نوح
Nooh
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦٓ أَنۡ أَنذِرۡ قَوۡمَكَ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 71:1Lalle Mu Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa cewa: “Ka gargaɗi mutanenka tun kafin azaba mai raɗaɗi ta zo musu.”
قَالَ يَٰقَوۡمِ إِنِّي لَكُمۡ نَذِيرٞ مُّبِينٌ
Open ayah 71:2Ya ce: “Ya ku mutanena, lalle ni mai gargaɗi ne mabayyani a gare ku.
أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُ وَأَطِيعُونِ
Open ayah 71:3“Kan ku bauta wa Allah, ku kiyaye dokokinsa, kuma ku bi ni.
يَغۡفِرۡ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمۡ وَيُؤَخِّرۡكُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمًّىۚ إِنَّ أَجَلَ ٱللَّهِ إِذَا جَآءَ لَا يُؤَخَّرُۚ لَوۡ كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 71:4“Zai gafarta muku zunubanku, Ya kuma jinkirta muku har zuwa wani lokaci iyakantacce. Lalle ajalin Allah idan ya zo ba a saurarawa; da kun kasance kun san (haka). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da tabbatar wa Manzonsa (() cewa, lalle ya aiko Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zuwa ga mutanensa domin ya kira su ya gargaɗe su da azaba mai raɗaɗi idan suka kafe a kan kafircinsu suka ƙi yin imani da shi. Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bi umarnin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mutanensa cewa, shi mai bayyana gargaɗi ne a gare su game da azabar Allah da take dakon su har idan ba su tuba suka daina yin shirka ba. Ya kuma umarce su da su bauta wa Allah (Mai tsarki da daukaka) shi kaɗai, kada su haɗa shi da komai, su kuma kiyaye dokokinsa, su bi umarninsa su kuma guje wa haninsa, su yi wa shi kansa Annabi Nuhu biyayya game da duk abin da yake umartar su da shi na kaɗaita Allah. Ya tabbatar musu cewa, idan har sun yarda da haka, to Allah zai gafarta musu laifukan da ke tsakaninsu da shi, zai kuma ba wa al’ummarsu tsawon rai har zuwa lokacin da ya iyakance musu, ta yadda za su ci gaba da raya ƙasa matuƙar ba su saki hanyarsa ba. Sannan ya jaddada musu cewa, lalle azabar Allah idan ta zo, to ba za a jinkirta ta ba, da sun san da haka da sun yi gaggawar yin imani da tuba zuwa ga Allah, da yin watsi da ayyukan shirka da kafirci da suke kai.
قَالَ رَبِّ إِنِّي دَعَوۡتُ قَوۡمِي لَيۡلٗا وَنَهَارٗا
Open ayah 71:5Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na kira mutanena dare da rana.
فَلَمۡ يَزِدۡهُمۡ دُعَآءِيٓ إِلَّا فِرَارٗا
Open ayah 71:6“To kiran nawa ba abin da ya ƙara musu sai tawaye.
وَإِنِّي كُلَّمَا دَعَوۡتُهُمۡ لِتَغۡفِرَ لَهُمۡ جَعَلُوٓاْ أَصَٰبِعَهُمۡ فِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَٱسۡتَغۡشَوۡاْ ثِيَابَهُمۡ وَأَصَرُّواْ وَٱسۡتَكۡبَرُواْ ٱسۡتِكۡبَارٗا
Open ayah 71:7“Lalle ni kuma duk sanda na kira su don Ka gafarta musu, sai su sanya ‘yan yatsunsu a cikin kunnuwansu, su kuma lulluɓu da tufafinsu kuma su kafe (a kan haka), su yi girman kai matuƙar girman kai.
ثُمَّ إِنِّي دَعَوۡتُهُمۡ جِهَارٗا
Open ayah 71:8“Sannan lalle na yi kiran su da babbar murya.
ثُمَّ إِنِّيٓ أَعۡلَنتُ لَهُمۡ وَأَسۡرَرۡتُ لَهُمۡ إِسۡرَارٗا
Open ayah 71:9“Sannan lalle na yi musu a bayyane, na kuma yi musu a ɓoye sosai.
فَقُلۡتُ ٱسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّكُمۡ إِنَّهُۥ كَانَ غَفَّارٗا
Open ayah 71:10“Sai na ce: “Ku nemi gafarar Ubangijinku, lalle Shi Ya kasance Mai yawan gafara ne.
