المدثر

Al-Muddaththir

The Cloaked One · Surah 74 · Ayahs: 56 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُدَّثِّرُ

    Open ayah 74:1

    Ya kai mai lulluɓa.

  2. قُمۡ فَأَنذِرۡ

    Open ayah 74:2

    Tashi ka yi gargaɗi.

  3. وَرَبَّكَ فَكَبِّرۡ

    Open ayah 74:3

    Kuma ka girmama Ubangijinka

  4. وَثِيَابَكَ فَطَهِّرۡ

    Open ayah 74:4

    Ka kuma tsarkake tufafinka.

  5. وَٱلرُّجۡزَ فَٱهۡجُرۡ

    Open ayah 74:5

    Ka kuma ƙaurace wa (bautar) gumaka .

  6. وَلَا تَمۡنُن تَسۡتَكۡثِرُ

    Open ayah 74:6

    Kada kuma ka goranta wa (Ubangijinka) da ganin yawan (ayyukanka na ƙwarai).

  7. وَلِرَبِّكَ فَٱصۡبِرۡ

    Open ayah 74:7

    Ka kuma yi haƙuri game da Ubangijinka.

  8. فَإِذَا نُقِرَ فِي ٱلنَّاقُورِ

    Open ayah 74:8

    To idan an busa ƙaho.

  9. فَذَٰلِكَ يَوۡمَئِذٖ يَوۡمٌ عَسِيرٌ

    Open ayah 74:9

    To wannan ranar rana ce mai tsanani.

  10. عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ غَيۡرُ يَسِيرٖ 

    Open ayah 74:10

    A kan kafirai, ba mai sauƙi ba ce. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da kiran Manzonsa Muhammadu (ﷺ) wanda yake lulluɓe da tufafinsa don tsoron mala’ikan da ya yi ido huɗu da shi a karon farko a kogon Hira, lokacin saukar masa da wahayi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya miƙe tsaye ya yi wa mutanensa gargaɗi game da azabar Allah. Ya kuma umarce shi da ya girmama Ubangijinsa ta hanyar kaɗaita shi da bauta, sannan ya umarce shi da ya tsarkake kansa daga duk wani zunubi da tufafinsa daga duk wata najasa. Sannan ya umarce shi da ya nisanci bautar gumaka, ya kuma hana shi ya goranta wa Ubangijinsa ta hanyar ya riƙa ganin yawan kyawawan ayyukansa, watau kada yawansu ya ruɗe shi, ya yi rauni wajen tsayuwa a kan ayyukan da’awa, kuma ya sani duk yawan aikinsa da nagartarsu wata baiwa ce daga Allah a gare shi. A wani tafsirin kuwa, ana yi masa hani ne game da yin kyauta don a saka masa da mafi yawanta, ko ya yi wa mutane alheri daga baya ya goranta musu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya yi haƙuri a kan cutarwar da za a yi masa. Haka kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan sakamakon kafirai a ranar alƙiyama, yayin da mala’ika zai busa ƙaho busa ta biyu, to wannan rana ce mai tsanani, ba mai sauƙi ce a kan kafirai ba, domin za su fitar da duk wani tsammani game da samun kuɓuta daga azaba ko rabauta da Aljanna.

  11. ذَرۡنِي وَمَنۡ خَلَقۡتُ وَحِيدٗا

    Open ayah 74:11

    Ka bar Ni da wanda Na halitta shi kaɗai.

  12. وَجَعَلۡتُ لَهُۥ مَالٗا مَّمۡدُودٗا

    Open ayah 74:12

    Na kuma yi masa baiwa da dukiya maɗuɗuwa.

  13. وَبَنِينَ شُهُودٗا

    Open ayah 74:13

    Da kuma ‘ya’ya masu halartar (tarurruka tare da shi).

  14. وَمَهَّدتُّ لَهُۥ تَمۡهِيدٗا

    Open ayah 74:14

    Na kuma shimfiɗa masa (kyakkyawar rayuwa) iyakar shinfiɗawa

  15. ثُمَّ يَطۡمَعُ أَنۡ أَزِيدَ

    Open ayah 74:15

    Sannan yake kwaɗayin in ƙara (masa).

