القيامة

Al-Qiyaama

The Resurrection · Surah 75 · Ayahs: 40 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. لَآ أُقۡسِمُ بِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ

    Open ayah 75:1

    Ina rantsuwa da ranar alƙiyama.

  2. وَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلنَّفۡسِ ٱللَّوَّامَةِ

    Open ayah 75:2

    Ina kuma rantsuwa da rai mai yawan zargin (kansa).

  3. أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجۡمَعَ عِظَامَهُۥ

    Open ayah 75:3

    Yanzu mutum yana tsammanin ba za Mu tattara ƙasusuwansa ba?

  4. بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُۥ

    Open ayah 75:4

    E, (Mu) Masu iko ne a kan Mu daidaita gaɓoɓin yatsunsa.

  5. بَلۡ يُرِيدُ ٱلۡإِنسَٰنُ لِيَفۡجُرَ أَمَامَهُۥ

    Open ayah 75:5

    Ba haka ba ne, mutum yana nufi ne kawai ya gurɓata gabansa (da saɓon Allah).

  6. يَسۡـَٔلُ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلۡقِيَٰمَةِ

    Open ayah 75:6

    Yana tambaya yaushe ne ranar alƙiyamar?

  7. فَإِذَا بَرِقَ ٱلۡبَصَرُ

    Open ayah 75:7

    To lokacin da gani ya ruɗe.

  8. وَخَسَفَ ٱلۡقَمَرُ

    Open ayah 75:8

    Wata kuma ya yi duhu.

  9. وَجُمِعَ ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ

    Open ayah 75:9

    Aka kuma haɗe rana da wata (a mafitarsu).

  10. يَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذٍ أَيۡنَ ٱلۡمَفَرُّ 

    Open ayah 75:10

    A wannan rana ne mutum zai ce: “Ina wurin gudu?”

  11. كَلَّا لَا وَزَرَ

    Open ayah 75:11

    Faufau, babu mafaka.

  12. إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمُسۡتَقَرُّ

    Open ayah 75:12

    Zuwa ga Ubangijinka ne kawai matabbata take a wannan rana.

  13. يُنَبَّؤُاْ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذِۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ

    Open ayah 75:13

    Za a bai wa mutum labari a wannan rana na abin da ya gabatar da kuma (abin da) ya jinkirtar (na ayyukansa).

  14. بَلِ ٱلۡإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ بَصِيرَةٞ

    Open ayah 75:14

    A’a, shi dai mutum mai shaida ne a kan kansa.

  15. وَلَوۡ أَلۡقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ

    Open ayah 75:15

    Ko da kuwa ya kawo uzururrukansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa da ranar alƙiyama, ranar da mutane za su tsaya a gaban Ubangijin talikai don sauraron hukuncinsa. Ya kuma yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa a kan gazawarsa wajen ayyukan alheri, ko a kan aikata laifuka. Ubangiji ya yi waɗannan rantse-rantse ne domin ya tabbatar da cewa, zai tashi dukkan halittunsa bayan mutuwarsu, domin yi musu hisabi da sakamako. Sannan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya zargi ɗan’adam kafiri da cewa, yanzu shi yana zaton Allah ba zai iya tattara ƙasusuwansa ba bayan ya mutu, sun rududduge sun zama turɓaya? Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya mayar masa da martani cewa, haka abin yake, shi mai iko ne a kan ya tattara shi har ma ya dawo masa da gaɓoɓin yatsunsa daidai yadda suke da farko ba tare da an sami wani saɓani ba. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) kuma ya bayyana cewa, jayayyar da ɗan’adam kafiri yake yi a kan tashi bayan mutum ba yana yin ta ba ne don rashin samun gamsasshen dalili a kan haka, a’a, kawai dai yana so ne ya ci gaba da sheƙe ayarsa da ayyukan fajirci ba tare da ana tsawatar masa ba, har ma yana tambaya cikin izgili da rashin kunya cewa, yaushe ne ma alƙiyamar za ta auku ? Watau ba gaskiya ba ce, babu ranar zuwanta a ganinsa. Sai Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana masa alamomi uku na aukuwarta: <b>Na ɗaya, </b> lokacin da gani ya ruɗe ya ɗaimauce yayin da zai ga abin da yake ƙaryatawa muraran a gabansa. <b>Na biyu, </b> yayin da shi kuma wata ya yi duhu, haskensa ya gushe, gushewa ta har abada. <b>Na uku, </b> aka haɗa rana da wata wuri ɗaya, waɗanda tun lokacin da Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya halicce su ba su taɓa haɗuwa wuri guda ba. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tabbatar da cewa, a wannan ranar ne kafiri mai ƙaryata alƙiyama zai riƙa sambatu yana cewa, ina wurin gudu? Sai a ba shi amsa da cewa, faufau, yau babu wurin gudu ko mafaka da zai fake a cikinta. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, zuwa gare shi kawai makoma take a wannan rana domin yi wa kowa hisabi a kan ayyukansa masu kyau da munana, domin a ranar ne za a ba wa mutum labarin duk abin da ya gabatar na ayyukansa da wanda ya jinkirtar, ban da wannan ma ɗan’adam a ranar shi kansa mai ba da shaida ne a kansa game da munanan ayyukansa da ya aikata, lokacin da gaɓoɓinsa da fatarsa za su ba da shaida a kansa, don haka duk wani hanzari nasa da zai kawo ba zai yi masa amfani ba, domin laifukansa sun riga sun tabbata a kansa kuma lokacin bayar da uzuri a karɓa ya riga ya wuce.

