الانسان
Al-Insaan
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
هَلۡ أَتَىٰ عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ حِينٞ مِّنَ ٱلدَّهۡرِ لَمۡ يَكُن شَيۡـٔٗا مَّذۡكُورًا
Open ayah 76:1Haƙiƙa wani yanki na zamani ya zo wa mutum yayin da bai zama wani abin ambato ba.
إِنَّا خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن نُّطۡفَةٍ أَمۡشَاجٖ نَّبۡتَلِيهِ فَجَعَلۡنَٰهُ سَمِيعَۢا بَصِيرًا
Open ayah 76:2Lalle Mun halicci mutum daga maniyyi gamin-gambiza don Mu jarrabe shi, sai Muka sanya shi mai ji mai gani.
إِنَّا هَدَيۡنَٰهُ ٱلسَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرٗا وَإِمَّا كَفُورًا
Open ayah 76:3Lalle Mun bayyana masa hanya, ko dai (ya zama) mai godewa ko kuma mai butulcewa. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya buɗe Surar da tabbatar wa ɗan’adam cewa, wani yankin lokaci mai tsawo ya shuɗe masa yayin da babu shi gaba ɗaya, babu kuma wanda ya san shi. Sannan lokacin da Allah ya tashi halittar sa sai ya halicci asalinsa daga yumɓu, watau halittar Annabi Adamu, sannan ya halicci sauran zuriyyarsa da maniyyi gamin-gambiza tsakanin na namiji da na mace, ya bayyana cewa, ya samar da shi ne don ya jarraba shi ya ga ko zai tuna yanayinsa na farko ko kuma zai manta shi ya ruɗu da kansa. Sai ya sanya shi mai ji ne mai ganin abin da aka ɗora masa yin aiki da shi a shari’a. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tabbatar da cewa, ya yi wa ɗan’adam cikakken bayanin hanyar shiriya da hanyar ɓata ta hanyar manzanninsa. Saboda haka ko dai ya bi tafarki madaidaici ya zama bawa mai godiya ga Allah ko kuma ya butulce ya bi hanyar ɓata, sai ya zama bawa kafiri mai musunta ayoyin Allah.
إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ سَلَٰسِلَاْ وَأَغۡلَٰلٗا وَسَعِيرًا
Open ayah 76:4Lalle Mun tanadar wa kafirai sarƙoƙi da ƙuƙumai da wutar Sa’ira.
إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ يَشۡرَبُونَ مِن كَأۡسٖ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورًا
Open ayah 76:5Lalle mutane nagari suna sha daga wani kofin (giya) da mahaɗinta ya kasance kafur ne.
عَيۡنٗا يَشۡرَبُ بِهَا عِبَادُ ٱللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفۡجِيرٗا
Open ayah 76:6Wani marmaro ne da bayin Allah suke sha daga gare shi suna ɓuɓɓugo shi ɓuɓɓugowa ta haƙiƙa.
يُوفُونَ بِٱلنَّذۡرِ وَيَخَافُونَ يَوۡمٗا كَانَ شَرُّهُۥ مُسۡتَطِيرٗا
Open ayah 76:7Suna cika alƙawari na bakance suna kuma tsoron ranar da sharrinta ya kasance mai bazuwa ne.
وَيُطۡعِمُونَ ٱلطَّعَامَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ مِسۡكِينٗا وَيَتِيمٗا وَأَسِيرًا
Open ayah 76:8Suna kuma ciyar da abinci tare da suna son sa ga miskini da maraya da kuma ribataccen yaƙi.
إِنَّمَا نُطۡعِمُكُمۡ لِوَجۡهِ ٱللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنكُمۡ جَزَآءٗ وَلَا شُكُورًا
Open ayah 76:9(Suna cewa): “Mu kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah, ba ma nufin sakamako ko godiya daga wurinka.
