الصافات
As-Saaffaat
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلصَّٰٓفَّٰتِ صَفّٗا
Open ayah 37:1Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).
فَٱلزَّٰجِرَٰتِ زَجۡرٗا
Open ayah 37:2Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.
فَٱلتَّٰلِيَٰتِ ذِكۡرًا
Open ayah 37:3Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
إِنَّ إِلَٰهَكُمۡ لَوَٰحِدٞ
Open ayah 37:4Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.
رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَرَبُّ ٱلۡمَشَٰرِقِ
Open ayah 37:5Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.
إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِزِينَةٍ ٱلۡكَوَاكِبِ
Open ayah 37:6Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.
وَحِفۡظٗا مِّن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ مَّارِدٖ
Open ayah 37:7Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.
لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ ٱلۡأَعۡلَىٰ وَيُقۡذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٖ
Open ayah 37:8Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.
دُحُورٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ وَاصِبٌ
Open ayah 37:9Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.
إِلَّا مَنۡ خَطِفَ ٱلۡخَطۡفَةَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ ثَاقِبٞ
Open ayah 37:10Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.
فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَهُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَم مَّنۡ خَلَقۡنَآۚ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّن طِينٖ لَّازِبِۭ
Open ayah 37:11Ka tambaye su: ";Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?"; Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.
بَلۡ عَجِبۡتَ وَيَسۡخَرُونَ
Open ayah 37:12Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
وَإِذَا ذُكِّرُواْ لَا يَذۡكُرُونَ
Open ayah 37:13Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.
وَإِذَا رَأَوۡاْ ءَايَةٗ يَسۡتَسۡخِرُونَ
Open ayah 37:14Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.
وَقَالُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٌ
Open ayah 37:15Kuma su ce, ";Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne.";
أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ
Open ayah 37:16";Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?
أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ
Open ayah 37:17";Ashe kõ da ubanninmu na farko?";
قُلۡ نَعَمۡ وَأَنتُمۡ دَٰخِرُونَ
Open ayah 37:18Ka ce: ";Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu.";
فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٞ وَٰحِدَةٞ فَإِذَا هُمۡ يَنظُرُونَ
Open ayah 37:19Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.
وَقَالُواْ يَٰوَيۡلَنَا هَٰذَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ
Open ayah 37:20Kuma su ce: ";Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako.";
هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Open ayah 37:21Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.
۞ٱحۡشُرُواْ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَأَزۡوَٰجَهُمۡ وَمَا كَانُواْ يَعۡبُدُونَ
Open ayah 37:22Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.
مِن دُونِ ٱللَّهِ فَٱهۡدُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:23Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.
وَقِفُوهُمۡۖ إِنَّهُم مَّسۡـُٔولُونَ
Open ayah 37:24Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.
مَا لَكُمۡ لَا تَنَاصَرُونَ
Open ayah 37:25Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
بَلۡ هُمُ ٱلۡيَوۡمَ مُسۡتَسۡلِمُونَ
Open ayah 37:26Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
وَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ
Open ayah 37:27Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
قَالُوٓاْ إِنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَأۡتُونَنَا عَنِ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 37:28Suka ce: ";Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince).";
قَالُواْ بَل لَّمۡ تَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ
Open ayah 37:29Suka ce: ";Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.
وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيۡكُم مِّن سُلۡطَٰنِۭۖ بَلۡ كُنتُمۡ قَوۡمٗا طَٰغِينَ
Open ayah 37:30";Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka.";
فَحَقَّ عَلَيۡنَا قَوۡلُ رَبِّنَآۖ إِنَّا لَذَآئِقُونَ
Open ayah 37:31";Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne.";
فَأَغۡوَيۡنَٰكُمۡ إِنَّا كُنَّا غَٰوِينَ
Open ayah 37:32";Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu.";
فَإِنَّهُمۡ يَوۡمَئِذٖ فِي ٱلۡعَذَابِ مُشۡتَرِكُونَ
Open ayah 37:33To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 37:34Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
إِنَّهُمۡ كَانُوٓاْ إِذَا قِيلَ لَهُمۡ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ يَسۡتَكۡبِرُونَ
Open ayah 37:35Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: ";Bãbu abin bautãwa, fãce Allah,"; sai su dõra girman kai.
وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوٓاْ ءَالِهَتِنَا لِشَاعِرٖ مَّجۡنُونِۭ
Open ayah 37:36Kuma sunã cẽwa, ";Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
بَلۡ جَآءَ بِٱلۡحَقِّ وَصَدَّقَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:37Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
إِنَّكُمۡ لَذَآئِقُواْ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَلِيمِ
Open ayah 37:38Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
وَمَا تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 37:39Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Open ayah 37:40Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ رِزۡقٞ مَّعۡلُومٞ
Open ayah 37:41Waɗannan sunã da abinci sananne.
