الجن
Al-Jinn
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
قُلۡ أُوحِيَ إِلَيَّ أَنَّهُ ٱسۡتَمَعَ نَفَرٞ مِّنَ ٱلۡجِنِّ فَقَالُوٓاْ إِنَّا سَمِعۡنَا قُرۡءَانًا عَجَبٗا
Open ayah 72:1Ka ce: “An yiwo min wahayi na cewa, wata jama’a ta aljannu sun saurari (karatun Alƙur’ani), sai suka ce: “Lalle mu mun ji Alƙur’ani mai ban mamaki.
يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلرُّشۡدِ فَـَٔامَنَّا بِهِۦۖ وَلَن نُّشۡرِكَ بِرَبِّنَآ أَحَدٗا
Open ayah 72:2“Yana shiryarwa zuwa ga daidai, saboda haka muka yi imani da shi; ba kuwa za mu haɗa wani da Ubangijinmu ba har abada.
وَأَنَّهُۥ تَعَٰلَىٰ جَدُّ رَبِّنَا مَا ٱتَّخَذَ صَٰحِبَةٗ وَلَا وَلَدٗا
Open ayah 72:3“Kuma lalle yadda lamarin yake, girman Ubangijinmu ya ɗaukaka, bai riƙi wata mata ko wani ɗa ba.
وَأَنَّهُۥ كَانَ يَقُولُ سَفِيهُنَا عَلَى ٱللَّهِ شَطَطٗا
Open ayah 72:4“Kuma lalle yadda lamarin yake, wani wawa daga cikinmu ya kasance yana faɗar mummunar ƙarya game da Allah.
وَأَنَّا ظَنَنَّآ أَن لَّن تَقُولَ ٱلۡإِنسُ وَٱلۡجِنُّ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا
Open ayah 72:5“Lalle kuma mun yi tsammanin mutum da aljan ba za su taɓa faɗar ƙarya game da Allah ba.
وَأَنَّهُۥ كَانَ رِجَالٞ مِّنَ ٱلۡإِنسِ يَعُوذُونَ بِرِجَالٖ مِّنَ ٱلۡجِنِّ فَزَادُوهُمۡ رَهَقٗا
Open ayah 72:6“Kuma lalle yadda lamarin yake, wasu mazaje daga mutane sun kasance suna neman tsari daga wasu mazaje na aljannu, saboda haka suka ƙara musu girman kai.
وَأَنَّهُمۡ ظَنُّواْ كَمَا ظَنَنتُمۡ أَن لَّن يَبۡعَثَ ٱللَّهُ أَحَدٗا
Open ayah 72:7“Kuma lalle su sun yi tsammanin-kamar yadda kuka yi tsammani-cewar Allah ba zai tashi kowa ba har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Manzonsa (ﷺ) ya faɗa wa al’ummarsa cewa, an yiwo masa wahayi game da wasu jama’a na aljannu waɗanda suka saurari karatunsa na Alƙur’ani mai girma a wani wuri da ake kira Baɗnu Nakhla, lokacin da yake yi wa sahabbansa sallar Asuba. Bayan sun gama sauraro sai suka koma wajen jama’arsu ta aljannu suna gaya musu cewa, lalle sun saurari wani abin karatu mai ban al’ajabi, yadda yake cike da fasaha da hikima. Yana kuma shiryarwa zuwa ga ingantacciyar aƙida da kyakkyawan aiki da kyawawan maganganu, don haka su sun yi imani da shi, kuma daga lokacin ba za su ƙara haɗa Allah da wani ba wajen bautarsu. Sun kuma yi imani da cewa, girman Ubangijinsu ya ɗaukaka, bai kuma riƙi wata mata ko ɗa ba, kamar yadda mushirikansu na aljannu da na mutane suke riyawa. Suka kuma tabbatar wa da jama\'arsu cewa, maganar da wawan cikinsu yake yi, watau Iblisu da ire-irensa na yi wa Allah ƙarya da jingina masa mata da ɗa mummunar ƙarya ce suke ƙirƙira masa. Suka kuma bayyana cewa, da farko sun zaci mushirikan mutane da na aljannu ba za su