إِنَّا نَخَافُ مِن رَّبِّنَا يَوۡمًا عَبُوسٗا قَمۡطَرِيرٗا
Open ayah 76:10“Lalle mu muna jin tsoron rana mai sa ɗaure fuska, matsananciya daga Ubangijinmu.
فَوَقَىٰهُمُ ٱللَّهُ شَرَّ ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمِ وَلَقَّىٰهُمۡ نَضۡرَةٗ وَسُرُورٗا
Open ayah 76:11Sai Allah Ya kare su (daga) sharrin wannan ranar Ya kuma ba su haske (a fuskokinsu) da kuma farin ciki.
وَجَزَىٰهُم بِمَا صَبَرُواْ جَنَّةٗ وَحَرِيرٗا
Open ayah 76:12Ya kuma saka musu da Aljanna da alharini saboda haƙurin da suka yi. A waɗannan ayoyi Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana sakamakon bayinsa bijirarru da waɗanda suka yi masa biyayya a lahira, da cewa ya yi wa waɗanda suka kafirce masa suka bijire wa manzanninsa tanadin sarƙoƙin da za a ja su da su a cikin wutar Jahannama da ƙuƙumai waɗanda za a haɗa hannayensu da wuyoyinsu a ɗaure su tamau da su. Ya kuma yi musu tanadin wata wuta mai ruruwa. Su kuma mutane nagari waɗanda suka yi wa Allah biyayya a ranar alƙiyama, ya tabbatar musu cewa, a gidajensu na Aljanna za su sha wani cikakken kofi na giya wadda aka gauraya ta da kafur mai daɗin ƙamshi. Wannan abin sha kuma daga wani marmaro ne marar ƙafewa wanda daga gare shi ne bayin Allah suke sha har su ƙoshi; suna ɓuɓɓugo da shi su kwararar da shi zuwa inda suka ga dama. Sannan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana kyawawan siffofin waɗannan bayi nasa nagari waɗanda da su ne suka cancanci wancan sakamako: <b>Na farko, </b> suna cika alƙawari na bakance, watau alƙawarin da suka yi na ɗora wa kawunansu wasu ayyuka na ɗa’a, kamar salloli ko azumi ko sadaka. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah ( <b>ﷺ </b>) ya ce: “Duk wanda ya yi bakancen zai yi wa Allah ɗa’a, to ya yi masa, wanda kuma ya yi bakancen zai saɓa wa Allah, to kada ya saɓa masa.” [Bukhari #6696]. <b>Na biyu, </b> suna ciyar da abinci tare da cewa suna son sa suna kuma buƙatar sa, amma sai su ba da shi ga mabuƙata da marayu da ribatattun yaƙi. <b>Na uku, </b> suna yin haka ne kuma da manufarsu ta neman yardar Allah, suna faɗa a ransu cewa, suna ciyar da waɗannan mabuƙata ne kawai don neman yardar Allah, don haka ba sa buƙatar wani sakamako ko godiya daga gare su. <b>Na huɗu, </b> suna tsoron wata rana da fuskokin ‘yan wuta za su murtuke su ɗaure saboda tsananin wannan ranar a gare su. Sai Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana cewa, ya biya musu dukkan buƙatunsu, ya kuma tsare su da falalarsa daga sharrin wannan ranar, ya kuma haɗa fuskokinsu da haske da annuri don girmama su da shigar musu da farin ciki a zukatansu. Kuma saboda haƙurinsu wajen bin Allah da abin da ya same su na ƙaddararsa sai ya saka musu da gidan Aljanna da za su shiga su more ni’imomin da ke cikinta, ya kuma ba su tufafin alharini wanda za su riƙa sakawa a jikinsu.
مُّتَّكِـِٔينَ فِيهَا عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِۖ لَا يَرَوۡنَ فِيهَا شَمۡسٗا وَلَا زَمۡهَرِيرٗا
Open ayah 76:13Suna masu kishingiɗa a cikinta a kan gadaje; ba sa ganin rana ko jin tsananin sanyi a cikinta.
