الحشر

Al-Hashr

The Exile · Surah 59 · Ayahs: 24 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 59:1

    Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa ya tsarkake Allah; Shi ne kuwa Mabuwayi, Mai hikima.

  2. هُوَ ٱلَّذِيٓ أَخۡرَجَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ مِن دِيَٰرِهِمۡ لِأَوَّلِ ٱلۡحَشۡرِۚ مَا ظَنَنتُمۡ أَن يَخۡرُجُواْۖ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُم مَّانِعَتُهُمۡ حُصُونُهُم مِّنَ ٱللَّهِ فَأَتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِنۡ حَيۡثُ لَمۡ يَحۡتَسِبُواْۖ وَقَذَفَ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلرُّعۡبَۚ يُخۡرِبُونَ بُيُوتَهُم بِأَيۡدِيهِمۡ وَأَيۡدِي ٱلۡمُؤۡمِنِينَ فَٱعۡتَبِرُواْ يَٰٓأُوْلِي ٱلۡأَبۡصَٰرِ

    Open ayah 59:2

    Shi ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kafirce daga ma’abota littafi daga gidajensu a fitarwa ta farko. Ba ku yi tsammanin cewa za su fita ba, su kuma sun zaci ganuwoyinsu za su kare su daga Allah, sai Allah Ya zo musu ta inda ba su yi tsammani ba; Ya kuma jefa tsoro a cikin zukatansu. Suka riƙa rushe gidajensu da hannayensu da kuma hannayen muminai, to sai ku luru da kyau ya ku ma’abota basira.

  3. وَلَوۡلَآ أَن كَتَبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡجَلَآءَ لَعَذَّبَهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابُ ٱلنَّارِ

    Open ayah 59:3

    Ba don Allah Ya ƙaddara musu ficewa ba, lalle da Ya azabtar da su a duniya, a lahira kuma suna da azabar wuta.

  4. ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ شَآقُّواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۖ وَمَن يُشَآقِّ ٱللَّهَ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