  16. كَلَّآۖ إِنَّهُۥ كَانَ لِأٓيَٰتِنَا عَنِيدٗا

    Open ayah 74:16

    Faufau! Lalle shi ya kasance mai tsaurin kai ne ga ayoyinmu.

  17. سَأُرۡهِقُهُۥ صَعُودًا

    Open ayah 74:17

    Ba da daɗewa ba zan ɗora masa (azaba) mai matsananciyar wahala.

  18. إِنَّهُۥ فَكَّرَ وَقَدَّرَ

    Open ayah 74:18

    Lalle shi ya yi tunani, ya kuma auna (a ransa).

  19. فَقُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ

    Open ayah 74:19

    Sai aka la’ane shi, yaya ya yi irin wannan awon?

  20. ثُمَّ قُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ 

    Open ayah 74:20

    Sannan aka kuma la’antar sa, yaya ya yi wannan awon?

  21. ثُمَّ نَظَرَ

    Open ayah 74:21

    Sannan ya yi nazari.

  22. ثُمَّ عَبَسَ وَبَسَرَ

    Open ayah 74:22

    Sannan ya ɗaure fuska, ya kuma murtuke.

  23. ثُمَّ أَدۡبَرَ وَٱسۡتَكۡبَرَ

    Open ayah 74:23

    Sannan ya ba da baya (daga imani) ya kuma yi girman kai.

  24. فَقَالَ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ يُؤۡثَرُ

    Open ayah 74:24

    Sai ya ce: “Wannan (Alƙur’ani) ba komai ba ne sai sihiri da aka samo (daga wasu).

  25. إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا قَوۡلُ ٱلۡبَشَرِ

    Open ayah 74:25

    “Wannan ba komai ba ne sai magana irin ta mutane.”

  26. سَأُصۡلِيهِ سَقَرَ

    Open ayah 74:26

    (Allah ya ce): Da sannu zan shigar da shi (wutar) Saƙara.

  27. وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سَقَرُ

    Open ayah 74:27

    Me ya sanar da kai abin da ake ce wa Saƙara?

  28. لَا تُبۡقِي وَلَا تَذَرُ

    Open ayah 74:28

    Ba ta ragewa kuma ba ta barin (komai).

  29. لَوَّاحَةٞ لِّلۡبَشَرِ

    Open ayah 74:29

    Mai ɗaɗɗaye fata ce.

