المرسلات
Al-Mursalaat
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلۡمُرۡسَلَٰتِ عُرۡفٗا
Open ayah 77:1Na rantse da iska mai bibiyar juna.
فَٱلۡعَٰصِفَٰتِ عَصۡفٗا
Open ayah 77:2Da kuma iska mai tasowa da tsanani.
وَٱلنَّٰشِرَٰتِ نَشۡرٗا
Open ayah 77:3Da iska mai watso ruwa watsowa.
فَٱلۡفَٰرِقَٰتِ فَرۡقٗا
Open ayah 77:4Da kuma (mala\'iku) masu rarrabe ƙarya da gaskiya iya rarrabewa.
فَٱلۡمُلۡقِيَٰتِ ذِكۡرًا
Open ayah 77:5Sannan masu sauko da wahayi.
عُذۡرًا أَوۡ نُذۡرًا
Open ayah 77:6Don yanke hanzari ko don gargaɗi.
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٞ
Open ayah 77:7Lalle abin da ake yi muku alƙawari tabbas mai afkuwa ne.
فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتۡ
Open ayah 77:8To idan taurari aka shafe haskensu.
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتۡ
Open ayah 77:9Idan kuma sama aka tsattsage ta.
وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ نُسِفَتۡ
Open ayah 77:10Idan kuma duwatsu aka sheƙe su.
وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتۡ
Open ayah 77:11Idan kuma manzanni aka tattara su.
لِأَيِّ يَوۡمٍ أُجِّلَتۡ
Open ayah 77:12Ga wacce rana ce aka ƙayyaje musu.
لِيَوۡمِ ٱلۡفَصۡلِ
Open ayah 77:13Ga rana ta yin hukunci.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ
Open ayah 77:14Me kuma ya sanar da kai ranar yin hukunci.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:15Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da rantsuwa da wasu muhimman halittunsa masu girma. Ya rantse da iska mai bibiyar juna, da iska mai tasowa da ƙarfi da iska mai watso da ruwa ƙasa. Allah kuma ya yi rantsuwa da mala’iku masu saukowa da abin da yake rarrabe tsakanin gaskiya da ƙarya, watau masu saukowa da wahayi zuwa ga manzannin Allah domin yanke wa bayi hanzari a wurin Allah da wurin mutane ko gargaɗi ga mutane game da azabar Allah. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya yi waɗannan rantse-rantse ne don ya tabbatar da cewa, lalle alƙawarin tashi bayan mutuwa da hisabi da sakamako, tabbas mai aukuwa ne babu makawa. Sai kuma Allah ya ambaci wasu alamomin wannan ranar da cewa, a lokacin da za a ga tsarin gudanar da duniya gaba ɗaya ya rikice, an tafiyar da hasken taurari, sama kuma ta tsattsage, mala’iku suna ta saukowa da umarnin Allah, an tumɓuke duwatsu daga wurarensu an dandaƙe su sun zama ƙura an sheƙe su; manzanni kuma an tattara su don wani ƙayyadajjen lokaci na wani yini mai girma, don su ba da shaida game da al’ummunsu cewa, sun isar musu da saƙon Allah, ranar da za a yi hukuncin tsakanin bayi a bayyana mai gaskiya da marar gaskiya da ɗan wuta da ɗan Aljanna. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya nuna wa Manzonsa girman wannan rana har ya yi masa tambayar cewa, me ma ya sanar da shi ranar yin hukunci? Sai Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tabbatar da cewa, tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryata manzannin Allah da gaskiyar da suka zo da ita.
أَلَمۡ نُهۡلِكِ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 77:16Yanzu ba Mu hallakar da na farko ba?
ثُمَّ نُتۡبِعُهُمُ ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 77:17Sannan Muka biyo su da na ƙarshe?
كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 77:18Kamar haka Muke yi wa masu manyan laifuka.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:19Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa.
أَلَمۡ نَخۡلُقكُّم مِّن مَّآءٖ مَّهِينٖ
Open ayah 77:20Yanzu ba Mu halicce ku daga wani wulaƙantaccen ruwa ba?
فَجَعَلۡنَٰهُ فِي قَرَارٖ مَّكِينٍ
Open ayah 77:21Sannan Muka sanya shi cikin matabbata mai aminci?
إِلَىٰ قَدَرٖ مَّعۡلُومٖ
Open ayah 77:22Zuwa wani lokaci sananne?
فَقَدَرۡنَا فَنِعۡمَ ٱلۡقَٰدِرُونَ
Open ayah 77:23Sannan Muka ƙaddara (komai ta yadda ya dace)? To madalla da Masu ƙaddarawa.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:24Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa.
أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ كِفَاتًا
Open ayah 77:25Yanzu ba Mu sanya ƙasa (ta zama) matattara ba?
أَحۡيَآءٗ وَأَمۡوَٰتٗا
Open ayah 77:26(Ga) rayayyu da matattu?
وَجَعَلۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ شَٰمِخَٰتٖ وَأَسۡقَيۡنَٰكُم مَّآءٗ فُرَاتٗا
Open ayah 77:27Muka kuma sanya kafaffun duwatsu dogaye a cikinta, Muka kuma shayar da ku ruwa mai daɗi?
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:28Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa. A waɗannan ayoyi Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tsoratar da kafirai cewa, shi ne ya hallaka al’ummun farko waɗanda suka kafirce masa, suka ƙaryata manzanninsa, sannan ya hallaka na bayansu waɗanda su ma suka ƙaryata manzanninsa, sannan ya yi alƙawarin cewa, kamar yadda ya hallaka waɗancan masu ƙaryatawar hakanan zai hallaka kafirai masu ƙaryata Manzon Allah ( <b>ﷺ </b>) da abin da ya zo da shi na gaskiya. Sai ya bayyana cewa, halaka da tsananin azaba sun tabbata ga masu ƙaryatawa a ranar alƙiyama. Sannan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana ni’imar halitta da ya yi wa ɗan’adam mai nuna cikakkiyar Ƙudurarsa. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tambayi bayinsa cewa, shin ba shi ne ya halicce su daga wani wulaƙantaccen ruwa ba, watau maniyyi? Ya ajiye wannan maniyyin a cikin wani wuri mai aminci, watau mahaifar ‘ya mace, har zuwa wani sanannen lokaci, watau tsawon lokacin zaman jariri a cikin mahaifiyarsa wata tara ko ƙasa da haka. Sannan Allah ya ƙaddara siffar wannan abin haihuwa da matsayinsa da kamanninsa da sauran yanayin halittarsa. To madalla da masu ƙaddara komai yadda ya dace, shi ne Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>). Sai Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya sake tabbatar da cewa, tsananin azaba ya tabbata ga masu ƙaryatawa a ranar alƙiyama. Sai Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya sake jawo hankalin mutane zuwa ga wata ni’imar da ya yi musu inda ya tambaye su cewa, shin ba shi ne ya sanya ƙasa ta zama mai tattara mutane gaba ɗaya ba; masu rai a cikin gidajensu a bayanta, matattu kuma a binne a cikin ƙaburburansu a ƙarƙashinta? Ya kuma sanya kafaffun duwatsu masu tsawo a cikinta waɗanda suke hana ta yin tangal-tangal, ya kuma shayar da mutane ruwa mai daɗi? To duk wanda yake da ikon yin wannan halittar, lalle sake tayar da matattu ba zai gagare shi ba. Don haka ya sake tabbatar da cewa, tsananin azaba ya tabbata ga masu ƙaryata waɗannan ni’imomin nasa a ranar alƙiyama.
ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Open ayah 77:29Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatawa.
ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ ظِلّٖ ذِي ثَلَٰثِ شُعَبٖ
Open ayah 77:30Ku tafi zuwa wata inuwa mai rassa uku.
لَّا ظَلِيلٖ وَلَا يُغۡنِي مِنَ ٱللَّهَبِ
Open ayah 77:31Ba mai ba da inuwa ba kuma ba mai karewa daga harshen wuta ba.
إِنَّهَا تَرۡمِي بِشَرَرٖ كَٱلۡقَصۡرِ
Open ayah 77:32Haƙiƙa ita tana jefa tartsatsi kamar ƙaton gini.
كَأَنَّهُۥ جِمَٰلَتٞ صُفۡرٞ
Open ayah 77:33Kai ka ce su raƙuma ne baƙaƙe.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:34Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa.
هَٰذَا يَوۡمُ لَا يَنطِقُونَ
Open ayah 77:35Wannan ita ce ranar da ba sa magana.
وَلَا يُؤۡذَنُ لَهُمۡ فَيَعۡتَذِرُونَ
Open ayah 77:36Kuma ba za a yi musu izini ba balle su kawo hanzari.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:37Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa.
هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِۖ جَمَعۡنَٰكُمۡ وَٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 77:38Wannan ita ce rana ta yin hukunci da Muka tara ku da na farko.
