المعارج

Al-Ma'aarij

The Ascending Stairways · Surah 70 · Ayahs: 44 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. سَأَلَ سَآئِلُۢ بِعَذَابٖ وَاقِعٖ

    Open ayah 70:1

    Mai tambaya ya yi tambaya game da wata azaba mai aukuwa.

  2. لِّلۡكَٰفِرِينَ لَيۡسَ لَهُۥ دَافِعٞ

    Open ayah 70:2

    Ga kafirai (wadda) ba ta da wani mai kaɗe ta.

  3. مِّنَ ٱللَّهِ ذِي ٱلۡمَعَارِجِ

    Open ayah 70:3

    Daga Allah Mai matattakalai.

  4. تَعۡرُجُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ إِلَيۡهِ فِي يَوۡمٖ كَانَ مِقۡدَارُهُۥ خَمۡسِينَ أَلۡفَ سَنَةٖ

    Open ayah 70:4

    Mala’iku tare da Jibrilu suna hawa zuwa gare Shi a cikin wata rana (wadda) gwargwadonta yake daidai da shekara dubu hamsin.

  5. فَٱصۡبِرۡ صَبۡرٗا جَمِيلًا

    Open ayah 70:5

    Sai ka yi haƙuri kyakkyawan haƙuri.

  6. إِنَّهُمۡ يَرَوۡنَهُۥ بَعِيدٗا

    Open ayah 70:6

    Lalle su suna ganin ta mai nisa ce.

  7. وَنَرَىٰهُ قَرِيبٗا

    Open ayah 70:7

    Mu kuma Muna ganin ta kusa-kusa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da bayanin izgili da mushirikai suke yi wa Manzon Allah (ﷺ) dangane da ranar lahira da azaba da yake faɗa musu cewa za ta same su in ba su yi imani ba, har ta kai saboda tsananin izgili da rashin kunya wani kafiri mai suna Nadru ɗan Haris ya riƙa cewa, idan da gaske ne Alƙur’ani daga Allah yake, to Allah ya yi musu ruwan duwatsu daga sama. [Dubi Suratul Anfal , aya ta 32 da Nasa’i, As-Sunan Al-Kubra #11556]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, babu makawa wannan azabar sai ta auku a kan kafirai a ranar alƙiyama, kuma babu mai iya ba su kariya daga gare ta, domin azaba ce daga Allah (Mai tsarki da daukaka) wanda ya siffantu da siffar ɗaukaka da manyan darajoji da ni’imomi masu tarin yawa. Mala’ikunsa tare da Mala’ika Jibrilu kuma suna hawa sama zuwa gare shi don cika umarninsa da zartar da tsare-tsarensa a ranar alƙiyama wadda rana ce mai tsawon gaske, gwargwadon tsawonta shekara dubu hamsin ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) tare sa umartar sa da yin kyakkyawan haƙuri, kada ya bayyana ƙosawarsa ko damuwarsa a fili, watau ya ci gaba da kiran mutanensa zuwa ga Allah da bauta masa shi kaɗai. Ya bayyana masa cewa mutanensa mushirikai suna ganin nisar azabar Allah, watau a ganinsu ba ma za ta same su ba sam, amma shi Allah mai girma da buwaya yana ganin ta kurkusa, za kuma ta auku babu makawa.

  8. يَوۡمَ تَكُونُ ٱلسَّمَآءُ كَٱلۡمُهۡلِ

    Open ayah 70:8

    A ranar da sama za ta kasance kamar narkakkiyar dalma.

  9. وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ

    Open ayah 70:9

    Duwatsu kuma su zama kamar kaɗaɗɗiyar auduga (ta gashin tumaki).

  10. وَلَا يَسۡـَٔلُ حَمِيمٌ حَمِيمٗا 

    Open ayah 70:10

    Kuma aboki ba ya tambayar aboki.

  11. يُبَصَّرُونَهُمۡۚ يَوَدُّ ٱلۡمُجۡرِمُ لَوۡ يَفۡتَدِي مِنۡ عَذَابِ يَوۡمِئِذِۭ بِبَنِيهِ

    Open ayah 70:11

    (Alhali kuma) ana nuna musu junansu. Mai laifi ya riƙa burin ina ma zai fanshi kansa daga azabar wannan rana da ‘ya’yansa.

  12. وَصَٰحِبَتِهِۦ وَأَخِيهِ

    Open ayah 70:12

    Da matarsa da ɗan’uwansa.

  13. وَفَصِيلَتِهِ ٱلَّتِي تُـٔۡوِيهِ

    Open ayah 70:13

    Da danginsa waɗanda suke kare shi.