  30. عَلَيۡهَا تِسۡعَةَ عَشَرَ 

    Open ayah 74:30

    Akwai (mala\'iku) goma sha tara suna tsaron ta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi magana a kan ƙasurgumin kafirin nan wanda ya yi suna wajen faɗa da gaskiya da addabar Manzon Allah, watau Alwalidu ɗan Mugira. Wata rana ya ji Annabi (ﷺ) yana karanta Alƙur’ani, sai ya ji kamar yana shigar sa. Da labari ya je kunnen Abu Jahl sai ya ce masa: “Ya kai baffana, mutanenka suna son su tara dukiya su ba ka a kan za ka je ka sami Muhammadu, ka fuskanci abin da yake tare da shi (watau Alƙur’ani).” Sai Alwalidu ya ce: “Lalle Ƙuraishawa sun san cewa na fi su yawan dukiya.” Sai Abu Jahl ya ce: “Ka faɗi wata magana game da Alƙur’ani da za ta je kunnen mutanenka su fahimci cewa kai ma ba ka yarda da shi ba, kuma ba ka son sa.” Sai ya ce: “To me zan faɗa? A cikinku kakaf babu wanda ya fi ni sanin waƙe-waƙe, wallahi abin da yake faɗa bai yi kama da waƙa ba. Wallahi zancen da yake faɗa yana da zaƙi, kuma tabbas yana da danshi, kuma samansa ya yi ‘ya’ya, ƙasansa kuma a jiƙe yake, kuma lalle shi ne a sama babu abin da ya kere shi.” Sai Abu Jahl ya ce: “Wallahi mutanenka ba za su yarda da kai ba har sai ka soke shi.” Sai ya ce: “Ƙyale ni in yi tunani a kai.” To bayan ya yi tunani sai ya ce: “Wannan (Alƙur’ani) ba komai ba ne face sihiri da aka samo shi daga wasu.” Sai aka saukar da waɗannan ayoyi. [Abdurrazaƙ, Tafsir , juzu’i na 2, shafi na 328, da Al-Hakim #3872]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Manzonsa (ﷺ) cewa ya bar shi da wannan azzalumi wanda shi ya halicce shi a cikin mahaifiyarsa ba tare da wata dukiya ko ‘ya’ya ba, haka ya zo duniya shi ɗaya tilo, amma Allah ya ci gaba da kulawa da shi har ya kai wani munzali, ya ba shi dukiya mai ɗimbin yawa, ya kuma yi masa baiwar ‘ya’ya maza waɗanda suke tare da shi a koyaushe, suna halartar wuraren tarurruka, ba sa fita ko’ina saboda tarin dukiyarsu, ya kuma hore masa kyakkyawar rayuwa. Duk da waɗannan abubuwa da aka ba shi amma fata yake Allah ya ƙara masa, duk kuwa da yawan kafircinsa. Sai kuwa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna masa cewa faufau, abin da yake tsammani ba mai yiwuwa ne ba, domin shi mutum ne mai taurin kai mai ƙaryata ayoyin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa Manzonsa (ﷺ). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ba da jimawa ba zai haɗa shi da azaba mai tsananin gaske da ba zai iya jure mata ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin taurin kan Alwalidu ɗan Mugira, watau duk da irin ɗimbin ni’imar da Allah ya yi masa, amma sai da ya shiga tunanin irin sukar da zai yi a kan Alƙur’ani da ɓatanci, don dai ya lalata shi. Sai da ya tsaya ya auna a ransa tare da zuzzurfan tunani wanda har aka la’ance shi game da wannan awon nasa, aka sake la’antar sa amma bai daina wannan awon a ransa ba. Da ya rasa samun abin suka, don tsabar baƙin ciki da damuwa sai ya ɗaure fuska ya murtuke, a ƙarshe dai ya juya baya ya bijire wa yin imani, ya fito ƙarara ya furta cewa, Alƙur’anin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo da shi sam ba maganar Allah ba ce; sihiri ne kawai, kuma maganar mutane ce wadda ya samu a wurin wasu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci mummunan sakamakon da yake jiran Alwalidu a ranar alƙiyama, domin zai shigar da shi wutar Saƙara mai tsananin zafi. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya kwarzanta wa Manzonsa (ﷺ) wannan wuta ta Saƙara wadda bai taɓa jin labarinta ba, da cewa ita wuta ce da ba ta rage komai daga jikin wanda aka jefa shi cikinta sai ta cinye shi kakaf, ta lashe shi tas, sannan a sake dawo da shi kamar yadda yake da farko, sannan ta sake tasar masa ta cinye shi, haka za ta yi ta yi ba ƙaƙƙautawa. Wuta ce mai tsananin ƙuna, mai saɓule fatar jiki, saboda tsananin zafinta, mala’iku har goma sha tara ne masu tsaron ta. <b> </b>

  31. وَمَا جَعَلۡنَآ أَصۡحَٰبَ ٱلنَّارِ إِلَّا مَلَٰٓئِكَةٗۖ وَمَا جَعَلۡنَا عِدَّتَهُمۡ إِلَّا فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ لِيَسۡتَيۡقِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَيَزۡدَادَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِيمَٰنٗا وَلَا يَرۡتَابَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَلِيَقُولَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡكَٰفِرُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَٰذَا مَثَلٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَمَا يَعۡلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلَّا هُوَۚ وَمَا هِيَ إِلَّا ذِكۡرَىٰ لِلۡبَشَرِ

