القلم
Al-Qalam
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
نٓۚ وَٱلۡقَلَمِ وَمَا يَسۡطُرُونَ
Open ayah 68:1NUN. (Allah ya ce): Na rantse da alƙalami da abin da (mala’iku) suke rubutawa.
مَآ أَنتَ بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ بِمَجۡنُونٖ
Open ayah 68:2Kai ba mahaukaci ba ne saboda ni’imar Ubangijinka.
وَإِنَّ لَكَ لَأَجۡرًا غَيۡرَ مَمۡنُونٖ
Open ayah 68:3Kuma lalle tabbas kana da lada marar yankewa.
وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٖ
Open ayah 68:4Lalle kuma kai kana kan halaye masu girma.
فَسَتُبۡصِرُ وَيُبۡصِرُونَ
Open ayah 68:5To ba da daɗewa ba za ka gani, su ma kuma su gani.
بِأَييِّكُمُ ٱلۡمَفۡتُونُ
Open ayah 68:6Wane ne daga cikinku mahaukaci?
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ
Open ayah 68:7Lalle Ubangijinka Shi Ya fi sanin wanda ya kauce wa hanyarsa kuma Shi Ya fi sanin shiryayyu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da harafin ‘Nun’ kamar yadda ya buɗe wasu surori da irin waɗannan haruffa don nuna mu’ujizar Alƙur’ani da zamantowarsa gagara-koyo duk kuwa da kasancewarsa yana magana ne da irin haruffan da su kansu Larabawa gwanayen fasaha suke magana da su. [Dubi farkon tafsirinmu na Suratul Baƙara don ƙarin bayani]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rantse da Alƙalami da abin da mutane suke rubutawa da alƙalumansu na littattafai a fannonin ilimi daban-daban. Mafificin alƙalami shi ne wanda aka rubuta ayyukan bayi da shi a Lauhul Mahfuzu . An karɓo daga Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle farkon abin da Allah ya halitta shi ne Alƙalami, ya kuma umarce shi ya rubuta komai.” [Abu Ya’ala #2329]. An karɓo daga Ubadatu ɗan Samit (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle farkon abin da Allah ya halitta shi ne Alƙalami sai ya ce masa: “Yi rubutu.” Sai ya ce: “Ya Ubangijina, me zan rubuta?” Sai ya ce: “Ka rubuta abubuwan da aka ƙaddara na komai har zuwa tashin alƙiyama.” [Abu Dawud #4700 da Tirmizi #2155]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, saboda ni’imar annabci da ya yi wa Manzonsa (ﷺ) ba zai taɓa zama mahaukaci ba, don haka ba shi da alaƙa da tuhumar da mushirikai suke yi masa ta cewa wai shi mahaukaci ne don ya zo musu da Alƙur’ani. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, Annabi (ﷺ) yana da lada marar yankewa a kan wahalhalun da yake sha wajen isar wa mutane saƙon Allah (Mai tsarki da daukaka), kuma babu wani mahluƙi da zai goranta wa Manzo (ﷺ) a kan haka. Sai kuma ya yi masa kyakkyawar shaida da cewa yana kan halaye masu girma, domin yana koyi ne da kyawawan halayen da Alƙur’ani ya zo da su. An karɓo daga Sa’ad ɗan Hisham ɗan Amir ya ce: Na zo wurin A’isha, (Allah ya kara mata yarda), na ce: “Ya Ummal Muminina, ba ni labarin halayen Manzon Allah (ﷺ).” Sai ta ce: “Halayensa sun kasance Alƙur’ani ne. Shin ba ka karanta Alƙur’ani ne? Ba ka ga faɗar Allah (Mai tsarki da daukaka) ba inda ya ce: “Lalle kai kana kan halaye masu girma”?” [Ahmad #24601]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya razana mushirikai da cewa ba da jimawa ba Annabi (ﷺ) zai gani, su ma kuma masu ƙaryata shi za su gani cewa a tsakaninsa da su, wane ne mahaukaci lokacin da gaskiya za ta bayyana ga kowa? Ya kuma tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, Ubangijinsa yana sane da wanda ya ɓace daga kan hanyarsa, yana kuma sane da shiryayyu masu bin hanyar Allah. Watau Allah (Mai tsarki da daukaka) ya san su ne ɓatattu waɗanda suka kauce wa hanyarsa, ya kuma san cewa Annabi (ﷺ) shi ne shiryayye da yake kan hanyar gaskiya.