وَدَانِيَةً عَلَيۡهِمۡ ظِلَٰلُهَا وَذُلِّلَتۡ قُطُوفُهَا تَذۡلِيلٗا
Open ayah 76:14Inuwoyinta kuma suna kusa da su, an kuma hore musu \'ya\'yan itatuwanta matuƙar horewa.
وَيُطَافُ عَلَيۡهِم بِـَٔانِيَةٖ مِّن فِضَّةٖ وَأَكۡوَابٖ كَانَتۡ قَوَارِيرَا۠
Open ayah 76:15Ana kuma kai-kawo a tsakaninsu da ƙorai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau.
قَوَارِيرَاْ مِن فِضَّةٖ قَدَّرُوهَا تَقۡدِيرٗا
Open ayah 76:16Ƙarau ɗin na azurfa ne, sun auna su, aunawa daidai da buƙata.
وَيُسۡقَوۡنَ فِيهَا كَأۡسٗا كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِيلًا
Open ayah 76:17Ana kuma shayar da su wata giya a cikinta, wadda mahaɗinta ya kasance citta mai yatsu ce.
عَيۡنٗا فِيهَا تُسَمَّىٰ سَلۡسَبِيلٗا
Open ayah 76:18Wani marmaro ne a cikinta da ake kiran sa Salsabilu .
۞وَيَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٞ مُّخَلَّدُونَ إِذَا رَأَيۡتَهُمۡ حَسِبۡتَهُمۡ لُؤۡلُؤٗا مَّنثُورٗا
Open ayah 76:19Samari hadimai dawwamammu (da ba sa tsufa) kuma suna kai-kawo tsakaninsu, idan ka gan su sai ka yi tsammanin su wani lu’ulu’u ne da aka baza.
وَإِذَا رَأَيۡتَ ثَمَّ رَأَيۡتَ نَعِيمٗا وَمُلۡكٗا كَبِيرًا
Open ayah 76:20Idan kuma ka yi kallo a can, za ka ga ni’ima da kuma mulki ƙasaitacce.
عَٰلِيَهُمۡ ثِيَابُ سُندُسٍ خُضۡرٞ وَإِسۡتَبۡرَقٞۖ وَحُلُّوٓاْ أَسَاوِرَ مِن فِضَّةٖ وَسَقَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡ شَرَابٗا طَهُورًا
Open ayah 76:21Suna sanye da korayen tufafin alharini marar kauri da na alharini mai kauri; aka kuma yi musu ado da warawarai na azurfa, Ubangijinsu kuma Ya shayar da su abin sha mai tsarki.
إِنَّ هَٰذَا كَانَ لَكُمۡ جَزَآءٗ وَكَانَ سَعۡيُكُم مَّشۡكُورًا
Open ayah 76:22Lalle wannan ya kasance sakamako ne a gare ku, kuma aikinku ya kasance abin godewa. A waɗannan ayoyi Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya ci gaba da bayyana ni’imomin da ya tanadar wa bayinsa nagari a Aljanna, inda ya ambaci cewa a cikin gidajensu na Aljanna ya tanadar musu da gadaje na alfarma waɗanda za su riƙa kishingiɗa a kansu, kuma ba za su ga wata rana a cikin Aljanna ba wadda zafinta zai cutar da su, ba kuma za su ji matsanancin sanyi ba, don haka koyaushe suna cikin inuwa wadda babu zafi a cikinta babu kuma matsanancin sanyi. Wata ƙarin ni’imar kuma a gare su, ita ce inuwoyin bishiyoyin gidan Aljanna waɗanda suke kusa da su, ba sa janyewa har abada, sannan an hore musu ‘ya’yan itatuwanta ga duk mai son ya tsinka zai tsinke su cikin sauƙi ba tare da ya sha wata wahala ba a kowane yanayi kuma yake ciki; a kwance yake ko a zaune ko a tsaye. Kuma hadimai suna kai-kawo a tsakaninsu da ƙorai na azurfa da kuma kofuna na ƙarau garai-garai cike da abin sha. Su waɗannan kofuna na azurfa garai-garai suke kamar ƙarau har ana ganin abin shan da yake cikinsu, hadiman da suke kai-kawo a tsakaninsu