الممتحنة

Al-Mumtahana

She that is to be examined · Surah 60 · Ayahs: 13 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ عَدُوِّي وَعَدُوَّكُمۡ أَوۡلِيَآءَ تُلۡقُونَ إِلَيۡهِم بِٱلۡمَوَدَّةِ وَقَدۡ كَفَرُواْ بِمَا جَآءَكُم مِّنَ ٱلۡحَقِّ يُخۡرِجُونَ ٱلرَّسُولَ وَإِيَّاكُمۡ أَن تُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ رَبِّكُمۡ إِن كُنتُمۡ خَرَجۡتُمۡ جِهَٰدٗا فِي سَبِيلِي وَٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِيۚ تُسِرُّونَ إِلَيۡهِم بِٱلۡمَوَدَّةِ وَأَنَا۠ أَعۡلَمُ بِمَآ أَخۡفَيۡتُمۡ وَمَآ أَعۡلَنتُمۡۚ وَمَن يَفۡعَلۡهُ مِنكُمۡ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ

    Open ayah 60:1

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku riƙi maƙiyana kuma maƙiyanku masoya, kuna nuna musu soyayya, alhali kuwa sun kafirce wa abin da ya zo muku na gaskiya, suna fitar da Manzo har da ku kanku don kun yi imani da Allah Ubangijinku, idan har kun zamanto kun fito don yin jihadi saboda Ni da kuma neman yardata. Kuna ɓoye ƙaunarku gare su, alhali kuwa Ina sane da abin da kuka ɓoye da kuma abin da kuka bayyana. Duk kuwa wanda ya aikata haka daga cikinku, to haƙiƙa ya ɓace wa hanya madaidaiciya.

  2. إِن يَثۡقَفُوكُمۡ يَكُونُواْ لَكُمۡ أَعۡدَآءٗ وَيَبۡسُطُوٓاْ إِلَيۡكُمۡ أَيۡدِيَهُمۡ وَأَلۡسِنَتَهُم بِٱلسُّوٓءِ وَوَدُّواْ لَوۡ تَكۡفُرُونَ

    Open ayah 60:2

    Idan suka samu nasara a kanku za su zama abokan gabanku, kuma za su miƙa hannayensu da harsunansu zuwa gare ku don munanawa, sun kuma yi burin ina ma da za ku kafirta.

  3. لَن تَنفَعَكُمۡ أَرۡحَامُكُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُكُمۡۚ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَفۡصِلُ بَيۡنَكُمۡۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