فَوَٰكِهُ وَهُم مُّكۡرَمُونَ
Open ayah 37:42Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Open ayah 37:43A cikin gidãjen Aljannar ni'ima.
عَلَىٰ سُرُرٖ مُّتَقَٰبِلِينَ
Open ayah 37:44A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
يُطَافُ عَلَيۡهِم بِكَأۡسٖ مِّن مَّعِينِۭ
Open ayah 37:45Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.
بَيۡضَآءَ لَذَّةٖ لِّلشَّٰرِبِينَ
Open ayah 37:46Farã mai dãɗi ga mashãyan.
لَا فِيهَا غَوۡلٞ وَلَا هُمۡ عَنۡهَا يُنزَفُونَ
Open ayah 37:47A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
وَعِندَهُمۡ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ عِينٞ
Open ayah 37:48Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
كَأَنَّهُنَّ بَيۡضٞ مَّكۡنُونٞ
Open ayah 37:49Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
فَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ
Open ayah 37:50Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
قَالَ قَآئِلٞ مِّنۡهُمۡ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٞ
Open ayah 37:51Wani mai magana daga cikinsu ya ce: ";Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya).";
يَقُولُ أَءِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُصَدِّقِينَ
Open ayah 37:52Yanã cewa, ";Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?";
أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَدِينُونَ
Open ayah 37:53";Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?";
قَالَ هَلۡ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ
Open ayah 37:54(Mai maganar) ya ce: ";Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?";
فَٱطَّلَعَ فَرَءَاهُ فِي سَوَآءِ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:55Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.
قَالَ تَٱللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرۡدِينِ
Open ayah 37:56Ya ce (masa), ";Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni.";
وَلَوۡلَا نِعۡمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ ٱلۡمُحۡضَرِينَ
Open ayah 37:57";Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã).";
أَفَمَا نَحۡنُ بِمَيِّتِينَ
Open ayah 37:58";Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba.";
إِلَّا مَوۡتَتَنَا ٱلۡأُولَىٰ وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ
Open ayah 37:59";Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?";
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 37:60Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.
لِمِثۡلِ هَٰذَا فَلۡيَعۡمَلِ ٱلۡعَٰمِلُونَ
Open ayah 37:61Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.
أَذَٰلِكَ خَيۡرٞ نُّزُلًا أَمۡ شَجَرَةُ ٱلزَّقُّومِ
Open ayah 37:62Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?
إِنَّا جَعَلۡنَٰهَا فِتۡنَةٗ لِّلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 37:63Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.
إِنَّهَا شَجَرَةٞ تَخۡرُجُ فِيٓ أَصۡلِ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:64Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.
طَلۡعُهَا كَأَنَّهُۥ رُءُوسُ ٱلشَّيَٰطِينِ
Open ayah 37:65Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.
فَإِنَّهُمۡ لَأٓكِلُونَ مِنۡهَا فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ
Open ayah 37:66To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.
ثُمَّ إِنَّ لَهُمۡ عَلَيۡهَا لَشَوۡبٗا مِّنۡ حَمِيمٖ
Open ayah 37:67Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.
ثُمَّ إِنَّ مَرۡجِعَهُمۡ لَإِلَى ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:68Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.
إِنَّهُمۡ أَلۡفَوۡاْ ءَابَآءَهُمۡ ضَآلِّينَ
Open ayah 37:69Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.
فَهُمۡ عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِمۡ يُهۡرَعُونَ
Open ayah 37:70Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.
وَلَقَدۡ ضَلَّ قَبۡلَهُمۡ أَكۡثَرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 37:71Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ
Open ayah 37:72Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.
فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُنذَرِينَ
Open ayah 37:73Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Open ayah 37:74Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
وَلَقَدۡ نَادَىٰنَا نُوحٞ فَلَنِعۡمَ ٱلۡمُجِيبُونَ
Open ayah 37:75Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.
وَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 37:76Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.
وَجَعَلۡنَا ذُرِّيَّتَهُۥ هُمُ ٱلۡبَاقِينَ
Open ayah 37:77Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 37:78Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.
سَلَٰمٌ عَلَىٰ نُوحٖ فِي ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 37:79Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 37:80Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 37:81Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai.
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Open ayah 37:82Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.
۞وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِۦ لَإِبۡرَٰهِيمَ
Open ayah 37:83Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.
إِذۡ جَآءَ رَبَّهُۥ بِقَلۡبٖ سَلِيمٍ
Open ayah 37:84A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.
إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَاذَا تَعۡبُدُونَ
Open ayah 37:85A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, ";Mẽne ne kuke bautãwa?";
أَئِفۡكًا ءَالِهَةٗ دُونَ ٱللَّهِ تُرِيدُونَ
Open ayah 37:86";Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?";
فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 37:87";To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?";
فَنَظَرَ نَظۡرَةٗ فِي ٱلنُّجُومِ
Open ayah 37:88Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.
فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٞ
Open ayah 37:89Sã'an nan ya ce: ";Nĩ mai rashin lãfiya ne.";
فَتَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ مُدۡبِرِينَ
Open ayah 37:90Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
فَرَاغَ إِلَىٰٓ ءَالِهَتِهِمۡ فَقَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ
Open ayah 37:91Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: ";Ashe bã zã ku ci ba?
مَا لَكُمۡ لَا تَنطِقُونَ
Open ayah 37:92";Me ya sãme ku, bã ku magana?";
فَرَاغَ عَلَيۡهِمۡ ضَرۡبَۢا بِٱلۡيَمِينِ
Open ayah 37:93Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.
فَأَقۡبَلُوٓاْ إِلَيۡهِ يَزِفُّونَ
Open ayah 37:94Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
قَالَ أَتَعۡبُدُونَ مَا تَنۡحِتُونَ
Open ayah 37:95Ya ce, ";Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,
وَٱللَّهُ خَلَقَكُمۡ وَمَا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 37:96";Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?";
قَالُواْ ٱبۡنُواْ لَهُۥ بُنۡيَٰنٗا فَأَلۡقُوهُ فِي ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:97Suka ce: ";Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm.";
فَأَرَادُواْ بِهِۦ كَيۡدٗا فَجَعَلۡنَٰهُمُ ٱلۡأَسۡفَلِينَ
Open ayah 37:98Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
وَقَالَ إِنِّي ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّي سَيَهۡدِينِ
Open ayah 37:99Kuma (Ibrahĩm] ya ce: ";Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni.";
رَبِّ هَبۡ لِي مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 37:100";Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne.";
فَبَشَّرۡنَٰهُ بِغُلَٰمٍ حَلِيمٖ
Open ayah 37:101Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.
فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ ٱلسَّعۡيَ قَالَ يَٰبُنَيَّ إِنِّيٓ أَرَىٰ فِي ٱلۡمَنَامِ أَنِّيٓ أَذۡبَحُكَ فَٱنظُرۡ مَاذَا تَرَىٰۚ قَالَ يَٰٓأَبَتِ ٱفۡعَلۡ مَا تُؤۡمَرُۖ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّٰبِرِينَ
Open ayah 37:102To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: ";Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?"; (Yãron) ya ce: ";Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri.";
فَلَمَّآ أَسۡلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلۡجَبِينِ
Open ayah 37:103To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa.
وَنَٰدَيۡنَٰهُ أَن يَٰٓإِبۡرَٰهِيمُ
Open ayah 37:104Kuma Muka kira shi cẽwa ";Ya Ibrahĩm!";
قَدۡ صَدَّقۡتَ ٱلرُّءۡيَآۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 37:105";Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin."; Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡبَلَٰٓؤُاْ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 37:106Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.
وَفَدَيۡنَٰهُ بِذِبۡحٍ عَظِيمٖ
Open ayah 37:107Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 37:108Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.
سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ
Open ayah 37:109Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.
كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 37:110Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 37:111Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
وَبَشَّرۡنَٰهُ بِإِسۡحَٰقَ نَبِيّٗا مِّنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 37:112Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
وَبَٰرَكۡنَا عَلَيۡهِ وَعَلَىٰٓ إِسۡحَٰقَۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحۡسِنٞ وَظَالِمٞ لِّنَفۡسِهِۦ مُبِينٞ
Open ayah 37:113Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).
وَلَقَدۡ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
Open ayah 37:114Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.
وَنَجَّيۡنَٰهُمَا وَقَوۡمَهُمَا مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 37:115Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.
وَنَصَرۡنَٰهُمۡ فَكَانُواْ هُمُ ٱلۡغَٰلِبِينَ
Open ayah 37:116Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.
وَءَاتَيۡنَٰهُمَا ٱلۡكِتَٰبَ ٱلۡمُسۡتَبِينَ
Open ayah 37:117Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.
وَهَدَيۡنَٰهُمَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ
Open ayah 37:118Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِمَا فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 37:119Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.
سَلَٰمٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
Open ayah 37:120Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 37:121Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
إِنَّهُمَا مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 37:122Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai.
وَإِنَّ إِلۡيَاسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:123Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ أَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 37:124A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, ";Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?";
أَتَدۡعُونَ بَعۡلٗا وَتَذَرُونَ أَحۡسَنَ ٱلۡخَٰلِقِينَ
Open ayah 37:125";Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?";
ٱللَّهَ رَبَّكُمۡ وَرَبَّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 37:126";Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?";
فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ
Open ayah 37:127Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Open ayah 37:128Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 37:129Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِلۡ يَاسِينَ
Open ayah 37:130Aminci ya tabbata ga Ilyãs.