    Open ayah 59:4

    Wannan kuwa saboda cewa sun saɓa wa Allah da Manzonsa ne, duk kuwa wanda ya saɓa wa Allah da Manzonsa, to lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da bayyana cewa, duk abin da yake cikin sammai da wanda yake ƙasa sun tsarkake Allah daga duk wani abu da bai dace da shi ba, domin shi Mabuwayi ne da babu mai iya tunkarar sa, mai hikima ne a cikin halittarsa da Ƙaddararsa da shari’arsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin Yahudawan Banun Nadhir waɗanda suka kafirce masa da Manzonsa (ﷺ), har ma suka shirya makircin hallaka Manzo (ﷺ). Yahudawa waɗanda suke tare da Annabi (ﷺ) a Madina sun ƙulla yarjejeniya da shi tun isowarsa Madina a kan abubuwa da dama da suka danganci zamantakewa tare. Daga cikin abubuwan da suka ƙulla alƙawari a kai, akwai cewa idan wata fitina za ta tunkaro su daga waje to za su haɗa kai gaba ɗaya su tunkare ta. Akwai wani sahabin Annabi (ﷺ) mai suna Amru ɗan Umayya Al-Dhamri ya kashe wasu mutanen Makka su biyu bisa kuskure, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ɗauki alƙawarin biyan diyyoyinsu, sai ya tafi shi da wasu sahabbansa zuwa Yahudawan Banun Nadhir don ya karɓo abin da za su taimaka da shi na dukiyar diyyar. Suka yi masa alƙawarin za su tattaro masa, suka neme shi da ya samu wuri ya zauna har su kammala tattara masa dukiyar. Daga nan sai wasu daga cikinsu suka keɓe suka tattauna a kan irin makircin da za su ƙulla wa Manzon Allah (ﷺ), Shaiɗan kuma ya raɗa musu cewa kawai su yi amfani da wannan damar su kashe shi su huta. Suka tambayi junansu cewa, wane ne a cikinsu zai iya ɗaukar dutsen niƙa ya hau kan bishiyar da Manzon Allah yake zaune a ƙarƙashinta ya jefo masa shi don ya hallaka shi? Sai wani shaƙiyyi daga cikinsu ya ce shi zai iya, amma sai aka samu wani mai ɗan hankali daga cikinsu ya yi musu kashedin cewa, kada su kuskura su ce za su yi wannan ɗanyen aiki, domin idan sun yi haka, to sun warware alƙawarin da suka ƙulla da Manzon Allah (ﷺ). Amma suka nuna masa ba za su fasa abin da suka yi niyya ba. A nan ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko wa Manzonsa (ﷺ) wahayi na irin abin da Yahudawan Banun Nadhir suke shirin yi masa, sai nan take ya tashi da gaggawa ya nufi cikin garin Madina, sahabbansa kuma suka bi shi daga baya, ya ba su labarin aika-aikar da Yahudawa suka shirya yi. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya aika musu cewa, lalle su tattara ya nasu-ya nasu su fita daga garin Madina, ba zai bar su su ci gaba da zama a cikinta ba har abada. Har sun yarda sun fara shirye-shiryen ficewa daga Madina sai shugaban munafukai Abdullahi ɗan Ubayyu ɗan Salulu ya aika musu da cewa, su yi zamansu kada su fita, kuma shi da jama’arsa lalle suna tare da su suna goyon bayansu, kuma a shirye suke su taimaka musu idan yaƙi ya ɓarke tsakaninsu da Musulmi. Daga nan sai suka fasa fita suka nuna taurin kansu. Sai Annabi (ﷺ) ya yi umarni da a kewaye gidajensu, aka yi musu ƙofar raggo, ya kuma yaƙe su ya sassare itatuwan dabinonsu ya ƙona su. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya jefa tsoro a zukatansu bayan munafukai sun ƙi cika musu alƙawarin da suka yi musu na taimako. Daga ƙarshe suka aika wa Manzon Allah (ﷺ) cewa sun amince da hukuncinsa, sun yarda za su fice daga Madina. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya amince su fice su da iyalansu da kayayyakin da raƙumansu za su iya ɗauka in ban da makamai. Suka fita suka nufi ƙasar Sham. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, shi ne wanda ya fitar da Yahudawan Banun Nadhir daga gidajensu a Madina a rukunin fitarwa ta farko zuwa Sham bayan sun warware alƙawarinsu da Manzon Allah (ﷺ) da haɗa kansu da mushirikai don yaƙar Musulmi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, muminai ba su taɓa zaton cewa waɗannan Yahudawa za su bar gidajensu ba, saboda ƙarfin tsaro da isasshen tanadin kariya da suke da shi. Su ma kansu Yahudawan, sun yi zaton cewa manya-manyan ganuwoyi masu ƙarfi da suka gina za su kare su daga uƙubar Allah idan ta zo musu, to sai ga shi azabar Allah ta zo musu ta inda ba su yi tsammanin zuwanta ba, yayin da Manzon Allah (ﷺ) ya ba da umarnin a yaƙe su, a fitar da su daga garin Madina. Allah kuma ya shigar da matsanancin tsoro a zukatansu, suka riƙa rushe gidajensu ta ciki da hannayensu, domin kada Musulmi su amfana da su, ta waje kuma Musulmi ne suka yi ta rushe su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ga masu hankali da basira da su ɗauki izina daga wannan azaba da ta auka wa waɗannan Yahudawa saboda kafircinsu da mugun nufinsu, don haka kada wasu su kuskura su kwatanta irin aikinsu, sai su ma su haɗu da azabar Allah irin wannan. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya ma yi rangwame ne ga waɗannan kafiran, ba don ya riga ya rubuta musu fitarwa daga gidajensu ba, to da lalle ya azabtar da su a duniya ta hanyar kisa da bauta, watau kamar yadda ya yi wa ‘yan’uwansu Banu Ƙuraiza. A lahira kuwa akwai azabar wuta tana nan tana jiran su, za su shige ta su dawwama a cikinta har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan sakamakon azabtarwa ya same su ne saboda sun saɓa wa Allah da Manzonsa (ﷺ), sun nuna musu ƙiyayya a sarari ta hanyar kafirci da warware alƙawari; duk wanda kuwa ya nuna ƙiyayyarsa ga Allah, to ya sani lalle Allah mai tsananin uƙuba ne.

  5. مَا قَطَعۡتُم مِّن لِّينَةٍ أَوۡ تَرَكۡتُمُوهَا قَآئِمَةً عَلَىٰٓ أُصُولِهَا فَبِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَلِيُخۡزِيَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

    Open ayah 59:5

    Duk abin da kuka sare na wata bishiyar dabino ko kuka bar ta a tsaye a kan tushiyoyinta, to da izinin Allah ne, don kuma Ya kunyata fasiƙai.