    Open ayah 60:3

    Danginku da ‘ya’yanku ba za su amfana muku komai ba. A ranar alƙiyama kuma za a yi hukunci a tsakaninku da su. Kuma Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne. Waɗannan ayoyi sun sauka ne game da labarin wani sahabi mai suna Haɗibu ɗan Abu Balta’ata, Shi ɗaya ne daga cikin sahabbai da suka yiwo hijira daga Makka zuwa Madina, ya kuma halarci yaƙin Badar tare da Manzon Allah (ﷺ). Ya baro ‘ya’yansa da dukiyarsa a Makka, kuma shi ba Baƙuraishe ne ba, don haka ba shi da wasu dangi a garin Makka da za su tsare masa ‘ya’yansa da dukiyarsa. Lokacin da Manzon Allah (ﷺ) ya ƙuduri niyyar zuwa Makka don yaƙar mutanenta bayan sun warware yarjejeniyar da aka ƙulla da su, sai Manzon Allah (ﷺ) ya sanar da wasu daga cikin sahabbai labarin abin da yake shirin aikatawa, daga cikinsu har da Haɗibu ɗan Abu Balta’ata. Sai Haɗibu (Allah ya kara masa yarda) ya rubuta wa Ƙuraishawa takarda yana ba su labarin abin da Manzon Allah yake shirya musu, ya danƙa takardar ga wata mace mushirika da ta zo Madina don ta kai musu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Manzonsa (ﷺ) abin da ake ciki, nan da nan ya umarci Aliyyu (Allah ya kara masa yarda) da Zubairu (Allah ya kara masa yarda) da Miƙidadu (Allah ya kara masa yarda) da su bi bayan wannan matar su karɓo takardar da take hannunta. Haka kuwa aka yi, suka karɓo takardar suka dowa da ita ga Manzon Allah (ﷺ). Da Ma’aki (ﷺ) ya tambayi Haɗibu dalilinsa na aikata wannan ɗanyen aiki, shi kuma ya faɗa masa uzurinsa cewa, ba kafirci ko munafurci ko yi wa Musulunci zagon ƙasa ne ya sanya shi wannan aiki ba, a’a, ya yi haka ne da kyakkyawar niyya, domin ya san Allah (Mai tsarki da daukaka) zai ba wa Manzonsa nasara a kan kafirai ko da kuwa sun sami labarin zuwansa domin yaƙar su, shi kuma yana buƙatar samun wani abu da zai yi wa Ƙuraishawa wanda zai faranta musu rai har su kula masa da ‘ya’yansa da dukiyarsa, kada su cutar da shi. Sai Annabi (ﷺ) ya karɓi hanzarinsa, Allah kuma ya yafe masa. [Dubi, Bukhari #3007 da Muslim #2494]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyi, yana kiran muminai waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa (ﷺ) da shari’ar da ya zo musu da ita cewa kada su riƙi duk wanda yake maƙiyansa kuma maƙiyansu a matsayin masoya har su nuna musu ƙauna, alhalin sun kafirce wa addinin da Manzonsa (ﷺ) ya zo musu da shi. Waɗannan ne fa suka kori Manzon Allah (ﷺ) har da su muminai mabiyansa daga gidajensu a Makka, ba su damu da dangantakar da take tsakaninsu ko zumunci ba. Kuma sun yi musu haka ne ba don wani laifi da suka aikata ba, sai don kawai sun yi imani da Allah Ubangijinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja kunnen muminai da kada su kuskura su riƙe su masoya matuƙar dai sun fito ne domin yin jihadi saboda shi da kuma neman yardarsa, ballantana ma su riƙa bayyana musu wani asiri na Musulmi don su nuna musu ƙauna, alhali kuwa Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sane da duk abin da za su ɓoye da wanda za su bayyana, domin babu abin da yake ɓuya a gare shi. Allah ya tabbatar musu da cewa duk wanda zai nuna ƙaunarsa da soyayyarsa ga kafirai, to lalle ya kauce wa hanyar Allah madaidaiciya ya rungumi ɓata da son zuciya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai tsananin ƙiyayyar da kafirai suke yi musu, da cewa, da abin a ce za su sami nasara a kan muminai ne, to lalle kuwa da za su fito da ƙiyayyar da ke cikin zukatansu a fili, za kuma su shimfiɗa hannayensu da nufin cutarwa, za kuma su saki kausasan harsunansu a kansu da zagi da cin mutunci, su kuma yi burin ina ma su ma muminan sun kafirce wa Allah da Manzonsa sun zama kamarsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa muminai cewa idan sun ɗauka cewa za su nuna wa kafirai ƙauna da soyayya saboda dangantaka ko dukiya, to su sani cewa danginsu da dukiyarsu ba za su amfana musu komai ba. A ranar alƙiyama Allah zai yi hukunci a tsakaninsu ya shigar da muminai daga cikinsu Aljanna, ya kuma shigar da mushirikai wuta, ashe kuwa ba wanda zai amfanar da wani daga cikinsu. Kuma Allah yana ganin duk abin da suke aikatawa, kuma zai yi wa kowa sakayya a kan aikinsa.

  4. قَدۡ كَانَتۡ لَكُمۡ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ فِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ إِذۡ قَالُواْ لِقَوۡمِهِمۡ إِنَّا بُرَءَٰٓؤُاْ مِنكُمۡ وَمِمَّا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ كَفَرۡنَا بِكُمۡ وَبَدَا بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمُ ٱلۡعَدَٰوَةُ وَٱلۡبَغۡضَآءُ أَبَدًا حَتَّىٰ تُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَحۡدَهُۥٓ إِلَّا قَوۡلَ إِبۡرَٰهِيمَ لِأَبِيهِ لَأَسۡتَغۡفِرَنَّ لَكَ وَمَآ أَمۡلِكُ لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖۖ رَّبَّنَا عَلَيۡكَ تَوَكَّلۡنَا وَإِلَيۡكَ أَنَبۡنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 60:4

    Haƙiƙa kyakkyawan abin koyi ya kasance a gare ku game da Ibrahimu da waɗanda suke tare da shi, lokacin da suka ce da mutanensu: “Lalle mu ba ruwanmu da ku, har ma da abin da kuke bauta wa ba Allah ba, mun kafirce muku, kuma gaba da ƙiyayya sun bayyana a tsakaninmu da ku har abada, har sai kun yi imani da Allah Shi kaɗai, in ban da faɗar Ibrahimu ga babansa cewa: ‘Lalle zan nema maka gafara, ba na kuma amfana maka komai game da (sakamakon) Allah’; ya Ubangijinmu gare Ka muka dogara, kuma zuwa wurinka muka mayar da lamuranmu, kuma makoma zuwa gare Ka ne.