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 37:131Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 37:132Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
وَإِنَّ لُوطٗا لَّمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:133Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
إِذۡ نَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 37:134A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ
Open ayah 37:135Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).
ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Open ayah 37:136Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.
وَإِنَّكُمۡ لَتَمُرُّونَ عَلَيۡهِم مُّصۡبِحِينَ
Open ayah 37:137Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
وَبِٱلَّيۡلِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Open ayah 37:138Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?
وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:139Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
إِذۡ أَبَقَ إِلَى ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ
Open ayah 37:140A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ ٱلۡمُدۡحَضِينَ
Open ayah 37:141Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
فَٱلۡتَقَمَهُ ٱلۡحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٞ
Open ayah 37:142Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
فَلَوۡلَآ أَنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُسَبِّحِينَ
Open ayah 37:143To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
لَلَبِثَ فِي بَطۡنِهِۦٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ
Open ayah 37:144Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
۞فَنَبَذۡنَٰهُ بِٱلۡعَرَآءِ وَهُوَ سَقِيمٞ
Open ayah 37:145Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
وَأَنۢبَتۡنَا عَلَيۡهِ شَجَرَةٗ مِّن يَقۡطِينٖ
Open ayah 37:146Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
وَأَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ مِاْئَةِ أَلۡفٍ أَوۡ يَزِيدُونَ
Open ayah 37:147Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
فَـَٔامَنُواْ فَمَتَّعۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ حِينٖ
Open ayah 37:148Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَلِرَبِّكَ ٱلۡبَنَاتُ وَلَهُمُ ٱلۡبَنُونَ
Open ayah 37:149Sabõda haka, ka tambaye su, ";Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?";
أَمۡ خَلَقۡنَا ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ إِنَٰثٗا وَهُمۡ شَٰهِدُونَ
Open ayah 37:150Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?
أَلَآ إِنَّهُم مِّنۡ إِفۡكِهِمۡ لَيَقُولُونَ
Open ayah 37:151To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.
وَلَدَ ٱللَّهُ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ
Open ayah 37:152";Allah Yã haihu,"; alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
أَصۡطَفَى ٱلۡبَنَاتِ عَلَى ٱلۡبَنِينَ
Open ayah 37:153Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?
مَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ
Open ayah 37:154Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)?
أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Open ayah 37:155Shin, bã ku tunãni?
أَمۡ لَكُمۡ سُلۡطَٰنٞ مُّبِينٞ
Open ayah 37:156Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
فَأۡتُواْ بِكِتَٰبِكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 37:157To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
وَجَعَلُواْ بَيۡنَهُۥ وَبَيۡنَ ٱلۡجِنَّةِ نَسَبٗاۚ وَلَقَدۡ عَلِمَتِ ٱلۡجِنَّةُ إِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ
Open ayah 37:158Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, ";Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)";
سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ
Open ayah 37:159Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Open ayah 37:160Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
فَإِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ
Open ayah 37:161To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
مَآ أَنتُمۡ عَلَيۡهِ بِفَٰتِنِينَ
Open ayah 37:162Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
إِلَّا مَنۡ هُوَ صَالِ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:163Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
وَمَا مِنَّآ إِلَّا لَهُۥ مَقَامٞ مَّعۡلُومٞ
Open ayah 37:164";Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne.";
وَإِنَّا لَنَحۡنُ ٱلصَّآفُّونَ
Open ayah 37:165";Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda).";
وَإِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡمُسَبِّحُونَ
Open ayah 37:166";Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi.";
وَإِن كَانُواْ لَيَقُولُونَ
Open ayah 37:167Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,
لَوۡ أَنَّ عِندَنَا ذِكۡرٗا مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 37:168";Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko.";
لَكُنَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Open ayah 37:169";Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.";
فَكَفَرُواْ بِهِۦۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 37:170Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
وَلَقَدۡ سَبَقَتۡ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:171Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
إِنَّهُمۡ لَهُمُ ٱلۡمَنصُورُونَ
Open ayah 37:172Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ ٱلۡغَٰلِبُونَ
Open ayah 37:173Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٖ
Open ayah 37:174Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
وَأَبۡصِرۡهُمۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ
Open ayah 37:175Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.
أَفَبِعَذَابِنَا يَسۡتَعۡجِلُونَ
Open ayah 37:176Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?
فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمۡ فَسَآءَ صَبَاحُ ٱلۡمُنذَرِينَ
Open ayah 37:177To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
وَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٖ
Open ayah 37:178Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
وَأَبۡصِرۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ
Open ayah 37:179Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
سُبۡحَٰنَ رَبِّكَ رَبِّ ٱلۡعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ
Open ayah 37:180Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
وَسَلَٰمٌ عَلَى ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:181Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
وَٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 37:182Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.