فَلَا تُطِعِ ٱلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 68:8Saboda haka kada ka bi masu ƙaryatawa.
وَدُّواْ لَوۡ تُدۡهِنُ فَيُدۡهِنُونَ
Open ayah 68:9Sun yi burin da za ka sassauto, sai su ma su sassauto.
وَلَا تُطِعۡ كُلَّ حَلَّافٖ مَّهِينٍ
Open ayah 68:10Kada kuma ka bi duk wani mai yawan rantsuwa, wulaƙantacce.
هَمَّازٖ مَّشَّآءِۭ بِنَمِيمٖ
Open ayah 68:11Mai yawan yin zunɗe, mai yawan yawo da annamimanci.
مَّنَّاعٖ لِّلۡخَيۡرِ مُعۡتَدٍ أَثِيمٍ
Open ayah 68:12Mai yawan hana alheri, mai ta’addanci, mai yawan saɓo.
عُتُلِّۭ بَعۡدَ ذَٰلِكَ زَنِيمٍ
Open ayah 68:13Mai busasshiyar zuciya, bayan wannan kuma marar asali ne.
أَن كَانَ ذَا مَالٖ وَبَنِينَ
Open ayah 68:14Don ya kasance mai dukiya da ‘ya’ya.
إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 68:15Idan ana karanta masa ayoyinmu sai ya ce: “Tatsuniyoyin mutanen farko ne.”
سَنَسِمُهُۥ عَلَى ٱلۡخُرۡطُومِ
Open ayah 68:16Ba da daɗewa ba za Mu yi masa alama a kan hancinsa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana daɗa ƙarfafa gwiwar Manzonsa (ﷺ) a kan kira da yake yi wa kafirai zuwa ga gaskiya, ya kuma gargaɗe shi da cewa kada ya biye wa masu ƙaryata Alƙur’anin da ya zo da shi. Har ma koyaushe buri suke yi ina ma Manzon Allah (ﷺ) zai yi musu wata kara ya sassauta musu wajen aibata gumakansu da allolinsu, sai su ma su yi masa kara su sassauto su daina sukan sa da sukan addininsa. Sannan Allah ya yi wa Manzonsa kashedi da kada ya kuskura ya yi biyayya ga duk wani kafiri mai yawan rantsuwa a kan ƙarya, wulaƙantacce marar mutunci, mai yawan zunɗe da yi da mutane a bayan idonsu, mai yawan yawo da yaɗa annamimanci don ɓata tsakanin mutane da raba kawunansu, mai yawan hana gudanar alheri; shi ba zai yi ba kuma ba zai ƙyale masu yi su yi ba, mai yawan ta’addanci a kan dukiyoyin mutane da mutuncinsu da rayukansu, ya hana kowa sakat da walwala, mai yawan aikata zunubai da laifuka, babu tsoron Allah a zuciyarsa, mai ƙeƙasasshiyar zuciya da kakkausan hali wajen mu’amala da mutane; babu tausayi a ransa, ga shi kuma marar asali a cikin mutanensa, mugu, mai nuna girman kai da ƙin gaskiya don kawai ya ga yana da tarin dukiya da ‘ya’ya, har wannan ya sanya shi idan an karanta masa ayoyin Allah ana yi masa wa’azi da gargaɗi sai ya buɗi baki ya ce, ai duk wannan tatsuniyoyin mutanen farko ne, don haka shi ba zai yi imani ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa kashedi da azabarsa da cewa, ba da jimawa ba zai tagayyara shi ta hanyar yi masa alama a karan hancinsa da za ta munana shi muni na har abada.
