الذاريات

Adh-Dhaariyat

The Winnowing Winds · Surah 51 · Ayahs: 60 · Meccan

Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. وَٱلذَّٰرِيَٰتِ ذَرۡوٗا

    Open ayah 51:1

    Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.

  2. فَٱلۡحَٰمِلَٰتِ وِقۡرٗا

    Open ayah 51:2

    Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).

  3. فَٱلۡجَٰرِيَٰتِ يُسۡرٗا

    Open ayah 51:3

    Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.

  4. فَٱلۡمُقَسِّمَٰتِ أَمۡرًا

    Open ayah 51:4

    Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).

  5. إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَصَادِقٞ

    Open ayah 51:5

    Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.

  6. وَإِنَّ ٱلدِّينَ لَوَٰقِعٞ

    Open ayah 51:6

    Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne

  7. وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلۡحُبُكِ

    Open ayah 51:7

    Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo).

  8. إِنَّكُمۡ لَفِي قَوۡلٖ مُّخۡتَلِفٖ

    Open ayah 51:8

    Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani).

  9. يُؤۡفَكُ عَنۡهُ مَنۡ أُفِكَ

    Open ayah 51:9

    Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).

  10. قُتِلَ ٱلۡخَرَّٰصُونَ 

    Open ayah 51:10

    An la'ani mãsu ƙiri-faɗi.

  11. ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي غَمۡرَةٖ سَاهُونَ

    Open ayah 51:11

    Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.

  12. يَسۡـَٔلُونَ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلدِّينِ

    Open ayah 51:12

    Sunã tambaya: ";Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?";

  13. يَوۡمَ هُمۡ عَلَى ٱلنَّارِ يُفۡتَنُونَ

    Open ayah 51:13

    Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.

  14. ذُوقُواْ فِتۡنَتَكُمۡ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تَسۡتَعۡجِلُونَ

    Open ayah 51:14

    (A ce musu): ";Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa.";

  15. إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّٰتٖ وَعُيُونٍ

    Open ayah 51:15

    Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.

  16. ءَاخِذِينَ مَآ ءَاتَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُحۡسِنِينَ

    Open ayah 51:16

    Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).

  17. كَانُواْ قَلِيلٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِ مَا يَهۡجَعُونَ

    Open ayah 51:17

    Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.

  18. وَبِٱلۡأَسۡحَارِ هُمۡ يَسۡتَغۡفِرُونَ

    Open ayah 51:18

    Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.

  19. وَفِيٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ حَقّٞ لِّلسَّآئِلِ وَٱلۡمَحۡرُومِ

    Open ayah 51:19

    Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.

  20. وَفِي ٱلۡأَرۡضِ ءَايَٰتٞ لِّلۡمُوقِنِينَ 

    Open ayah 51:20

    Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.

  21. وَفِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ

    Open ayah 51:21

    Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?

  22. وَفِي ٱلسَّمَآءِ رِزۡقُكُمۡ وَمَا تُوعَدُونَ

    Open ayah 51:22

    Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari.

  23. فَوَرَبِّ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ إِنَّهُۥ لَحَقّٞ مِّثۡلَ مَآ أَنَّكُمۡ تَنطِقُونَ

    Open ayah 51:23

    To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,

  24. هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ضَيۡفِ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡمُكۡرَمِينَ

    Open ayah 51:24

    Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?

  25. إِذۡ دَخَلُواْ عَلَيۡهِ فَقَالُواْ سَلَٰمٗاۖ قَالَ سَلَٰمٞ قَوۡمٞ مُّنكَرُونَ

    Open ayah 51:25

    A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce ";Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!";

  26. فَرَاغَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ فَجَآءَ بِعِجۡلٖ سَمِينٖ

    Open ayah 51:26

    Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,

  27. فَقَرَّبَهُۥٓ إِلَيۡهِمۡ قَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ

    Open ayah 51:27

    Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: ";Bã zã ku ci ba?";

  28. فَأَوۡجَسَ مِنۡهُمۡ خِيفَةٗۖ قَالُواْ لَا تَخَفۡۖ وَبَشَّرُوهُ بِغُلَٰمٍ عَلِيمٖ

    Open ayah 51:28

    Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: ";Kada kaji tsõro."; Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.

  29. فَأَقۡبَلَتِ ٱمۡرَأَتُهُۥ فِي صَرَّةٖ فَصَكَّتۡ وَجۡهَهَا وَقَالَتۡ عَجُوزٌ عَقِيمٞ

    Open ayah 51:29

    Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: ";Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!";

  30. قَالُواْ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡعَلِيمُ 

    Open ayah 51:30

    Suka ce: ";Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi.";

  31. ۞قَالَ فَمَا خَطۡبُكُمۡ أَيُّهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ

    Open ayah 51:31

    (Ibrãĩm) ya ce: ";To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!";

  32. قَالُوٓاْ إِنَّآ أُرۡسِلۡنَآ إِلَىٰ قَوۡمٖ مُّجۡرِمِينَ

    Open ayah 51:32

    Suka ce: ";Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.