  14. وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا ثُمَّ يُنجِيهِ

    Open ayah 70:14

    Da ma duk wanda yake a bayan ƙasa baki ɗaya, sannan (fansar) ta tserar da shi.

  15. كَلَّآۖ إِنَّهَا لَظَىٰ

    Open ayah 70:15

    Faufau! Lalle ita (wutar) Laza ce.

  16. نَزَّاعَةٗ لِّلشَّوَىٰ

    Open ayah 70:16

    Mai ɗaɗɗaye fatar kai.

  17. تَدۡعُواْ مَنۡ أَدۡبَرَ وَتَوَلَّىٰ

    Open ayah 70:17

    Tana kiran wanda ya juya ya ba da baya.

  18. وَجَمَعَ فَأَوۡعَىٰٓ

    Open ayah 70:18

    Ya kuma tara (dukiya) sai ya ɓoye (ta). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu lamura da za su faru a ranar alƙiyama lokacin da sama za ta tsattsage ta zama kamar narkakkiyar dalma ko tagulla, duwatsu kuma su zama kamar kaɗaɗɗiyar audugar gashin tumaki. A ranar kowa zai kiɗime yana ta kansa; wani makusanci ba zai tambayi halin da makusancinsa yake ciki ba; a ranar ne mutum zai ga ɗan’uwansa makusanci ya gane shi sarai, amma ba wanda zai tsaya tambayar abin da ɗan’uwansa yake ciki don tsananin tsoro da firgita. A ranar kafiri zai yi burin ina ma a ce zai iya ba da ‘ya’yansa ya fanshi kansa da su daga azabar Allah, ko ya fanshi kansa da matarsa ko ɗan’uwansa, ko kuma da danginsa na kusa waɗanda suke tsaya masa lokacin da ya shiga cikin wasu wahalhalu; kai ko ma ya fanshi kansa da duk waɗanda suke a bayan ƙasa mutane da aljannu da dabbobi da sauransu, domin shi dai ya samu ya kuɓuta daga azabar wuta. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar masa da martani cewa, abin ba haka yake ba, babu mai iya amfana masa komai daga duk waɗanda ya ambata, domin kuwa wannan azabar da yake gani azaba ce ta wutar Laza mai tsananin ruruwa, mai ɗaɗɗaye fatar kai saboda tsananin zafi, za ta riƙa kiran duk wanda ya juya wa gaskiya baya ya bijire wa bautar Allah shi kaɗai; babu abin da ya sanya a gaba a rayuwarsa ta duniya sai tara dukiya da ɓoye ta ba tare da ya amfanar da kowa da ita ba.

  19. ۞إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ خُلِقَ هَلُوعًا

    Open ayah 70:19

    Lalle mutum an halicce shi mai rashin nutsuwa ne.

  20. إِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ جَزُوعٗا 

    Open ayah 70:20

    (Watau) idan sharri ya same shi ya zama mai raki.

  21. وَإِذَا مَسَّهُ ٱلۡخَيۡرُ مَنُوعًا

    Open ayah 70:21

    Idan kuma alheri ya same shi ya zama mai maƙo.

  22. إِلَّا ٱلۡمُصَلِّينَ

    Open ayah 70:22

    Sai dai masallata.

  23. ٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ دَآئِمُونَ

    Open ayah 70:23

    Waɗanda suke masu dawwama a kan sallarsu.

  24. وَٱلَّذِينَ فِيٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ حَقّٞ مَّعۡلُومٞ

    Open ayah 70:24

    Waɗanda kuma suke akwai haƙƙi sananne a cikin dukiyoyinsu.

  25. لِّلسَّآئِلِ وَٱلۡمَحۡرُومِ

    Open ayah 70:25

    Ga mai roƙo da wanda ake hana wa (saboda ba ya roƙo).

  26. وَٱلَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ

    Open ayah 70:26

    Waɗanda kuma suke gaskata ranar sakamako.

  27. وَٱلَّذِينَ هُم مِّنۡ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشۡفِقُونَ

    Open ayah 70:27

    Waɗanda kuma suke tsoron azabar Ubangijinsu.

  28. إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمۡ غَيۡرُ مَأۡمُونٖ

    Open ayah 70:28

    Lalle azabar Ubangijinsu ba abar amincewa ba ce.

  29. وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ

    Open ayah 70:29

    Waɗanda kuma suke kiyaye al’aurarsu (daga yin zina).

