الجمعة

Al-Jumu'a

Friday · Surah 62 · Ayahs: 11 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ ٱلۡمَلِكِ ٱلۡقُدُّوسِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ

    Open ayah 62:1

    Duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa yana yin tasbihi ga Allah Sarki, Tsarkakakke, Mabuwayi, Mai hikima.

  2. هُوَ ٱلَّذِي بَعَثَ فِي ٱلۡأُمِّيِّـۧنَ رَسُولٗا مِّنۡهُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِهِۦ وَيُزَكِّيهِمۡ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلُ لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

    Open ayah 62:2

    Shi ne wanda Ya aiko wa (Larabawa) ummiyyai (watau waɗanda ba sa karatu da rubutu) Manzo daga cikinsu, yana karanta musu ayoyinsa, yana kuma tsarkake su, kuma yana sanar da su Alƙur’ani da hikima, ko da yake a da can sun kasance cikin ɓata mabayyani.

  3. وَءَاخَرِينَ مِنۡهُمۡ لَمَّا يَلۡحَقُواْ بِهِمۡۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 62:3

    Da kuma wasunsu (waɗanda) tukuna ba su riske su ba. Shi ne kuwa Mabuwayi, Mai hikima.

  4. ذَٰلِكَ فَضۡلُ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ

    Open ayah 62:4

    Wannan falala ce daga Allah, Yana bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuwa Ma’abocin babbar falala ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da bayanin cewa, duk abin da yake sammai da wanda yake ƙasa suna yi masa tasbihi, watau suna tsarkake shi daga duk wani aibi da nakasa da duk abin da bai dace da shi ba. Shi ne cikakken Sarki wanda ya kaɗaita da mulkin duk abin da yake cikin sammai da wanda yake ƙasa. Tsarkakakke daga kowace irin tawaya. Mabuwayi wanda babu mai gagarar sa. Mai hikima a cikin halittarsa da shari’arsa da ƙaddararsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin babbar baiwa da ya yi wa wannan al’umma da ya aiko musu da Manzo daga cikin al’ummar Larabawa ummiyyai, watau waɗanda ba sa karatu ba sa rubutu, kamar yadda shi ma Manzon haka yake ba ya karatu da rubutu. Ya zo yana karanta musu ayoyin Littafin Allah da ya saukar masa, watau Alƙur’ani, yana kuma tsarkake su daga ƙazantar kafirci da ta shirka da ta miyagun ɗabi’u; yana kuma koyar da su hukunce-hukuncen Alƙur’ani da sunnarsa da bayanin ma’anonin ayoyin Allah. A da kafin zuwansa su Larabwa sun kasance suna rayuwa cikin duhu ne da ɓata mabayyani, domin ba su san komai ba sai bautar gumaka da aikata miyagun ɗabi’u na jahiliyya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, aiken Manzon Allah (ﷺ) bai taƙaita a cikin Larabawa kaɗai ba; ya haɗa har da wasu al’ummu daban waɗanda su ma saƙon zai kai gare su nan gaba, su yi imani da shi, su zamanto cikin al’ummarsa, domin shi Allah mabuwayi ne babu abin da ya fi ƙarfinsa, kuma mai hikima ne a halittarsa da shari’arsa da ƙaddararsa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mun kasance muna zaune a wurin Manzon Allah (ﷺ) sai aka saukar masa ‘Suratul Jumu’a’, a cikinta Allah yake cewa: “Da kuma wasu waɗanda tukunna ba su riske su ba .” , Sai na ce: “Su wane ne waɗannan ya Manzon Allah?” Annabi bai amsa wa Abu Huraira tambayarsa ba, har sai da ya maimaita ta sau uku. Abu Huraira ya ce: Salmanu mutumin Farisa yana zaune cikinmu, sai Manzon Allah (ﷺ) ya dafa Salmanu da hannunsa ya ce: “Da a ce imani yana can wajen tauraron Surayya ne, to da wasu mazaje daga waɗannan sun kai gare shi.” [Bukhari #4897 da Muslim #2546]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan aike da ya yiwo na Manzonsa (ﷺ) wanda kuma ya shafi kowa da kowa, wata falalarsa ce da yake bayar da ita ga wanda ya ga dama, don haka ya zaɓi wannan al’umma ya yi mata wannan babbar baiwa, domin shi ma’abocin falala ne wadda take mai girma.

  5. مَثَلُ ٱلَّذِينَ حُمِّلُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ ثُمَّ لَمۡ يَحۡمِلُوهَا كَمَثَلِ ٱلۡحِمَارِ يَحۡمِلُ أَسۡفَارَۢاۚ بِئۡسَ مَثَلُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 62:5

    Misalin waɗanda aka ɗora wa Attaura sannan ba su ɗauke ta ba, kamar misalin jaki ne da yake ɗauke da wagagen littattafai. Misalin mutanen da suka ƙaryata ayoyin Allah ya munana. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane azzalumai.