إِنَّا بَلَوۡنَٰهُمۡ كَمَا بَلَوۡنَآ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ إِذۡ أَقۡسَمُواْ لَيَصۡرِمُنَّهَا مُصۡبِحِينَ
Open ayah 68:17Lalle Mu Mun jarrabe su (wato mutanen Makka) kamar yadda Muka jarrabi ma’abota gona, lokacin da suka rantse cewa, lalle tabbas za su girbe ta da asussuba.
وَلَا يَسۡتَثۡنُونَ
Open ayah 68:18Ba sa kuma togaciya (da faɗar insha Allah ).
فَطَافَ عَلَيۡهَا طَآئِفٞ مِّن رَّبِّكَ وَهُمۡ نَآئِمُونَ
Open ayah 68:19Sai wani bala’i daga Ubangijinka ya kewaye ta alhali su suna bacci.
فَأَصۡبَحَتۡ كَٱلصَّرِيمِ
Open ayah 68:20Sai ta wayi gari (baƙi ƙirin) kamar duhun dare.
فَتَنَادَوۡاْ مُصۡبِحِينَ
Open ayah 68:21Sai suka kirawo junansu da asussuba.
أَنِ ٱغۡدُواْ عَلَىٰ حَرۡثِكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰرِمِينَ
Open ayah 68:22Cewa: \"Ku yi sammako ga amfanin gonarku idan kun kasance masu yin girbi.\"
فَٱنطَلَقُواْ وَهُمۡ يَتَخَٰفَتُونَ
Open ayah 68:23Sai suka tafi alhali suna yi wa junansu raɗa.
أَن لَّا يَدۡخُلَنَّهَا ٱلۡيَوۡمَ عَلَيۡكُم مِّسۡكِينٞ
Open ayah 68:24Cewa: \"Lalle a yau kada wani miskini ya shigar muku cikinta.\"
وَغَدَوۡاْ عَلَىٰ حَرۡدٖ قَٰدِرِينَ
Open ayah 68:25Suka kuwa yi sammako suna masu zaton su masu iko ne a kan hana (mabuƙata).
فَلَمَّا رَأَوۡهَا قَالُوٓاْ إِنَّا لَضَآلُّونَ
Open ayah 68:26To lokacin da suka gan ta sai suka ce: “Lalle mu tabbas mun yi ɓatan kai.
بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ
Open ayah 68:27\"A’a, mu dai an hana mu ne kawai.\"
قَالَ أَوۡسَطُهُمۡ أَلَمۡ أَقُل لَّكُمۡ لَوۡلَا تُسَبِّحُونَ
Open ayah 68:28Sai wanda ya fi su kirki ya ce: “Ban gaya muku ya kamata ku tsarkake Allah ba?”
قَالُواْ سُبۡحَٰنَ رَبِّنَآ إِنَّا كُنَّا ظَٰلِمِينَ
Open ayah 68:29Suka ce, “Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu, lalle mu mun kasance azzalumai.”
فَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَلَٰوَمُونَ
Open ayah 68:30Sai sashinsu ya fuskanci sashi suna zargin juna.
قَالُواْ يَٰوَيۡلَنَآ إِنَّا كُنَّا طَٰغِينَ
Open ayah 68:31Suka ce: “Kaiconmu, lalle mu mun kasance masu shisshigi.
عَسَىٰ رَبُّنَآ أَن يُبۡدِلَنَا خَيۡرٗا مِّنۡهَآ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا رَٰغِبُونَ
Open ayah 68:32\"Tsammanin Ubangijinmu zai musanya mana wadda ta fi ta, lalle mu masu kwaɗayi ne a wurin Ubangijinmu.”