  16. لَا تُحَرِّكۡ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعۡجَلَ بِهِۦٓ

    Open ayah 75:16

    (Allah ya ce da Annabinsa): Kada ka motsa harshenka da shi (Alƙur’ani) don gaggauta (karanta) shi.

  17. إِنَّ عَلَيۡنَا جَمۡعَهُۥ وَقُرۡءَانَهُۥ

    Open ayah 75:17

    Lalle tattara shi (a zuciyarka) da karanta shi yana kanmu.

  18. فَإِذَا قَرَأۡنَٰهُ فَٱتَّبِعۡ قُرۡءَانَهُۥ

    Open ayah 75:18

    Saboda haka idan Muka karanta (maka) shi sai ka bi karatunsa.

  19. ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا بَيَانَهُۥ

    Open ayah 75:19

    Sannan kuma bayaninsa yana kanmu.

  20. كَلَّا بَلۡ تُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ 

    Open ayah 75:20

    Haba, ku dai kawai kuna son duniya ne.

  21. وَتَذَرُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ

    Open ayah 75:21

    Kuna kuma barin lahira.

  22. وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاضِرَةٌ

    Open ayah 75:22

    Wasu fuskokin a wannan rana a ni’imce suke.

  23. إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٞ

    Open ayah 75:23

    Suna masu kallon Ubangijinsu.

  24. وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذِۭ بَاسِرَةٞ

    Open ayah 75:24

    Wasu fuskokin kuma a wannan rana a ɗaɗɗaure suke.

