الواقعة
Al-Waaqia
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
إِذَا وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ
Open ayah 56:1Idan mai aukuwa ta auku.
لَيۡسَ لِوَقۡعَتِهَا كَاذِبَةٌ
Open ayah 56:2Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
خَافِضَةٞ رَّافِعَةٌ
Open ayah 56:3(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
إِذَا رُجَّتِ ٱلۡأَرۡضُ رَجّٗا
Open ayah 56:4Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
وَبُسَّتِ ٱلۡجِبَالُ بَسّٗا
Open ayah 56:5Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
فَكَانَتۡ هَبَآءٗ مُّنۢبَثّٗا
Open ayah 56:6Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
وَكُنتُمۡ أَزۡوَٰجٗا ثَلَٰثَةٗ
Open ayah 56:7Kuma kun kasance nau'i uku.
فَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ
Open ayah 56:8Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ
Open ayah 56:9Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
وَٱلسَّٰبِقُونَ ٱلسَّٰبِقُونَ
Open ayah 56:10Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلۡمُقَرَّبُونَ
Open ayah 56:11Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Open ayah 56:12A ckin Aljannar ni'ima.
ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 56:13Jama'a ne daga mutãnen farko.
وَقَلِيلٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 56:14Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
عَلَىٰ سُرُرٖ مَّوۡضُونَةٖ
Open ayah 56:15(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيۡهَا مُتَقَٰبِلِينَ
Open ayah 56:16Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
يَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٞ مُّخَلَّدُونَ
Open ayah 56:17Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
بِأَكۡوَابٖ وَأَبَارِيقَ وَكَأۡسٖ مِّن مَّعِينٖ
Open ayah 56:18Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
لَّا يُصَدَّعُونَ عَنۡهَا وَلَا يُنزِفُونَ
Open ayah 56:19Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
وَفَٰكِهَةٖ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ
Open ayah 56:20Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
وَلَحۡمِ طَيۡرٖ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ
Open ayah 56:21Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.
وَحُورٌ عِينٞ
Open ayah 56:22Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
كَأَمۡثَٰلِ ٱللُّؤۡلُوِٕ ٱلۡمَكۡنُونِ
Open ayah 56:23Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.
جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 56:24A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
لَا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا تَأۡثِيمًا
Open ayah 56:25Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
إِلَّا قِيلٗا سَلَٰمٗا سَلَٰمٗا
Open ayah 56:26Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 56:27Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
فِي سِدۡرٖ مَّخۡضُودٖ
Open ayah 56:28(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
وَطَلۡحٖ مَّنضُودٖ
Open ayah 56:29Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.
وَظِلّٖ مَّمۡدُودٖ
Open ayah 56:30Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
وَمَآءٖ مَّسۡكُوبٖ
Open ayah 56:31Da wani ruwa mai gudãna.
وَفَٰكِهَةٖ كَثِيرَةٖ
Open ayah 56:32Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.
لَّا مَقۡطُوعَةٖ وَلَا مَمۡنُوعَةٖ
Open ayah 56:33Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
وَفُرُشٖ مَّرۡفُوعَةٍ
Open ayah 56:34Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
إِنَّآ أَنشَأۡنَٰهُنَّ إِنشَآءٗ
Open ayah 56:35Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
فَجَعَلۡنَٰهُنَّ أَبۡكَارًا
Open ayah 56:36Sa'an nan Muka sanya su budurwai.
عُرُبًا أَتۡرَابٗا
Open ayah 56:37Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
لِّأَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 56:38Ga mazõwa dãma.
ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 56:39Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
وَثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 56:40Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
وَأَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ
Open ayah 56:41Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
فِي سَمُومٖ وَحَمِيمٖ
Open ayah 56:42Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
وَظِلّٖ مِّن يَحۡمُومٖ
Open ayah 56:43Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
لَّا بَارِدٖ وَلَا كَرِيمٍ
Open ayah 56:44Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.
إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُتۡرَفِينَ
Open ayah 56:45Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
وَكَانُواْ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلۡحِنثِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 56:46Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
وَكَانُواْ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ
Open ayah 56:47Kuma sun kasance sunã cẽwa: ";Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?";
أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ
Open ayah 56:48";Shin, kuma da ubanninmu na farko?";
قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَوَّلِينَ وَٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 56:49Ka ce: ";Lalle mutãnen farko da na ƙarshe.";
لَمَجۡمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ
Open ayah 56:50";Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne.";
ثُمَّ إِنَّكُمۡ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلۡمُكَذِّبُونَ
Open ayah 56:51";Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!";
لَأٓكِلُونَ مِن شَجَرٖ مِّن زَقُّومٖ
Open ayah 56:52";Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã).";
فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ
Open ayah 56:53";Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta.";
فَشَٰرِبُونَ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡحَمِيمِ
Open ayah 56:54";Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi.";
فَشَٰرِبُونَ شُرۡبَ ٱلۡهِيمِ
Open ayah 56:55";Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa.";
هَٰذَا نُزُلُهُمۡ يَوۡمَ ٱلدِّينِ
Open ayah 56:56Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
نَحۡنُ خَلَقۡنَٰكُمۡ فَلَوۡلَا تُصَدِّقُونَ
Open ayah 56:57Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
أَفَرَءَيۡتُم مَّا تُمۡنُونَ
Open ayah 56:58Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
ءَأَنتُمۡ تَخۡلُقُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡخَٰلِقُونَ
Open ayah 56:59Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
نَحۡنُ قَدَّرۡنَا بَيۡنَكُمُ ٱلۡمَوۡتَ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ
Open ayah 56:60Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,
عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمۡثَٰلَكُمۡ وَنُنشِئَكُمۡ فِي مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 56:61A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُولَىٰ فَلَوۡلَا تَذَكَّرُونَ
Open ayah 56:62Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَحۡرُثُونَ
Open ayah 56:63Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
ءَأَنتُمۡ تَزۡرَعُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلزَّٰرِعُونَ
Open ayah 56:64Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
لَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَٰهُ حُطَٰمٗا فَظَلۡتُمۡ تَفَكَّهُونَ
Open ayah 56:65Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
إِنَّا لَمُغۡرَمُونَ
Open ayah 56:66(Kunã cẽwa) ";Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!";
بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ
Open ayah 56:67";Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!";
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلۡمَآءَ ٱلَّذِي تَشۡرَبُونَ
Open ayah 56:68Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
ءَأَنتُمۡ أَنزَلۡتُمُوهُ مِنَ ٱلۡمُزۡنِ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنزِلُونَ
Open ayah 56:69Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
لَوۡ نَشَآءُ جَعَلۡنَٰهُ أُجَاجٗا فَلَوۡلَا تَشۡكُرُونَ
Open ayah 56:70Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي تُورُونَ
Open ayah 56:71Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
ءَأَنتُمۡ أَنشَأۡتُمۡ شَجَرَتَهَآ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنشِـُٔونَ
Open ayah 56:72Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
نَحۡنُ جَعَلۡنَٰهَا تَذۡكِرَةٗ وَمَتَٰعٗا لِّلۡمُقۡوِينَ
Open ayah 56:73Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 56:74Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
۞فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ
Open ayah 56:75To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٞ لَّوۡ تَعۡلَمُونَ عَظِيمٌ
Open ayah 56:76Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
إِنَّهُۥ لَقُرۡءَانٞ كَرِيمٞ
Open ayah 56:77Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
فِي كِتَٰبٖ مَّكۡنُونٖ
Open ayah 56:78A cikin wani littafi tsararre.
لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُطَهَّرُونَ
Open ayah 56:79Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 56:80Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
أَفَبِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَنتُم مُّدۡهِنُونَ
Open ayah 56:81Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
وَتَجۡعَلُونَ رِزۡقَكُمۡ أَنَّكُمۡ تُكَذِّبُونَ
Open ayah 56:82Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
فَلَوۡلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلۡحُلۡقُومَ
Open ayah 56:83To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
وَأَنتُمۡ حِينَئِذٖ تَنظُرُونَ
Open ayah 56:84Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُبۡصِرُونَ
Open ayah 56:85Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
فَلَوۡلَآ إِن كُنتُمۡ غَيۡرَ مَدِينِينَ
Open ayah 56:86To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
تَرۡجِعُونَهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 56:87Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.
فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ
Open ayah 56:88To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
فَرَوۡحٞ وَرَيۡحَانٞ وَجَنَّتُ نَعِيمٖ
Open ayah 56:89Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 56:90Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
فَسَلَٰمٞ لَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 56:91Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ
Open ayah 56:92Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
فَنُزُلٞ مِّنۡ حَمِيمٖ
Open ayah 56:93Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
وَتَصۡلِيَةُ جَحِيمٍ
Open ayah 56:94Da ƙõnuwa da Jahĩm,
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلۡيَقِينِ
Open ayah 56:95Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 56:96Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.