الصف
As-Saff
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 61:1Duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa ya yi tasbihi ga Allah; Shi kuma Mabuwayi ne, Mai hikima.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِمَ تَقُولُونَ مَا لَا تَفۡعَلُونَ
Open ayah 61:2Ya ku waɗanda suka yi imani, don me kuke faɗar abin da ba kwa aikatawa?
كَبُرَ مَقۡتًا عِندَ ٱللَّهِ أَن تَقُولُواْ مَا لَا تَفۡعَلُونَ
Open ayah 61:3Ya isa babban abin ƙi a wurin Allah, ku riƙa faɗin abin da ba kwa aikatawa.
إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلَّذِينَ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِهِۦ صَفّٗا كَأَنَّهُم بُنۡيَٰنٞ مَّرۡصُوصٞ
Open ayah 61:4Lalle Allah Yana son waɗanda suke yin yaƙi dominsa sahu-sahu kai ka ce su gini ne wanda yake ɗamfare da juna. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da bayanin girmansa da ɗaukakarsa da cewa, duk abin da yake sammai da wanda yake ƙasa sun tsarkake shi daga duk wani abu wanda bai dace da shi ba, kuma shi ne mabuwayi wanda babu abin da yake gagarar sa, mai hikima ne cikin halittarsa da ƙaddararsa da shari’arsa. Sai kuma ya kira muminai ya tsawatar musu game da faɗin maganar da ba za su yi aiki da ita ba, domin ba abu ne mai kyau ga mumini ba ya riƙa faɗa ba cikawa, domin wannan wani babban abin ƙi ne a wurin Allah bawansa ya faɗi abin da ba zai yi aiki da shi ba, ko ya faɗi abin da bai aikata ba ya ce ya aikata, dole ne ya zamanto mai gaskiya tare da Allah (Mai tsarki da daukaka). Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Kafin a wajabta wa Musulmi yin jihadi wasu daga cikin muminai sun riƙa cewa: Ina ma a ce Allah ya nuna mana wani aiki na kirki da ya fi so, da mun aikata shi? Sai Allah ya sanar da Manzonsa cewa, mafi soyuwar ayyuka a wajensa shi ne imani da Allah imanin da babu shakka a cikinsa da yaƙar masu saɓa masa waɗanda suka ƙi yin imani da shi, suka ƙi yarda da shi. To lokacin da umarni da yin jihadi ya sauko, sai wasu daga cikin muminai abin bai yi musu daɗi ba; umarnin ya yi musu nauyi, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce musu: “Don me kuke faɗar abin da ba kwa aikatawa?” [Ibn Jarir, Tafsir, juzu’i na 23, shafi na 606-607]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Alamar munafuki uku ce; idan ya yi magana sai ya yi ƙarya; idan kuma an yi alƙawari da shi sai ya saɓa; idan kuma aka amince masa sai ya ci amana.” [Bukhari #33 da Muslim #59]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi masu yaƙi don ɗaukaka addininsa, da cewa, lalle yana son muminai masu fita suna yaƙi saboda Allah sahu-sahu a kan dawakansu ko tafe da ƙafafunsu, kamar gini wanda sashinsa yake manne da sashe, watau a cikin tsari da haɗin kai ba tare da sun bar wani giɓi a tsakaninsu ba. An karɓo daga Muɗarrif ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na sami labarin wani hadisi na Abu Zarri sai na so mu haɗu don in tambaye shi, sai muka haɗu wata rana sai na ce masa: Na sami labarin wani hadisi naka nake son haɗuwa da kai don in tambaye ka, sai ya ce: To ga shi mun haɗu, tambayi abin da kake so. Sai na ce: Na sami labarin cewa kai kana cewa: Ka ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Mutum uku Allah yana son su mutum uku kuma Allah yana ƙin su.” Sai ya ce: Haka ne. Kuma ba na zaton zan yi wa badaɗayina Muhammad (ﷺ) ƙarya. Ya faɗi haka har sau uku. Sai na ce masa: Su wane ne ukun da Allah (Mai tsarki da daukaka) yake so? Sai ya ce: Mutumin da ya fita yaƙi domin Allah, ya haɗu da abokin gaba yana