  5. رَبَّنَا لَا تَجۡعَلۡنَا فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ وَٱغۡفِرۡ لَنَا رَبَّنَآۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 60:5

    “Ya Ubangijinmu, kada Ka sanya mu fitina ga waɗanda suka kafirta, Ka kuma gafarta mana ya Ubangijinmu; lalle Kai ne Mabuwayi, Mai hikima.”

  6. لَقَدۡ كَانَ لَكُمۡ فِيهِمۡ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ لِّمَن كَانَ يَرۡجُواْ ٱللَّهَ وَٱلۡيَوۡمَ ٱلۡأٓخِرَۚ وَمَن يَتَوَلَّ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ

    Open ayah 60:6

    Haƙiƙa abin koyi kyakkyawa ya kasance a gare ku game da su, ga duk wanda ya kasance yana kyakkyawan fatar haɗuwa da Allah da ranar lahira. Duk kuma wanda ya ba da baya, to lalle Allah Shi ne Mawadaci, Sha-Yabo. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar wa muminai cewa dangantaka ta jini ba za ta amfanar da su ba, domin imani da Allah shi ne kaɗai abin da zai ƙulla soyayya tsakanin muminai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba su misali da ƙissar Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mabiyansa tare da mutanensa, inda ya tabbatar musu cewa, suna da kyakkyawan abin koyi da su lokacin da suke faɗa wa mutanensu kafirai cewa lalle su ba ruwansu da su da kuma gumakan da suke bauta wa ba Allah ba, suka bayyana musu ƙarara cewa, sun kafirce wa addininsu na ƙarya, kuma gaba da ƙiyayya sun bayyana a tsakaninsu ta har abada har sai lokacin da suka yi imani da Allah shi kaɗai, suka daina haɗa shi da komai. Don haka su ma Musulmi dole ne su nuna bara’arsu ga danginsu kafirai, watau ba ruwansu da su kamar yadda Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanensa suka yi. Amma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi togaciya game da alƙawarin da Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi na cewa zai roƙa wa mahaifinsa kafiri gafarar Allah. A nan kuma Musulmi ba za su yi koyi da shi ba, domin Annabi Ibrahimu ya faɗi haka ne kafin ya kai ga fitar da ran cewa mahaifinsa zai yi imani. Amma bayan ya tabbatar cewa mahaifin nasa maƙiyin Allah ne sai ya nesanta kansa daga gare shi ya fita daga sha’aninsa, kamar yadda Allah ya ambata a cikin Suratut Tauba, aya ta 114. Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana wa mahaifinsa cewa, ba zai kare masa komai na azabar Allah ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara nuna wa muminai cewa, suna da kyakkyawan abin koyi da Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanensa lokacin da suke addu’a, suka mayar da al’amarinsu ga Ubangijinsu suna cewa, a gare shi kaɗai suka dogara cikin dukkan al’amuransu, kuma gare shi suke mayar da al’amuransu suna masu tuba, kuma suka tabbatar da cewa, zuwa gare shi ne makomarsu take. Suka ci gaba da roƙon Allah a kan kada ya nufe su da zama fitina ga kafirai ta hanyar samun galabar kafirai a kansu har su riƙa cewa, da a kan gaskiya Musulmi suke da ba za su yi nasara a kansu ba. Suka kuma roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gafarta musu zunubansu, domin shi mabuwayi ne babu abin da yake gagararsa, mai hikima ne cikin halittarsa da shari’arsa da Ƙaddararsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tabbatar wa muminai cewa, wannan kyakkyawan abin koyi na Annabi Ibrahimu da mutanensa ba kowa ne zai iya koyi da su ba a kan haka sai wanda yake fatan samun alherin duniya da lahira daga Allah (Mai tsarki da daukaka). Wanda kuwa ya bijire wa wannan kyakkyawan abin koyi, to Allah mawadaci ne ba ya buƙatar komai daga bayinsa, shi ne sha-yabo a cikin kowane hali.