  6. وَمَآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنۡهُمۡ فَمَآ أَوۡجَفۡتُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ خَيۡلٖ وَلَا رِكَابٖ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يُسَلِّطُ رُسُلَهُۥ عَلَىٰ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

    Open ayah 59:6

    Kuma duk abin da Allah Ya bai wa Manzonsa na wata dukiya tasu (don falalarsa), to ba wani hari kuka kai na dawaki ko raƙuma ba saboda shi, sai dai kuma Allah Shi ne Yake ɗora manzanninsa a kan wanda Ya ga dama. Allah kuwa Mai iko ne a kan komai.

  7. مَّآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰ فَلِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ كَيۡ لَا يَكُونَ دُولَةَۢ بَيۡنَ ٱلۡأَغۡنِيَآءِ مِنكُمۡۚ وَمَآ ءَاتَىٰكُمُ ٱلرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَىٰكُمۡ عَنۡهُ فَٱنتَهُواْۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

    Open ayah 59:7

    Abin da Allah ya bai wa Manzonsa na wata dukiya daga mutanen alƙaryu, to na Allah ne da Manzonsa da kuma danginsa na kusa da marayu da miskinai da matafiyin (da guzuri ya yanke wa), don kada ya zama mai juyawa tsakanin mawadata daga cikinku. Kuma abin da Manzo ya ba ku sai ku karɓe shi, abin kuma da ya hana ku sai ku hanu. Ku kuma kiyaye dokokin Allah; lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Musulmi cewa dabinan da suka sassare a lokacin yaƙi da Yahudawan Banun Nadhir don su ƙara cusa musu baƙin ciki, ko waɗanda suka bar su a tsaye a kan tushiyoyinsu domin su amfana da su, to sun yi wannan ne duka da izinin Allah da umarninsa, ba su yi gaban kansu ba, ba kuma sun yi haka ne don ɓarnata dukiya ba, kamar yadda Yahudawan suka riƙa yayatawa don su soki Musulmi da shi, ba su kuma san cewa Allah ne ya yi musu umarni da haka ba, Allah kuma ya yi haka ne domin ya wulaƙanta fasiƙai, watau Yahudawa masu bijire wa dokokinsa da shirya makirce-makirce don cutar da Manzonsa da karya alƙawarin zamantakewa da suka ɗauka. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Musulmi cewa, dukiyar Yahudawan Banun Nadhir da ya dawo wa Manzonsa ita su Musulmi suna sane da cewa ba su kai wani hari da dawakansu ko raƙumansu ba, ba su kuma sha wata wahala wajan samun ta ba, Allah ne kawai yake ɗora manzanninsa a kan wanda ya ga dama, don babu abin da ya fi ƙarfinsa, saboda haka ya ɗora Manzonsa (ﷺ) a kan Yahudawan Banun Nadhir ya kuma ci nasara a kansu ba tare da wani yaƙi na a zo a gani ya auku ba, domin shi Allah mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kasafin dukiyar ganimar da ya ba wa Manzonsa a wannan yaƙi, inda ya bayyana cewa, dukiyar gaba ɗayanta ta Allah ce, yana bayar da ita ga wanda ya so, don haka ya mallaka ta ga Manzonsa (ﷺ) da danginsa na kusa, watau Banu Hashim da Banul Muɗɗalib waɗanda aka haramta wa cin dukiyar sadaka, da kuma marayu da miskinai da matafiyan da guzurinsu ya yanke. Allah kuma ya yi wannan kasafin ne don kada dukiyoyi su yi ta jujjuyawa tsakanin mawadata kaɗai ba sa kaiwa ga talaka marar ƙarfi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Musulmi cewa su karɓi abin da Annabi (ﷺ) ya ba su daga cikin dukiyar ganima da aka samu ba tare da yaƙi ba (watau fai\'u ), abin da kuma ya hana su sai su hanu, watau su nisance shi, kuma su kiyaye dokokinsa, ta hanyar aikata abin da ya umarce su da barin abin da ya hana su; su kuma guji abin da zai jawo musu uƙubar Allah, domin Allah mai tsananin uƙuba ne. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Allah ya la’anci mata masu shasshawa da masu neman a yi musu da masu gyaran girar ido da masu yin wushirya domin ado, da masu sauya halittar Allah mai girma da buwaya.” Sai wannan magana ta Abdullahi ɗan Mas’ud ta je kunnen wata mata ana ce mata Ummu Yaƙub, sai nan da nan ta zo wurin Abdullahi ɗan Mas’ud ta ce masa: “Labari ya zo min kana faɗar kaza da kaza.” Sai ya ce: “Me zai hana in la’anci wanda Manzon Allah (ﷺ) ya la’anta? Wannan ma ya zo a cikin Littafin Allah, watau Alƙur’ani.” Sai ta ce: “Lalle ni fa na sha karanta Alƙur’ani daga bango zuwa bango amma ban taɓa samun wannan maganar a cikinsa ba.” Sai ya ce: “Idan har kin taɓa karanta shi, to lalle kin taɓa cin karo da ita. Ba ki taɓa karanta faɗar Allah ba: “Abin da Manzon Allah (ﷺ) ya ba ku to ku karɓe shi, abin da kuma ya hana ku sai ku hanu”? Sai ta ce: “Lalle na gani.” Sai ya ce: “To lalle Annabi (ﷺ) ya hana hakan.” Sai ta ce masa: “To lalle ina zaton iyalanka ma suna aikata haka.” Sai ya ce mata: “Ki je ki duba.” Sai ta je amma ba ta ga abin da ta yi zato ba. Sai ta ce: “Ban ga komai ba.” Sai ya ce: “Da ta kasance kamar yadda kika faɗa, to da ba ta sake zama da mu ba.” [Bukhari #4886 da Muslim #2125].

