الفاتحة

Al-Faatiha

The Opening · Surah 1 · Ayahs: 7 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

  1. بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

    Open ayah 1:1

    Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai Malamai sun haɗu a kan cewa, Bisimilla Alƙur\'ani ce, kuma aya ce a cikin ‘Suratun Namli’; sai dai sun saɓa a kan cewa, shin aya ce a farkon kowace sura ko a\'a? Zance dai mafi rinjaye shi ne ita aya ce a farkon ‘Suratul Fatiha’ , sannan an saukar da ita a farkon kowace sura don bambance tsakanin ƙarshen sura da farkon wata sura. Amma ban da tsakanin ‘Suratul Anfal’ da ‘Taubah’ . Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Alƙur’ani da ambaton sunansa Allah , wato sunan da ya cancanta a bauta masa shi kaɗai da shi, saboda ya siffantu da siffofin kamala. Daga cikinsu akwai siffofinsa kuma sunayensa: Arrahman wanda yake nuna yalwatacciyar rahmar Allah wadda take shafar kowa da komai a nan duniya da kuma sunansa Arrahim , wanda suke nuna keɓantacciyar rahamarsa a lahira ga muminai kawai masu tsoran sa. Don haka wajibi ne mumini ya tabbatar wa Allah dukkan sunayensa da siffofinsa kamar yadda suka zo a Alƙur\'ani da sunnar Annabi (ﷺ) ba tare da canza musu ma\'ana ba, ko kamanta su da siffofin halittarsa ba.

  2. ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 1:2

    Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Duk wata siffa ta yabo da kirari ta tabbata ga Allah shi kaɗai. Shi ne Ubangijin ɗaukacin talikai mahaliccinsu wanda yake renon su da ni\'imominsa. Renon Allah ga halittarsa iri biyu ne: Na ɗaya, ya shafi kowa da komai, wanda ya haɗa da halittarsa da bayar da arziki da nuna wa halittunsa abin da yake maslaha gare su. Na biyu, renonsa ga muminai waɗanda suka amsa kiran annabawansa, watau datar da su wajen karɓar shiriya da gaskiya da kuma aiki da ita. Wannan reno ne da tarbiyya da ta keɓanci annabawa da mabiyansu kaɗai.

  3. ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

    Open ayah 1:3

    Mai rahama Mai jin ƙai.

  4. مَٰلِكِ يَوۡمِ ٱلدِّينِ

    Open ayah 1:4

    Mamallakin ranar sakamako. Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne mai mulki na haƙiƙa, wanda yake sawa a yi kuma ya hana, yake kuma ba da sakamako kyakkyawa da mummuna, yake yin abin da ya ga dama a masarautarsa wadda ta haɗe sama da ƙasa da duk abin da yake tsakaninsu. Hakanan shi ne mai mulki ranar alƙiyama yayin da zai yi wa kowa hisabi bisa ga ayyukansa na ƙwarai ko mummuna. A ranar kowa zai tabbatar da cewa, Allah shi ne Ɗaya mai cikakken iko, yayin da zai ga sarakuna da talakawasu da masu kuɗi da matalauta da iyayen giji da bayinsu, duk sun daidaita a gaban mai mulki Ɗaya shi ne Allah, wanda babu mai ja da shi a wannan ranar.

  5. إِيَّاكَ نَعۡبُدُ وَإِيَّاكَ نَسۡتَعِينُ

    Open ayah 1:5

    Kai kaɗai muke bautata wa, kuma Kai kaɗai muke neman taimakonka. Watau Allah kaɗai muka yarda mu bauta wa; dukkan nau\'o\'in ibada gare shi ake ba da su. Ibada kuwa ita ce, duk wani abu da Allah yake son sa kuma ya yarda da shi, na ƙuduri ne a zuciya ko magana ta baka ko kuma aiki na gaɓobi. Sannan mun tabbata ba za mu iya bauta masa yadda ya dace ba sai da taimakonsa. Don haka a wajensa kaɗai muke neman taimako a cikin lamuranmu gaba ɗaya. Wannan yana nuna ba a neman taimakon wani wanda ba Allah ba a duk wani abu da Allah ne kaɗai zai iya yin sa, kamar bayar da arziki ko neman lafiya ko neman \'ya\'ya da makamantansu. Bai halatta wani ya kira wani annabi ko wani waliyyi ko wani salihin bawa ba yayin da yake cikin wata musiba don ya taimake shi, idan har ya yi haka to ya bayar da haƙƙin Allah ga wani, watau ya yi shirka da Allah.

  6. ٱهۡدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ

    Open ayah 1:6

    Ka shiryar da mu tafarkin nan madaidaici. Muna roƙon Allah ya nuna mana hanaya miƙaƙƙiya wadda za ta kai mu ga samun yardarsa da rahamarsa, watau sanin gaskiya da aiki da ita da kama addinin Musulunci da barin duk wani addini da ba shi ba. Wannan addu\'a ce mai matuƙar amfani ga rayuwar bawa mumini; shi ya sa Allah ya shar\'anta mana karanta Fatiha a cikin kowace raka\'a a sallolinmu na farilla da na nafila.

  7. صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمۡتَ عَلَيۡهِمۡ غَيۡرِ ٱلۡمَغۡضُوبِ عَلَيۡهِمۡ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ

    Open ayah 1:7

    Tafarkin waɗanda Ka yi wa ni\'ima, ba waɗanda aka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba. Miƙaƙƙen tafarki shi ne tafarkin annabawa da siddiƙai da shahidai da salihan bayi, kamar yadda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambata hakan a \'Suratun Nisa’i\' aya ta 69. Su ne waɗanda Allah ya yi musu katari da ni\'imar shiriya a duniya, don haka suka cancanci ni\'imar lahira. Hanyar waɗannan bayin Allah kuwa ta yi hannun riga da hanyar waɗanda suka san gaskiya amma suka take ta, suka koma ga bin soye-soyen zukatansu, kamar Yahudawa. Hakanan ta yi hannun riga da hanyar waɗanda suke bautar Allah da jahilci da ɓata, kamar Nasara.