الحاقة

Al-Haaqqa

The Reality · Surah 69 · Ayahs: 52 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. ٱلۡحَآقَّةُ

    Open ayah 69:1

    Mai tabbata (watau alƙiyama)

  2. مَا ٱلۡحَآقَّةُ

    Open ayah 69:2

    Mece ce mai tabbata?

  3. وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحَآقَّةُ

    Open ayah 69:3

    Me ya sanar da kai abin da ake kira mai tabbata?

  4. كَذَّبَتۡ ثَمُودُ وَعَادُۢ بِٱلۡقَارِعَةِ

    Open ayah 69:4

    Samudawa da Adawa sun ƙaryata mai ƙwanƙwasa (zukata da tsoro).

  5. فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهۡلِكُواْ بِٱلطَّاغِيَةِ

    Open ayah 69:5

    To amma Samudawa sai aka halaka su da tsawa mai tsanani.

  6. وَأَمَّا عَادٞ فَأُهۡلِكُواْ بِرِيحٖ صَرۡصَرٍ عَاتِيَةٖ

    Open ayah 69:6

    Adawa kuma sai aka hallaka su da iska mai tsananin sanyi mai ƙarfi.

  7. سَخَّرَهَا عَلَيۡهِمۡ سَبۡعَ لَيَالٖ وَثَمَٰنِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومٗاۖ فَتَرَى ٱلۡقَوۡمَ فِيهَا صَرۡعَىٰ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٍ خَاوِيَةٖ

    Open ayah 69:7

    Ya aiko musu da ita dare bakwai da wuni takwas a jere, sai ka riƙa ganin mutane a cikinta matattu a yashe, kai ka ce rarakakkun kututturan dabinai ne (a zube).

  8. فَهَلۡ تَرَىٰ لَهُم مِّنۢ بَاقِيَةٖ

    Open ayah 69:8

    To shin za ka iya ganin sauran ɓurɓushinsu?

  9. وَجَآءَ فِرۡعَوۡنُ وَمَن قَبۡلَهُۥ وَٱلۡمُؤۡتَفِكَٰتُ بِٱلۡخَاطِئَةِ

    Open ayah 69:9

    Fir’auna kuma da waɗanda suke gabaninsa da (alƙaryar) da aka kifar, sun zo da manyan laifuka.

  10. فَعَصَوۡاْ رَسُولَ رَبِّهِمۡ فَأَخَذَهُمۡ أَخۡذَةٗ رَّابِيَةً 

    Open ayah 69:10

    Sai suka saɓa wa Manzon Ubangijinsu, sai Muka kama su kamawa mai ƙaruwa.

  11. إِنَّا لَمَّا طَغَا ٱلۡمَآءُ حَمَلۡنَٰكُمۡ فِي ٱلۡجَارِيَةِ

    Open ayah 69:11

    Mu lalle yayin da ruwa ya mamaye komai Mun ɗauke ku a cikin jirgin ruwa.