كَذَٰلِكَ ٱلۡعَذَابُۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَكۡبَرُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 68:33Kamar haka ne azaba take tabbata; kuma tabbas azabar lahira ta fi girma. Da sun kasance sun san haka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin cewa, duk wanda ya hore masa dukiya, to ya ba shi ita ne don ya jarrabe shi ya ga ko zai gode masa, zai kuma sarrafa ta wajen bin Allah da taimakon mabuƙata, ko kuma zai butulce masa ne, ya yi rowa da wadatar da ya ba shi, Allah kuma ya ƙwace dukiyar ya raba shi da ita. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, ya jarrabi mutanen Makka da fari da yunwa, kamar yadda ya jarrabi wasu mutane masu gona, lokacin da suka ga ta nuna ta isa girbi sai suka yi rantsuwa cewa, lalle da sassafe za su fita da gaggawa su je su girbe amfanin gonarsu, don kada wani mabuƙaci ya sami labari ya zo ya roƙe su taimakon abinci, amma suka ƙi cewa ‘insha Allahu’ a lokacin rantsuwarsu, ba su san Allah yana nan a madakata ba, sai kuwa ga shi ya aiko musu wata wuta da ta cinye amfanin gonar nan tatas, a lokacin da suke can suna sharar barci ba su san me yake faruwa ba. Don haka babu yadda za su iya kare ta daga wannan bala’in gobara. Gona ta ƙone ƙurmus ta wayi gari baƙa ƙirin kamar duhun dare. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan masu gona da muku-mukun asuba suka riƙa kiran junansu, da cewa, lalle su yi sammako su fita zuwa gonarsu kafin mabuƙata su farka su san abin da suke ciki, suka ƙarfafa wa juna cewa, lalle su hanzarta idan har suna son girbe amfanin gonarsu ba tare da wani ya amfana da shi ba. Suka daka sammako suka kama hanya cikin gaggawa suna yi wa junansu raɗa cewa, kada su bari wani miskini ya shigar musu gonarsu, suna zaton cewa za su iya hana mabuƙata amfanin gonarsu. Suna isa sai suka ga gonarsu ta ƙone ƙurmus, sai wasunsu suka ce, haƙiƙa sun yi ɓatan kai, domin wannan ba ita ce gonarsu ba, sai wasu kuma suka tabbatar da cewa, ba ɓatan kai suka yi ba, sun dai tabka asara ne, saboda mummunan ƙudurinsu na hana mabuƙata haƙƙinsu. Sai wanda ya fi su kirki ya tuna musu da abin da ya faɗa musu lokacin da suke tattaunawa a kan za su hana mabuƙata haƙƙoƙinsu, inda ya faɗa musu cewa, me ya hana su su riƙa tsarkake Allah suna masa tasbihi, su tuba su koma gare shi? Amma kuma suka ƙi jin nasiharsa, sai bayan wannan mummunar musiba ta auka musu sannan ne za su koma suna cewa tsarki ya tabbata ga Ubangijinsu. Ba shakka sun tabbata azzalumai waɗanda suka cuci kansu yayin da suka yi niyyar hana mabuƙata haƙƙinsu daga amfanin gonarsu. Daga nan nadama ta lulluɓe su suka fuskanci junansu suna zargin kansu, sai suka sake tabbatar wa da juna cewa kaiconsu, lalle sun kasance masu ƙetare iyakar Ubangijinsu yayin da suka ɗauka cewa, za su iya cinye haƙƙin talakawa su kwana lafiya. A nan ne kuma suka dawo cikin nadama suna roƙon Allah, tare da fatan ya canja musu da wata gonar wadda ta fi tasu, domin yanzu kam sun koma gare shi shi kaɗai suna kwaɗayin ya ba su wata gonar da ta fi tasu, suna kuma fatan ya yi musu afuwa, ya yafe musu kuskuren da suka tafka har ya kai su ga wannan mummunan yanayi da suke ciki. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da irin wannan azabar ne yake hana arzikinsa ga wasu masu saɓon sa, zai kuma azabtar da duk wanda zai butulce masa, ya zaɓi saɓa masa, a duniya zai ga azaba irin wannan. Ya kuma kamata su sani cewa, azabar lahira ta fi wannan girma nesa ba kusa ba. Da a ce su mutane ne masu hankali da basira da sun wa’azantu, sun guji saɓa wa Allah sun dawo cikin hayyacinsu.
إِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Open ayah 68:34Lalle masu taƙawa suna da gidajen Aljannar ni’ima a wurin Ubangijinsu.
أَفَنَجۡعَلُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ كَٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 68:35Yanzu za Mu sanya Musulmi kamar kangararru?
مَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ
Open ayah 68:36Me ya same ku ne, yaya kuke irin wannan hukuncin?
أَمۡ لَكُمۡ كِتَٰبٞ فِيهِ تَدۡرُسُونَ
Open ayah 68:37Ko kuna da wani littafi ne wanda a cikinsa kuke karantawa?
إِنَّ لَكُمۡ فِيهِ لَمَا تَخَيَّرُونَ
Open ayah 68:38(Cewa) a cikinsa lalle kuna da abin da kuke zaɓa?
أَمۡ لَكُمۡ أَيۡمَٰنٌ عَلَيۡنَا بَٰلِغَةٌ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ إِنَّ لَكُمۡ لَمَا تَحۡكُمُونَ
Open ayah 68:39Ko kuwa kuna da wasu alƙawura na rantsuwa ne (tabbatattu) a kanmu har zuwa ranar alƙiyama cewa, lalle kuna da abin da kuke hukunta wa (kanku)?
سَلۡهُمۡ أَيُّهُم بِذَٰلِكَ زَعِيمٌ
Open ayah 68:40Ka tambaye su wane ne a cikinsu ya yi lamuni game da wannan?
أَمۡ لَهُمۡ شُرَكَآءُ فَلۡيَأۡتُواْ بِشُرَكَآئِهِمۡ إِن كَانُواْ صَٰدِقِينَ
Open ayah 68:41Ko kuwa suna da wasu ababan tarayya ne? To su kawo ababan tarayyar tasu idan sun kasance masu gaskiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ni’imar da ya tanadar wa muminai masu kiyaye dokokinsa, suna aikata abin da ya umarce su, suna kuma guje wa haninsa, Allah ya yi musu tanadin gidajen Aljanna na ni’ima waɗanda za su shige su, su mori ni’imomin cikinsu ba tare da yankewa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a bisa girman hikimarsa ba zai taɓa daidaita tsakanin Musulmi masu bin dokokinsa da kafirai kangararru ba, kamar yadda mushirikan Makka suke da’awar cewa, su ma a lahira za a ba su fiye da abin da za a ba wa muminai na jin daɗi, in har da gaske ne akwai ranar lahira ɗin. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙaryata wannan da’awa tasu da cika baki na banza da wofi, ya soke su da kakkausar murya cewa, me ya same su ne suke faɗar irin wannan ɗanyen hukunci mai cike da zalunci? Ko suna da wani littafi ne wanda a cikinsa suka karanta daidaito tsakanin mai bin Allah da mai saɓa masa, suka kuma sami cewa lalle su a lahira suna da abin da suke zaɓa wa kansu? Idan kuwa ba haka ba, to shin suna da wasu tabbatattun alƙawura na rantsuwa ne da suka yi da Allah cewa lalle suna da abin da suke hukunta wa kawunansu na sakamako? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nemi Manzonsa (ﷺ) ya tambaye su, wane ne a cikinsu ya lamunce musu wannan sakamako da suka zaɓa wa kawunansu ? Idan duk ba haka ba, to suna da wasu ababan tarayya da Allah ne waɗanda su ne za su daidaita sakamakonsu da na muminai a lahira? To idan sun ce suna da su to sai su kawo su idan sun kasance masu gaskiya, su zo su yi musu abin da suke da’awa. Tabbas sun san ƙarya suke ba su da wannan.
يَوۡمَ يُكۡشَفُ عَن سَاقٖ وَيُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ
Open ayah 68:42(Ka tuna) ranar da za a yaye ƙwauri a kuma kirawo su zuwa yin sujjada sannan su rasa ikon yi.