    Open ayah 74:31

    Ba Mu kuwa sanya masu tsaron wutar ba sai mala’iku, ba Mu kuma sanya adadinsu ba sai don fitina ga waɗanda suka kafirta, don kuma waɗanda aka bai wa littafi su sami yaƙini, waɗanda kuma suka yi imani su ƙara imani, waɗanda aka bai wa littafi da muminai kuma kada su yi tababa, don kuma waɗanda suke da raunin imani a zukatansu da kuma kafirai su ce: “Me Allah Yake nufi da yin misali da wannan (adadin)?” Kamar haka Allah Yake ɓatar da wanda Ya ga dama, Yake kuma shiryar da wanda Ya ga dama. Ba kuma wanda ya san (yawan) rundunar Ubangijinka sai Shi. Ita (Saƙara) kuma ba wata abu ba ce face wa’azi ga mutane.

  32. كَلَّا وَٱلۡقَمَرِ

    Open ayah 74:32

    A’a. Na rantse da wata.

  33. وَٱلَّيۡلِ إِذۡ أَدۡبَرَ

    Open ayah 74:33

    Da kuma dare idan ya ba da baya.

  34. وَٱلصُّبۡحِ إِذَآ أَسۡفَرَ

    Open ayah 74:34

    Da kuma asuba idan ta bayyana (da haskenta).

  35. إِنَّهَا لَإِحۡدَى ٱلۡكُبَرِ

    Open ayah 74:35

    Lalle ita (Saƙara) tana ɗaya daga manya-manyan (bala’o’i).

  36. نَذِيرٗا لِّلۡبَشَرِ

    Open ayah 74:36

    Gargaɗi ce ga mutane.

  37. لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَتَقَدَّمَ أَوۡ يَتَأَخَّرَ

    Open ayah 74:37

    Ga wanda ya ga dama daga cikinku, ya ci gaba ko ya ci baya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba wasu ne ya sanya tsaron wuta ba sai mala’iku, don haka babu yadda mutane za su ci galaba a kansu, kamar yadda Abu Jahl ya riƙa cika baki yana cewa, shi ko an je lahira aka sanya su a wuta, to za su yi amfani da yawansu da ƙarfinsu su murƙushe mala’ikun nan goma sha tara masu tsaron wuta, su fita daga cikin wutar su gudu. Yana kuma faɗar wannan ne cikin izgili da ba\'a, domin da ma bai yi imani da ranar lahira ba. Sai kuma Allah ya sanar da su hikimar ambaton wannan adadi na mala’iku ga mutane kashi-kashi kamar haka: <b>Na ɗaya, </b>ga <b> </b>waɗanda suka kafirta, wannan adadin zai zame musu fitina da jarraba da za ta kai su ga wasu miyagun maganganu na izgili da kafirci wanda zai jawo musu a ninninka musu azaba. <b>Na biyu, </b>ga ma\'abota littafi, watau Yahudawa waɗanda aka ba wa Attaura da Nasara da aka ba wa Injila, su kuma za su ƙara tabbatar da gaskiyar Alƙur\'ani, domin za su ga lalle abin da ya zo da shi bai saɓa wa abin da yake cikin littattafansu ba, don haka su da sauran muminai ba za su yi wata tababa a game da gaskiyar Alƙur’ani ba. <b>Na uku, </b> su kuma muminai imaninsu zai ƙara haɓaka, domin sun ga abin da Alƙur’ani yake bayani yana yin daidai da abin da yake wurin ma\'abota littafi. <b>Na huɗu, </b> waɗanda suke da shakka a zukatansu kuwa da kafirai, za su dabirce ne su riƙa tambayar juna cewa, me Allah yake nufi da ambaton wannan adadi goma sha tara? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, kamar yadda wasu suke ƙaryata wannan adadi suna izgili da shi, to hakanan Allah (Mai tsarki da daukaka) yake shiryar da wanda ya ga dama, yake kuma ɓatar da wanda ya ga damar ɓatarwa. Idan kafirai ba su san yawan rundunar Allah ba, ai wannan ba abin mamaki ba ne, domin babu wanda ya san iya adadin rundunarsa sai shi kaɗai, kuma wuta ba wani abu ce ba face wa’azi ga mutane don su gane girman Ubangijinsu. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙaryata kafiran Makka game da maganarsu ta cewa, wai za su yi taron dangi su nuna wa mala’iku masu tsaron wuta cewa, sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. To Allah ya yi musu rantsuwa da wata da kuma dare yayin da ya ba da baya da duhunsa da kuma asuba idan ta bayyana da haskenta, don ya tabbatar musu cewa, lalle wutar Saƙara tana ɗaya daga cikin manya-manyan bala’o’i, domin gargaɗi ce ga mutane.

