓon Allah da ta’addanci da saɓa wa Manzonsa (ﷺ) to wannan daga Shaiɗan ne, shi ne yake ƙawata wa masoyansa yana ingiza su da aikata hakan, ba don wani dalili ba sai kawai don ya shigar da baƙin ciki a zukatan muminai ya ƙuntata musu. To su sani cewa Shaiɗan duk makircinsa bai isa ya cutar da muminai da wani abu ba sai abin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya riga ya ƙaddara zai same su da izininsa, don haka sai muminai su dogara gare shi shi kaɗai a cikin dukkan al’amarinsu na addininsu da rayuwarsu. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan kun kasance ku uku, to kada biyu su shiga ganawa su bar ɗaya, domin yin haka zai baƙanta masa rai.” [Bukhari #6290 da Muslim #2184].

  11. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا قِيلَ لَكُمۡ تَفَسَّحُواْ فِي ٱلۡمَجَٰلِسِ فَٱفۡسَحُواْ يَفۡسَحِ ٱللَّهُ لَكُمۡۖ وَإِذَا قِيلَ ٱنشُزُواْ فَٱنشُزُواْ يَرۡفَعِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡ وَٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ دَرَجَٰتٖۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

    Open ayah 58:11

    Ya ku waɗanda suka yi imani, idan aka ce da ku: “Ku yalwata a wuraren zama,” to sai ku yalwata, Allah zai yalwata muku; idan kuma aka ce: “Ku tashi (daga wurinku),” to sai ku tashi, Allah zai ɗaga darajojin waɗanda suka yi imani daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilimi. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya koyar da muminai ladabi na yadda za su kyautata wa junansu, musamman a majalisansu, inda ya kira su da siffarsu ta waɗanda suka yi imani da shi da kuma Manzonsa (ﷺ), ya umarce su da cewa, idan wasu da za su halarci majalisa daga baya, sai aka buƙaci a buɗa musu wuraren zama to su buɗa musu, su ma sai Allah ya buɗa musu a rayuwarsu ta duniya da ta lahira. Idan kuma an roƙe su da su tashi domin wani aiki na addini ko wata buƙata da ta taso, to su tashi ba tare da jin wata damuwa ko ƙorafi ba. Allah ya yi musu alkwarin cewa idan sun yi haka zai ɗaga darajojin waɗanda suka yi imani daga cikinsu da waɗanda aka ba su ilimi suka yi aiki da shi, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) masanin komai ne, zai kuma saka wa kowa gwargwadon aikinsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya hana a tashi wani mutum daga mazauninsa sannan wani ya zauna a wurin, amma ku buɗa ku kuma yalwata. Ibn Umar ya kasance ba ya son wani ya tashi daga wurin zamansa don shi ya zauna a wurin. [Bukhari #6270 da Muslim #2177]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada mutum ya tashi wani daga wurin zamansa sannan shi ya zauna a wurin, sai dai su bubbuɗa su kuma yalwata.” [Bukhari #6269 da Muslim #2177]. Waɗannan hadisan suna nuna cewa idan mutum ya riga zama a wuri, to haƙƙinsa ne ya ci gaba da zama har sai ya ga dama ya tashi da kansa, kada a tilasta masa tashi don a zaunar da wani a wurin. Amma wannan ba ya hana idan an roke shi ya yi alfarma ya ba wa wani wurin zamansa ko ya buɗa masa don wata masalahar ya yi haka, domin yin haka shi ne kyautata ladabin zamantakewa da biyayya ga shugabanci wanda wannan ayar take jan hankali a kansa.

  12. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نَٰجَيۡتُمُ ٱلرَّسُولَ فَقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيۡ نَجۡوَىٰكُمۡ صَدَقَةٗۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ لَّكُمۡ وَأَطۡهَرُۚ فَإِن لَّمۡ تَجِدُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

    Open ayah 58:12

    Ya ku waɗanda suka yi imani, idan za ku gana da Manzo, to sai ku gabatar da wata sadaka kafin ganawar taku. Wannan shi ya fi muku alheri da tsarkaka. Sannan idan ba ku samu ba, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai rahama.