  8. لِلۡفُقَرَآءِ ٱلۡمُهَٰجِرِينَ ٱلَّذِينَ أُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَأَمۡوَٰلِهِمۡ يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗا وَيَنصُرُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّٰدِقُونَ

    Open ayah 59:8

    (Za a bayar da dukiyar) ga matalauta da suka yi hijira waɗanda aka fitar da su daga gidajensu da dukiyoyinsu don neman falala daga Allah da yardarsa, suna kuma taimakon (addinin) Allah da Manzonsa. Waɗannan su ne masu gaskiya.

  9. وَٱلَّذِينَ تَبَوَّءُو ٱلدَّارَ وَٱلۡإِيمَٰنَ مِن قَبۡلِهِمۡ يُحِبُّونَ مَنۡ هَاجَرَ إِلَيۡهِمۡ وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمۡ حَاجَةٗ مِّمَّآ أُوتُواْ وَيُؤۡثِرُونَ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ وَلَوۡ كَانَ بِهِمۡ خَصَاصَةٞۚ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفۡسِهِۦ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

    Open ayah 59:9

    Da kuma waɗanda suka tanadi gida (mutanen Madina) suka kuma (karɓi) imani gabaninsu (masu hijira), suna son waɗanda suka yi hijira zuwa gare su, ba sa samun wani ƙyashi a zukatansu game da abin da aka ba su (masu hijira), suna kuma fifita (masu hijira) a kan kawunansu, ko da kuwa suna da tsananin buƙata. Duk kuwa wanda aka kiyaye shi daga son kansa, to waɗannan su ne masu babban rabo.

  10. وَٱلَّذِينَ جَآءُو مِنۢ بَعۡدِهِمۡ يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لَنَا وَلِإِخۡوَٰنِنَا ٱلَّذِينَ سَبَقُونَا بِٱلۡإِيمَٰنِ وَلَا تَجۡعَلۡ فِي قُلُوبِنَا غِلّٗا لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ رَبَّنَآ إِنَّكَ رَءُوفٞ رَّحِيمٌ 