  12. لِنَجۡعَلَهَا لَكُمۡ تَذۡكِرَةٗ وَتَعِيَهَآ أُذُنٞ وَٰعِيَةٞ

    Open ayah 69:12

    Don Mu sanya shi wa\'azi a gare ku, kuma kunne mai kiyayewa ya kiyaye shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da batun ranar alƙiyama, inda ya kira ta da sunan mai tabbata, domin a cikinta ne abubuwan da mushirikai suke ƙaryatawa, kamar tashi bayan mutuwa da sakamakon Aljanna da wuta da sauran ababan ban tsoro da za su auku su kuma tabbata a zahiri kowa ya gani da idonsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya girmama lamarin wannan rana da cewa, ita wannan mai tabbata ɗin mece ce ita? Kuma me ya sanar da mai karatu abin da ake kira mai tabbata? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani ɓangare na labarin kafirai da suka gabata waɗanda suka ƙaryata manzannin Allah, kuma ya saukar musu da azabarsa, kamar Samudawa mutanen Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda suka ƙaryata ranar alƙiyama mai ƙwanƙwasar zukata da matsanancin tsoro. Amma su Samudawa sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su da tsawa mai tsananin gaske. Su kuma Adawa sai ya hallaka su da iska mai tsananin sanyi mai ƙarfin gaske, wadda ya aiko musu da ita har tsawon dare bakwai da wuni takwas wadda ta ƙarar da ilahirinsu, ta bar su matattu a yaryashe a ƙasa ba mai motsi kamar dai rarakakkun kututturan dabinai waɗanda suke zube a ƙasa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tambaya cewa, ko akwai wani wanda ya ga ɗaya daga cikinsu ya yi saura a bayan ƙasa bayan da Allah ya hallaka su? Babu ko mutum ɗaya da ya rage, duk sun hallaka. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu al’ummu da suka zo bayan Adawa da Samudawa waɗanda su ma suka ƙaryata manzanninsu, kamar Fir’auna wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aika masa Annabi Musa da Annabi Haruna (() ya ƙaryata su. Hakanan akwai wasu al’ummu da suka gabace shi da wasu alƙaryu da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar musu da azaba, watau alƙaryun Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda Allah ya kifar da su saboda miyagun laifukansu na shirka da saɓon Allah (Mai tsarki da daukaka). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, duk waɗannan al’ummu sun saɓa wa manzon da ya aiko musu, sun ƙaryata shi, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kama su da azaba mai ƙaruwa a kan gwargwadon wadda ta isa ta hallaka su, saboda tsananin kafircinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani ɓangare na labarin Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) watau farkon Manzo da ya aiko duniya wanda mutanensa suka ƙaryata shi, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sako musu ruwan Ɗufana sama da ƙasa ya hallaka su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yayin da ruwan ya yi sama ya yi toroƙo ya mamaye komai a bayan ƙasa, sai ya ɗauki iyayensu waɗanda suke cikin tsatsonsu a cikin jirgin ruwa wanda Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sassaƙa da umarnin Allah (Mai tsarki da daukaka), don haka wannan wata ni’ima ce ga duk waɗanda za su zo bayansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hikimar yin haka da cewa, don ya sanya wannan jirgin ruwa da labarinsa su zamanto wa’azi mai nuna yadda yake hallaka kafirai ya tserar da muminai, kuma duk wani mai kunnen kiyaye labarai ya kiyaye da wannan labarin, ya zame masa izina.

  13. فَإِذَا نُفِخَ فِي ٱلصُّورِ نَفۡخَةٞ وَٰحِدَةٞ

    Open ayah 69:13

    To idan aka busa ƙaho busa ɗaya.

  14. وَحُمِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةٗ وَٰحِدَةٗ

    Open ayah 69:14

    Aka kuma ɗaga ƙasa da duwatsu sai aka dandaƙe su dandaƙewa baki ɗaya.

  15. فَيَوۡمَئِذٖ وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ

    Open ayah 69:15

    To a wannan rana ce mai afkuwa ta afku (watau alƙiyama).

  16. وَٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَهِيَ يَوۡمَئِذٖ وَاهِيَةٞ

    Open ayah 69:16

    Sama kuma ta kekkece, don kuwa a wannan ranar ita mai rauni ce.

  17. وَٱلۡمَلَكُ عَلَىٰٓ أَرۡجَآئِهَاۚ وَيَحۡمِلُ عَرۡشَ رَبِّكَ فَوۡقَهُمۡ يَوۡمَئِذٖ ثَمَٰنِيَةٞ

    Open ayah 69:17

    Mala’iku kuma suna a sasanninta. A wannan ranar kuma (mala’iku) takwas za su ɗauki Al’arshin Ubangijinka a samansu.

  18. يَوۡمَئِذٖ تُعۡرَضُونَ لَا تَخۡفَىٰ مِنكُمۡ خَافِيَةٞ

    Open ayah 69:18

    A wannan ranar ne kuma za a bujuro da ku, ba wani abu naku mai ɓuya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana abubuwan da za su faru yayin da ranar alƙiyama ta tabbata, wadda a cikinta Allah (Mai tsarki da daukaka) zai yi wa masu ƙaryata ta hisabi da sakamako cikakke a kan duk ayyukansu. Wannan rana za ta fara lokacin da Mala’ika Israfilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zai yi busa ɗaya a ƙaho, watau busa ta biyu, a lokacin rayukan ɗaukacin halittu za su koma cikin jikkunan masu su, su miƙe su tsaya cirko-cirko a firgice. A lokacin Allah zai ruguje duk tsarin duniya, a ɗaga ƙasa da duwatsu a niƙe su niƙewa ta bai-ɗaya, ƙasa ta koma fili fetal babu tudu babu kwari, duwatsu kuma su rududduge su zama kamar ƙura abar ɗaiɗaitawa. To a wannan ranar ne ranar alƙiyama mai aukuwa ta auku, watau ta tabbata. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin da sama za ta kasance a ranar da cewa, za ta kekkece ta yi ƙofofi don saukar mala’iku, domin ita a wannan ranar ta zama mai rauni, bayan a da ta kasance rufi ne mai tsananin ƙarfi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, su kuma mala’iku za su tsaya a gefunan sama suna masu ƙasƙantar da kai ga Allah (Mai tsarki da daukaka). A wannan rana mai girma mala’iku takwas ne suke ɗauke da Al’arshin Allah (Mai tsarki da daukaka). A ranar za a bujuro da halittu gaba ɗayansu a gaban Allah, su bayyana a fili babu wani wanda zai ɓoye wa Allah, domin ya san komai yana kuma ganin kowa, zai yi wa kowa hisabi, ya saka masa gwargwadon aikinsa.