  13. ءَأَشۡفَقۡتُمۡ أَن تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيۡ نَجۡوَىٰكُمۡ صَدَقَٰتٖۚ فَإِذۡ لَمۡ تَفۡعَلُواْ وَتَابَ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمۡ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۚ وَٱللَّهُ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 58:13

    Yanzu kun samu damuwa ne ta gabatar da sadaka kafin ganawarku? To idan ba ku aikata haka ba Allah kuma ya karɓi tubarku, to sai ku tsayar da salla, ku ba da zakka, ku kuma bi Allah da Manzonsa. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne. </b>Sahabban Manzon Allah (ﷺ) koyaushe suna matuƙar ƙaunar ganawa da shi, domin suna son jin maganarsa da kuma samun albarkar kusantarsa. Wannan kuwa ya zamanto yana wahalar da Manzon Allah (ﷺ) yana kuma ɗaukar masa lokacinsa da yawa. To shi ne a waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai masu son ganawa da Manzonsa (ﷺ) da su fara gabatar da sadaka ga miskinai kafin ganawar, domin ta haka ne za su sami alheri mai yawa da tsarkaka daga zunubansu da kurakuransu, kuma zukatansu su tsarkaka da ɗa’ar Allah (Mai tsarki da daukaka). To kuma wannan sadakar ba dole ce a kan kowa ba, ta taƙaita ne a kan masu hali, amma miskinai da suke son ganawa da Manzon Allah (ﷺ) kuma ba su sami abin da za su gabatar na sadaka ba, to Allah bai ƙuntata musu ba, ya yafe musu bayar da wannan sadakar; suna iya ganawa da Manzo (ﷺ) ba tare da sun bayar da komai ba, domin shi mai rahama ne ga bayinsa ba ya ɗora musu abin da ya fi ƙarfinsu. To yayin da gabatar da sadaka gabanin ganawa da Manzon Allah (ﷺ) ta yi wa muminai wahala sosai, har sun fara tsoron talauci, saboda yawan sadakar da za su riƙa bayarwa ga msikinai duk sanda suka tashi ganawa da Manzon Allah (ﷺ), sai Allah ya sassauta musu wannan hukuncin, ya ɗauke musu bayar da wannan sadakar ya karɓi tubansu, don haka sai ya umarce su da su tsayar da salla yadda ya dace, su fitar da zakkar dukiyoyinsu, su bi Allah su bi Manzonsa (ﷺ), kuma su tuna cewa Allah masanin duk abubuwan da suke aikatawa ne, zai kuma yi musu sakamako a kansu.

  14. ۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ قَوۡمًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مَّا هُم مِّنكُمۡ وَلَا مِنۡهُمۡ وَيَحۡلِفُونَ عَلَى ٱلۡكَذِبِ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 58:14

    Shin ba ka ga waɗanda suka yi abota da wasu mutane da Allah Ya yi fushi da su ba, su ba cikinku suke ba, ba kuma cikinsu suke ba; su kuma riƙa rantsuwa a kan ƙarya, alhali kuwa su suna sane (da yin ta)?

  15. أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدًاۖ إِنَّهُمۡ سَآءَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 58:15

    Allah Ya tanadar musu azaba mai tsanani, lalle su abin da suke aikatawa ya munana.

  16. ٱتَّخَذُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُمۡ جُنَّةٗ فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

    Open ayah 58:16

    Sun ɗauki rantse-rantsensu su zama garkuwa, sai suka kange hanyar Allah, saboda haka suna da (sakamakon) azaba mai wulaƙantarwa.

  17. لَّن تُغۡنِيَ عَنۡهُمۡ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُهُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔاۚ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

    Open ayah 58:17

    Dukiyoyinsu da ‘ya’yansu ba za su amfanar musu komai ba a wurin Allah. Waɗannan su ne ‘yan wuta; su madawwama ne a cikinta.

  18. يَوۡمَ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ جَمِيعٗا فَيَحۡلِفُونَ لَهُۥ كَمَا يَحۡلِفُونَ لَكُمۡ وَيَحۡسَبُونَ أَنَّهُمۡ عَلَىٰ شَيۡءٍۚ أَلَآ إِنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ

    Open ayah 58:18

    A ranar da Allah zai tashe su baki ɗaya sai su rantse Masa kamar yadda suke rantse muku, su kuma riƙa tsammanin su sun yi wani abu (mai amfani). Ku saurara, lalle kam su ne maƙaryata.