  7. ۞عَسَى ٱللَّهُ أَن يَجۡعَلَ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَ ٱلَّذِينَ عَادَيۡتُم مِّنۡهُم مَّوَدَّةٗۚ وَٱللَّهُ قَدِيرٞۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 60:7

    Zai yiwu Allah Ya sanya ƙauna tsakaninku da waɗanda kuka yi gaba da su. Allah kuwa Mai ikon (yin haka) ne. Allah kuma Mai gafara ne Mai jin ƙai.

  8. لَّا يَنۡهَىٰكُمُ ٱللَّهُ عَنِ ٱلَّذِينَ لَمۡ يُقَٰتِلُوكُمۡ فِي ٱلدِّينِ وَلَمۡ يُخۡرِجُوكُم مِّن دِيَٰرِكُمۡ أَن تَبَرُّوهُمۡ وَتُقۡسِطُوٓاْ إِلَيۡهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُقۡسِطِينَ

    Open ayah 60:8

    Allah bai hana ku ba game da waɗanda ba su yaƙe ku don addini ba, ba su kuma fitar da ku daga gidajenku ba, kan ku kyautata musu, ku kuma yi musu adalci. Lalle Allah Yana son masu adalci.

  9. إِنَّمَا يَنۡهَىٰكُمُ ٱللَّهُ عَنِ ٱلَّذِينَ قَٰتَلُوكُمۡ فِي ٱلدِّينِ وَأَخۡرَجُوكُم مِّن دِيَٰرِكُمۡ وَظَٰهَرُواْ عَلَىٰٓ إِخۡرَاجِكُمۡ أَن تَوَلَّوۡهُمۡۚ وَمَن يَتَوَلَّهُمۡ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ

    Open ayah 60:9

    Allah kawai Yana hana ku ne a kan ku ƙaunaci waɗanda suka yaƙe ku don addini, suka kuma fitar da ku daga gidajenku, suka kuma taimaka a kan fitar da ku. Duk kuwa wanda ya ƙaunace su, to waɗannan su ne azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa, umarnin da ya yi musu na yanke alaƙar soyayya tsakaninsu da kafirai ba yana nufin ba za su taɓa dawowa masoya ba har abada; akwai yiwuwar Allah ya sanya soyayya a tsakaninsu da abokan gabarsu kafirai, yayin da zai shiryar da su zuwa hanyar gaskiya, su rungumi Musulunci, sai a ƙarshe su zama ‘yan’uwan juna a addini, domin Allah mai iko ne yana iya juyo zukatansu zuwa imani, kuma mai gafara ne ga bayinsa idan sun tuba sun bar kafirici, mai rahama ne gare su. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amr (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle zukatan ‘yan’adam gaba ɗayansu suna tsakanin yatsu biyu daga Yatsun Allah mai rahama kamar zuciya ɗaya, yana jujjuya ta yadda ya ga dama.” Sai kuma Manzon Allah (ﷺ) ya yi addu’a da cewa: “Ya Allah mai sarrafa zukata, ka sarrafa zukatanmu a kan ɗa’arka.” [Muslim #2654]. An karɓo daga Amru ɗan Asi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: \"Lalle na samu kaina a wani lokaci babu mutumin da nake ƙi kamar Manzon Allah (ﷺ), babu kuma wanda nake fatan in samu dama a kansa in kashe shi kamarsa. Da a ce na mutu a kan haka, da tabbas na zama ɗan wuta. Lokacin da Allah ya shigar da Musulunci cikin zuciyata, sai na zo wajen Manzon Allah (ﷺ) na ce masa: \'Shimfiɗa hannunka in yi maka mubaya\'a\'. Sai ya shifiɗa hannunsa na dama, amma sai ni kuma na danƙe hannuna\". Sai ya ce: \"Me ya same ka ne ya Amru?\" Sai na ce: \'Ina so ne in sa sharaɗi\'. Sai ya ce: \"Wane sharaɗi kuma?\". Sai na ce: \'A gafarta mini zunubaina\'. Sai ya ce: \"Ba ka san cewa Musulunci yana rushe abin da ya gabace shi ba? Hijira ma tana rushe abin da ya gabace ta. Hajji ma yana rushe abin da ya gabace shi?\" Amru ya ce: \"Babu wani mutum da na ji ina so, ina kuma ganin girmansa kamar Manzon Allah (ﷺ), har ta kai ba na iya ƙura masa ido, don ganin girmansa da nake yi. Da a ce za a nemi in yi bayanin siffofinsa to ba zan iya ba, saboda ba na iya ƙura masa idanu. Idan zan mutu a wannan yanayi, to zan yi fatan in zama ɗan Aljanna….\" [Muslim#121]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda), lokacin da Sumamatu ɗan Usal ya yi Kalmar Shahada ya karɓi Musulunci, sai ya ce wa Manzon Allah (ﷺ): \"Ya Muhammd, a da babu wata fuska da na ƙi jinin in gani a bayan ƙasa kamar fuskarka, to lalle yanzu kuma an wayi gari bubu fuskar da nake so in gani kamar fuskarka. Na rantse da Allah a da can babu addinin da na tsana kamar addininka, yanzu kuwa an wayi gari babu wani addinin da nake so kamar addininka. Na rantse da Allah a da can