  19. فَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَيَقُولُ هَآؤُمُ ٱقۡرَءُواْ كِتَٰبِيَهۡ

    Open ayah 69:19

    To duk wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na dama zai ce: “Ku karɓi littafina ku karanta.

  20. إِنِّي ظَنَنتُ أَنِّي مُلَٰقٍ حِسَابِيَهۡ 

    Open ayah 69:20

    “Lalle ni na tabbata haka zan haɗu da sakamakona.”

  21. فَهُوَ فِي عِيشَةٖ رَّاضِيَةٖ

    Open ayah 69:21

    To shi zai zama cikin rayuwa abar yarda.

  22. فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٖ

    Open ayah 69:22

    Cikin Aljanna maɗaukakiya.

  23. قُطُوفُهَا دَانِيَةٞ

    Open ayah 69:23

    ‘Ya’yan itatuwanta dab da dab suke.

  24. كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَآ أَسۡلَفۡتُمۡ فِي ٱلۡأَيَّامِ ٱلۡخَالِيَةِ

    Open ayah 69:24

    (A ce da su): “Ku ci ku sha kuna masu farin ciki saboda abin da kuka gabatar a kwanakinku da suka shuɗe (na duniya).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin hukuncin da zai zartar ga bayinsa ranar alƙiyama da sakamakon kowanne daga cikinsu, da cewa, duk wanda aka ba shi littafin ayyukansa a hannunsa na dama, to wannan zai cika da farin ciki da annashawa har ma ya dinga nuna wa mutane littafinsa, yana roƙon da su karɓi littafinsa su karanta su ga karramawar da Allah ya yi masa. Har ma da bayyana musu cewa, da ma ya sani kuma ya tabbatar za a sake tashin sa kuma zai haɗu da kyakkyawan sakamakonsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan bawa nasa nagari ɗan Aljanna ne, yana cikin rayuwar da zai yarda ya amince da ita, saboda ta ƙunshi ni’imomi waɗanda ba sa yankewa har abada, domin zai shiga cikin Aljanna maɗaukakiya, cikin manya-manyan gidaje na alfarma, ga gonaki da lambuna kewaye da shi, ‘ya’yan itatuwansu kuwa dab da dab suke ba su da wahalar tsinkowa. A nan ne za a riƙa faɗa wa ‘yan Aljanna cewa, su ci lafiyayyen abinci su kuma sha daddaɗan abin sha, saboda kyawawan ayyuka da suka gabatar a rayuwarsu ta duniya na salloli da azumi da sadaka da hajji da kyautata wa mutane da nesantar miyagun ayyuka.

  25. وَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِشِمَالِهِۦ فَيَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي لَمۡ أُوتَ كِتَٰبِيَهۡ

    Open ayah 69:25

    Amma kuma wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na hagun sai ya ce: “Kaicona, ina ma da ba a ba ni littafina ba!

  26. وَلَمۡ أَدۡرِ مَا حِسَابِيَهۡ

    Open ayah 69:26

    “Kuma ban san mene ne sakamakona ba.

  27. يَٰلَيۡتَهَا كَانَتِ ٱلۡقَاضِيَةَ

    Open ayah 69:27

    “Kaiconta (watau mutuwa), ina ma da ta zama ita ce ƙarshe!

  28. مَآ أَغۡنَىٰ عَنِّي مَالِيَهۡۜ

    Open ayah 69:28

    “Dukiyata ba ta wadata min komai ba.

  29. هَلَكَ عَنِّي سُلۡطَٰنِيَهۡ

    Open ayah 69:29

    “Mulkina ya ɓace min da gani.”

  30. خُذُوهُ فَغُلُّوهُ 

    Open ayah 69:30

    (Sai a ce da mala’iku): Ku kama shi ku ƙuƙunce shi!

  31. ثُمَّ ٱلۡجَحِيمَ صَلُّوهُ

    Open ayah 69:31

    Sannan ku shigar da shi (wutar) Jahimu.