فَإِن كَانَ لَكُمۡ كَيۡدٞ فَكِيدُونِ
Open ayah 77:39To idan kuna da wani tanadi na makirci sai ku ƙulla Mini.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:40Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa. A waɗannan ayoyi, bayan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tabbatar wa kafirai gaskiyar zuwan ranar alƙiyama, sai kuma ya bayyana musu irin mummunar azabar da za su gamu da ita matuƙar ba su yi imani ba. Rana ce wadda mala’iku masu tsaron Jahannama za su gargaɗa su su ce musu, su tafi zuwa ga azabar da suka kasance suna ƙaryatawa, su tafi zuwa wata inuwa ta hayaƙin wuta mai rassa uku: Inuwa ce wadda ba ta da sanyi irin na inuwa, ba ta kuma kare mutum daga harshen wuta da zafinta. Sannan ya siffanta wannan wutar da cewa, lalle ita wuta ce wadda take jefo tartsatsinta, kowane tartsatsi girmansa kamar wani katafaren gini ne, sannan ga shi baƙi wuluk kamar baƙaƙen raƙuma. Don haka duk masu ƙaryatawa su sani cewa, tsananin azaba a ranar lahira ya tabbata a gare su. Sannan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana musu siffar wannan rana da cewa, rana ce da ba za a bar su su yi wata magana ba, kuma ba za a ba su izini su faɗi wani hanzarinsu ba a gaban Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) game da kafircinsu da laifukan da suka aikata. Don haka tsananin azaba ya tabbata a wannan rana ga masu ƙaryata labaran wannan rana ta alƙiyama. Sai kuma Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya sanar da kafirai cewa, wannan fa ita ce ranar alƙiyama, kuma ga shi duk ya tattara su a cikinta su da sauran al’ummun da suka gabata a farfajiya ɗaya. Don haka idan suna da wani tanadi na makirci da suka shirya na yadda za su kuɓuce wa azabar wannan rana, to ga fili ga mai doki sai su nuna shi. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya daɗa tabbatar musu cewa, tsananin azaba ya tabbata ga masu ƙaryata ranar yin hukunci a tsakaninsu.
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي ظِلَٰلٖ وَعُيُونٖ
Open ayah 77:41Lalle masu taƙawa suna cikin inuwoyi da idanuwan ruwa.
وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشۡتَهُونَ
Open ayah 77:42Da kuma ababan marmari daga abin da suke sha’awa.
كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 77:43Ku ci kuma ku sha kuna masu farin ciki saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 77:44Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:45Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa.
كُلُواْ وَتَمَتَّعُواْ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجۡرِمُونَ
Open ayah 77:46Ku ci kuma ku ji daɗi kaɗan (a duniya), lalle ku kun tabbata manyan masu laifi.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:47Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa.
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرۡكَعُواْ لَا يَرۡكَعُونَ
Open ayah 77:48Idan kuma aka ce da su: “Ku yi ruku\'u”, to ba za su yi ruku\'u ba.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:49Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa.
فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 77:50To da wane irin zance ne bayansa (Alƙur’ani) za su yi imani? A waɗannan ayoyi kuma Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana kyakkyawan sakamakon masu taƙawa, watau waɗanda suka bi umarninsa suka kuma guje wa haninsa da cewa, za su sami shiga ƙarƙashin inuwoyin bishiyoyin Aljanna masu ni’ima, za su kuma sha daga idanuwan wani marmaro mai gudana mai matuƙar daɗi, za a kuma wadata su da kayan marmari irin duk wanda suke sha’awar su ci; mala’iku suna ce musu su ci daɗaɗan abin cikinta, su sha ruwanta mai daɗi saboda kyawawan ayyukan da suka aikata a duniya. Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya tabbatar da cewa, irin wannan sakamako da ya yi musu shi ne yake yi wa bayinsa masu kyautatawa. Don haka tsananin azaba ya tabbata ga masu ƙaryata abin da ya tanadar wa bayinsa masu taƙawa a wannan ranar. Sai kuma Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya sake juyowa ga mushirikai, ya tsoratar da su da cewa, su ci su more rayuwar duniya na ɗan lokaci kaɗan, to amma su tabbata cewa, su masu manyan laifuka ne saboda kafirce wa Allah da ƙaryata manzanninsa da suka yi. Don haka tsananin azaba ya tabbata ga masu ƙaryatawa a ranar alƙiyama. Sai kuma Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana mummunan taurin kansu a nan duniya lokacin da aka umarce su da su yi salla, suka ƙi yarda su yi, don haka tsananin azaba a wannan ranar ya tabbata ga masu ƙaryata abin da manzannin Allah suka zo da shi daga Allah. Sannan Allah ( <b>Mai tsarki da daukaka </b>) ya bayyana cewa, idan har waɗannan kafiran sun guje wa Alƙur’ani da ya saukar mai cike da ɗimbin hikimomi da hujjoji kuma gagara-koyo, to da wane zance ne kuma za su yi imani? Lalle babu shi.