  30. إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ 

    Open ayah 70:30

    Sai a wajan matayensu ko kuma ƙwarƙarorinsu; to su a nan ba ababen zargi ba ne.

  31. فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ

    Open ayah 70:31

    To duk wanda ya nemi (wani abu) bayan wannan, to waɗannan su ne masu ƙetare iyaka.

  32. وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ

    Open ayah 70:32

    Waɗanda kuma suke kiyaye amanoninsu da alƙawuransu.

  33. وَٱلَّذِينَ هُم بِشَهَٰدَٰتِهِمۡ قَآئِمُونَ

    Open ayah 70:33

    Waɗanda kuma suke tsai da shaidarsu.

  34. وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ يُحَافِظُونَ

    Open ayah 70:34

    Waɗanda kuma suke kiyaye sallolinsu. <b>

  35. أُوْلَٰٓئِكَ فِي جَنَّٰتٖ مُّكۡرَمُونَ

    Open ayah 70:35

    Waɗannan su ne waɗanda ake girmamawa cikin gidajen Aljanna. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu munanan ɗabi’u da ya halicci jinsin mutum da su da kuma hanyar magance su, inda ya tabbatar da cewa, ya halicci ɗan’adam mai rashin nutsuwa ne da saurin karayar zuciya, watau idan wani sharri ya same shi, kamar rashin lafiya ko talauci, to sai ya zamanto mai yawan raki, idan kuma wani abin alheri ne ya same shi, kamar wadata ko yalwa, to sai ya zama mai maƙo, ba ya ciyar da dukiyarsa don Allah, don tsoron talaucewa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci waɗanda za a kuɓutar daga waɗannan munanan halaye, su ne masu tsai da salla, waɗanda ya siffanta su da siffofi takwas : <b>Na ɗaya </b>, su ne masu dimantar sallolinsu na farilla, babu abin da yake ɗauke musu hankali a kansu, suna yin su a lokutansu ƙayyadaddu. <b>Na biyu </b>, su ne waɗanda suke akwai haƙƙi sananne a cikin dukiyoyinsu, watau na zakka da sadaka, suna kuma bayar da shi ga wanda ya roƙe su da ma wanda ya rasa amma bai roƙa ba. <b>Na uku </b>, su ne waɗanda suke gaskata zuwan ranar alƙiyama sanda Allah (Mai tsarki da daukaka) zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa. <b>Na huɗu </b>, su ne masu tsoron azabar Ubangijinsu tare da cewa sun yi ayyuka kyawawa, domin azabar Allah abin tsoro ce, duk mai hankali ba zai aminta daga gare ta ba. <b>Na biyar </b>, su ne waɗanda suke kiyaye al’aurarsu, ba sa kusantar zina da sauran ayyukan alfasha. Sun taƙaita kawai a kan abin da Allah ya halatta musu na matayensu na aure ko kuma saɗakunsu waɗanda suka mallaka ta hanyar da shari’a ta amince. To idan sun kusanci waɗannan domin biyan buƙatarsu, su kam ba ababan zargi ba ne, domin Allah ya halatta musu su. Amma duk wani wanda ya nemi biyan buƙatarsa ba ta hanyar waɗannan ba, to waɗannan su ne masu ƙetare iyakar Allah, masu auka wa haramun. <b>Na shida </b>, su ne waɗanda suke kiyaye amanar da aka ba su ta dukiya ko ta wani sirri, suke kuma kiyaye duk wani alƙawari da aka ƙulla da su, ba sa cin amana, ba sa kuma karya alƙawari. <b>Na bakwai </b>, su ne masu tsayawa su bayar da shaidarsu yadda ya dace, ba tare da la’akari da kusanci ko gaba ba. <b>Na takwas </b>, su ne masu kiyaye sallolinsu, suna yin su a kan lokutansu tare da cikakkiyar ɗahara da nutsuwa, babu kuma abin da yake shagaltar da su har ya ɗauke musu hankali. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, masu waɗannan siffofi su ne waɗanda za a karrama su a gidajen Aljanna, inda za a sanya su a cikin ni’ima ta har abada, su kuma dace da ganin fuskar Ubangijinsu Maɗaukakin Sarki.

  36. فَمَالِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ قِبَلَكَ مُهۡطِعِينَ

    Open ayah 70:36

    To me ya sami waɗanda suka kafirta suke gaggawa zuwa gare ka?

  37. عَنِ ٱلۡيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ عِزِينَ

    Open ayah 70:37

    Ƙungiya-ƙungiya, ta damanka da ta hagunka.