mai jihadi mai neman lada, ya yi yaƙi har aka kashe shi. Kuma wannan abu ne da za ku same shi a Littafin Allah, inda yake cewa: “Lalle Allah yana son masu yaƙi domin addininsa sahu-sahu.”; da mutumin da maƙocinsa yake cutar da shi shi kuma yana ta haƙuri game da cutarwarsa, yana neman lada a wurin Allah har lokacin da Allah ya isar masa shi ta hanyar mutuwa ko rayuwa; da mutumin da yake tafiya cikin ƙungiya ta mutane, sai sun yi tafiya har sun gaji barci ko gyangyaɗi ya fara kama su sai su ya da zango a ƙarshen dare, shi kuma sai ya tashi ya nufi wajen alwalarsa da sallarsa. To sai na ce: Su wane ne kuma mutum ukun da Allah yake ƙi? Sai ya ce: Mai fariya mai taƙama, kuma za ku samu wannan a Littafin Allah, inda yake cewa: “Lalle Allah ba ya so mai taƙama mai fariya.” [Luƙman: 18]; da kuma marowaci mai gori; da ɗan kasuwa mai yawan rantsuwa. [Ahmad #21530 da Tirmizi #2568].
وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ لِمَ تُؤۡذُونَنِي وَقَد تَّعۡلَمُونَ أَنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡۖ فَلَمَّا زَاغُوٓاْ أَزَاغَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُمۡۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ
Open ayah 61:5Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da mutanensa: “Ya ku mutanena, don me kuke cuta ta, alhali kuma kun san cewa lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku?” To lokacin da suka kauce sai Allah ya kautar da zukatansu. Allah kuma ba ya shiryar da mutane fasiƙai.
وَإِذۡ قَالَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ يَٰبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُم مُّصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيَّ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَمُبَشِّرَۢا بِرَسُولٖ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِي ٱسۡمُهُۥٓ أَحۡمَدُۖ فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ قَالُواْ هَٰذَا سِحۡرٞ مُّبِينٞ
Open ayah 61:6Kuma (ka tuna) lokacin da Isa ɗan Maryamu ya ce: “Ya ku ‘ya’yan Isra’ila, lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da yake gabanina na Attaura, kuma mai albishir da wani manzo da zai zo bayana, sunansa Ahmadu.” To lokacin da ya zo musu da (ayoyi) bayyanannu sai suka ce: “Wannan sihiri ne mabayyani.” A waɗannan ayoyi kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi muminai ne ya ja musu kunne ta hanyar nuna musu mummunan halin Yahudawa ga Annabin da Allah ya aiko musu, watau Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) don ya shiryar da su ya kuma kuɓutar da su daga zaluncin Fir’auna da mutanensa, amma sai suka riƙa cutar da shi da maganganunsu da ayyukansu, har ya riƙa kiran su yana tambayar su cewa, me ya sa suke cutar da shi, alhalin sun san cewa shi Manzon Allah ne zuwa gare su? Watau wanda ya kamata su fi kula da haƙƙinsa da girmansa da kiyaye masa mutuncinsa, saboda shi manzo ne ya fi kowa kyautatawa ga mutanensa don girman abin da ya zo musu da shi. To amma Banu Isra’ila sai suka kauce wa tafarki madaidaici, suka yi watsi da abin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo musu da shi, don haka sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kautar da zukatansu daga karɓar gaskiya da aiki da ita, saboda wannan shi ne zaɓinsu; Allah kuma ba ya shiryar da mutanen da suka tabbata fasiƙai masu bijire wa manzannin Allah waɗanda suka zo musu da shiriya. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa muminai labarin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), lokacin da ya kirawo mutanensa Banu Isra’ila ya tabbatar musu cewa, shi Manzon Allah ne zuwa gare su, ya zo musu yana mai gaskata littafin Attaura da ya gabace shi, don haka ba shi ne farkon manzo a cikinsu ba, sannan ba shi zai zama manzo na ƙarshe da Allah zai aiko a bayan ƙasa ba, don haka ne ma yake yi musu albishir da wani manzo da zai zo a bayansa mai suna Ahmadu, watau Annabi Muhammadu (ﷺ). An karɓo daga Ubadatu ɗan Samit (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An ce: Ya Manzon Allah, ba mu labarin kanka, sai ya ce: “Ni ne addu’ar babana Ibrahim, kuma ƙarshen wanda ya yi albishir da ni shi ne Isa ɗan Maryam (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).” [Ibni Asakir, Tarikhu Dimashaƙ , juzu’i na 3, shafi na 393. Dubi, Albani, As-Silsilatus Sahiha , #1546]. An karɓo daga Jubairu ɗan Muɗ’im (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ina da sunaye biyar: Ni ne Muhammad; ni ne Al-Mahi wanda Allah yake share kafirci da ni; ni ne Al-Hashiru, wanda Allah yake tattaro mutane a bayana (ranar alƙiyama); ni ne Al-Aƙibu.” [Bukhari #4896 da Muslim #2354]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk da kasancewar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo wa mutanensa da hujjoji bayyanannu masu tabbatar da gaskiyarsa, amma sai mutanensa suka ƙaryata shi suka ce abin da ya zo musu da shi sihiri ne bayyananne, don haka ba za su bi shi ba.
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ وَهُوَ يُدۡعَىٰٓ إِلَى ٱلۡإِسۡلَٰمِۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 61:7Ba wanda kuma ya fi zalunci kamar wanda ya ƙaga wa Allah ƙarya, alhali kuwa shi ana kiran sa zuwa Musulunci. Allah kuma ba Ya shiryar da mutane azzalumai.
يُرِيدُونَ لِيُطۡفِـُٔواْ نُورَ ٱللَّهِ بِأَفۡوَٰهِهِمۡ وَٱللَّهُ مُتِمُّ نُورِهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Open ayah 61:8Suna nufin su dusashe hasken Allah da bakunansu, Allah kuwa Mai cika haskensa ne ko da kafirai sun ƙi.
هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُشۡرِكُونَ
Open ayah 61:9Shi ne Wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya don Ya ɗora shi a kan kowane addini, ko da kuwa mushirikai sun ƙi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tabbatar da cewa, da’awar Musulunci da ƙarfafan hujjojinta sun zo wa mutane, to amma wasu da dama sun zaɓi su kafirce mata, su yaƙi manzannin Allah bisa zalunci, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babu wani azzalumi kamar wanda ya ƙiriƙri ƙarya ya jingina wa Allah, inda ya riƙa ɗaukar gumaka yana bauta musu ba Allah ba, alhalin shi kuma ana kiran sa zuwa Musulunci addinin kaɗaita Allah da bauta, an kuma bayyana masa hujjoji daban-daban amma saboda zaluncinsa ya sa ƙafa ya shure su; to ya sani Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai, waɗanda suka cuci kansu da aikata shirka da saɓon Allah. Ba ma iya nan suka tsaya ba; suna ma ta ƙoƙarin ganin sai sun disashe hasken Allah da irin miyagun maganganunsu da suke yi don su ɓata Musulunci. To amma ko sun ƙi ko sun so, sai Allah ya cika addininsa, ya bayyana shi a ko’ina a bayan ƙasa, ya kuma ba shi rinjaye a kan sauran gurɓatattun addinai, ya ɗaukaka kalmarsa, domin kuwa Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne wanda ya aiko da Manzonsa Muhammadu ɗan Abdullahi (ﷺ) da addinin Musulunci, addinin shiriya mai ƙunshe da ɗimbin alherai, kuma addinin gaskiya mai ɗauke da ilimi mai matuƙar amfani da aiki nagari, domin ya ɗora shi a kan dukkan addinai ko da kuwa mushirikai suna ƙin haka. To tabbas sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kafa shi a bayan ƙasa da ƙarfin hujja da gamsassun bayanai. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Dare da rana ba za su gushe ba har sai an bauta wa gumaka, watau Lata da Uzza.” Ta ce na ce: Ya Manzon Allah, ni a da ina zaton cewa yayin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “Shi ne wanda ya aiko da Manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya don ya ɗora shi a kan dukkanin addinai ko da kuwa mushirikai sun ƙi .”, na zaci cewa hakan ya gama tabbata. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Nan gaba dai hakan zai kasance lokacin da Allah ya ga dama.” [Muslim #2907]. An karɓo daga Saubanu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah ya tattaro mini duniya wuri guda sai na ga gabashinta da yammacinta, kuma lalle sai mulkin al’ummata ya kai inda aka tattaro mini daga gare ta.” [Muslim #2889]. An karɓo daga Tamimuddari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle wannan al’amari (wato Musulunci) sai ya kai duk inda dare da rana suka kai, Allah ba zai bar wani gidan laka ba ko na gashin raƙuma (wato birni da ƙauye) face sai ya shigar da wannan addinin cikinsa, da izzar mai izza ko da ƙasƙancin ƙasƙantacce, izzar da Allah zai ɗaukaka Musulunci da ita da ƙasƙancin da zai ƙasaƙantar da kafirci da shi.” [Ahmad #16957].
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ هَلۡ أَدُلُّكُمۡ عَلَىٰ تِجَٰرَةٖ تُنجِيكُم مِّنۡ عَذَابٍ أَلِيمٖ
Open ayah 61:10Ya ku waɗanda suka yi imani, yanzu ba Na nuna muku ku wani ciniki da zai tserar da ku daga azaba mai raɗaɗi ba?
تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتُجَٰهِدُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ بِأَمۡوَٰلِكُمۡ وَأَنفُسِكُمۡۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 61:11(Shi ne) ku yi imani da Allah da Manzonsa ku kuma yi jihadi don Allah da dukiyoyinku da rayukanku. Wannan shi ne ya fiye muku alheri, idan kun kasance kuna sane (da haka).
يَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡ وَيُدۡخِلۡكُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ وَمَسَٰكِنَ طَيِّبَةٗ فِي جَنَّٰتِ عَدۡنٖۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 61:12(Idan kun yi haka) zai gafarta muku zunubanku Ya kuma shigar da ku gidajen Aljanna (waɗanda) ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu da kuma wuraren zama masu kyau, a cikin gidajen Aljanna na dawwama. Wannan shi ne babban rabo.
وَأُخۡرَىٰ تُحِبُّونَهَاۖ نَصۡرٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَتۡحٞ قَرِيبٞۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 61:13Da kuma wata ɗayar da kuke so; (watau) nasara daga Allah da kuma buɗi a kusa. Ka kuma yi wa muminai albishir. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira muminai kira na musamman, domin ya kwaɗaitar da su a kan wani gagarumin aiki mai cike da tagomashi wanda ya kira shi da kasuwanci da zai tserar da su daga azaba mai raɗaɗi. Wannan kasuwanci mai riba kuwa shi ne, su yi imani da Allah da Manzonsa (ﷺ), su kuma yi jihadi don ɗaukaka addinin Allah ta hanyar aiki da dukiyoyinsu da kawunansu, su kuma daure ko da ransu ba haka yake so ba saboda wahalar da ke cikinsa. To amma su sani yin haka babban alheri ne a gare su in sun kasance sun san haka. An karɓo daga Abdullahi ɗan Hubshi Al-Khas’ami (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa, waɗanne ayyuka ne suka fi falala? Sai ya ce: “Imanin da babu kokwanto a cikinsa, da jihadin da babu satar