babu garin da nake ƙi kamar garinka, amma yanzu an wayi gari babu garin da na fi so kamar garinka…\" [Bukhari#4372 da Muslim#1764]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa muminai cewa hana su su nuna soyayya da ƙauna ga kafirai ba ya nufin kada su yi musu kyakkyawar mu’amala ko su kyautata musu. Allah bai hana su kyautata wa kafiran da ba su yaƙe su saboda Musuluncinsu ba, ba su kuma fitar da su daga gidajensu ba, suna iya kyautata musu, su yi musu adalci, su bai wa kowa haƙƙinsa yadda shari’a ta tsara, lalle Allah yana son masu yi wa kansu adalci su yi wa wasu. An karɓo daga Asma’u ‘yar Abubakar, (Allah ya kara mata yarda), ta ce: Mahaifiyata wadda take mushirika ce, watau ba ta musulunta ba, ta zo wurina a Madina a daidai lokacin da Manzon Allah (ﷺ) ya yi sulhun zaman lafiya da Ƙuraishawa tana neman taimakona, sai na tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa zan iya sadar da zumuncin mahaifiyata? Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Na’am, ki sadar da zumuncin mahaifiyarki.” [Bukhari #2620 da Muslim #1003]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Akwai wani yaro Bayahude yana yi wa Manzon Allah (ﷺ) hidima, sai ya yi rashin lafiya, sai Manzon Allah (ﷺ) ya je duba shi, ya zauna daidai kansa ya ce masa: \"Ka musulunta mana\". Sai yaron ya kalli babansa da ke zaune a wurinsa, sai baban ya ce masa: \"Yi wa baban Alƙasim biyayya\". Sai nan take ya musulunta. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya fito yana cewa: \"Na gode wa Allah da ya tserar da shi daga shiga wuta\". [Bukhari#1356]. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin kafiran da ya hana muminai su kyautata wa da cewa, su ne waɗanda suka yaƙe su saboda addininsu, suka kuma kore su daga gidajensu, ko suka taimaka wajen korarsu, to waɗannan bai halatta muminai su ƙulla soyayya da su ba, waɗanda kuwa suka kuskura suka ƙulla wata soyayya da su, to waɗannan sun zalunci kawunansu, domin sun jefa kawunansu cikin hallaka, don kuwa sun saɓa wa hanin Allah (Mai tsarki da daukaka).

  10. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا جَآءَكُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ مُهَٰجِرَٰتٖ فَٱمۡتَحِنُوهُنَّۖ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِإِيمَٰنِهِنَّۖ فَإِنۡ عَلِمۡتُمُوهُنَّ مُؤۡمِنَٰتٖ فَلَا تَرۡجِعُوهُنَّ إِلَى ٱلۡكُفَّارِۖ لَا هُنَّ حِلّٞ لَّهُمۡ وَلَا هُمۡ يَحِلُّونَ لَهُنَّۖ وَءَاتُوهُم مَّآ أَنفَقُواْۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ أَن تَنكِحُوهُنَّ إِذَآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّۚ وَلَا تُمۡسِكُواْ بِعِصَمِ ٱلۡكَوَافِرِ وَسۡـَٔلُواْ مَآ أَنفَقۡتُمۡ وَلۡيَسۡـَٔلُواْ مَآ أَنفَقُواْۚ ذَٰلِكُمۡ حُكۡمُ ٱللَّهِ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡۖ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ 