  6. قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ هَادُوٓاْ إِن زَعَمۡتُمۡ أَنَّكُمۡ أَوۡلِيَآءُ لِلَّهِ مِن دُونِ ٱلنَّاسِ فَتَمَنَّوُاْ ٱلۡمَوۡتَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

    Open ayah 62:6

    Ka ce: “Ya ku waɗanda suka zama Yahudawa, idan kun riya cewa ku ne masoyan Allah ban da sauran mutane, to ku yi burin mutuwa, idan kun kasance masu gaskiya ne.”

  7. وَلَا يَتَمَنَّوۡنَهُۥٓ أَبَدَۢا بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 62:7

    Ba za su yi burin ta ba har abada saboda abin da hannayensu suka gabatar. Allah kuwa Masanin azzalumai ne.

  8. قُلۡ إِنَّ ٱلۡمَوۡتَ ٱلَّذِي تَفِرُّونَ مِنۡهُ فَإِنَّهُۥ مُلَٰقِيكُمۡۖ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَىٰ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 62:8

    Ka ce (da su): “Lalle ita mutuwar da kuke gudun ta, lalle za ta haɗu da ku; sannan za a mayar da ku wurin Masanin ɓoye da sarari, sannan Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake fito da bayanin girman ni’imar da ya yi wa wannan al’umma ta aiko musu Manzon Allah (ﷺ) a cikinsu, wanda a dalilinsu suka zarce duk sauran al’ummu da suka gabata, duk kuwa da kasancewar Larabawa ummiyyai ne lokacin da aka aiko shi, amma har sun zo sun fi Yahudawa falala da ɗaukaka, domin malamansu da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da su Attaura ya kuma umarce su da su yi aiki da ita su koyar da ‘yan’uwansu hukunce-hukuncenta, domin su ma su yi aiki da ita, sun sa ƙafa sun take ilimin da Allah ya ba su, sun ƙi aiki da shi, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, misalinsu kamar misalin jaki ne wanda yake ɗauke da wagagen littattafan ilimi a bayansa, amma bai san abin da yake ɗauke da shi ba, ballantana ya san darajarsa, kawai dai yana dakon wahala ne a bayansa, babu wata daraja da za su ƙara masa. To hakanan su ma waɗannan Yahudawan babu wata ɗaukaka da za su samu don sun san littafin Attaura amma ba su yi aiki da shi ba, ba su kuma amfana da abin da yake cikinsa na bushara da zuwan Manzon Allah (ﷺ) ba, don haka suka ci gaba da ƙaryata ayoyin da ya zo musu da su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tir da misalin waɗannan mutane azzalumai masu ƙaryata ayoyinsa, ya kuma tabbatar musu cewa, shi ba ya shiryar da azzaluman mutane waɗanda suka zaɓi kafirci suna sane. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani zaluncin na Yahudawa da cika bakinsu da taurin kansu, yayin da suke da’awar cewa, wai su ne masoyan Allah ban da sauran mutane, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da cewa ya kira su ya ƙalubalance su a kan wannan da’awar tasu cewa, su yi burin mutuwa idan har gaskiya suke faɗa na cewa, su ne masoyan Allah ban da sauran mutane, domin duk masoyi zai so gaggawar haɗuwa da masoyinsa, musamman idan yana da tabbacin cewa abin da zai samu a wurinsa ya fi wanda yake ciki. To amma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya san ƙarya suke yi ba za su iya burin mutuwa ba har abada, sun ma fi burin su dawwama a duniya ko su yi tsawon rai saboda ayyukansu na kafirci da saɓon Allah da suka tabka a rayuwarsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) masani ne ga azzalumai, babu abin da zai ɓuya gare shi na ayyukansu, zai kuma yi musu sakayya a kai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya tabbatar wa Yahudawa cewa, mutuwar nan da suke gudu babu makawa sai ta cim musu ko ba daɗe ko ba jima, domin Allah ya riga ya rubuta ta a kan kowanne ɗan’adam, don haka su ba bare ne ba. Idan kuma sun mutu to za a mayar da su ranar alƙiyama zuwa ga Allah Masanin abin da yake ɓoye da na sarari, sai ya ba su labarin duk abin da suka kasance suna aikatawa a duniya, ya kuma yi musu sakayya a kai.