taɓa yi wa Allah ƙarya ba ballantana har su riƙa cewa yana da mata da ɗa, wannan ne ya sa har suka ɗauki maganarsu a matsayin gaskiya, sai suka bi su ido-rufe. Sannan suka bayyana wata mummunar aƙida ta wasu mutane waɗanda, a lokacin jahiliyya idan sun yi tafiya sun sauka a wani wuri mai ban tsoro, kamar wani kwari, sukan nemi tsarin wasu mazajen aljannu, watau ɗayansu yakan ce, yana neman shugaban wannan kwarin ya kare shi daga sharrin wawayen jama’arsa. Wannan lamari ya janyo mazajen mutane suka ƙara firgita da tsorata daga mazajen aljannu. Suka kuma tabbatar wa da jama\'arsu cewa, sun gano cewa, kamar yadda su aljannu suka yi zaton babu wanda Allah zai tashe shi domin yi masa hisabi, hakanan su ma mutane suka yi wannan zaton. Watau wannan mummunan zato nasu ne ya sanya su yin shirka da Allah da ɗagawa a bayan ƙasa.
وَأَنَّا لَمَسۡنَا ٱلسَّمَآءَ فَوَجَدۡنَٰهَا مُلِئَتۡ حَرَسٗا شَدِيدٗا وَشُهُبٗا
Open ayah 72:8“Kuma lalle mu mun nemi hawa sama, sai muka same ta an cika ta da matsanancin tsaro da taurari (masu jifa da garwashi).
وَأَنَّا كُنَّا نَقۡعُدُ مِنۡهَا مَقَٰعِدَ لِلسَّمۡعِۖ فَمَن يَسۡتَمِعِ ٱلۡأٓنَ يَجِدۡ لَهُۥ شِهَابٗا رَّصَدٗا
Open ayah 72:9“Lalle kuma mun zamanto a da muna hawa wasu wurare nata don yin sauraro; to duk wanda ya nemi yin sauraro a yanzu zai sama wa kansa wani tauraro wanda aka tanada (don jifan sa).
وَأَنَّا لَا نَدۡرِيٓ أَشَرٌّ أُرِيدَ بِمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ أَرَادَ بِهِمۡ رَبُّهُمۡ رَشَدٗا
Open ayah 72:10“Kuma lalle mu ba mu sani ba, shin wani sharri ake nufi da waɗanda ke ƙasa, ko kuwa Ubangijinsu Yana nufin su da shiriya ne? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba da labarin irin maganganun da aljannu suka gaya wa jama\'arsu bayan sun saurari karatun Alƙur’ani daga bakin Manzon Allah (ﷺ), inda suka shaida wa ‘yan’uwansu aljannu cewa, lalle sun nemi su hau sama don su sato labarai kamar yadda suka saba yi a can baya, amma sai suka same ta an cika ta maƙil da mala’iku ƙarfafa masu tsaron ta daga duk wani aljani mai ƙoƙarin satar bayanai daga sama, an kuma cika ta da taurari masu jifa da harasan wuta, domin ƙona duk wanda ya matso kusa da inda zai yi satar sauraro. Aljannu suka ci gaba da ba da labarin cewa, su a da can suna samun wuraren zama a sama don sauraron tattaunawar mala’iku su saci bayanai daga gare su sai su isar da su ga bokaye a bayan ƙasa, to yanzu abu ya canja, duk wani wanda ya yi yunƙurin yiwo sauraro daga cikin aljannu, to zai samar wa kansa wani harshen wuta wanda aka tanada domin jifan sa da shi, yana matsawa kusa kuwa za a sakar masa shi ya ƙona shi murus har lahira. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Annabi (ﷺ) yana zaune a tsakiyar wasu sahabbansa mutanen Madina, sai aka yi jifa da wani tauraro sai ya yi haske, sai Manzon Allah (ﷺ) ya tambayi waɗannan sahabban cewa: “Idan irin wannan ya faru a zamanin jahiliyya me kuka kasance kuna cewa?” Sai suka ce: “Mun kasance muna cewa, wani babban mutum zai mutu, za kuma a haifi wani babban mutum.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce musu: “Ba haka ba ne, ba a jefo tauraro don mutuwar wani ko don rayuwarsa, sai dai yayin da Ubangijinmu (Mai tsarki da daukaka) ya hukunta faruwar wani abu, sai mala’iku masu ɗauke da Al’arshi su yi tasbihi, sai kuma mala’ikun da suke sama mai biye da su su ma su yi tasbihi, har sai tasbihin nan nasu ya iso wannan samaniyar, sannan sai mala’ikun da suke sama ta bakwai su tambayi masu ɗauke da Al’arshi labarin abin da Ubangijinsu ya faɗa. Sai su faɗa musu, sannan mala’ikun kowace sama su tambayi na sama da su, har sai labari ya iso wannan samaniyar (ta kusa) sai aljannu su wafci labarin, sai a jefe su da tauraro mai garwashi. Duk kuma abin da suka zo da shi yadda yake gaskiya ne, sai dai suna ƙare-ƙare a cikinsa.” [Ahmad #1882 da Tirmizi #3503]. Sai aljannu suka ci gaba da bayanin cewa, su ba su san dalilin da ya kawo wannan matakin tsaro mai tsanani haka ba; shin ana nufin wani sharri ne ga waɗanda suke rayuwa a bayan ƙasa a duniya, ko kuma dai Allah ya yi nufin su da wani alheri ne? Domin ga shi dai labarai sun daina zuwa daga sama, watau dai babu makawa akwai ɗaya daga cikin abubuwan nan guda biyu da ya faru, amma su ba su san wane ne dalilin ba.
وَأَنَّا مِنَّا ٱلصَّٰلِحُونَ وَمِنَّا دُونَ ذَٰلِكَۖ كُنَّا طَرَآئِقَ قِدَدٗا
Open ayah 72:11“Lalle daga cikinmu akwai salihai, daga cikinmu kuma akwai waɗanda ba haka suke ba; mun zamanto hanyoyi daban-daban.
وَأَنَّا ظَنَنَّآ أَن لَّن نُّعۡجِزَ ٱللَّهَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَن نُّعۡجِزَهُۥ هَرَبٗا
Open ayah 72:12“Kuma lalle mu mun tabbatar cewa ba za mu gagari Allah ba a bayan ƙasa, ba kuma za mu gagare Shi ba a guje.
وَأَنَّا لَمَّا سَمِعۡنَا ٱلۡهُدَىٰٓ ءَامَنَّا بِهِۦۖ فَمَن يُؤۡمِنۢ بِرَبِّهِۦ فَلَا يَخَافُ بَخۡسٗا وَلَا رَهَقٗا
Open ayah 72:13“Lalle kuma mu lokacin da muka ji Alƙur’ani, sai muka yi imani da shi, to duk wanda zai yi imani da Ubangijinsa, to zai tsoron ƙwara ko zalunci ba.
وَأَنَّا مِنَّا ٱلۡمُسۡلِمُونَ وَمِنَّا ٱلۡقَٰسِطُونَۖ فَمَنۡ أَسۡلَمَ فَأُوْلَٰٓئِكَ تَحَرَّوۡاْ رَشَدٗا
Open ayah 72:14“Kuma lalle mu a cikinmu akwai Musulmi, a cikinmu kuma akwai karkatattu; saboda haka duk wanda ya musulunta, to waɗannan sun nufi hanyar shiriya.
وَأَمَّا ٱلۡقَٰسِطُونَ فَكَانُواْ لِجَهَنَّمَ حَطَبٗا
Open ayah 72:15“Amma kuma karkatattu, to sun kasance makamashi ne ga (wutar) Jahannama.”