  25. تَظُنُّ أَن يُفۡعَلَ بِهَا فَاقِرَةٞ

    Open ayah 75:25

    Suna tabbatar da cewa, za a saukar musu da wani bala’i. A waɗannan ayoyi Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana tsananin kwaɗayin Manzonsa (ﷺ) wajen sauraron ayoyin Allah da ake saukar masa, da ƙoƙarinsa na son ya gaggauta haddace su don isar da su ga mutanensa. Wannan ya sanya shi yana wahala matuƙa, to sai Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya nusar da shi cewa, kada ya riƙa motsa harshensa da karatun Alƙur’ani yayin da ake yi masa wahayinsa, don ya gaggauta haddace shi don kada ya kuɓuce masa. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tabbatar masa cewa, ya yi masa alƙawarin zai tattara masa shi a zuciyarsa, ya tabbatar masa da karatunsa a kan harshensa, ba zai manta shi ba, don haka idan Mala’ika Jibrilu yana karanta masa, to ya tsaya tsit ya saurare shi, to sannan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya yi masa alƙawarin fassara masa shi daki-daki. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah ( <b>ﷺ </b>) yana shan wahala wajen karɓar wahayin Alƙur’ani, sai ya kasance yana motsa harshensa da leɓensa don kada ya kuɓuce masa, yana son ya haddace shi, sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Kada ka motsa harshenka da shi (Alƙur’ani) don gaggauta (karanta) shi. Lalle tattara shi (a zuciyarka) da karanta shi yana kanmu.” Sai Manzon Allah ( <b>ﷺ </b>) ya zamanto bayan haka idan Jibrilu ya zo masa, sai ya sunkuyar da kansa ya riƙa sauraron sa, idan ya tafi sai ya karanta Alƙur’ani kamar yadda Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya yi masa alƙawari. [Bukhari #4927 da Muslim #5044]. Sai kuma Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya soki mushirikai, ya bayyana dalilin da ya sanya su ba sa son maganar ranar alƙiyama, har kuma suke riya cewa babu tashi bayan mutuwa duk kuwa da sun san cewa, wanda ya ƙagi halittarsu da farko, ai tashin su bayan mutuwa ba abu ne da zai gagare shi ba, to amma suna ƙaryatawa ne saboda yadda suke tsananin son rayuwar duniya mai saurin gushewa, da watsi da suka yi da rayuwar lahira wadda hanyar samun ta shi ne bin umarnin Allah da guje wa haninsa. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana musu kasuwar mutane a ranar lahira kashi biyu: <b>Kashi na farko, </b> su ne muminai ‘yan Aljanna waɗanda fuskokinsu za su yi haske da hasken imani, su ne kuma masu ganin Ubangijinsu ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ba tare da wani shamaki ba. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri ( <b>Allah ya kara masa yarda </b>) ya ce: Mun ce: “Ya Manzon Allah, shin za mu ga Ubangijinmu a ranar alƙiyama?” Sai ya ce: “Shin za ku sha wahala wajen ganin rana a lokacin azahar sama fayau babu wani girgije?” Sai muka ce: “A’a, ya Manzon Allah.” Sai ya ce: “Shin za ku sha wahala wajen ganin wata daren goma sha huɗu sama fayau babu wani girgije?” Sai suka ce: “A’a, ya Manzon Allah.” Sai ya ce: “Ba za ku sha wahalar ganin sa ba a ranar alƙiyama, kamar yadda ba kwa shan wahala wajen ganin rana ko wata.” [Bukhari #458 da Muslim #182]. <b>Kashi na biyu, </b> su ne kafirai ‘yan wuta waɗanda fuskokinsu za su murtuke cikin ƙasƙanci, za su tabbatar da cewa, za a saukar musu da azaba mai girma mai tsanani.

  26. كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِيَ

    Open ayah 75:26

    Ku saurara, yayin da rai ya iso a karankarama.

  27. وَقِيلَ مَنۡۜ رَاقٖ

    Open ayah 75:27

    Aka kuma ce: “Wane ne mai tawaida?”

  28. وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلۡفِرَاقُ

    Open ayah 75:28

    Ya kuma tabbata cewar (wannan) shi ne rabuwarsa (da duniya).

  29. وَٱلۡتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ

    Open ayah 75:29

    Kuma tsananin bala\'i ya haɗu.

  30. إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمَسَاقُ 

    Open ayah 75:30

    To zuwa Ubangijinka ne (za a) kora ka a wannan ranar.

  31. فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ

    Open ayah 75:31

    To bai ba da gaskiya ba bai kuma yi salla ba.

  32. وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ

    Open ayah 75:32

    Sai dai ya ƙaryata ya kuma ba da baya.

  33. ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ

    Open ayah 75:33

    Sannan ya tafi zuwa ga iyalinsa yana taƙama.

  34. أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰ

    Open ayah 75:34

    (Azaba) ta doso ka, ta fa doso ka!