يُرۡسِلِ ٱلسَّمَآءَ عَلَيۡكُم مِّدۡرَارٗا
Open ayah 71:11“Zai saukar muku da ruwan sama mai yawa.
وَيُمۡدِدۡكُم بِأَمۡوَٰلٖ وَبَنِينَ وَيَجۡعَل لَّكُمۡ جَنَّٰتٖ وَيَجۡعَل لَّكُمۡ أَنۡهَٰرٗا
Open ayah 71:12“Kuma Ya daɗe ku da dukiyoyi da ‘ya’yaye, Ya kuma sanya muku gonaki Ya kuma gudanar muku da ƙoramu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kai kukansa zuwa gare shi, yana faɗa masa irin yadda ya duƙufa a kan kiran mutanensa zuwa ga tauhidi da watsi da shirka, ya kuma bi hanyoyi daban-daban wajen yi musu da’awa amma kamar ba ya yi. Ya bayyana wa Allah cewa, ya dimanci kiran su ba dare ba rana, amma maimakon kiransa ya ƙara musu kusanci da Allah sai ma ya ƙara musu bijirewa da yi masa tawaye. Abin har ya kai duk sanda yake yi musu wa’azi, yana kiran su zuwa bautar Allah don su sami gafararsa, sai su toshe kunnuwansu da ‘yan yatsunsu don kada su saurari abin da yake faɗa musu, su kuma rufe fuskokinsu da tufafinsu don kada ma su gan shi, suka doge da ci gaba a kan kafircinsu, girman kansu ya hana su miƙa wuya gare shi. Sannan Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana hanyoyi daban-daban da ya bi wajen kiran su zuwa ga Allah; ya bi salon yi musu wa’azi a bayyane kowa yana ji; sannan ya kira su da babbar murya don wanda bai jiyo abin da yake faɗa ba ya ji shi, musamman a wuraren tarukansu da haɗuwarsu, ya kuma bi wasu har gida ya yi musu wa’azi a ɓoye daga shi sai su, watau musamman manyansu waɗanda ba za su saurari gaskiya a bainar jama’a ba. Haka kuma ya yi amfani da salon kwaɗaitar da su samun ni’imomin rayuwa idan suka yi imani da shi, ya bayyana musu cewa su tuba su nemi gafarar Allah, domin shi Allah mai yawan gafara ne ga duk wanda ya tuba. Ya tabbatar musu da cewa idan sun yi haka, to Allah (Mai tsarki da daukaka) da falalarsa zai saukar musu da ruwan sama mai yawan zuba a kai-a kai duk sanda suka buƙata su samu, don haka ba za su ji tsoron fari ba. Zai kuma ƙara musu yawan dukiya da ‘ya’ya, ya kuma sanya musu gonaki masu yawan ‘ya’yan itatuwa, ya kuma gudanar musu da ƙoramu waɗanda za su riƙa shan ruwansu su kuma shayar da gonakinsu da dabbobinsu. Babu shakka waɗannan muhimman ni’imomi ne da ɗan’adam yake matuƙar buƙata.
مَّا لَكُمۡ لَا تَرۡجُونَ لِلَّهِ وَقَارٗا
Open ayah 71:13“Me ya same ku ne ba kwa ganin girman Allah?
وَقَدۡ خَلَقَكُمۡ أَطۡوَارًا
Open ayah 71:14“Haƙiƙa kuma Ya halicce ku ta mataki-mataki.
أَلَمۡ تَرَوۡاْ كَيۡفَ خَلَقَ ٱللَّهُ سَبۡعَ سَمَٰوَٰتٖ طِبَاقٗا
Open ayah 71:15“Shin ba kwa ganin yadda Allah Ya halicci sammai bakwai rufi-rufi?
وَجَعَلَ ٱلۡقَمَرَ فِيهِنَّ نُورٗا وَجَعَلَ ٱلشَّمۡسَ سِرَاجٗا
Open ayah 71:16“Ya kuma sanya wata mai haske a cikinsu; rana kuma Ya sanya ta fitila?
وَٱللَّهُ أَنۢبَتَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ نَبَاتٗا
Open ayah 71:17“Allah ne kuma Ya tsiro da ku daga ƙasa a tsirowa (ta halitta).