وَأَلَّوِ ٱسۡتَقَٰمُواْ عَلَى ٱلطَّرِيقَةِ لَأَسۡقَيۡنَٰهُم مَّآءً غَدَقٗا
Open ayah 72:16Da kuwa (mutan Makka) sun daidaita a kan (Musulunci), to lalle da Mun shayar da su ruwa mai yawa.
لِّنَفۡتِنَهُمۡ فِيهِۚ وَمَن يُعۡرِضۡ عَن ذِكۡرِ رَبِّهِۦ يَسۡلُكۡهُ عَذَابٗا صَعَدٗا
Open ayah 72:17Don Mu jarrabe su game da shi. Duk kuwa wanda ya kau da kai daga ambaton Ubangijinsa to zai saka shi cikin azaba mai wahala. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba da labarin maganganun aljannu ga jama’arsu, inda suka ci gaba da sanar da su cewa, lalle su aljannu a cikinsu akwai salihai masu tsoron Allah akwai kuma kafirai da fasiƙai a cikinsu, sun zamanto ƙungiyoyi daban-daban masu mabambanta ra’ayoyi da soye-soyen zuciya. Suka kuma tabbatar da cewa, su sun san ba za su gagari Allah a bayan ƙasa ba idan ya so kama su da wani al’amari, hakanan babu inda za su iya guduwa su tsere masa, domin ikonsa a kewaye yake da su ta kowane ɓari. Sai kuma suka bayyana cewa, su tun lokacin da suka ji karatun Alƙur’ani suka kuma ji yana kiran su zuwa ga shiriya sai suka yi imani da shi, kuma sun tabbata duk wanda ya yi imani da Ubangijinsa Allah, ba zai ji tsoron a tauye masa ladansa ba kuma ba zai yi fargabar za a ƙara masa wani laifin da bai aikata ba a kan laifukansa. Watau dai sun sakankance da adalcin Ubangiji da alherin da yake kiran su zuwa gare shi ba tare da wata cutuwa ba. Sai suka sake bayyana kasha-kashensu da sakamakon kowane kashi, inda suka tabbatar da cewa, a cikinsu akwai Musulmai masu bin Allah sau-da-ƙafa akwai kuma karkatattu waɗanda suka saki hanyar Allah da gaskiya, don haka duk wanda ya musulunta ya miƙa wuya ga Allah (Mai tsarki da daukaka), to waɗannan su ne suka nufi hanyar shiriya da gaskiya, watau sun kama hanyar zuwa Aljanna. Amma karkatattu masu sakin hanyar gaskiya, to waɗannan su ne za su kasance makamashin wutar Jahannama da za a riƙa rura ta da su da ire-irensu daga cikin mutane. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi wa Manzonsa (() wahayi cewa, da mutane da aljannu za su daidaita a kan hanyar Musulunci su ƙanƙame wa koyarwarsa, to da zai shayar da su ruwa mai yawa, ya ƙara musu ni’imomi masu ɗimbin yawa, domin ya jarrabe su da su, don bayyana waɗanda za su gode masa da waɗanda za su yi masa butulci daga cikinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tsoratar da su cewa, duk wanda ya bijire wa Alƙur’ani da wa’azuzzukan da ke cikinsa, to ya sani Ubangijinsa Allah zai shigar da shi wata azaba mai wahalar da ba zai iya jure mata ba.
وَأَنَّ ٱلۡمَسَٰجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدۡعُواْ مَعَ ٱللَّهِ أَحَدٗا
Open ayah 72:18Kuma lalle masallatai na Allah ne, saboda haka kada ku bauta wa wani tare da Allah.
وَأَنَّهُۥ لَمَّا قَامَ عَبۡدُ ٱللَّهِ يَدۡعُوهُ كَادُواْ يَكُونُونَ عَلَيۡهِ لِبَدٗا
Open ayah 72:19Kuma lalle yadda lamarin yake, yayin da Bawan Allah (Annabi Muhammadu) ya tashi yana bauta masa, sai (aljannu) suka kusa su zamo wasu kan wasu don cincirindo a kansa.