خَٰشِعَةً أَبۡصَٰرُهُمۡ تَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۖ وَقَدۡ كَانُواْ يُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ وَهُمۡ سَٰلِمُونَ
Open ayah 68:43Idanuwansu a ƙasƙance, wulaƙanci ya lulluɓe su. Haƙiƙa kuwa a duniya sun kasance ana kiran su zuwa yin sujjada alhali suna lafiyayyu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tsananin azaba da mawuyacin hali da kafirai za su fuskanta a ranar alƙiyama domin a ranar ne abubuwan ban tsoro masu girma za su bayyana, a lokacin Allah (Mai tsarki da daukaka) zai zo don yin hukunci tsakanin bayinsa, sai ya kware ƙwaurinsa mai daraja wanda bai yi kama da wani abu na halittarsa ba, lokacin ne bayinsa za su ƙara sanin girmansa da darajarsa, sai a kirawo su zuwa ga yin sujjada, sai muminai su faɗi su yi masa sujjada, kafirai da munafukai kuwa su yi tsaye ƙiƙam su kasa yin sujjada, idanuwansu a ƙasƙance, nadama da wulaƙanci sun lulluɓe su, alhali sun kasance a duniya an neme su da su yi wa Allah sujjada lokacin da suke cikin ƙoshin lafiya, amma suka ƙi yi, don haka a ranar alƙiyama Allah zai fallasa su, ya bayyana ainihin taurin kansu da mummunan halinsu. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: Ubangijinmu zai yaye Ƙwaurinsa, sai kowane mumini namiji da kowace mumina mace su yi masa sujjada, sai wanda a duniya yake yi masa sujjada don riya ko don a faɗa, ya yi saura (a tsaye), sai ya yunƙura zai yi sujjada sai gadon bayansa ya koma falle ɗaya, (watau ya sandare).” [Bukhari #4919 da Muslim #183].
فَذَرۡنِي وَمَن يُكَذِّبُ بِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِۖ سَنَسۡتَدۡرِجُهُم مِّنۡ حَيۡثُ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 68:44Saboda haka ka bar Ni da wanda yake ƙaryata wannan Alƙur’ani; ba da daɗewa ba za Mu yi musu talala ta inda ba za su sani ba.
وَأُمۡلِي لَهُمۡۚ إِنَّ كَيۡدِي مَتِينٌ
Open ayah 68:45Kuma zan saurara musu. Lalle kaidina mai ƙarfi ne.
أَمۡ تَسۡـَٔلُهُمۡ أَجۡرٗا فَهُم مِّن مَّغۡرَمٖ مُّثۡقَلُونَ
Open ayah 68:46Ko kuwa kana tambayar su wani lada ne, saboda haka biyan (wannan lada) ya yi musu nauyi?
أَمۡ عِندَهُمُ ٱلۡغَيۡبُ فَهُمۡ يَكۡتُبُونَ
Open ayah 68:47Ko kuwa sanin gaibu a wurinsu yake, saboda haka suke rubuto shi?
فَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ وَلَا تَكُن كَصَاحِبِ ٱلۡحُوتِ إِذۡ نَادَىٰ وَهُوَ مَكۡظُومٞ
Open ayah 68:48To ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar ma’abocin kifi (Yunus) a yayin da ya yi kira, alhali shi yana cike da baƙin ciki.
لَّوۡلَآ أَن تَدَٰرَكَهُۥ نِعۡمَةٞ مِّن رَّبِّهِۦ لَنُبِذَ بِٱلۡعَرَآءِ وَهُوَ مَذۡمُومٞ
Open ayah 68:49Ba don wata rahama daga Ubangijinsa ta riske shi ba, da an jefar da shi a ƙungurmin daji alhali shi yana abin suka.
فَٱجۡتَبَٰهُ رَبُّهُۥ فَجَعَلَهُۥ مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 68:50Sai Ubangijinsa Ya zaɓe shi Ya sanya shi daga (bayi) nagari.
