المزمل
Al-Muzzammil
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُزَّمِّلُ
Open ayah 73:1Ya kai wannan mai lulluɓa!
قُمِ ٱلَّيۡلَ إِلَّا قَلِيلٗا
Open ayah 73:2Ka yi tsaiwar dare sai ɗan kaɗan (daga cikinsa).
نِّصۡفَهُۥٓ أَوِ ٱنقُصۡ مِنۡهُ قَلِيلًا
Open ayah 73:3Rabinsa ko kuma ka rage kaɗan daga gare shi.
أَوۡ زِدۡ عَلَيۡهِ وَرَتِّلِ ٱلۡقُرۡءَانَ تَرۡتِيلًا
Open ayah 73:4Ko ka ƙara a kansa, ka kuma karanta Alƙur’ani daki-daki.
إِنَّا سَنُلۡقِي عَلَيۡكَ قَوۡلٗا ثَقِيلًا
Open ayah 73:5Lalle Mu da sannu za Mu saukar maka da zance mai nauyi.
إِنَّ نَاشِئَةَ ٱلَّيۡلِ هِيَ أَشَدُّ وَطۡـٔٗا وَأَقۡوَمُ قِيلًا
Open ayah 73:6Lalle tsayuwar dare ita ta fi tsananin dacewa (game da nutsuwa), ta kuma fi daidaitar magana.
إِنَّ لَكَ فِي ٱلنَّهَارِ سَبۡحٗا طَوِيلٗا
Open ayah 73:7Lalle da rana kana da harkoki masu yawa.
وَٱذۡكُرِ ٱسۡمَ رَبِّكَ وَتَبَتَّلۡ إِلَيۡهِ تَبۡتِيلٗا
Open ayah 73:8Ka kuma ambaci sunan Ubangijinka kuma ka yanke alaƙarka da komai don bautarsa.
رَّبُّ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱتَّخِذۡهُ وَكِيلٗا
Open ayah 73:9(Shi ne) Ubangijin mahudar rana da mafaɗar rana, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, saboda haka ka riƙe Shi Abin dogara. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da kiran Manzonsa (ﷺ) da sunan wanda yake lulluɓe da tufafinsa, ya umarce shi ya tashi cikin dare ya yi salla kada ya rage komai daga cikin darensa sai ɗan kaɗan. Ko kuma ya sallaci rabin daren idan yana so, ko ya sallaci ƙasa da rabi har ya koma sulusi, watau kashi ɗaya bisa uku, ko kuma idan ya ga dama ya ƙara har ya kai kashi biyu bisa uku, watau dai gwargwadon buƙatarsa da ƙoƙarinsa. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda), ta ce: Annabi (ﷺ) ya zamanto baccinsa kaɗan ne bayan da aka saukar masa faɗar Allah: “Ka raya dare sai ɗan kaɗan daga cikinsa.” [Nasa’i, Al-Kubra #11564 da Abu Ya’ala #4939]. Sannan Allah ya umarce shi da ya karanta Alƙur’ani cikin nutsuwa daki-daki, don ya sami tuntuntuni a kansa yadda ya kamata. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “A ranar alƙiyama za a ce wa makarancin Alƙur’ani: “Karanta shi ka ƙara ɗaukaka, karanta shi a natse daki-daki kamar yadda kake karanta shi a natse daki-daki a duniya, domin matsayinka yana kan ƙarshen ayar da za ka karanta.” [Ahmad #6799 da Abu Dawud #1464 da Tirmizi #3141, 3142]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi wa Manzonsa (ﷺ) wannan umarni ne, don ya shirya sosai, domin lalle zai sauko masa da zance mai nauyi, watau Alƙur’ani da zai yiwo masa wahayinsa. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Al-Harisu ɗan Hisham ya tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa: “Yaya wahayi yake zuwa maka?” Sai ya ce: “Wani lokaci yana zuwa mini kamar ƙarar ƙaraurawa, shi ne mafi tsanani a gare ni har zuwa lokacin da zai gushe mini bayan na kiyaye abin da Mala’ika Jibrilu ya faɗa min. A wani lokaci kuwa, Mala’ika Jibrilu yakan fito mini a surar mutum ya yi magana da ni, sai in kiyaye duk abin da ya faɗa mini.” A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Tabbas na gan shi ana yi masa wahayi a lokaci mai tsananin sanyi, amma ana gama yi masa wahayi sai ka ga goshinsa yana tsattsafo da gumi. [Bukhari #2]. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Annabi (ﷺ) ya kasance idan ana yi masa wahayi yana kan taguwarsa, takan yi ƙasa da ƙirjinta har ta kasa motsawa.” Sai ta karanta wannan ayar. [Al-Hakim #3865 da Musnad #24868]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) hikimar sallar dare da cewa, ta fi dacewa da nutsuwar zuciya da taimakawa wajen fahimtar zance daidai, domin da zuciya da harshe za su haɗu a kan abin da mutum yake karantawa, sai ya fi saurin fahimtar sa, domin rashin samun abin da zai ɗauke masa hankali a lokacin. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, da rana kuwa yana da ayyuka masu yawa da za su hana shi shagaltuwa da sallolin nafila, don haka sai ya ribaci dare ya yi ta salla a cikinsa. Ya kuma umarce shi da ambaton sa da kowane irin nau’in zikiri, kuma ya watsar da komai ya duƙufa wajen bauta masa da tsantsanta bautarsa gare shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, shi ne Ubangijin mahudar rana da mafaɗarta, kuma babu wani abin bauta da gaskiya sai shi, don haka ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya riƙe shi abin dogaro a cikin dukkan al’amuransa na rayuwa da na addini.
وَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَٱهۡجُرۡهُمۡ هَجۡرٗا جَمِيلٗا
Open ayah 73:10Kuma ka yi haƙuri a kan abin da suke faɗa, kuma ka ƙaurace musu kyakkyawar ƙauracewa.
وَذَرۡنِي وَٱلۡمُكَذِّبِينَ أُوْلِي ٱلنَّعۡمَةِ وَمَهِّلۡهُمۡ قَلِيلًا
Open ayah 73:11Ka kuma bar ni da masu ƙaryatawa ma’abota ni’ima, ka kuma ɗan saurara musu.
إِنَّ لَدَيۡنَآ أَنكَالٗا وَجَحِيمٗا
Open ayah 73:12Lalle a wurinmu akwai maruruwa da kuma (wutar) Jahimu.
وَطَعَامٗا ذَا غُصَّةٖ وَعَذَابًا أَلِيمٗا
Open ayah 73:13Da kuma abinci mai shaƙewa da kuma azaba mai raɗaɗi.
يَوۡمَ تَرۡجُفُ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ وَكَانَتِ ٱلۡجِبَالُ كَثِيبٗا مَّهِيلًا
Open ayah 73:14A ranar da ƙasa da duwatsu za su girgiza, duwatsun kuma su kasance rairayi tilis.
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ رَسُولٗا شَٰهِدًا عَلَيۡكُمۡ كَمَآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ رَسُولٗا
Open ayah 73:15Lalle Mu Muka aiko muku da Manzo yana mai shaida a kanku kamar yadda Muka aiko wani manzo zuwa ga Fir’auna.
فَعَصَىٰ فِرۡعَوۡنُ ٱلرَّسُولَ فَأَخَذۡنَٰهُ أَخۡذٗا وَبِيلٗا
Open ayah 73:16Sai Fir’auna ya saɓa wa Manzon, sai Muka kama shi kamu mai tsanani.
فَكَيۡفَ تَتَّقُونَ إِن كَفَرۡتُمۡ يَوۡمٗا يَجۡعَلُ ٱلۡوِلۡدَٰنَ شِيبًا
Open ayah 73:17Ta yaya idan kuka kafirta za ku iya kare kanku daga ranar da za ta mayar da yara ƙanana su zama masu furfura?