    Open ayah 59:10

    Duk kuma waɗanda suka zo daga bayansu suna cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana mu da ‘yan’uwanmu waɗanda suka rigaye mu yin imani, kada kuma Ka sanya wata ƙullata a zukatanmu game da waɗanda suka yi imani, ya Ubangijinmu, lalle Kai Mai tausayawa ne, Mai jin ƙai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani ɓangare da za a ba wa dukiyar ‘fai’u ’, watau su ne matalauta masu hijira don Allah, waɗanda aka tilasta musu barin dukiyoyinsu da ‘ya’yansu, suka yiwo ƙaura zuwa Madina wurin Manzon Allah (ﷺ) suna sanya tsammani Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu falalar wani arziki na duniya su kuma dace da samun yardarsa a lahira, suka kuma kasance tare da Manzon Allah (ﷺ) suna taimakon sa suna kuma taimakon addinin Allah ta hanyar jihadi don Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, waɗanda suke da waɗannan siffofi su ne masu gaskiya waɗanda imani ya ratsa zukatansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci mutanen Madina waɗanda suka karɓi Annabi (ﷺ) da sahabbansa masu hijira hannu bibbiyu, ya siffanta su da siffofi huɗu: <b>Ta ɗaya </b>, sun zaɓi yin imani da Allah da Manzonsa (ﷺ). <b>Ta biyu </b>, suna son waɗanda suka yiwo ƙaura daga Makka zuwa wajensu. <b>Ta uku </b>, ba sa jin wani ƙyashi ko hassada ga muhajirai idan an ba su wani abu daga cikin dukiyar ‘fai’u ’ su ba a ba su ba. <b>Ta huɗu </b>, suna fifita masu hijirar a kan kawunansu game da wani abin duniya ko da kuwa su suna da buƙata. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kirawo mutanen Madina don ya ba su wani yanki daga dukiyar Bahraini, sai suka ce masa a’a, sai dai in zai ba wa ‘yan’uwansu mutanen Makka masu hijira. Annabi (ﷺ) ya ce musu: “To tun da haka ne sai dai su yi haƙuri har su haɗu da ni.” watau a ranar alƙiyama. [Bukhari #3794]. An karɓo daga Abu Hurairah (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mutanen Madina sun ce wa Manzon Allah (ﷺ): “Ka raba gonakin dabinanmu tsakaninmu da ‘yan’uwanmu masu hijira.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A’a.” Sai suka ce wa masu hijira: “Ku ɗauke mana ɗawainiyar shayar da su, sai mu yi tarayya a kan amfaninsu.” Sai suka ce: “Mun ji, mun kuma bi.” [Bukhari #2326]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda ya kare shi daga tsananin kwaɗayin dukiya ga kansa, ya fito da ita ya bayar saboda Allah, to lalle irin waɗannan su ne masu samun babban rabo, domin za su dace da abin da ransu yake ƙauna, za su kuma kuɓuta daga duk abin da suke tsoro. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku kiyayi zalunci, domin zalunci duffai ne a ranar alƙiyama, kuma ku kiyayi tsananin rowa, domin tsananin rowa ce ta hallaka waɗanda suka gabace ku, ta sanya su suka riƙa zubar da jinin junansu, suka kuma riƙa halatta cin mutuncin junansu.” [Muslim #2578]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin mutanen ƙwarai waɗanda suka zo bayan sahabban Manzon Allah (ﷺ) da cewa, su ne masu roƙon Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gafarta musu tare da ‘yan’uwansu da suka rigaye su yin imani da Allah da Manzonsa, suke kuma roƙon sa da kada ya sanya wata ƙullata a zukatansu game da wani mumini, domin shi Allah mai tausayi ne ga bayinsa, kuma mai jin ƙai.

  11. ۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ نَافَقُواْ يَقُولُونَ لِإِخۡوَٰنِهِمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَئِنۡ أُخۡرِجۡتُمۡ لَنَخۡرُجَنَّ مَعَكُمۡ وَلَا نُطِيعُ فِيكُمۡ أَحَدًا أَبَدٗا وَإِن قُوتِلۡتُمۡ لَنَنصُرَنَّكُمۡ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ

    Open ayah 59:11

    Ba ka ga waɗanda suka yi munafunci suna ce wa ‘yan’uwansu waɗanda suka kafirta daga ma’abota littafi: “Tabbas idan aka fitar da ku, lalle za mu fita tare da ku, ba kuma za mu bi wani mutum game da ku ba har adaba, kuma idan aka yaƙe ku tabbas za mu taimake ku.” Allah kuma Ya san tabbas ƙarya suke yi.

  12. لَئِنۡ أُخۡرِجُواْ لَا يَخۡرُجُونَ مَعَهُمۡ وَلَئِن قُوتِلُواْ لَا يَنصُرُونَهُمۡ وَلَئِن نَّصَرُوهُمۡ لَيُوَلُّنَّ ٱلۡأَدۡبَٰرَ ثُمَّ لَا يُنصَرُونَ

    Open ayah 59:12

    Tabbas idan aka fitar da su ba za su fita tare da su ba, kuma tabbas idan aka yaƙe su ba za su taimake su ba, tabbas kuwa idan ma sun taimake su ɗin, lalle za su gudu su ba da baya, sannan kuma ba za a ba su nasara ba.

  13. لَأَنتُمۡ أَشَدُّ رَهۡبَةٗ فِي صُدُورِهِم مِّنَ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَفۡقَهُونَ

    Open ayah 59:13

    Tabbas ku suka fi tsoro a zukatansu fiye da Allah. Wannan kuwa saboda su mutane ne da ba sa fahimta.