قُلۡ إِنَّمَآ أَدۡعُواْ رَبِّي وَلَآ أُشۡرِكُ بِهِۦٓ أَحَدٗا
Open ayah 72:20Ka ce: “Lalle ina bauta wa Ubangijina ne kawai, ba kuwa na tara wani da Shi.”
قُلۡ إِنِّي لَآ أَمۡلِكُ لَكُمۡ ضَرّٗا وَلَا رَشَدٗا
Open ayah 72:21Kuma ka ce: “Lalle ni ban mallaki kare muku wata cuta ko janyo muku wani alhairi ba.”
قُلۡ إِنِّي لَن يُجِيرَنِي مِنَ ٱللَّهِ أَحَدٞ وَلَنۡ أَجِدَ مِن دُونِهِۦ مُلۡتَحَدًا
Open ayah 72:22Ka ce: “Lalle ni ba wani mai kare ni daga (azabar) Allah, kuma ba zan taɓa samun wata mafaka in ba tasa ba.
إِلَّا بَلَٰغٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِسَٰلَٰتِهِۦۚ وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ لَهُۥ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًا
Open ayah 72:23“Sai dai isar da aike daga Allah da kuma saƙwanninsa. Duk kuwa waɗanda suka saɓa wa Allah da Manzonsa, to lalle suna da wutar Jahannama, suna madawwama a cikinta har abada.”
حَتَّىٰٓ إِذَا رَأَوۡاْ مَا يُوعَدُونَ فَسَيَعۡلَمُونَ مَنۡ أَضۡعَفُ نَاصِرٗا وَأَقَلُّ عَدَدٗا
Open ayah 72:24Har yayin da (kafirai) suka ga abin da ake yi musu alƙawari da shi, to ba da daɗewa ba za su san wa ya fi raunanan mataimaka da kuma ƙanƙantar jama’a. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, daga cikin abubuwan da ya yi wa Manzonsa (ﷺ) wahayi da su akwai cewa, lalle masallatai nasa ne, domin bautar sa shi kaɗai, don haka kada su sake kiran wasu da sunan bauta a cikinsu har abada, domin idan sun yi haka sun zama kamar Yahudu da Nasara a wuraren bautarsu inda suke bautar wasu annabawa da salihai tare da Allah a cikinsu. An karɓo daga Ummu Habiba da Ummu Salama ((), sun ba wa Manzon Allah (ﷺ) labarin wata coci da suka gano a Habasha mai cike da hotuna. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Waɗannan mutane sun kasance idan mutumin kirki ya mutu a cikinsu sai su gina masallaci a kan ƙabarinsa, su zana irin waɗannan hotunan. Waɗannan su ne ashararan halitta a wurin Allah Ta’ala a ranar alƙiyama.” [Bukhari #427 da Muslim #528]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lokacin da bawansa Annabi Muhammadu (ﷺ) yake tsaye a Baɗnu Nakhla yana bauta masa aljannu sun kusa su zamo wasu kan wasu a wurinsa saboda tsananin cinkoso yayin da suke sauraron karatun Alƙur’ani da yake yi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya bayyana wa mushirikai tsantsar abin da yake kiran su a kansa, da cewa, lalle shi Ubangijinsa kaɗai yake bauta wa, kuma ba zai yarda ya haɗa wani da bautar sa ba kowane ne. Ya kuma sanar da su cewa, shi ba zai iya kare su daga wata cuta da Allah ya ƙaddara musu ba, ba kuma zai iya janyo musu wani amfani da Allah ya hana musu ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya bayyana musu cewa, shi a karan-kansa ba mai iya kare kansa ba ne, ballantana ya kare wani daga azabar Allah, domin babu mai iya tserar da shi daga kamun Allah idan ya saɓa masa ya ƙi bin umarninsa, ba kuma zai taɓa samun wata mafaka in ba tasa ba. Ya sanar da su cewa, abin da kawai ya mallaka shi ne ya isar musu da saƙon da Allah ya umarce shi ya isar musu da manzancin da ya aiko shi da shi zuwa gare su, don hujjar Allah ta tsaya a kansu da sauran mutane. Don haka duk wanda ya saɓa wa Allah da Manzonsa, to makomarsa ita ce wutar Jahannama da za a jefa shi a cikinta ya dawwama ba zai taɓa fitowa daga cikinta ba har abada. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Manzonsa (ﷺ) cewa, duk da wannan gargaɗi da yake yi wa kafirai, ba fa za su bar kafircinsu ba har sai yayin da a ranar alƙiyama suka ga dahir, watau azabar da ake yi musu alƙawarin zuwanta a duniya, to a lokacin ne za su san wane ne ya fi raunanan mataimaka ya kuma fi ƙarancin jama’a masu kawo masa ɗauki.