  38. كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡ رَهِينَةٌ

    Open ayah 74:38

    Kowane rai jingina ne ga abin da ya tsuwurwurta.

  39. إِلَّآ أَصۡحَٰبَ ٱلۡيَمِينِ

    Open ayah 74:39

    Sai dai ga ma\'abota dama.

  40. فِي جَنَّٰتٖ يَتَسَآءَلُونَ 

    Open ayah 74:40

    (Su kam suna) cikin gidajen Aljanna suna tambayar juna.

  41. عَنِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

    Open ayah 74:41

    Game da manyan masu laifuka.

  42. مَا سَلَكَكُمۡ فِي سَقَرَ

    Open ayah 74:42

    (Suna cewa): “Me ya shigar da ku cikin Saƙara?”

  43. قَالُواْ لَمۡ نَكُ مِنَ ٱلۡمُصَلِّينَ

    Open ayah 74:43

    Suka ce: “Ba mu zama daga cikin masallata ba.

  44. وَلَمۡ نَكُ نُطۡعِمُ ٱلۡمِسۡكِينَ

    Open ayah 74:44

    “Kuma ba mu kasance muna ciyar da miskini ba.

  45. وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ ٱلۡخَآئِضِينَ

    Open ayah 74:45

    “Mun kuma kasance muna kutsawa (cikin ɓarna) tare da masu kutsawa.

  46. وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ

    Open ayah 74:46

    “Kuma mun kasance muna ƙaryata ranar sakamako.

  47. حَتَّىٰٓ أَتَىٰنَا ٱلۡيَقِينُ

    Open ayah 74:47

    “Har mutuwa ta zo mana.”

  48. فَمَا تَنفَعُهُمۡ شَفَٰعَةُ ٱلشَّٰفِعِينَ

    Open ayah 74:48

    Saboda haka ceton masu ceto ba zai amfane su ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, kowane rai a ranar alƙiyama za a jinginar da shi ga ayyukansa, ko dai su hallakar da shi ko kuma su kuɓutar da shi, su ‘yanta shi. Sai dai muminai ma’abota dama, watau waɗanda za su karɓi littattafan ayyukansu ta hannayensu na dama, su kam ba za a kama su da zunubansu ba, za a yafe musu laifukansu ne, saboda kyawawan ayyukansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, su waɗannan muminan a ranar suna cikin gidajen Aljanna suna yi wa junansu tambaya game da kafirai waɗanda suka hallakar da kansu da miyagun ayyukansu. Muminai za su riƙa cewa, mene ne ya shigar da waɗannan kafirai cikin wutar Saƙara? Sai kafiran da kansu su amsa musu da cewa, abubuwa huɗu ne suka jawo musu shiga wannan azabar : <b>Na ɗaya, </b> a duniya ba su zamanto cikin muminai masu tsayar da salloli na farilla ba, domin ba su yi imani da cewa wajibi ne a kansu su yi salla ba. <b>Na biyu, </b> ba su zamanto suna ciyar da mabuƙata daga dukiyar da Allah ya ba su ba. <b>Na uku, </b> sun kasance tare da maɓarnata suna to kutsawa cikin ɓarna, suna faɗar ƙarairayi game da Annabi (ﷺ) da Alƙur’ani da Musulunci da Musulmi, don kawai son ransu. <b>Na huɗu, </b> sun zamanto suna ƙaryata zuwan ranar alƙiyama, ranar sakamako. Suka kuma ci gaba da ɓarna da ƙaryatawa har mutuwa ta zo musu, aka karɓi rayukansu ba tare da sun tuba sun koma ga Allah ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mutane masu irin waɗannan manyan laifuka, ceton masu ceto a ranar alƙiyama, watau mala’iku da annabawa da salihai, ba zai amfane su ba, domin sharaɗin karɓar ceto shi ne a yarda da wanda za a ceta, su kuwa waɗannan ba su zo da aikin da Allah zai yarda da su ba, don haka za su tabbata a cikin wutar Saƙara.