kuma suna auna musu abin shan su daidai buƙatarsu, ba sa cika musu kofunan fal har suna zuba, ba kuma sa yi musu ƙwauro ya kasa isar su. Ana kuma shayar da su wata giya cike da kofi wadda aka gauraya ta da citta mai yatsu, mai daɗin ɗanɗano da ƙamshi. Suna kuma sha daga wani marmaro na Aljanna wanda ake kira ‘salsabilu’ . Sannan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana siffofin masu kai-kawo suna yi musu hidima a Aljanna da cewa, wasu samari ne waɗanda koyaushe suna cikin ƙuruciyarsu ba sa tsufa; idan mutum ya gan su saboda hasken fuskokinsu da kyan fatar jikinsu da yawansu sai ya yi tsammanin wani lu’ulu’u ne wanda aka baza a ko’ina. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya kwarzanta wa Manzonsa ( <b>ﷺ </b>) bayanin ni’imomin Aljanna da cewa, idan ya ga ni’imomin gidan Aljanna abin ya fi ƙarfin a siffanta shi, domin zai ga ƙasaitaccen mulki yana gudana, zai ga abin da bai taɓa gani ko jin irinsa ba. Kuma ga ‘yan Aljanna sanye da tufafi koraye na alfahari waɗanda aka ɗinka su da alharini marar kauri, ga wasu kuma masu kauri, an kuma yi musu ado da warawarai na azurfa, sannan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya shayar da su wani tataccen abin sha da zai tsaftace musu dukkan jikinsu ciki da waje. Sai kuma Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana wa muminai cewa, duk waɗannan ni’imomi da aka yi musu bayaninsu an tanade su ne domin su kasance sakamako a gare su a kan kyawawan ayyukansu a duniya, kuma ana yi musu godiya a kan ayyukansu karɓaɓɓu a wajen Allah.
إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ تَنزِيلٗا
Open ayah 76:23Lalle Mu Muka saukar maka da Alƙur’ani daki-daki.
فَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ وَلَا تُطِعۡ مِنۡهُمۡ ءَاثِمًا أَوۡ كَفُورٗا
Open ayah 76:24Saboda haka ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka kada kuwa ka bi mai yawan saɓo ko mai yawan kafircewa daga cikinsu.
وَٱذۡكُرِ ٱسۡمَ رَبِّكَ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلٗا
Open ayah 76:25Ka kuma ambaci sunan Ubangijinka safe da yamma.
وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَٱسۡجُدۡ لَهُۥ وَسَبِّحۡهُ لَيۡلٗا طَوِيلًا
Open ayah 76:26Da daddare kuma sai ka yi sujjada a gare Shi, ka kuma yi nafiloli saboda Shi a tsawon dare.
إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ يُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ وَيَذَرُونَ وَرَآءَهُمۡ يَوۡمٗا ثَقِيلٗا
Open ayah 76:27Lalle waɗannan suna son mai gaggawar ƙarewa (watau duniya), suna kuma watsi da rana mai nauyi a bayansu.
نَّحۡنُ خَلَقۡنَٰهُمۡ وَشَدَدۡنَآ أَسۡرَهُمۡۖ وَإِذَا شِئۡنَا بَدَّلۡنَآ أَمۡثَٰلَهُمۡ تَبۡدِيلًا
Open ayah 76:28Mu Muka halicce su Muka kuma ƙarfafa gaɓoɓinsu; idan kuwa Muka ga dama sai Mu musanya irinsu (kyakkyawar) musanyawa.