    Open ayah 60:10

    Ya ku waɗanda suka yi imani, idan muminai mata sun zo muku suna masu yin hijira, sai ku jarraba su; Allah ne Ya fi sanin imaninsu; to idan kuka san cewa su muminai ne, to kada ku mayar da su wurin kafirai; su ba halal ba ne gare su (kafirai), su ma (kafiran) ba halal ba ne a gare su; kuma ku ba su abin da suka kashe. Kuma babu laifi a kanku ku aure su idan kun ba su sadakinsu. Kada kuma ku riƙe igiyar auren mata kafirai, ku tambayi abin da kuka kashe, su ma su tambayi abin da suka kashe. Wannan shi ne hukuncin Allah da Yake hukuntawa a tsakaninku. Allah kuma Masani ne, Mai hikima,

  11. وَإِن فَاتَكُمۡ شَيۡءٞ مِّنۡ أَزۡوَٰجِكُمۡ إِلَى ٱلۡكُفَّارِ فَعَاقَبۡتُمۡ فَـَٔاتُواْ ٱلَّذِينَ ذَهَبَتۡ أَزۡوَٰجُهُم مِّثۡلَ مَآ أَنفَقُواْۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ أَنتُم بِهِۦ مُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 60:11

    Idan wasu matanku sun guje muku zuwa ga kafirai, sai kuka yi yaƙi kuka samu galaba, to ku bai wa waɗanda matansu suka guje musu kamar abin da suka kashe. Ku kuma ku kiyaye dokokin Allah wanda kuke imani da Shi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin wasu hukunce-hukunce waɗanda suka danganci aure tsakanin muminai da mushirikai. Bayan Manzon Allah (ﷺ) ya yi sulhu da mushirikan Makka a shekara ta shida bayan hijira a Hudaibiyya, daga cikin abin da takardar sulhun ta ƙunsa akwai cewa, duk wanda zai gudu daga wajen Musulmi zuwa wurin mushirikai, to ba za su mayar musu da shi ba, amma kuma duk wanda zai gudu daga cikin mushirikai zuwa wurin Musulmi, to dole su dawo musu da shi. Annabi (ﷺ) ya sa hannu a kan wannan yarjejeniya, ya mayar musu da duk wani namiji da ya gudo daga wajensu. Sai dai su mata Allah (Mai tsarki da daukaka) ya togace su daga wannan sharaɗin, saboda girman ɓarnar da za ta faru idan an mayar da su wurin kafirai bayan sun gudo suna muminai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ga muminai ya bayyana musu cewa, idan muminai mata masu hijira suka zo musu, watau waɗanda suka gudo daga ƙasar kafirai zuwa ƙasar Musulmi, to su jarraba gaskiyar imaninsu. Allah dai shi ne mafi sanin imaninsu, domin shi ne ya san abin da yake ɓoye a cikin zukata. To idan sun bincika sun gane su muminai ne da gaske, to kada su mayar da su ga mazajensu kafirai, domin ba ya halatta ga muminai mata su auri mazaje kafirai, su ma kafirai maza ba ya halatta su auri mata muminai. To idan Musulmi suka riƙe matan kafirai waɗanda suka gudo suna masu imani, to sai su mayar wa da mazajensu sakadin da suka kashe wajen aurensu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa babu laifi su auri waɗannan matan bayan sun gama iddarsu sun kuma biya sadakinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana mumini zama da matarsa kafira ko wadda ta yi ridda ta bar Musulunci, domin kafircinta ya yanke igiyar aure da ke tsakaninsu. Sannan duk matan da suka yi ridda suka gudu zuwa wajen kafirai, to su nemi kafirai su biya su abin da suka kashe na sadakin aurensu, su ma kafiran su nemi Musulmi su biya su sadakin matansu da suka musulunta suka gudo wajen Musulmi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, wannan abin da aka ambata na mayar wa da kowa sadakinsa shi ne hukuncinsa da ya yanke a tsakaninsu, domin shi masanin halayen bayinsa ne da ayyukansu, babu abin da yake ɓuya gare shi, kuma mai hikima ne cikin duka ayyukansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, idan aka ƙaddara cewa wasu daga cikin matan Musulmi sun yi ridda sun gudu wajen kafirai suka nemi kafirai su dawo musu da abin da suka kashe wajen aurensu amma suka ƙi, to idan an samu wata ganima ta yaƙi daga waɗannan kafiran, to sai a ba wa mazajen da matansu suka yi ridda suka gudu zuwa kafirai gwargwadon abin da suka kashe wajen aurensu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su kiyaye dokokin Allah wanda suka yi imani da shi, su bi umarninsa su kuma guje wa haninsa. An karɓo daga Al-Miswaru ɗan Makhrama (Allah ya kara masa yarda) da Marwana ɗan Hakam suka ce: Yayin da Manzon Allah (ﷺ) ya rubuta takardar sulhu tare da Suhailu ɗan Amru a ranar Hudaibiyya, yana daga cikin abin da Suhailu ya sharɗanta cewa: \"Duk wani wanda zai zo wajenka daga cikinmu, ko da kuwa yana kan addininka, to za ka dawo mana da shi\". A nan ne Manzon Allah (ﷺ) ya mayar da Abu Jandal ɗan Suhailu. Duk kuma wani namiji da ya zo wa Manzon Allah a wannan lokaci sai da ya mayar da shi ko da kuwa Musulmi ne. Sannan sai mata muminai masu hijira suka zo. Ummu Kulsum ‘yar Uƙbata ɗan Abu Mu’aiɗ tana cikin waɗanda suka gudu zuwa ga Manzon Allah (ﷺ) tana budurwa ‘yar ƙarama, sai danginta suka zo suna neman Manzon Allah (ﷺ) ya mayar musu da ita, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar. [Bukhari #2711]. An karɓo daga Al-Miswaru ɗan Makhrama (Allah ya kara masa yarda) da Marwana ɗan Hakam suka ce: Lokacin da Manzon Allah (ﷺ) ya ƙulla yarjejeniya da Ƙuraishawa a ranar Hudaibiyya, sai wasu mata muminai suka je masa, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar har zuwa inda yake cewa: (Kuma babu laifi a kanku idan kun aure su....) Sai Umar (Allah ya kara masa yarda) a wannan lokacin ya saki wasu mata biyu waɗanda suke kan shirka, watau ba su musulunta ba. [Bukhari #2731].