ثُمَّ يُعِيدُكُمۡ فِيهَا وَيُخۡرِجُكُمۡ إِخۡرَاجٗا
Open ayah 71:18“Sannan Ya mayar da ku cikinta, zai kuma fitar da ku haƙiƙar fitarwa.
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ بِسَاطٗا
Open ayah 71:19“Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa a shimfiɗe.
لِّتَسۡلُكُواْ مِنۡهَا سُبُلٗا فِجَاجٗا
Open ayah 71:20“Don ku riƙa bin manya-manyan hanyoyi a cikinta.” A waɗannan ayoyi Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ci gaba da jan hankalin mutanensa da nuna musu ƙarfafan hujjoji masu nuna Ƙudurar Allah da cikar ikonsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai. Ya ja hankalinsu da cewa, me ya sa ba sa ganin girman Allah, ba sa fatan samun ladansa kuma ba sa jin tsoron uƙubarsa, alhali kuwa sun san shi ne ya halicce su mataki bayan mataki, yayin da ya fara halittar babansu Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga ƙasa, sannan ya halicci kowane ɗaya daga cikinsu daga ɗigon maniyyi, sannan ya mayar da shi jini, sannan gudar tsoka, sannan ya zama mutum cikakke. Da haka suka fito duniya suna jarirai har suka yi wayo suka zama cikakkun mutane masu hankali. Annabi Nuhu kuma ya ja hankalinsu da cewa, ba sa ganin yadda Allah ya halicci sammai bakwai hawa-hawa, wata a saman wata, sannan ya sanya wata a sama mafi kusa ya zama haske mai haskaka doron ƙasa, ita kuma rana ya sanya ta ta zama fitila mai haskaka ko’ina. Su kuma mutane idan suka dubi yanayin halittarsu za su ga shi ne ya halicce su daga ƙasa ta hanyar halittar babansu Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ƙasa, suna kuma cin abin da ƙasar ta tsiro da shi. Bayan mutuwarsu kuma zai mayar da su cikin ƙasar ne har sai lokacin tashin alƙiyama ya yi sai ya fito da su don yi musu hisabi. Don haka Allah shi ne wanda rayuwa da mutuwa suke hannunsa shi ne kuma mai iya tayar da matattu bayan mutuwa. Allah kuma shi ne wanda ya halitta wa mutane ƙasa a shimfiɗe daidai da yadda za su ji daɗin rayuwa a kanta, ya kuma hore musu bin manya-manyan hanyoyinta masu yalwa don neman arziki na halal.
قَالَ نُوحٞ رَّبِّ إِنَّهُمۡ عَصَوۡنِي وَٱتَّبَعُواْ مَن لَّمۡ يَزِدۡهُ مَالُهُۥ وَوَلَدُهُۥٓ إِلَّا خَسَارٗا
Open ayah 71:21Nuhu ya ce, “Ya Ubangijina, lalle su sun saɓa mini, sun kuma bi duk wanda dukiyarsa da ‘ya’yansa ba su ƙara masa komai ba sai asara.
وَمَكَرُواْ مَكۡرٗا كُبَّارٗا
Open ayah 71:22“Suka kuma shirya makirci babba.
وَقَالُواْ لَا تَذَرُنَّ ءَالِهَتَكُمۡ وَلَا تَذَرُنَّ وَدّٗا وَلَا سُوَاعٗا وَلَا يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسۡرٗا
Open ayah 71:23“Suka kuma ce: ‘Kada ku bar abubuwan bautarku, kuma lalle kada ku bar Waddu da Suwa’u da Yagusu da Ya’uƙu da Nasaru .’
وَقَدۡ أَضَلُّواْ كَثِيرٗاۖ وَلَا تَزِدِ ٱلظَّٰلِمِينَ إِلَّا ضَلَٰلٗا
Open ayah 71:24“Haƙiƙa kuwa sun ɓatar da adadi mai yawa; kar kuma Ka ƙari kafirai da komai sai ɓata.”