وَإِن يَكَادُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَيُزۡلِقُونَكَ بِأَبۡصَٰرِهِمۡ لَمَّا سَمِعُواْ ٱلذِّكۡرَ وَيَقُولُونَ إِنَّهُۥ لَمَجۡنُونٞ
Open ayah 68:51Lalle kuma waɗanda suka kafirta sun yi kusa su kayar da kai da kallonsu yayin da suka ji Alƙur’ani, suka kuma riƙa cewa: “Lalle shi tabbas mahaukaci ne!”
وَمَا هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 68:52Shi kuwa (Alƙur’ani) ba wani abu ba ne face gargaɗi ga talikai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) game da ƙaryata Alƙur’ani da kafirai suke yi, da cewa zai yi musu talala, ya riƙa ba su dukiya da ‘ya’ya, domin su ruɗu da haka, su yi zaton babu wata azaba da zai yi musu, alhali kuwa wannan wani shiri ne nasa mai ƙarfi a gare su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wani ruɗani ta fuskar kafirai wanda wataƙila ko shi ne ya hana su karɓar gaskiya: <b>Na ɗaya, </b> ya tambayi Manzonsa (ﷺ) cewa, ko yana neman wani lada ne a wurinsu game da abin da yake kiran su zuwa gare shi, saboda haka biyan wannan ladan ya yi musu nauyi, don haka suka bijire wa kiransa? Babu shakka ba haka abin yake ba, Manzo (ﷺ) ba ya neman wani lada a wurinsu, to me ya hana su su yi imani da shi? <b>Na biyu, </b>ko kuma sun san gaibu ne, don haka suke rubuto abin da suke so su yi jayayya da Manzon Allah (ﷺ) da shi da hujjojinsa masu ƙarfi, wannan ya sa ba dole ne su yi imani da shi ba? Sai kuma ya umarci Manzonsa (ﷺ) da cewa, ya yi haƙuri da hukuncin da Ubangijinsa ya yi na cewa, zai yi musu talala har lokacin damƙar su ya yi, watau ya ci gaba da isar musu da saƙon Allah, kada muzgunawarsu ta hana shi faɗa musu gaskiya, kada kuma ya zama kamar Annabi Yunusa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) <b> </b>wanda ya yi fushi ya bar mutanensa ya hau jirgin ruwa ya guje musu. Yayin da nauyi ya yi wa jirgin ruwa yawa sai mutanen cikinsa suka yi ƙuri’a a kan wanda ya cancanta su jefa cikin ruwa don rage wa jirgin nauyi, sai ƙuri’a ta faɗa kansa, sai suka jefa shi cikin ruwa, kifi kuma ya haɗiye shi yana abin zargi. Sannan ne ya yi ta kiran Allah yana maƙare da baƙin ciki a cikin duhun kogi da duhun cikin kifi, yana yi wa Allah tasbihi da yin iƙirari na cewa lalle ya aikata laifi, ya zalunci kansa. Sai ko Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karɓi addu’arsa ya tserar da shi daga cikin cikin kifi ya yaye masa damuwarsa, wanda ba don rahamar Allah (Mai tsarki da daukaka) ta riske shi ba, da kifin nan ya jefar da shi can cikin wani ƙungurmin daje yana abin suka, to amma sai Ubangijinsa ya zaɓe shi ya sanya shi cikin bayi nagari. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin tsananin gabar mushirikai ga Manzonsa (ﷺ) da muguwar hassadar da ta cika musu zukata har ta bayyana a idanunsu, har saura ƙiris su kayar da Manzon Allah (ﷺ) saboda mugun kallon da suke yi masa da idanuwansu masu cike da hassada, yayin da suka ji yana karanta musu Alƙur’ani, amma saboda tsananin bin son zuciya da bijire wa gaskiya sai suka riƙa cewa, lalle Manzon Allah mahaukaci ne, alhali sun san cewa Alƙur’ani ba wani abu ne ba face wa’azi da faɗakarwa ga talikai mutune da aljannu.