  38. أَيَطۡمَعُ كُلُّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ أَن يُدۡخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٖ

    Open ayah 70:38

    Yanzu ashe kowane mutum daga cikinsu yana kwaɗayin a shigar da shi Aljannar ni’ima?

  39. كَلَّآۖ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّمَّا يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 70:39

    Faufau! Lalle Mu Mun halitta su daga abin da suka sani.

  40. فَلَآ أُقۡسِمُ بِرَبِّ ٱلۡمَشَٰرِقِ وَٱلۡمَغَٰرِبِ إِنَّا لَقَٰدِرُونَ 

    Open ayah 70:40

    To, ina yin rantsuwa da Ubangijin wuraren hudowar rana da wuraren faɗuwarta, lalle Mu Masu iko ne.

  41. عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ

    Open ayah 70:41

    A kan Mu musanya wasu fiye da su, kuma Mu ba Masu kasawa ba ne.

  42. فَذَرۡهُمۡ يَخُوضُواْ وَيَلۡعَبُواْ حَتَّىٰ يُلَٰقُواْ يَوۡمَهُمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ

    Open ayah 70:42

    To ka ƙyale su su kutsa su yi wasa har sai sun haɗu da ranarsu wadda ake yi musu alƙawarinta.

  43. يَوۡمَ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ سِرَاعٗا كَأَنَّهُمۡ إِلَىٰ نُصُبٖ يُوفِضُونَ

    Open ayah 70:43

    A ranar da za su fito daga ƙaburbura a gurguje, kai ka ce su suna gaggawa ne zuwa ga wata tuta (ta matattara).

  44. خَٰشِعَةً أَبۡصَٰرُهُمۡ تَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۚ ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلَّذِي كَانُواْ يُوعَدُونَ

    Open ayah 70:44

    Idanuwansu a ƙasƙance, wulaƙanci ya lulluɓe su. Wannan ne ranar da ake yi musu alƙawarinta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani abin takaici na mushirikan Makka yayin da suke taƙarƙarewa a kan ƙaryata Manzonsa (ﷺ). Sukan yi cincirindo je wajensa ƙungiya-ƙungiya su kewaye shi ta ko’ina dama da hagu, kamar suna sauraron sa, amma ba sauraro ne na amfanuwa ba, suna dai jin sa ne kawai domin izgili su samu damar ƙaryata shi, har da furta cewa, idan ma da gaske ne akwai lahira, akwai kuma Aljanna, to ai su ne za su riga shigar ta kafin muminai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa, faufau wannan ruɗu ne kawai da tsageranci irin nasu. Idan ba haka ba ta yaya ma za a ce, tantagaryar kafiri mai ƙaryata Allah da Manzonsa kuma ya mutu kafiri bai tuba ba, a ce wai shi ne Allah zai mutunta ya shigar da shi Aljannar ni’ima? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsawatar musu wannan tunani da cewa, faufau, wannan ruɗu ne kawai da ƙin gaskiya, alhali sun tabbatar da cewa, Allah ne ya halicce su daga wani wulaƙantaccen ruwa na maniyyi har suka fito duniya suna raunana, ba sa iya amfana wa kansu komai, amma kuma sai ga shi yanzu suna ƙaryata tashi bayan mutuwa. A kan haka Allah ya yi rantsuwa da Zatinsa, cewa shi ne Ubangijin mahudar rana da mafaɗarta, kuma lalle shi mai iko ne a kan ya hallaka su gaba ɗayansu, ya musanya su da wasu da suka fi su alheri waɗanda za su yi masa biyayya. Yin haka kuwa ba abu ne da zai gagare shi ba duk sanda ya so aiwatar da shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da cewa, ya ƙyale su su yi ta kutsawa cikin ƙarya da ɓarna, su yi ta wasanni a rayuwarsu ta duniya har sai sun haɗu da ranar alƙiyama wadda ake yi musu alƙawarin zuwanta, ranar da za su yi nadama wadda ba za ta yi musu amfani ba. Rana ce da za su fito daga ƙaburburansu a gurguje kamar suna yin tsere zuwa wata tuta; a ranar babu wanda zai iya bijire wa mai kiran sa duk taurin kansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, za su yi ta gaggawa zuwa tsayuwa gaban Ubangijinsu, idanuwansu a ƙasƙance, wulaƙanci ya lulluɓe su, a lokacin za a tabbatar musu cewa, wannan ita ce ranar da ake ta yi musu alƙawarin zuwanta tun a duniya, amma ba su ɗauka da gaske ne ba, don haka ga shi alƙawarin Allah ya tabbata.