مِّمَّا خَطِيٓـَٰٔتِهِمۡ أُغۡرِقُواْ فَأُدۡخِلُواْ نَارٗا فَلَمۡ يَجِدُواْ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ أَنصَارٗا
Open ayah 71:25Saboda saɓonsu ne aka nutsar da su, sai aka shigar da su wuta, don haka, ba su sami wasu mataimaka ba Allah ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya koka wa Ubangijinsa da cewa, wa’azin da ya daɗe shekaru aru-aru yana yi wa mutanensa bai yi musu wani amfani ba, domin sun saɓa masa sun bijire wa da’awarsa, sun bi wasu manyan mutane masu dukiya waɗanda kuma dukiyarsu da ‘ya’yansu ba su ƙara musu komai ba sai taɓewa da asara, domin kuwa ba abin da suka sa a gaba sai shirya mummunan makirci da yaɗa shirka da saɓon Allah da zuga wawayensu kan kada su kuskura su watsar da bautar gumakansu waɗanda suka gada iyaye da kakanni, musamman gumakan Waddu da Suwa’u da Yagusu da Ya’uƙu da Nasru. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, da irin waɗannan kalaman nasu suka ɓatar da yawancin mutane. Don haka Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roƙi Allah cewa, muddin dai mutanensa sun zalunci kawunansu sun zaɓi kafewa a kan kafirci da saɓon Allah, to kada ya ƙara musu wani abu sai ɓata da dulmiya cikin kafirci, watau wannan shi ne abin da suka zaɓa wa kansu da kansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana uƙubarsu ta duniya da ta lahira, da cewa, saboda miyagun laifukansu na kafirci da bijire wa kiran da Manzonsa Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake yi musu, wannan ya sa ya nutsar da su a ruwan Ɗufana tun a nan duniya, suna hallaka kuwa sai ya shigar da su wata azabar ta wuta ba tare da wani jinkiri ba, don haka ba su samu wasu mataimaka waɗanda ba Allah ba da suka iya kuɓutar da su daga nutsewa a ruwa da shiga wuta bayan mutuwarsu.
وَقَالَ نُوحٞ رَّبِّ لَا تَذَرۡ عَلَى ٱلۡأَرۡضِ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ دَيَّارًا
Open ayah 71:26Nuhu ya ce: “Ya Ubangijina, kada Ka bar wani mutum ɗaya daga kafirai a bayan ƙasa.
إِنَّكَ إِن تَذَرۡهُمۡ يُضِلُّواْ عِبَادَكَ وَلَا يَلِدُوٓاْ إِلَّا فَاجِرٗا كَفَّارٗا
Open ayah 71:27“Lalle idan har Ka bar su, to za su ɓatar da bayinka, kuma ba za su haifi kowa ba sai fajiri mai tsananin kafirci.
رَّبِّ ٱغۡفِرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيَّ وَلِمَن دَخَلَ بَيۡتِيَ مُؤۡمِنٗا وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۖ وَلَا تَزِدِ ٱلظَّٰلِمِينَ إِلَّا تَبَارَۢا
Open ayah 71:28“Ya Ubangijina, Ka gafarta min ni da mahaifana da kuma waɗanda suka shiga gidana suna muminai, da kuma (sauran) muminai maza da mata, kada kuma Ka ƙari kafirai da komai sai hallaka.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roƙe shi da ya hallaka mutanensa bayan ya yi masa wahayi cewa, babu sauran waɗanda za su yi imani da shi bayan ‘yan kaɗan da suka riga suka yi imani, don haka sai ya kira Ubangijinsa ya roƙe shi cewa, kada ya bar wani kafiri ɗaya yana karakaina a bayan ƙasa, domin ya tabbata cewa, idan har Allah ya ƙyale su, to za su ci gaba da ɓatar da bayinsa muminai, kuma nan gaba ba za su ƙara haihuwar wani wanda zai bi Allah ba sai dai su haifi fajiri wanda zai kangare masa, mai tsananin kafirci wanda ba zai gode wa ni’imominsa ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karɓi addu’ar Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya hallakar da mutanensa ta hanyar dulmiyar da su cikin ruwan Ɗufana gaba ɗayansu, ya tserar da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da waɗanda suka yi imani da shi. Sai kuma a ayar ƙarshe Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ɗaga hannu ya roƙi Ubangijinsa cewa, ya gafarta masa zunubansa, ya kuma gafarta wa mahaifansa biyu da duk wani mumini da ya shiga gidansa, watau ya lizimce shi yana mai imani da shi, ya kuma gafarta wa muminai mazansu da matansu, su kuma azzalumai waɗanda suka cutar da kansu da kafirci da saɓon Allah kada ya ƙara musu komai sai hallaka da asara.