  49. فَمَا لَهُمۡ عَنِ ٱلتَّذۡكِرَةِ مُعۡرِضِينَ

    Open ayah 74:49

    To me ya same su ne suke bijire wa wa’azi?

  50. كَأَنَّهُمۡ حُمُرٞ مُّسۡتَنفِرَةٞ 

    Open ayah 74:50

    Kai ka ce su jakunan jeji ne da aka firgitar.

  51. فَرَّتۡ مِن قَسۡوَرَةِۭ

    Open ayah 74:51

    Da suka guje wa zaki.

  52. بَلۡ يُرِيدُ كُلُّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ أَن يُؤۡتَىٰ صُحُفٗا مُّنَشَّرَةٗ

    Open ayah 74:52

    A’a, kowane mutum daga cikinsu yana so ne a ba shi takardu buɗaɗɗu (kafin su bi Annabi).

  53. كَلَّاۖ بَل لَّا يَخَافُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ

    Open ayah 74:53

    Faufau! A’a, su dai ba sa tsoron ranar lahira ne.

  54. كَلَّآ إِنَّهُۥ تَذۡكِرَةٞ

    Open ayah 74:54

    Tabbas, lalle shi (Alƙur’ani) wa’azi ne.

  55. فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ

    Open ayah 74:55

    To duk wanda ya ga dama sai ya wa’azantu.

  56. وَمَا يَذۡكُرُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ هُوَ أَهۡلُ ٱلتَّقۡوَىٰ وَأَهۡلُ ٱلۡمَغۡفِرَةِ

    Open ayah 74:56

    Ba sa kuma wa’azantuwa sai idan Allah Ya ga dama. Shi ne Ya cancanci taƙawa, kuma Shi ne Ya cancanci yin gafara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin kafirai da cewa, me ya same su ne suke bijire wa Alƙur’ani suna bazama duk sanda ake karanta musu shi kamar dai yadda jakunan jeji suke bazama su arce idan sun hango zaki tafe ko wani maharbi mai shirin farautar su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, tare da irin wannan bijirewa ta kafirai amma kuma kowanne ɗaya daga cikinsu yana son ya wayi gari a daidai kansa ya ga wani buɗaɗɗen littafi wanda zai ba shi labarin cewa Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma fa suna neman haka ne ba domin rashin samun gamsasshiyar hujja ba game da gaskiyar Manzon Allah, sai don tsabar taurin kai da kangara. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa, al’amarin ba haka yake ba, abin da kawai yake ƙara musu kafewa a kan ɓarnarsu shi ne saboda ba su yi imani da azabar lahira ba, wannan ya sa suka ci gaba da aikata kafircinsu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, Alƙur’ani wa’azi ne da tunatarwa, don haka duk mai son ya karanta Alƙur’ani ya wa’azantu da shi, to sai ya karanta shi zai ga komai a fili dalla-dalla, to amma ba za su wa’azantu ɗin ba sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ga dama su wa’azantu, domin komai sai da ganin damarsa yake aukuwa, kuma shi ne ya cancanci a kiyaye dokokinsa, a yi aiki da umarninsa, a guji haninsa, kuma shi ne ya cancanci ya gafarta wa bayinsa zunubansu idan sun tuba sun koma gare shi.