المنافقون
Al-Munaafiqoon
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
إِذَا جَآءَكَ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ قَالُواْ نَشۡهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُۥ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَكَٰذِبُونَ
Open ayah 63:1Idan munafukai suka zo maka sai suka ce: “Muna shaidawa cewa lalle kai Manzon Allah ne.” Allah kuma Yana sane da cewa kai tabbas Manzonsa ne, kuma Allah Yana shaidawa cewa munafukai tabbas ƙarya suke yi.
ٱتَّخَذُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُمۡ جُنَّةٗ فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ إِنَّهُمۡ سَآءَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 63:2Sun ɗauki rantse-rantsensu garkuwa, saboda haka suka kange (mutane) daga hanyar Allah. Lalle su abin da suka kasance suna aikatawa ya munana.
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ ثُمَّ كَفَرُواْ فَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَفۡقَهُونَ
Open ayah 63:3Wannan kuwa saboda cewa sun yi imani sannan suka kafirta, sai aka rufe zukatansu, saboda haka su ba sa fahimta.
۞وَإِذَا رَأَيۡتَهُمۡ تُعۡجِبُكَ أَجۡسَامُهُمۡۖ وَإِن يَقُولُواْ تَسۡمَعۡ لِقَوۡلِهِمۡۖ كَأَنَّهُمۡ خُشُبٞ مُّسَنَّدَةٞۖ يَحۡسَبُونَ كُلَّ صَيۡحَةٍ عَلَيۡهِمۡۚ هُمُ ٱلۡعَدُوُّ فَٱحۡذَرۡهُمۡۚ قَٰتَلَهُمُ ٱللَّهُۖ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ
Open ayah 63:4Idan ka gan su sai jikkunansu su ƙayatar da kai; idan kuma suka yi magana za ka saurari maganarsu; kai ka ce su wasu gumaguman itatuwa ne a jingine; suna tsammanin kowace irin kururuwa saboda su ne. Su ne maƙiya, saboda haka ka yi hattara da su. Allah kuma Ya la’ance su; ta ina ne ake karkatar da su? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura ne da bayanin wata halayya ta yaudara da ƙarya ta munafukai yayin da suke zuwa wurin Manzon Allah (ﷺ) suna tabbatar masa tare da yin rantsuwa cewa, su lalle sun shaida cewa shi Manzon Allah ne wanda ya zo da saƙon gaskiya daga Allah, alhalin suna ɓoye kafirci a zukatansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa yana sane da cewa shi Manzonsa ne na gaskiya, amma kuma ya tabbatar da cewa, munafukai maƙaryata ne kawai; ba da gaske suke shaidawa cewa shi Manzonsa ne ba, watau yaudara ce kawai irin tasu. Kuma ya bayyana cewa, rantse-rantsen da suke yi a gaban Manzon Allah (ﷺ) duk na banza ne, domin sun mayar da su kamar wata garkuwa ce da suke kare kansu da ita daga kisa ko ɗauri, wannan kuma ya ba su damar hana mutane yin imani, saboda abin da suke ta yayatawa na ruɗani da maganganu masu tayar da fitina a bainar jama’a. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, abin da suke aikatawa na munafurci da rantse-rantsen ƙarya ya munana matuƙa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babban abin da ya jawo musu faɗawa cikin wannan mummunan hali nasu shi ne, saboda sun yi imani ne tun farko irin na munafurci wanda bai kai har zuciya ba, sannan sai suka kafirce wa Allah a ɓoye, saboda haka sai Allah ya rufe musu zukatansu, imani ba ya shiga, ya zamanto ba sa fahimtar duk wata shiriya da ake nuna musu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin kyan surar ginin gangar jiki da kyan kama da ya yi musu ta yadda idan mutum ya gan su kamalar jikkunansu ta zahiri za ta ƙayatar da shi, a dalilin rayuwar jin daɗi da suke ciki, saboda haka da zarar sun buɗi baki suna magana sai ya kasa kunne ya yi ta sauraron su, don fasahar maganar da suke da ita. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mutum zai gan su a majalisin Manzon Allah (ﷺ) sundumdum a zaune kamar gumaguman itatuwa marasa amfani waɗanda aka jinige su, watau dai wannan cika fuskar duka fankanfayo ne ba sa fahimtar komai daga bayanan da Manzon Allah (ﷺ) yake yi, suna kuma ji a jikinsu duk wata kururuwa kansu za ta faɗa, saboda tsoro da rashin gaskiya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi Manzonsa cewa, su fa maƙiyansa ne, ya yi hattara da su kada su riƙa yaɗa sirrinsa ko su shirya masa wani makirci bai sani ba. Allah ya la’ane su, har ta yaya ake kawar da su daga yin imani tare da bayyanar dalilansa da ƙarfafan hujjojinsa a fili?
وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ يَسۡتَغۡفِرۡ لَكُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ لَوَّوۡاْ رُءُوسَهُمۡ وَرَأَيۡتَهُمۡ يَصُدُّونَ وَهُم مُّسۡتَكۡبِرُونَ
Open ayah 63:5Idan kuma aka ce da su: “Ku zo Manzon Allah ya nema muku gafara,” sai su kau da kansu, sai ka gan su suna bijirewa, alhalin suna masu girman kai.
سَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ أَسۡتَغۡفَرۡتَ لَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تَسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ لَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ
Open ayah 63:6Duk ɗaya ne game da su, ka nema musu gafara, ko ba ka nema musu gafara ba, Allah ba zai gafarta musu ba har abada. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane fasiƙai. A waɗannan ayoyi kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin tsananin taurin kan munafukai da mugun halinsu wanda yake ƙara tabbatar da munafurcinsu, shi ne duk sanda aka faɗa musu cewa, su je su samu Manzon Allah (ﷺ) su faɗa masa hanzarinsu game da mummunan abin da suka aikata, domin ya nema musu gafarar zunubbansu, sai su kawar da kawunansu domin yin izgili ga abin da suka ji, daga nan sai su bijire wa shawarar da aka ba su, suna nuna girman kai game da karɓar gaskiya da miƙa wuya gare ta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rashin amfanin nema musu gafara, ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, duk ɗaya ne ko ya nema musu gafara ko bai nema musu ba, domin shi Allah ba zai taɓa gafarta musu zunubansu ba, saboda sun tabbata cikakkun fasiƙai, Allah kuwa ba ya shiryar da fasiƙan mutane masu bijire wa ɗa’arsa da dagewa a kan saɓonsa.
هُمُ ٱلَّذِينَ يَقُولُونَ لَا تُنفِقُواْ عَلَىٰ مَنۡ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ حَتَّىٰ يَنفَضُّواْۗ وَلِلَّهِ خَزَآئِنُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَا يَفۡقَهُونَ
Open ayah 63:7Su ne waɗanda suke cewa: “Kada ku ciyar da waɗanda suke wurin Manzon Allah har sai sun dare”. Alhali kuwa taskokin sammai da ƙasa na Allah ne, sai dai kuma munafukai ba sa ganewa.