  14. لَا يُقَٰتِلُونَكُمۡ جَمِيعًا إِلَّا فِي قُرٗى مُّحَصَّنَةٍ أَوۡ مِن وَرَآءِ جُدُرِۭۚ بَأۡسُهُم بَيۡنَهُمۡ شَدِيدٞۚ تَحۡسَبُهُمۡ جَمِيعٗا وَقُلُوبُهُمۡ شَتَّىٰۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَعۡقِلُونَ

    Open ayah 59:14

    Ba sa yaƙar ku a tare sai a cikin wasu alƙaryu katangaggu ko ta bayan katangu. Yaƙi a tsakaninsu mai tsanani ne. Za ka tsammaci kansu a haɗe yake, alhali zukatansu a rarrabe suke. Wannan kuwa saboda cewar su mutane ne da ba sa hankalta.

  15. كَمَثَلِ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ قَرِيبٗاۖ ذَاقُواْ وَبَالَ أَمۡرِهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 59:15

    Sun yi kama da waɗanda suke a gabaninsu ba da daɗewa ba, sun ɗanɗani azabar al’amarinsu, suna kuma da (sakamakon) azaba mai raɗaɗi.

  16. كَمَثَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِ إِذۡ قَالَ لِلۡإِنسَٰنِ ٱكۡفُرۡ فَلَمَّا كَفَرَ قَالَ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّنكَ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَ رَبَّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 59:16

    Sun yi kama da Shaiɗan lokacin da ya ce wa mutum: “Ka kafirta.” To yayin da ya kafirta sai ya ce: “Lalle ni ba ruwana da kai, lalle ni ina tsoron Allah Ubangijin talikai.”

  17. فَكَانَ عَٰقِبَتَهُمَآ أَنَّهُمَا فِي ٱلنَّارِ خَٰلِدَيۡنِ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَٰٓؤُاْ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 59:17

    Sai ƙarshen al’amarinsu ya kasance cewa su duka biyun masu dawwama ne cikin wuta. Wannan kuwa shi ne sakamakon azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) alƙawarin da munafukai suka yi wa Yahudawan Banun Nadhir yayin da suka riƙa zuga su suna tabbatar musu da cewa lalle su ci gaba da zama a gidajensu kada su yarda su fita, ko da kuwa Annabi ne ya umarce su da fita, suka rantse musu da Allah cewa ba za su bari a wulaƙanta su su kaɗai ba, domin har idan Musulmi za su kore su daga gidajensu, to su ma sun yi alƙawarin za su fita tare da su, don su nuna musu goyon baya, kuma ba za su saurari wani wanda zai hana su fita tare da su ba. Suka kuma rantse musu da Allah cewa lalle idan Musulmi suka yaƙe su, to tabbas za su taimaka musu wajen yaƙar Musulmi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tona asirinsu ya bayyana wa Manzonsa cewa ya shaida lalle tabbas munafukai ƙarya suke ba za su taɓa fita tare da Yahudawa su bar gidajensu ba, kuma ba za su taɓa taimaka musu wajen yaƙar Musulmi ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, tabbas idan Musulmi suka fitar da Yahudawa daga gidajensu munafukai ba za su fita tare da su ba kamar yadda suke yi musu daɗin baki. Idan kuma Musulmi suka fara yaƙar Yahudawa, munafukai ba za su taimaka musu ba, kuma ko da za su fito da sunan taimakon su, to da zaran sun ga an fara yaƙi za su juya da baya su gudu su bar su, sannan kuma ba za a taɓa taimaka wa su munafukan ba, sai dai Allah ya wulaƙanta su su yi ta ganin ƙasƙanci. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙarfafa wa Musulmi gwiwa, ya kuma bayyana musu dalilin da zai sa munafukai ba za su taɓa taimaka wa Yahudawa a kan muminai a wajen yaƙi ba, saboda tabbas munafukai da Yahudawa sun fi tsoron muminai a zukatansu fiye da yadda ma suke tsoron Allah, ba kuma don wani abu ba sai don zamantowarsu mutane ne da ba sa fahimtar duk wata gaskiya da ake faɗa musu, domin da a ce suna ganewa to da kamata ya yi su ji tsoron Allah fiye da komai, domin shi ne yake ba wa muminai nasara a kansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tsananin tsoron Yahudawa ga muminai da cewa, ba za su taɓa yaƙar muminai a tare ba sai ta cikin garuruwa waɗanda suke kewaye da ganuwoyi, ko kuma ta bayan katangu, domin ba za su iya yin gaba-da-gaba da Musulmi ba saboda tsananin tsoronsu da raggwancinsu. Su kuma a tsakaninsu ba sa ga-maciji don tsananin gabar da take tsakaninsu, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa idan ya gan su zai yi zaton kansu a haɗe yake babu wata ɓaraka a tsakaninsu, alhalin ba haka ne ba; zukatansu a rarrabe suke, saboda su mutane ne da ba sa hankalta, domin da suna aiki da hankalinsu da sun gane gaskiya ɗaya ce sun haɗa kansu a kanta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da misalin irin yadda munafukai suke yaudarar Yahudawa da zaƙin baki da alƙawuran ƙarya, daga ƙarshe su kai su su baro. Ya bayyana cewa, sun yi kama da mushirikan Makka ne a ɗan wani lokaci baya ba da jimawa ba, watau lokacin yaƙin Badar, lokacin da suka ɗanɗani kuɗarsu a hannun Musulmi, aka kashe na kashewa aka kama na kamawa, sannan ga azaba can mai tsanani a lahira tana jiran su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, misalin Yahudawa waɗanda suke sauraron zaƙi bakin munafukai, kamar Shaiɗan ne lokacin da ya ƙawata wa mutum ya kafurta, to da zaran ya yarda ya kafirta ɗin sai Shaiɗan ya fito sarari yana faɗa masa cewa, shi fa ba ruwansa da kafircinsa, don shi yana jin tsoron azabar Allah. Ƙarshen lamarin Shaiɗan kuwa da duk wanda ya bi umarninsa, shi ne su tabbata a wuta ranar alƙiyama, su kuma dawwama a cikinta har abada; wannan kuma shi ne sakamakon da yake jiran azzalumai masu ƙetare iyakokin Allah.