  32. ثُمَّ فِي سِلۡسِلَةٖ ذَرۡعُهَا سَبۡعُونَ ذِرَاعٗا فَٱسۡلُكُوهُ

    Open ayah 69:32

    Sannan ku sa shi cikin sarƙa mai tsawo kamu saba’in.

  33. إِنَّهُۥ كَانَ لَا يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ ٱلۡعَظِيمِ

    Open ayah 69:33

    Lalle shi ya kasance ba ya imani da Allah Mai girma.

  34. وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ

    Open ayah 69:34

    Ba ya kuma kwaɗaitarwa bisa ciyar da mabuƙaci.

  35. فَلَيۡسَ لَهُ ٱلۡيَوۡمَ هَٰهُنَا حَمِيمٞ

    Open ayah 69:35

    To a yau ba shi da wani masoyi a nan.

  36. وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنۡ غِسۡلِينٖ

    Open ayah 69:36

    Kuma ba shi da wani abinci sai na mugunyar ‘yan wuta.

  37. لَّا يَأۡكُلُهُۥٓ إِلَّا ٱلۡخَٰطِـُٔونَ

    Open ayah 69:37

    Ba mai cin ta sai masu laifukan ganganci. A waɗannan ayoyi kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon wanda za a ba shi littafin ayyukansa a hannunsa na hagu, to wannan kam zai cika da baƙin ciki da nadama har ma ya riƙa cewa, ina ma ba a ba shi littafin ayyukansa ba, saboda abin da zai gani a ciki na miyagun ayyukan da ya aikata, waɗanda za su jawo masa azabar Allah da hushinsa. Ya kuma riƙa burin ina ma a ce bai san yadda za a yi masa hisabi ba har a nuna masa sakamakonsa. Kai ina ma a ce, mutuwar da ya yi ita ce ƙarshensa, ba za a sake tashin sa ba bayanta. Sannan kuma ya shiga nadama game da sakacin da ya yi a duniya ya yi watsi da aikin alheri ya rungumi abin da zai cutar da shi a lahira, ya yi ta hanƙoron tara dukiya da taskake ta a duniya, ga shi a lahira ba ta amfana masa komai ba. Ga shi kuma ya rasa wata hujja ko wani ƙarfi da mulki da zai kare shi daga azabar Allah (Mai tsarki da daukaka). Hakanan zai yi ta yin sambatu marar amfani, daga ƙarshe Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mala’iku masu tsaron wuta da su damƙe shi su haɗa hannayensa da wuyansa su ɗaure tamau sannan su jefa shi cikin wutar Jahimu, don ya ɗanɗani ƙunarta bayan sun ɗaure shi da sarƙa mai tsawon kamu saba’in ba tare da wani sassauci ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu miyagun ayyukan wannan bawa a duniya waɗanda suka jawo masa wannan mummunan sakamako. Ga shi dai bai yi imani da Allah mai girma ba balle ya bauta masa, sannan ya ƙaryata manzannin Allah da gaskiyar da suka zo masa da ita. Har ila yau kuma ba shi da tausayi ko kaɗan a zuciyarsa, domin ba ya tallafa wa mabuƙata kuma ba ya barin wani ya tallafa musu ballantana har ya kwaɗaitar da wani a kan haka. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, a ranar lahira wannan mutum ba shi da wani makusanci da zai kare shi daga azabar Allah ko ya cece shi a wurin Allah. Kuma a zamansa na cikin wuta ba ya da wani abinci da zai ci in ban da mugunyar abokansa ‘yan wuta, shi kuwa wannan abinci babu mai cin sa sai masu laifuka irin nasa, waɗanda suka kauce wa tafarki madaidaici, suka bi tafarkin ‘yan wuta.

  38. فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَا تُبۡصِرُونَ

    Open ayah 69:38

    Ina yin rantsuwa da abin da kuke gani.

  39. وَمَا لَا تُبۡصِرُونَ

    Open ayah 69:39

    Da kuma abin da ba kwa gani.

  40. إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ 

    Open ayah 69:40

    Lalle shi (Alƙur’ani) tabbas zance ne na wani manzo mai girma.

  41. وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَاعِرٖۚ قَلِيلٗا مَّا تُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 69:41

    Shi kuwa ba zancen mawaƙi ba ne. Kaɗan ne ƙwarai kuke yin imani.

  42. وَلَا بِقَوۡلِ كَاهِنٖۚ قَلِيلٗا مَّا تَذَكَّرُونَ

    Open ayah 69:42

    Ba kuma zance ne na boka ba. Kaɗan ne ƙwarai kuke wa’azantuwa.