  9. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَوٰةِ مِن يَوۡمِ ٱلۡجُمُعَةِ فَٱسۡعَوۡاْ إِلَىٰ ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَذَرُواْ ٱلۡبَيۡعَۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

    Open ayah 62:9

    Ya ku waɗanda suka yi imani, idan aka yi kiran salla ranar Juma’a sai ku tafi zuwa zikirin Allah, kuma ku bar ciniki. Wannan (shi) ya fi muku alheri, idan kun kasance kuna sane (da haka).

  10. فَإِذَا قُضِيَتِ ٱلصَّلَوٰةُ فَٱنتَشِرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَٱبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا لَّعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ 

    Open ayah 62:10

    Sannan idan aka gama salla sai ku bazu a bayan ƙasa ku kuma nema daga falalar Allah, kuma ku ambaci Allah da yawa don ku rabauta.

  11. وَإِذَا رَأَوۡاْ تِجَٰرَةً أَوۡ لَهۡوًا ٱنفَضُّوٓاْ إِلَيۡهَا وَتَرَكُوكَ قَآئِمٗاۚ قُلۡ مَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ مِّنَ ٱللَّهۡوِ وَمِنَ ٱلتِّجَٰرَةِۚ وَٱللَّهُ خَيۡرُ ٱلرَّٰزِقِينَ

    Open ayah 62:11

    Idan kuma suka ga kasuwanci ko wasa sai su watse zuwa gare su, su bar ka a tsaye (kana huɗuba). Ka ce: “Abin da yake wurin Allah ya fi wasa da ciniki. Kuma Allah Fiyayyen masu arzutawa ne.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su yi gaggawa wajen halartar sallar Juma’a da zarar sun ji an yi kiran salla bayan liman ya hau mimbari, su kuma bar duk wata sabga ta saye da sayarwa, domin kada wannan ya ɗauke musu hankali har su rasa sallar Juma’a ko su je a makare. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, lalle wannan umarni da ya yi musu na halartar Juma’a da barin sabgogin kasuwanci shi ne ya fi musu alheri idan sun kasance sun san haka, don haka su yi iya ƙoƙarinsu wajen bin umarninsa da kiyaye haninsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, idan sun kammala sallar Juma’a, to sai su koma su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum na neman halaliya, su kuma kiyaye wajen neman arzikinsu, su nemi aiki na halal da riba ta halal daga falalar Allah, amma kada su manta da ambaton Allah, su ambaci Allah sosai, domin su rabauta da samun abin da suke so, kuma su kuɓuta daga wanda suke ƙi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin abin da ya faru ga wasu sahabbai lokacin da Manzon Allah (ﷺ) yake tsaye a kan mimbari ranar Juma’a yana huɗuba, sai suka sami labarin isowar ayarin fatake ɗauke da kayan kasuwanci, sai suka fashe suka bar Manzon Allah (ﷺ) tsaye tare da wasu mutane su goma sha biyu, suka nufi waɗancan fatake don sayen kayan masarufi a wurinsu. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Muna tsaka da salla (yana nufin huɗuba) tare da Manzon Allah (ﷺ) sai wasu ayarin fatake suka shigo Madina ɗauke da abinci, sai mutane suka watse suka nufi wannan ayari, har ya zamanto mutum goma sha biyu ne kacal suka rage tare da Annabi (ﷺ), sai wannan ayar ta sauka. [Bukhari #936 da Muslim #863]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya soki wannan abu da ya faru, ya bayyana cewa, idan wasu daga Musulmi suka ga wani kasuwanci ko wasa, watau gangunan da attajiran suke bugawa idan sun iso gari domin sanar da mutane zuwansu, sai su watse su nufi inda wannan kasuwancin yake, su bar Manzon Allah (ﷺ) tsaye a kan mimbari yana huɗuba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya sanar da su cewa sakamakon kyakkyawan aiki da ke wurinsa ya fi wannan kasuwancin da wasan da suka bar sauraron huɗuba suka nufi wajensa, kuma haƙuri wajen biyar Allah (Mai tsarki da daukaka) ba ya hana samun arzukin da Allah ya ƙaddara wa kowane bawa, domin shi ne fiyayyen mai arzutawa, don haka wanda ya ji tsoron sa ya kiyaye dokokinsa, to zai arzuta shi ta inda ba ya tsammani. An karɓo daga Jabir ɗan Samura (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya kasance yana yin huɗuba a tsaye.” [Muslim #862]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya kasance yana yin huɗuba a ranar Juma’a a tsaye, sannan ya zauna, sannan kuma ya tashi ya sake yin huɗuba. [Bukhari #920 da Muslim #861]. An karɓo daga Jabir ɗan Samura (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) yana yin huɗubobi biyu (a ranar Juma’a), yana zama a tsakaninsu. Yana karanta Alƙur’ani ya kuma tunatar da mutane. [Muslim #862].