  18. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلۡتَنظُرۡ نَفۡسٞ مَّا قَدَّمَتۡ لِغَدٖۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 59:18

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma kowane rai ya dubi abin da ya gabatar don gobe (lahira); ku kuma kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne.

  19. وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ نَسُواْ ٱللَّهَ فَأَنسَىٰهُمۡ أَنفُسَهُمۡۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

    Open ayah 59:19

    Kada kuma ku zama kamar waɗanda suka manta da Allah, sai Ya mantar da su kawunansu. Waɗannan su ne fasiƙai.

  20. لَا يَسۡتَوِيٓ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۚ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ 

    Open ayah 59:20

    ‘Yan wuta da ‘yan Aljanna ba za su yi daidai ba. ‘Yan Aljanna su ne masu rabauta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira muminai ya umarce su da su kiyaye dokokinsa, su aikata abin da ya umarce su da shi, su kuma guji abin da ya hana su, sannan kowane mutum ya dubi kyakkyawan aikin da ya tanadar wa kansa domin ranar alƙiyama, watau su sanya tunanin wannan rana shi ne a zukatansu koyaushe, ya kuma sake jaddada musu umarnin su kiyaye dokokinsa sau-da-ƙafa, kada su bari wani abu na duniya ya ɗauke musu hankali, su kuma sani cewa Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sane da duk abin da suke aikatawa mai kyau ko mummuna, kuma zai yi musu hisabi a kansa ranar alƙiyama. An karɓo daga Jarir ɗan Abdullahi Al-Bajali (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana muna zaune a gaban Manzon Allah (ﷺ) da rana, sai ga wasu mutane sun zo masa, babu takalma a ƙafafunsu, suna kuma sanye da wasu yagaggun tufafi tsirara-tsirara, ɗauke da takubbansu, yawancinsu ko kuma dukkansu ‘yan ƙabilar Mudar ne. Da Annabi (ﷺ) ya ga irin tsananin talaucin da suke ciki sai fuskarsa ta canja, ya shiga gidansa ya fito, ya umarci Bilalu ya yi kiran salla ya yi iƙama. Annabi (ﷺ) ya yi wa mutane salla, sannan ya miƙe tsaye ya yi wa mutane jawabi, ya karanta faɗar Allah (Mai tsarki da daukaka): “Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guɗa ɗaya....” [An-Nisa’i, aya ta 1]. Ya kuma karanta wannan ayar da ke cikin wannan Surar, sannan ya ce: “Kowane mutum ya bayar da sadaka daga dinarinsa ko dirhaminsa ko tufafinsa ko sa’in alkamarsa ko na dabinonsa.” Har ma ya ce: “Ko da da tsagin dabino ne....” [Muslim #1017]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja wa muminai kunne da cewa, kada su zama kamar waɗanda suka manta da Allah, watau suka yi watsi da aiki da umarninsa da guje wa haninsa, a kan haka sai Allah ya mantar da su kawunansu, suka ƙi yin aikin da zai tserar da su daga azabar Allah da hushinsa, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, irin waɗannan mutane su ne fasiƙai waɗanda suka kangare wa ɗa’ar Allah da Manzonsa (ﷺ) suka zamanto ‘yan wuta. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ‘yan wuta da ‘yan Aljanna ba za su taɓa zama daidai ba, domin dole ne sakamakonsu ya sha bamban, kamar yadda a duniya ayyukansu suka sha bamban. ‘Yan Aljanna su ne masu rabauta a lahira, Allah (Mai tsarki da daukaka) zai ba su duk abin da suke so, zai kuma kuɓutar da su daga duk abin da suke ƙi.