  43. تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 69:43

    Shi saukakke ne daga Ubangijin halittu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da duk abin da halittu kan iya gani da ma wanda ba sa iya gani, waɗannan abubuwa sun ƙunshi ɗaukacin halittarsa har da shi kansa mahaliccin komai, don ya tabbatar da gaskiyar Manzon Allah (ﷺ) da Alƙur’anin da ya zo da shi cewa, lalle maganar Allah ne wanda kuma Manzon Allah (ﷺ) ya isar wa mutane. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsarkake Manzonsa (ﷺ) daga duk wata tuhuma da maƙiyansa suke yi masa na cewa, shi mawaƙi ne, alhalin suna ganin Alƙur’ani, su san ba waƙa ba ne, don ba shi da salon zubin waƙa, ba kuma maganar boka ne ba, domin maganar bokaye ta yi hannun-riga da salon Alƙur’ani nesa ba kusa ba. Abin da ya jawo mushirikai suke yi wa Manzon Allah (ﷺ) irin waɗannan tuhumce-tuhumce na banza shi ne rashin imaninsu da rashin wa’azantuwarsu, domin da sun yi imani, sun yi tunani game da kyawawan halayen Manzon Allah (ﷺ) da sun tabbatar da cewa, Alƙur’ani ba ƙirƙirarsa ba ne, saukakke ne daga Allah Ubangijin halittu gaba ɗaya.

  44. وَلَوۡ تَقَوَّلَ عَلَيۡنَا بَعۡضَ ٱلۡأَقَاوِيلِ

    Open ayah 69:44

    Kuma da ya ƙaga Mana wasu maganganu.

  45. لَأَخَذۡنَا مِنۡهُ بِٱلۡيَمِينِ

    Open ayah 69:45

    Tabbas da Mun kama shi da ƙarfi.

  46. ثُمَّ لَقَطَعۡنَا مِنۡهُ ٱلۡوَتِينَ

    Open ayah 69:46

    Sannan da Mun yanke masa jijiyar zuciyarsa.

  47. فَمَا مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ عَنۡهُ حَٰجِزِينَ

    Open ayah 69:47

    Sannan kuma ba wani ɗaya daga cikinku da zai kare shi.

  48. وَإِنَّهُۥ لَتَذۡكِرَةٞ لِّلۡمُتَّقِينَ

    Open ayah 69:48

    Lalle shi (Alƙur’ani) wa’azi ne ga masu kiyaye dokokin Allah.

  49. وَإِنَّا لَنَعۡلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ

    Open ayah 69:49

    Lalle kuma Mu Muna sane da cewa a cikinku akwai masu ƙaryatawa.

  50. وَإِنَّهُۥ لَحَسۡرَةٌ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ 

    Open ayah 69:50

    Kuma lalle shi tabbas nadama ce ga kafirai.

  51. وَإِنَّهُۥ لَحَقُّ ٱلۡيَقِينِ

    Open ayah 69:51

    Kuma lalle shi tabbas gaskiya ce ta sakankancewa.

  52. فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ

    Open ayah 69:52

    Saboda haka ka yi tasbihi da sunan Ubangijinka Mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar wa kafirai cewa, lalle Alƙur’ani maganarsa ce, ba Manzon Allah ne ya ƙirƙiro shi ya danganta shi da Allah ba, domin kuwa da a ce ya ƙirƙiri wasu zantuka na ƙarya ya jingina wa Allah (Mai tsarki da daukaka) to tabbas da ya yi masa matsanancin kamu, sannan da ya tsinke masa jijiyar zuciyarsa nan take ya hallaka, kuma ba za a sami wani mutum ɗaya wanda zai iya kare shi daga uƙubar Allah ba, don haka babu yadda za a yi ya ƙagi ƙarya ga Allah saboda wasu mutane waɗanda ba za su iya ba shi wata kariya daga azabar Allah ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, shi Alƙur’ani wa’azi ne ga mutane masu kiyaye dokokinsa, masu bin umarninsa, masu guje wa haninsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, yana sane lalle a cikinsu akwai masu ƙaryata Alƙur’ani, to masu yin haka su sani cewa, tabbas wannan ƙaryatawar tasu za ta zame musu babbar nadama a ranar alƙiyama. Sannan su sani cewa, lalle Alƙur’ani gaskiya ce tabbatacciya wadda babu sofanen ƙarya a cikinta, domin daga Allah yake. Sai kuma a ayar ƙarshe Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya yi masa tasbihi, ya tsarkake sunan Ubangijinsa mai girma daga duk wata tawaya ko wani aibu.