إِنَّ هَٰذِهِۦ تَذۡكِرَةٞۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلٗا
Open ayah 76:29Lalle wannan wa\'azi ne; saboda haka wanda ya ga dama sai ya riƙi hanya zuwa ga Ubangijinsa.
وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Open ayah 76:30Kuma ba ganin damarku ba ce sai abin da Allah ya ga dama. Lalle Allah Ya kasance Masani, Mai hikima.
يُدۡخِلُ مَن يَشَآءُ فِي رَحۡمَتِهِۦۚ وَٱلظَّٰلِمِينَ أَعَدَّ لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمَۢا
Open ayah 76:31Yana shigar da wanda Ya ga dama cikin rahamarsa. Azzalumai kuwa Ya tanadar musu azaba mai raɗaɗi. A waɗannan ayoyi Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) girman matsayin da ya ba shi, domin kuwa shi ne ya saukar masa da Alƙur’ani guntu-guntu, bai saukar masa shi a dunƙule ba lokaci ɗaya, don haka ya ci gaba da riƙo da hukunce-hukuncensa da shari’o’insa, ya isar da su ga al’ummarsa. Ya kuma umarce shi da yin haƙuri da abin da Ubangijinsa zai hukunta masa na shari’a ko na ƙaddara, kada kuma ya biye wa wani mai saɓo a kan abin da yake yi na saɓon Allah, kada kuma ya biye wa wani kafiri a kan kafircinsa, saboda biye musu saɓa wa Allah ne, domin ba za su taɓa kawo wani abu ba sai wanda ya dace da son zuciyarsu. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya umarci Manzonsa da ya ambaci Ubangijinsa a sallar asuba da safe da sallar azahar da la’asar a ƙarshen yini. Ya kuma ambace shi a sallolinsa na dare, watau sallar magariba da sallar isha, sannan ya yi sallolin nafiloli, watau tahajjud a tsawon dare. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tabbatar wa Manzonsa ( <b>ﷺ </b>) cewa, mushirikai ba komai suke so ba in ban da more rayuwar duniya mai saurin ƙarewa, amma suna watsi da rana mai nauyi, watau alƙiyama a bayansu, bayan kuma cike take da wahalhalu da musibu iri-iri, duk da haka sun ƙi yi mata wani kyakkyawan tanadi sai kafirci da saɓon Allah. Sannan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya kafa musu ƙwaƙƙwarar hujja ta hankali a kan sake tashin su bayan sun mutu domin yi musu hisabi a ranar alƙiyama da suke ƙaryatawa, Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tabbatar musu cewa, shi ne ya halicce su tun da farko ya kuma ƙarfafa halittarsu ta hanyar ƙarfafa musu gaɓoɓinsu da sauran halittar jikinsu, don haka idan ya ga dama sai ya hallaka su ya kawo wasu irinsu, wannan kuma ba abu ne da zai gagare shi ba. Ko kuma idan ya ga dama sai ya hallaka su ya maye gurbinsu a nan duniya da wasu irinsu waɗanda ba za su saɓa masa ba ko su kafirce masa. Daga ƙarshen Sura Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana cewa, lalle wannan Sura wa’azi ce da tunatarwa, don haka duk wanda ya ga dama yana iya kama hanya madaidaiciya da za ta sadar da shi da samun yardar Ubangijinsa a ranar alƙiyama. Sannan ya bayyana cewa, mutane ba su ne suke yin abin da suka ga dama ba, sai abin da Allah ya ga damar aukuwarsa, domin komai yana hannunsa, shi ne kuma masanin abin da ya fi dacewa ga bayinsa da wanda bai dace da su ba, mai hikima ne a cikin halittarsa da ƙaddararsa da shari’arsa. Yana kuma shigar da wanda ya ga dama daga cikin bayinsa a cikin rahamarsa, ya yi musu gamon-katarin imani da ayyuka nagari. Ya kuma tanadar wa azzalumai masu cutar kawunansu da kafirci da laifuka wata azaba mai raɗaɗi a lahira, ita ce azabar wutar Jahannama.