يَقُولُونَ لَئِن رَّجَعۡنَآ إِلَى ٱلۡمَدِينَةِ لَيُخۡرِجَنَّ ٱلۡأَعَزُّ مِنۡهَا ٱلۡأَذَلَّۚ وَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِۦ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَلَٰكِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 63:8Suna cewa: “Tabbas idan muka koma Madina, lalle mafi daraja zai fitar da mafi wulaƙanci daga cikinta”. Alhali kuwa girma na Allah ne da Manzonsa da kuma muminai, sai dai kuma munafukai ba sa sanin (haka). A waɗannan ayoyi kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fallasa wata mummunar magana da munafukai suke faɗa wa junansu ne game da Manzon Allah (ﷺ) da sahabbansa, yayin da suke ba wa junansu shawara a kan su daina kashe dukiyarsu suna ciyar da faƙirai da mutanen ƙauye da suke tare da Manzon Allah (ﷺ) har sai sun watse sun bar shi, watau su a tunaninsu, ba don wannan dukiyar da suke kashewa wajen ciyar da waɗannan sahabban ba, da ba za su iya zama da Manzon Allah (ﷺ) ba, kuma ba zai iya tattara su ba har su taimaki addinin Allah, don haka idan suka riƙe dukiyoyinsu suka hana su, to a ƙarshe duk za su watse su bar shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa, dukkan taskokin arziki da ke sammai da waɗanda suke a ƙasa nasa ne, yana arzuta wanda ya ga dama daga cikin bayinsa, to amma su munafukai ba sa fahimtar haka, shi ya sa suke yin maganganunsu na jahilci da duhun kai. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya fallasa wata mummunar magana da suka yi a kan Manzon Allah (ﷺ) yayin da shugabansu Abdullahi ɗan Ubayyu ɗan Salul ya buɗe baki ya furta har da rantsuwa cewa, lalle tabbas idan sun koma Madina daga wajen yaƙi, wai sai shi maɗaukaki tare da jama’arsa sun fitar da maƙasƙanci, yana nufin Manzon Allah (ﷺ) da jama’arsa, daga birnin Madina. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da kyakkyawan martani a taƙaice da cewa, ai izza, watau ɗaukaka da daraja duka na Allah ne da Manzonsa da muminai, amma munafukai ba su san haka ba, don haka suke ganin su ne masu girma masu izza.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُلۡهِكُمۡ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُكُمۡ عَن ذِكۡرِ ٱللَّهِۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Open ayah 63:9Ya ku waɗanda suka yi imani, kada dukiyoyinku da ‘ya’yanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Duk wanda ya aikata haka kuwa, to waɗannan su ne taɓaɓɓu.
وَأَنفِقُواْ مِن مَّا رَزَقۡنَٰكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ فَيَقُولَ رَبِّ لَوۡلَآ أَخَّرۡتَنِيٓ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖ فَأَصَّدَّقَ وَأَكُن مِّنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 63:10Kuma ku ciyar daga abin da Muka arzuta ku tun kafin mutuwa ta zo wa ɗayanku sannan ya riƙa cewa: “Ya Ubangijina, me ya hana Ka saurara min zuwa wani ɗan lokaci na kusa sai in ba da gaskiya in kuma zama cikin bayi nagari.”
وَلَن يُؤَخِّرَ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِذَا جَآءَ أَجَلُهَاۚ وَٱللَّهُ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 63:11Allah kuwa ba zai taɓa saurara wa wani rai ba idan ajalinsa ya zo. Allah kuwa Masanin abin da kuke aikatawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsawatar wa muminai game da koyi da halaye na munafukai masu shagalta da rashin ambaton Allah, ya gargaɗe su cewa, kada dukiyoyinsu da ‘ya’yansu su ɗauke musu hankali game da ambaton Allah, watau salla da sauran farillan Musulunci da zikirin Ubangiji. Ya tabbatar musu cewa, duk wanda dukiyarsa da ‘ya’yansa suka shagaltar da shi game da abin da Allah ya wajabta masa, to waɗannan sun tabbata asararru a lahira waɗanda suka yi asarar kawaunansu da iyalansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su ciyar daga cikin dukiyoyin da ya arzuta su da su, tun kafin mutuwa ta zo wa ɗayansu a lokacin ya riƙa yin nadama a kan sakacin da ya yi, har ya riƙa roƙon Allah cewa, ina ma ya ɗan jinkirta masa zuwa wani ɗan lokaci kaɗan, don ya yi amfani da shi ya ba da sadaka daga dukiyarsa don Allah, ya zamanto cikin bayin Allah na ƙwarai waɗanda suka kyautata ayyukansu. A nan ne Allah (Mai tsarki da daukaka) zai mayar masa da martani cewa, ba zai taɓa saurara wa wani rai ba idan ajalinsa ya zo, rayuwarsa ta duniya ta zo ƙarshe ke nan. Kuma Allah masanin abin da suke aikatawa ne, zai kuma saka wa kowa gwargwadon aikinsa mai kyau ko mummuna.