قُلۡ إِنۡ أَدۡرِيٓ أَقَرِيبٞ مَّا تُوعَدُونَ أَمۡ يَجۡعَلُ لَهُۥ رَبِّيٓ أَمَدًا
Open ayah 72:25Ka ce: “Ni ban sani ba, shin kusa yake abin da ake yi muku alƙawarinsa ko kuwa Ubangijina zai sanya masa zamani mai tsawo?”
عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ فَلَا يُظۡهِرُ عَلَىٰ غَيۡبِهِۦٓ أَحَدًا
Open ayah 72:26“(Shi ne) Masanin gaibu, sannan ba Ya bayyana gaibunsa ga wani.
إِلَّا مَنِ ٱرۡتَضَىٰ مِن رَّسُولٖ فَإِنَّهُۥ يَسۡلُكُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَمِنۡ خَلۡفِهِۦ رَصَدٗا
Open ayah 72:27“Sai manzo da ya yarda da shi, shi kuma lalle Yakan sanya masa tsaro ta gabansa da ta bayansa.
لِّيَعۡلَمَ أَن قَدۡ أَبۡلَغُواْ رِسَٰلَٰتِ رَبِّهِمۡ وَأَحَاطَ بِمَا لَدَيۡهِمۡ وَأَحۡصَىٰ كُلَّ شَيۡءٍ عَدَدَۢا
Open ayah 72:28“Don Ya bayyanar da cewa, haƙiƙa sun isar da saƙwannin Ubangijinsu, Ya kuma kewaye da (sanin) abin da yake tare da su, Ya kuma ƙididdige adadin kowane abu.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya amsa wa kafirai tambayar izgili da suke damun sa da ita na cewa, sai ya faɗa musu yaushe ne alƙiyama za ta zo? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya bayyana musu cewa, shi ba shi da masaniya ga abin da ake yi musu alƙawarin zuwansa na alƙiyama ko na azaba, kusa yake ko kuma Ubangijinsa zai sanya masa wani lokaci mai tsawo da ba wanda ya san shi sai shi (Mai tsarki da daukaka)? Domin shi ne masanin gaibu gaba ɗaya, kuma ba ya bayyana wa wani mahaluƙi gaibinsa, shi kaɗai ne ya keɓanta da saninsa, sai dai kuma yakan sanar da wani manzo da ya zaɓa abin da ya ga dama ya sanar da shi gwargwadon hikimarsa, domin ya zamanto mu’ujiza a gare shi. Yana kuma aiko da mala’iku ga wannan Manzon ta gabansa da bayansa suna tsaron sa don kada shaiɗanu su sami kusantar sa har su ƙara wani abu ko su rage daga cikin wahayin da yake yi masa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi haka ne don ya tabbatar da cewa, manzanninsa sun isar da saƙwannin Ubangijinsu ba daɗi ba ragi. Allah kuwa ya kewaye da sanin duk abin da yake tare da su ya kuma ƙididdige adadin komai, domin babu abin da yake ɓuya gare shi.