ٱلسَّمَآءُ مُنفَطِرُۢ بِهِۦۚ كَانَ وَعۡدُهُۥ مَفۡعُولًا
Open ayah 73:18Sama za ta kece saboda ita (ranar). Alƙawarinsa ya kasance abin aikatawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya yi haƙuri game da maganganun izgili da cin fuska da yake ji daga mushirikai masu ƙaryata shi, ya ci gaba da da’awarsa zuwa ga Allah, kada ya daka ta waɗanda suke so su hana ruwansa gudu, ya kuma ƙaurace musu kyakkyawar ƙauracewa wadda babu cutarwa a cikinta. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da kada ya damu da al’amarin masu ƙaryata shi, ‘yan tamore kawai a rayuwar duniya, ya bar shi ya ga yadda zai yi da su, ya kuma saurara musu kaɗan har lokacin zuwan ajalinsu inda ido zai raina fata. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da kafirai tsananin azabarsa ta lahira, ya tabbatar musu cewa, ya yi tanadin maruruwa masu nauyi da wuta mai tsananin ruruwa. Abincinsu ma irin mai shaƙe maƙoshi ne saboda tsananin ɗacinsa da warinsa, ga kuma wuta mai tsananin zafi da ƙuna. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan azaba za ta sami waɗannan masu ƙaryatawar ne a ranar da ƙasa da duwatsu za su girgiza, duwatsu kuma su zama rairayi tilis, saboda tsananin tsoro na wannan ranar. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da waɗannan ‘yan tamore da azabar duniya irin wadda ta auka wa kafirai irinsu a baya da cewa, ya aiko musu da manzo don ya zama mai ba da shaida a kan ayyukansu a ranar alƙiyama kamar yadda ya aika wa Fir’auna Manzo shi ne Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), to amma sai Fir’auna ya saɓa wa wannan Manzon ya ƙaryata shi, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa matsanancin kamu, watau ya nutsar da shi har da jama’arsa cikin kogin Maliya, suka hallaka baki ɗaya; azabar lahira kuma tana nan tana jiran su. Don haka su ma mutanen Makka su guji saɓa wa Manzonsu, in ba haka ba, kuma irin abin da ya sami Fir’auna da mutanensa ya same su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tsoratar da su azabar lahira yana tsawatar musu da cewa, ta yaya za su iya kare kansu daga azabar wata rana mai tsawo da tsananin gaske, mai mayar da yara ƙanana su zama masu furfura, saboda tsananin firgicin da ke cikinta da ababen ban tsoro da ta ƙunsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, saboda tashin hankalin da ke cikin wannan rana sama za ta tsattsage, duk abubuwan da suke cikinta su tarwatse. Wannan kuma alƙawarin Allah ne, alƙawarinsa kuwa abin aikatawa ne babu kokwanto.
إِنَّ هَٰذِهِۦ تَذۡكِرَةٞۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلًا
Open ayah 73:19Lalle wannan wa’azi ne, saboda haka duk wanda ya ga dama sai ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa.
۞إِنَّ رَبَّكَ يَعۡلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدۡنَىٰ مِن ثُلُثَيِ ٱلَّيۡلِ وَنِصۡفَهُۥ وَثُلُثَهُۥ وَطَآئِفَةٞ مِّنَ ٱلَّذِينَ مَعَكَۚ وَٱللَّهُ يُقَدِّرُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَۚ عَلِمَ أَن لَّن تُحۡصُوهُ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنَ ٱلۡقُرۡءَانِۚ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم مَّرۡضَىٰ وَءَاخَرُونَ يَضۡرِبُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَبۡتَغُونَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَءَاخَرُونَ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنۡهُۚ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَقۡرِضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗاۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيۡرٗا وَأَعۡظَمَ أَجۡرٗاۚ وَٱسۡتَغۡفِرُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمُۢ
Open ayah 73:20Lalle Ubangijinka Yana sane da cewa kai kana tsayawa ƙasa da kashi biyu cikin uku na dare, da kuma rabinsa, da kuma ɗaya bisa ukunsa, kai da wata jama’ar da take tare da kai. Allah ne kuma Yake ƙaddara dare da rana. Ya san kuma cewa, ba za ku iya ƙididdige (sa\'o\'insa) ba, don haka sai Ya yafe muku; to sai ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga Alƙur’ani. Ya san cewa daga cikinku akwai waɗanda za su kasance marasa lafiya, waɗansu kuma suna tafiya a bayan ƙasa don fatauci suna neman falala daga Allah, waɗansu kuma suna yin yaƙi saboda Allah; to sai ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi (Alƙur’ani). Ku kuma tsayar da salla, ku kuma ba da zakka, kuma ku bai wa Allah rance kyakkyawa. Kuma abin da kuka gabatar wa kanku na wani alheri, to za ku same shi wurin Allah, shi ya fi alheri ya kuma fi girman lada. Ku kuma nemi gafarar Allah; lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, dukkan bayanan da suka gabata a wannan Sura da abin da ta ƙunsa na ban tsoro da azaba a ranar lahira, wa’azi ne wanda muminai ne kaɗai za su amfana da su. Don haka duk wanda yake son ya riƙi hanyar da za ta sadar da shi da Ubangijinsa, to sai ya riƙi wannan wa’azi da Surar ta zo da shi, ya bi shari’ar Allah sau da ƙafa da koyarwar Manzon Allah (ﷺ). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani sauƙi da rangwame da ya yi wa Manzonsa (ﷺ) da al’ummarsa masu koyi da shi wajen Ƙiyamul Laili , tare da tabbatar masa cewa, yana sane da yanayin tsayuwarsa wadda ba ta kai biyu bisa uku na dare ba, wani lokaci kuma rabin dare ne, wani lokaci kuma ɗaya bisa ukunsa; wata jama’a ta muminai da suke tare da shi su ma suna koyi da shi a irin wannan tsayuwar. To Allah shi ne yake ƙaddara dare da yini, yake kuma ƙididdige sa’o’insu, ya kuma san Annabi (ﷺ) da muminai ba za su iya ƙididdige su ba, don haka sai suke shan wahala wajen tsayuwa a mafi yawan dare domin su cim ma abin da suke buƙata na tsawon lokacin tsayuwarsu. To sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da su cewa, ya sassauta musu, ya kuma yafe musu, don haka suna iya sallatar duk abin da ya sauwaƙa cikin dare. An karɓo daga Sa’ad ɗan Hisham ya ce: Na tambayi A’isha (Allah ya kara mata yarda) cewa, ta ba ni labarin sallar dare ta Manzon Allah (ﷺ). Sai ta ce: “Ba ka karanta Ya Ayyuhal Muzzammil ne?” Sai na ce: Ina yi. Sai ta ce: “To Allah mai girma da buwaya ya farlanta tsayuwar dare a farkon wannan Sura, Annabi (ﷺ) da sahabbansa suka shekara suna tsayuwar dare. Allah ya riƙe ƙarshen Surar bai saukar da shi ba har tsawon wata goma sha biyu, sai kuma a ƙarshen Surar Allah ya saukar da rangwame game da haka, sai tsayuwar dare ta koma taɗawwa’i bayan tana farilla.” [Muslim #746]. Sannan kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata hikimar wadda ta sanya ya yi musu sassauci wajen ƙaddara lokacin tsayuwarsu, watau ta yin la’akari da wasu abubuwa guda uku da rayuwar al’umma take da buƙata: <b>Na farko, </b> marasa lafiya waɗanda ba za su iya tsayuwar rabin dare ba ko biyu bisa uku ko ɗaya bisa ukunsa, to waɗannan sai su yi abin da ya sauwaƙa a gare su. Kuma ko sallar farilla idan mutum ba zai iya tsayawa ba sai ya yi ta a zaune, ita ma nafilar yana iya barin ta ɗungurungum idan za ta wahalar da shi, yana kuma da ladan abin da ya saba yi yana da lafiya. <b>Na biyu, </b> akwai matafiya masu balaguro don fatauci a bayan ƙasa, to su ma an sassauta musu, har a sallolinsu na farilla ma za su yi ƙasaru, watau raka’a bibbiyu a salloli masu raka’a huɗu. <b>Na uku, </b> su ne mayaƙa masu fita don yaƙi da kafirai saboda Allah, don ɗaukaka kalmar Allah. To duk waɗannan, tsayuwar dare kamar yadda suka saba a da za ta yi musu wahala, don haka sai su sallaci abin da ya sauwaƙa na dare ba tare da sun matsa wa kansu ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa da tsayar da sallolin farilla kamar yadda ya kamata, su kula da lokutansu da rukunansu da wajibansu da sunnoninsu, su kuma bayar da zakkar dukiyoyinsu, sannan su ba wa Allah kyakkyawan rance, watau su ciyar da dukiyoyinsu don Allah a wuraren da suka dace, ya kuma nuna musu cewa, duk wani aikin alheri da za su yi domin amfanin kawunansu za su sami ladansa a wurin Allah fiye da aikin nasu, domin zai ninninka musu shi. Su kuma nemi gafarar Allah, lalle Allah mai gafarta wa wanda ya tuba daga bayinsa ne, mai jin ƙansu ne.