  12. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا جَآءَكَ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ يُبَايِعۡنَكَ عَلَىٰٓ أَن لَّا يُشۡرِكۡنَ بِٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَلَا يَسۡرِقۡنَ وَلَا يَزۡنِينَ وَلَا يَقۡتُلۡنَ أَوۡلَٰدَهُنَّ وَلَا يَأۡتِينَ بِبُهۡتَٰنٖ يَفۡتَرِينَهُۥ بَيۡنَ أَيۡدِيهِنَّ وَأَرۡجُلِهِنَّ وَلَا يَعۡصِينَكَ فِي مَعۡرُوفٖ فَبَايِعۡهُنَّ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُنَّ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 60:12

    Ya kai wannan Annabi, idan muminai mata suka zo maka suna yi maka mubaya’a a kan ba za su yi shirka da Allah ba, kuma ba za su yi sata ba, ba kuma za su yi zina ba, kuma ba za su kashe ‘ya’yansu ba, kuma ba za su zo da wani ƙage ba wanda za su ƙirƙira (game da ɗan da suka haifa) a tsakanin hannayensu da ƙafafuwansu, kuma ba za su saɓa maka ba game da wani aiki na kirki, to sai ka yi musu mubaya’a, ka kuma nema musu gafarar Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) sigar da zai yi wa mata mubaya’a a kanta idan sun zo masa don yi masa mubaya’a, kamar yadda ya faru lokacin buɗe Makka. Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya yi musu mubaya’a a kan abubuwa shida: <b>Na farko </b>, ba za su haɗa Allah da komai ba, za su bauta masa shi kaɗai. <b>Na biyu </b>, ba za su yi sata ba. <b>Na uku </b>, ba za su yi zina ba, kamar yadda abin ya watsu a zamanin jahiliyya a tsakanin mata masu zaman kansu da waɗanda suke riƙar su a matsayin dadiro. <b>Na huɗu </b>, ba za su kashe ‘ya’yansu ba, kamar yadda kashe ‘ya’ya mata ya zama ruwan dare a tsakanin kafiran Larabawa a zamanin jahiliyya. <b>Na biyar </b>, ba za su zo da wani ƙage ba na \'ya\'yan da za su haifa su maƙala wa mazajen da ba su ne iyayensu ba, kamar yadda mace a jahiliyya za ta yi zina da mazaje da yawa idan ta haihu sai ta zaɓi ɗaya daga cikinsu ta maƙala masa ɗan; ko tana matar aure sai ta haifi ɗan zina sannan ta jingina wa mijinta. <b>Na shida </b>, ba za su saɓa wa Manzon Allah (ﷺ) game da wani aikin alheri ba, kamar idan ya hana su koke-koken mutuwa ko aske kai ko yaga tufafi saboda faruwar wata musiba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) cewa, idan sun yarda da waɗannan sharuɗɗa to ya yi musu mubaya’a, ya kuma nema musu gafarar Allah game da zunubbansu bayan ya gama mubaya’a da su, lalle Allah mai gafara ne ga duk wanda ya tuba daga cikin bayinsa, mai jin ƙai ne a gare su. An karɓo daga A’isha, (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance ya riƙa jarraba mata muminai da suka yiwo hijira da wannan, duk wadda ta yarda da wannan sharaɗin sai ya ce mata: “Na yi miki mubaya’a” da magana. Na rantse da Allah, hannunsa bai taɓa hannun wata mace ba yayin yi mata mubaya’a. Bai yi musu mubaya’a ba sai da faɗarsa: “Na yi miki mubaya’a a kan haka.” [Bukhari #2713 da Muslim #1866]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na halarci sallar idin Ramadana tare da Manzon Allah (ﷺ), sai ya gangaro ya zo inda mata suke sai ya karanta musu wannan ayar har zuwa ƙarshenta, sannan ya ce musu: “Shin kuna kan wannan ne?” Sai wata mata ta ce: “Na’am.” [Bukhari #979 da Muslim #4895]. An karɓo daga Umaima ‘yar Ruƙaiƙa (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Na zo wurin Annabi (ﷺ) tare da mata don yi masa mubaya’a, sai ya sharɗanta mana abin da ya zo a cikin Alƙur’ani cewa ba za mu haɗa Allah da komai ba, har ya kai inda Allah yake cewa: (Kuma ba za su saɓa maka ba game da wani aiki na kirki...) sai ya ce: “Cikin abin da za ku iya wanda bai fi ƙarfinku ba.” Sai muka ce: “Allah da Manzonsa sun fi tausaya mana fiye da kawunanmu. Ya Manzon Allah, shin ba ka yi hannu da mu ba?” Sai ya ce: “Ni ba na hannu da mata, kawai maganata ga mace ɗari daidai take da maganata ga mace ɗaya.” [Ahmad #27010 da Tirmizi #1687 da Nasa’i #4181 da Ibn Maja #2874].

  13. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَوَلَّوۡاْ قَوۡمًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ قَدۡ يَئِسُواْ مِنَ ٱلۡأٓخِرَةِ كَمَا يَئِسَ ٱلۡكُفَّارُ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡقُبُورِ

    Open ayah 60:13

    Ya ku waɗanda kuka yi imani, kada ku jiɓinci mutanen da Allah ya yi fushi da su, haƙiƙa sun ɗebe ƙauna daga lahira kamar yadda kafirai suka ɗebe ƙauna daga na ƙabarurruka. A wannan aya ta ƙarshen Sura Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira muminai ya ja kunnensu da cewa kada su kuskura su jiɓinci mutanen da ya yi fushi da su, watau Yahudawa waɗanda, saboda yawan saɓonsu da kafircinsu har Allah ya yi hushi da su, sun ɗebe ƙauna daga samun wani rabo a lahira, domin ba rashin sanin gaskiya ba ne ya jefa su cikin kafirci, sun san gaskiya sarai amma sai suka take ta, don haka ba sa sa ran samun wani kyakkyawan sakamako daga Allah a ranar lahira, kamar yadda kafirai waɗanda suka mutu aka binne su a ƙaburburansu, aka nuna musu makomarsu a wutar Jahannama suka fitar da tsammanin samun kuɓuta a ranar alƙiyama.