  19. ٱسۡتَحۡوَذَ عَلَيۡهِمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ فَأَنسَىٰهُمۡ ذِكۡرَ ٱللَّهِۚ أُوْلَٰٓئِكَ حِزۡبُ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ أَلَآ إِنَّ حِزۡبَ ٱلشَّيۡطَٰنِ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

    Open ayah 58:19

    Shaiɗan ya ci ƙarfinsu, sai ya mantar da su ambaton Allah. Waɗannan su ne ƙungiyar Shaiɗan. Ku saurara, lalle ƙungiyar Shaiɗan su ne taɓaɓɓu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani mummunan hali na munafukai waɗanda suke abota da Yahudawa waɗanda Allah ya yi fushi da su saboda kafircinsu da laifuffukansu, ga shi kuma su ba daga cikin muminai suke ba, domin addini ya raba su, kuma ba daga cikin Yahudawan suke ba, domin su ma addini ya raba tsakaninsu sannan jinsinsu ba ɗaya ne ba, domin su munafukai Larabawa ne mutanen Madina, su kuma Yahudawa Isra’ilawa ne baƙi a Madina. Kuma duk da wannan zagon ƙasa da suke yi wa Musulunci, suna yi wa Musulmi rantsuwa da cewa su ma lalle Musulmi ne, wai kuma ba sa kai wa Yahudawa labarin Musulmi, alhalin ƙarya suke yi, kuma su ba muminai ne ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu tanadin azaba mai tsanani a lahira lokacin da zai jefa su can ƙarƙashin wutar Jahannama, domin mummunan aikin da suka yi a duniya na kafirci da munafurci da yi wa Musulmi zagon ƙasa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, munafukai sun mayar da rantse-rantsensu da suke yi a gaban Musulmi wata garkuwa ce da suke fakewa da ita, don gudun kada a kashe su idan yaƙi ya ɓarke tsakanin Musulmi da kafirai, don haka sai suke bayyana Musuluncinsu a fili suke ɓoye kafircinsu a zuciya, saboda haka ba za a taɓa su ba, ba kuma za a taɓa dukiyoyinsu ba, sai su tsira da rayuwarsu da dukiyoyinsu. Wannan ya ba su damar ci gaba da zama a tsakiyar muminai sai suka ci gaba da kange mutane daga hanyar Allah, don haka suna da azaba mai wulaƙantarwa, sakamakon rashin imaninsu da Allah da rashin miƙa wuya ga umarninsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, tarin dukiya da yawan ‘ya’ya da suke tinƙaho da shi a duniya ba zai amfana musu komai ba a lahira yayin da za su ga azabar Allah. Waɗannan su ne ‘yan wuta waɗanda za su dawwama a cikinta har abada babu ranar fita, kuma azaba ba za ta taɓa yanke musu ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan mummunan hali da munafukai suka rayu a kansa a nan duniya, da shi za su tashi a ranar alƙiyama, ranar da Allah zai tashi kowa a cikinta domin yi masa sakamako; to a ranar ne za su dinga yi wa Allah rantsuwa cewa su ba su taɓa aikata kafirci ko munafurci ba, wai su muminai ne masu aiki da abin da Allah ya umarce su da shi. Za su yi wa Allah (Mai tsarki da daukaka) rantsuwa a lahira kamar yadda suke yi wa muminai rantsuwa a duniya, su tabbatar musu cewa, su fa Musulmi ne, tsammaninsu wannan rantsuwar za ta yi musu wani amfani ko ta kare musu wata azaba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, lalle su maƙaryata ne a duniya da lahira, sun riga sun sayi ɓata da shiriyar da Allah ya nuna musu, sun zaɓi shiga wuta a kan shiga Aljanna, domin Shaiɗan ya riga ya yi galaba a kansu ya cika musu zukatansu da waswasi har ya mantar da su tunawa da Allah da ambatonsa, don haka sun ƙi aikata abin da zai yarda da su, sun rungumi ayyukan da suke fusatar da shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lalle masu waɗannan siffofi su ne ƙungiyar Shaiɗan kuma mabiyansa sau da ƙafa, kuma tabbas ƙungiyar Shaiɗan su ne asararru duniya da lahira.