  21. لَوۡ أَنزَلۡنَا هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ عَلَىٰ جَبَلٖ لَّرَأَيۡتَهُۥ خَٰشِعٗا مُّتَصَدِّعٗا مِّنۡ خَشۡيَةِ ٱللَّهِۚ وَتِلۡكَ ٱلۡأَمۡثَٰلُ نَضۡرِبُهَا لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ

    Open ayah 59:21

    Da za Mu saukar da wannan Alƙur’ani ga wani dutse, da lalle ka gan shi yana mai ƙasƙantar da kai mai tsattsagewa don tsoron Allah. Waɗannan misalan Muna buga wa mutane su ne don su yi tunani.

  22. هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۖ هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ

    Open ayah 59:22

    Shi ne Allah wanda babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Masanin ɓoye da sarari; kuma Shi ne Mai rahama, Mai jin ƙai.

  23. هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡقُدُّوسُ ٱلسَّلَٰمُ ٱلۡمُؤۡمِنُ ٱلۡمُهَيۡمِنُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡجَبَّارُ ٱلۡمُتَكَبِّرُۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

    Open ayah 59:23

    Shi ne Allah wanda babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Shi ne Sarki, Mai tsarki, Amintacce, Mai amintarwa, Mai kula da komai, Mabuwayi, Mai tsananin ƙarfi; Mai nuna isa. Allah Ya tsarkaka daga abin da suke tara (Shi da shi).

  24. هُوَ ٱللَّهُ ٱلۡخَٰلِقُ ٱلۡبَارِئُ ٱلۡمُصَوِّرُۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ يُسَبِّحُ لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 59:24

    Shi ne Allah Mahalicci, Mai ƙagawa Mai surantawa; Yana da sunaye mafiya kyau. Duk abin da yake cikin sammai da ƙasa yana tsarkake Shi; kuma Shi Mabuwayi ne, Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) girman Alƙur’ani da tasirin wa’azuzzukansa, ba ga ɗan’adam da aljan ba kaɗai, har da daskararrun abubuwa, domin da a ce Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da shi ga dutse to da za a gan shi ya tsattsage saboda tsananin tsoron Allah, domin abin da yake cikin Alƙur’ani na wa’azi da tsoratarwa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan misalai ne yake buga wa mutane don su yi aiki da hankulansu, su wa’azantu da abin da ayoyin Alƙur’ani da wa’azozinsa masu ratsa jiki. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu daga cikin sunayensa mafiya kyau waɗanda suke ɗauke da siffofin kamala da isa, da cewa, shi ne Allah wanda babu wani abin bauta na gaskiya sai shi, masanin abin da yake ɓoye da na sarari, mai yalwar rahama a nan duniya ga kowa da kowa, mai jin ƙai a duniya da lahira ga bayinsa muminai. Shi ne Sarki mai cikakkiyar sarauta da mulkin komai a ƙasa da sama, tsarkakakke daga duk wani aibi, amintacce daga duk wata tawaya ko cuta, mai gaskata manzanninsa da ayoyin da yake ba su, mai kula da komai na ayyukan bayinsa, mabuwayi wanda babu mai iya karawa da shi, mai tsananin ƙarfi wanda ya fi ƙarfin kowane abu cikin halittarsa, mai nuna isa a kan kowa da komai, ya tsarkaka daga duk wani abu da mushirikai suke masa shirka da shi. A ayar ƙarshe ta wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana cewa shi ne Allah mahaliccin komai, mai ƙagar halittar komai, mai suranta kamanninsu yadda ya ga dama, babu mai tarayya da shi a kan haka. Yana da sunaye mafiya kyau waɗanda suka ƙunshi siffofi mafiya ɗaukaka; duk abin da yake cikin sammai da wanda yake ƙasa suna tsarkake shi daga duk wani aibi ko tawaya; shi ne mabuwayi wanda babu mai iya karawa da shi, mai hikima cikin halittarsa da shari’arsa da Ƙaddararsa.