  33. لِنُرۡسِلَ عَلَيۡهِمۡ حِجَارَةٗ مِّن طِينٖ

    Open ayah 51:33

    ";Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).

  34. مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ لِلۡمُسۡرِفِينَ

    Open ayah 51:34

    ";Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna.";

  35. فَأَخۡرَجۡنَا مَن كَانَ فِيهَا مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 51:35

    Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.

  36. فَمَا وَجَدۡنَا فِيهَا غَيۡرَ بَيۡتٖ مِّنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

    Open ayah 51:36

    Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.

  37. وَتَرَكۡنَا فِيهَآ ءَايَةٗ لِّلَّذِينَ يَخَافُونَ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ

    Open ayah 51:37

    Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.

  38. وَفِي مُوسَىٰٓ إِذۡ أَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ

    Open ayah 51:38

    Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne.

  39. فَتَوَلَّىٰ بِرُكۡنِهِۦ وَقَالَ سَٰحِرٌ أَوۡ مَجۡنُونٞ

    Open ayah 51:39

    Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: ";Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!";

  40. فَأَخَذۡنَٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّ وَهُوَ مُلِيمٞ 

    Open ayah 51:40

    Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.

  41. وَفِي عَادٍ إِذۡ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلرِّيحَ ٱلۡعَقِيمَ

    Open ayah 51:41

    Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.

  42. مَا تَذَرُ مِن شَيۡءٍ أَتَتۡ عَلَيۡهِ إِلَّا جَعَلَتۡهُ كَٱلرَّمِيمِ

    Open ayah 51:42

    Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.

  43. وَفِي ثَمُودَ إِذۡ قِيلَ لَهُمۡ تَمَتَّعُواْ حَتَّىٰ حِينٖ

    Open ayah 51:43

    Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: ";Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,";

  44. فَعَتَوۡاْ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهِمۡ فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّٰعِقَةُ وَهُمۡ يَنظُرُونَ

    Open ayah 51:44

    Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.

  45. فَمَا ٱسۡتَطَٰعُواْ مِن قِيَامٖ وَمَا كَانُواْ مُنتَصِرِينَ

    Open ayah 51:45

    Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.

  46. وَقَوۡمَ نُوحٖ مِّن قَبۡلُۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ

    Open ayah 51:46

    Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.

  47. وَٱلسَّمَآءَ بَنَيۡنَٰهَا بِأَيۡيْدٖ وَإِنَّا لَمُوسِعُونَ

    Open ayah 51:47

    Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.

  48. وَٱلۡأَرۡضَ فَرَشۡنَٰهَا فَنِعۡمَ ٱلۡمَٰهِدُونَ

    Open ayah 51:48

    Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,

  49. وَمِن كُلِّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَا زَوۡجَيۡنِ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ

    Open ayah 51:49

    Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.

  50. فَفِرُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِۖ إِنِّي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ مُّبِينٞ 

    Open ayah 51:50

    Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.

  51. وَلَا تَجۡعَلُواْ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۖ إِنِّي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ مُّبِينٞ

    Open ayah 51:51

    Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.

  52. كَذَٰلِكَ مَآ أَتَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا قَالُواْ سَاحِرٌ أَوۡ مَجۡنُونٌ

    Open ayah 51:52

    Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: ";Mai sihiri ne kõ mahaukaci.";

  53. أَتَوَاصَوۡاْ بِهِۦۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٞ طَاغُونَ

    Open ayah 51:53

    shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.

  54. فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ فَمَآ أَنتَ بِمَلُومٖ

    Open ayah 51:54

    Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.

  55. وَذَكِّرۡ فَإِنَّ ٱلذِّكۡرَىٰ تَنفَعُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 51:55

    Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.

  56. وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ

    Open ayah 51:56

    Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.

  57. مَآ أُرِيدُ مِنۡهُم مِّن رِّزۡقٖ وَمَآ أُرِيدُ أَن يُطۡعِمُونِ

    Open ayah 51:57

    Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.

  58. إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلرَّزَّاقُ ذُو ٱلۡقُوَّةِ ٱلۡمَتِينُ

    Open ayah 51:58

    Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.

  59. فَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ ذَنُوبٗا مِّثۡلَ ذَنُوبِ أَصۡحَٰبِهِمۡ فَلَا يَسۡتَعۡجِلُونِ

    Open ayah 51:59

    To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.

  60. فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن يَوۡمِهِمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ 

    Open ayah 51:60

    Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.