  20. إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحَآدُّونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ أُوْلَٰٓئِكَ فِي ٱلۡأَذَلِّينَ 

    Open ayah 58:20

    Lalle waɗanda suke saɓa wa Allah da Manzonsa waɗannan suna cikin mafiya ƙasƙanci.

  21. كَتَبَ ٱللَّهُ لَأَغۡلِبَنَّ أَنَا۠ وَرُسُلِيٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٞ

    Open ayah 58:21

    Allah Ya rubuta cewa: Lalle Ni da manzannina ne za mu yi galaba. Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwayi.

  22. لَّا تَجِدُ قَوۡمٗا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ يُوَآدُّونَ مَنۡ حَآدَّ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَوۡ كَانُوٓاْ ءَابَآءَهُمۡ أَوۡ أَبۡنَآءَهُمۡ أَوۡ إِخۡوَٰنَهُمۡ أَوۡ عَشِيرَتَهُمۡۚ أُوْلَٰٓئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلۡإِيمَٰنَ وَأَيَّدَهُم بِرُوحٖ مِّنۡهُۖ وَيُدۡخِلُهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ رَضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُۚ أُوْلَٰٓئِكَ حِزۡبُ ٱللَّهِۚ أَلَآ إِنَّ حِزۡبَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

    Open ayah 58:22

    Ba za ka taɓa samun wasu mutane da suke yin imani da Allah da ranar lahira ba, su riƙa ƙaunar waɗanda suke gaba da Allah da Manzonsa, ko da kuwa sun kasance iyayensu ne ko ‘ya’yansu ko ‘yan’uwansu ko kuma danginsu. Waɗannan Allah Ya rubuta imani a cikin zukatansu, Ya kuma ƙarfafe su da wani ruhi daga wurinsa; zai kuma shigar da su gidajen Aljanna (waɗanda) ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, madawwama a cikinsu. Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi. Waɗannan ne ƙungiyar Allah. Ku saurara, lalle ƙungiyar Allah su ne masu samun babban rabo. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana narkonsa da mummunan sakamako ga waɗanda suke gaba da Allah da Manzonsa suke saɓa wa umarninsu ta hanyar aikata kafirci da munafurci, ya tabbatar musu cewa, suna cikin waɗanda ya ƙasƙantar da su duniya da lahira zai kuma wulaƙanta su kamar yadda ya wulaƙanta kafiran da suka gabace su. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya yi rantsuwa cewa tabbas shi da manzanninsa su ne za su yi nasara da ƙarfin hujja da kuma a fagen daga, domin Allah mai ƙarfi ne zai iya taimakon manzanninsa da ƙarfinsa, kuma mabuwayi ne, babu wanda zai ja da shi ya kai labari. A ayar ƙarshe ta wannan Surar kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, ba zai taɓa samun wasu mutane da suka yi imani da Allah da ranar lahira ba, a same su suna son wanda yake gaba da Allah da Manzonsa suna jiɓintar al’amarinsa, ko da kuwa su maƙiyan na Allah da Manzonsa iyayensu ne ko ‘ya’yansu ko ‘yan’uwansu ko danginsu, domin imaninsu ba zai bar su su so maƙiyan Allah da Manzonsa (ﷺ) ba har su riƙa jiɓintar al’amuransu, kuma sun san cewa dangantakar imani sama take da duk wata dangantaka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mutane masu irin wannan siffar su ne waɗanda ya tabbatar da imani wanda ba zai girgiza ba a cikin zukatansu, ya kuma ƙarfafe su da wata hujja daga wajensa da haske. A ranar alƙiyama kuma zai shigar da su gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudu ta ƙarƙashinsu, za su kuma dawwama a cikinsu har abada, suna cikin ni’imomin da ba za su yanke ba. Kuma Allah ya yarda da su, ba zai yi fushi da su ba har abada, su ma sun yarda da shi sun gamsu da sakamakon da ya yi musu da ni’imomin da ya tanadar musu a ciki, mafi girman ni’imominsa gare su kuwa shi ne ganin Zatinsa (Mai tsarki da daukaka). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan su ne ƙungiyar Allah, su ne kuma masu samun babban rabo a duniya da lahira, domin Allah zai tserar da su daga duk abin da suke ƙi, zai kuma haɗa su da duk abin da suke so.