ganima a cikinsa, da hajji karɓaɓɓiya.” [Nasa’i #4986]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa: Wane aiki ne ya fi falala? Sai ya ce: “Imani da Allah da Manzonsa.” Sai aka ce: Sai kuma me? Sai ya ce: “Jihadi domin Allah.” Sai aka ce: Sai kuma me? Sai ya ce: “Hajji karɓaɓɓiya.” [Bukhari #1519 da Muslim #83]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana gwaggwaɓar ribar da muminai za su samu idan sun shiga wannan kasuwanci, shi ne zai gafarta musu zunubansu manya da ƙanana, a ranar lahira kuma zai shigar da su gidajen Aljanna da ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashin gine-ginensu da bishiyoyinsu, ya kuma shigar da su wasu wuraren zama masu kyau a cikin gidajen Aljanna na zama dindindin babu ranar fita daga cikinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wannan sakamako nasu a lahira a matsayin babban rabo da babu wani rabo da ya kai shi daraja. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, bayan wancan rabo na lahira, akwai kuma wata ribar kuma ta duniya wadda zai gaggauto musu da ita wadda kuma suke matuƙar son ta, ita ce Allah ya ba su nasara a kan maƙiyansu, da kuma wani buɗi na kusa, watau cin garin Makka da yaƙi da ma wasu garuruwa bayansa da Allah zai faɗaɗa da’irar Musulunci da shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa ya yi wa muminai albishir da ganin abin da zai faranta musu rai na samun nasara a nan duniya da dacewa da babban rabo a lahira.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُونُوٓاْ أَنصَارَ ٱللَّهِ كَمَا قَالَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ لِلۡحَوَارِيِّـۧنَ مَنۡ أَنصَارِيٓ إِلَى ٱللَّهِۖ قَالَ ٱلۡحَوَارِيُّونَ نَحۡنُ أَنصَارُ ٱللَّهِۖ فَـَٔامَنَت طَّآئِفَةٞ مِّنۢ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَكَفَرَت طَّآئِفَةٞۖ فَأَيَّدۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ عَلَىٰ عَدُوِّهِمۡ فَأَصۡبَحُواْ ظَٰهِرِينَ
Open ayah 61:14Ya ku waɗanda suka yi imani, ku zama masu taimaka wa (addinin) Allah, kamar yadda Isa ɗan Maryamu ya ce da Hawariyawa: “Su wane ne masu taimaka mini zuwa ga Allah?” Hawariyawan suka ce: “Mu ne masu taimaka wa Allah.” Sai wata ƙungiya daga Bani Isra’ila suka yi imani, wata ƙungiya kuma ta kafirta, sai Muka ƙarfafa waɗanda suka yi imani a kan maƙiyansu, sai suka wayi gari suna masu cin nasara. A ayar ƙarshe ta wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake jaddada kiransa ga muminai da su tashi tsaye su zama masu taimakon addinin Allah a koyaushe, su taimaka wa Manzon Allah (ﷺ) wajen yaɗa kiran Allah da isar da shi ko’ina a duniya, kamar yadda Hawariyawa almajiran Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka taimaka masa wajen yaɗa addininsa, lokacin da ya tambaye su cewa, su wane ne za su taimaka masa zuwa ga Allah? Sai suka amsa masa da cewa, su ne waɗanda za su taimaki addinin Allah. An karɓo daga Abdullah ɗan Mas\'ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: \"Babu wani annabi gabanina da Allah ya aiko shi cikin al\'ummarsa, sai ya kasance a cikin al\'ummar tasa yana da hawariyawa da sahabbai waɗanda suke riƙo da sunnarsa, suke kuma koyi da umarninsa...\" [Muslim#50]. Daga nan sai Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ci gaba da yaɗa addinin Allah shi da Hawariyawa almajiransa, har ya zamanto an samu wata ƙungiya daga cikin Banu Isra’ila sun yi imani da shi, wasu kuma sun kafirce masa, sai Allah ya ƙarfafi waɗanda suka yi imani a kan maƙiyansu kafirai, sai suka wayi gari su ne masu rinjaye a kansu.