  35. ثُمَّ أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰٓ

    Open ayah 75:35

    Sannan ta doso ka, ta fa doso ka! A waɗannan ayoyi Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana ƙarshen rayuwar kowane ɗan’adam a duniya, don ya tabbatar wa mushirikai cewa, abin ba kamar yadda suke tsammani ba ne cewa, idan sun mutu ba za a yi musu wata azaba ba. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana cewa, lokacin da rai zai zo ga karankarama, watau ƙasusuwan ƙirji a lokacin gargarar mutuwa, masu jinya su riƙa tambayar junansu cewa, wane ne zai yi masa ruƙuya ko ya sami sauƙi? A lokacin shi kuma ya tabbatar cewa, lokacin rabuwa da duniya ta zo, watau mutuwa, ga shi kuma tsananin bala’i ya haɗu, rai ya zo fita daga gangar jiki, to yayin da haka ta faru ne za a kora mamaci zuwa ga Ubangijinsa, to a nan komai zai bayyana ƙarara ga mutum. Sai Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana mawuyacin halin da kafiri zai samu kansa ciki a ranar domin ya je wa Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) da kafircinsa da taurin kansa, bai gaskata Allah da Manzonsa ba, bai yi salla domin Allah ba, duniya kawai ta ruɗe shi ya ƙaryata abin da Manzon Allah ( <b>ﷺ </b>) ya zo masa da shi, ya bijire wa ɗa’a ga Allah da Manzonsa hankalinsa a kwance babu tsoron Allah ko kaɗan a zuciyarsa, bugu da ƙari kuma yayin da yake juya baya cikin iyalinsa yana taƙama, wannan ya nuna babu abin da yake damun sa. Sai Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya yi masa alƙawarin narkon azaba cewa, yana nan ya doso shi yana dab da ya auka masa. Allah ya nanata masa wannan narkon don ya tabbatar da cewa, babu makawa sai ya same shi. <b> </b>

  36. أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَن يُتۡرَكَ سُدًى

    Open ayah 75:36

    Yanzu mutum yana tsammanin za a bar shi haka sasakai?

  37. أَلَمۡ يَكُ نُطۡفَةٗ مِّن مَّنِيّٖ يُمۡنَىٰ

    Open ayah 75:37

    Shin bai kasance wani ɗigo na maniyyi da ake zuba shi (a mahaifa) ba?

  38. ثُمَّ كَانَ عَلَقَةٗ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ

    Open ayah 75:38

    Sannan ya zama gudan jini sannan (Allah) Ya halicce (shi) sai Ya daidaita (shi)?

  39. فَجَعَلَ مِنۡهُ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ

    Open ayah 75:39

    Sannan Ya halicci dangi biyu daga gare shi, namiji da mace?

  40. أَلَيۡسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰ 

    Open ayah 75:40

    Yanzu wannan bai zama Mai iko a kan ya raya matattu ba? A waɗannan ayoyi Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) yana tunatar da kafiri mai ƙaryata tashi bayan mutuwa wasu dalilai biyu masu tabbatar da tashin alƙiyama da yi wa mutane hisabi. <b>Na farko, </b>shin kafiri yana zaton cewa, Allah da ya halicce shi zai bar shi hakanan sakaka babu umarni babu hani, watau ya ƙyale shi ya yi abin da ya ga dama ba tare da zuwan ranar da zai ga sakamakon ayyukansa ba? Lalle wannan zaton banza ne a wurin duk wani mai hankali, domin bai dace da aikin mai hikima ba kamar Allah. <b>Na biyu, </b>Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tambaye shi cewa, ashe ba shi ne wata rana ya zamanto ɗigon maniyyi wanda ake zuba shi a cikin mahaifa ba? Bayan haka kuma ya zama gudan jini daskararre, sannan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya halicce shi ya kuma daidaita halittarsa, ya sanya shi jinsi biyu, namiji da mace? To yanzu a tunaninsa, Allah wanda ya halicce shi daga wannan ƙasƙantaccen ruwa ba zai iya sake raya matattu ba don yi musu hisabi? Tabbas Allah mai iko ne a kan komai. An karɓo daga Musa ɗan Abu A’isha ya ce: Wani mutum ya kasance yana salla a saman gidansa, sai ya zamanto idan ya karanta faɗar Allah: “Yanzu wannan bai zama mai iko a kan ya raya matattu ba?” Sai ya ce: ‘Subhanaka Fa Bala’ , (watau tsarki ya tabbata gare ka, haka ne za ka iya). Sai suka tambaye shi game da wannan abu da yake faɗa, sai ya ce: Na ji shi ne daga Manzon Allah ( <b>ﷺ </b>). [Abu Dawud #884]. <b> </b>