النبإ

An-Naba

The Announcement · Surah 78 · Ayahs: 40 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ

    Open ayah 78:1

    Game da me suke tambayar junansu?

  2. عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلۡعَظِيمِ

    Open ayah 78:2

    Game da labari ne mai girma.

  3. ٱلَّذِي هُمۡ فِيهِ مُخۡتَلِفُونَ

    Open ayah 78:3

    Wanda game da shi ne suke saɓani

  4. كَلَّا سَيَعۡلَمُونَ

    Open ayah 78:4

    Ba haka ne ba, da sannu za su sani.

  5. ثُمَّ كَلَّا سَيَعۡلَمُونَ

    Open ayah 78:5

    Sannan kuma tabbas, da sannu za su sani.

  6. أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ مِهَٰدٗا

    Open ayah 78:6

    Yanzu ba mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?

  7. وَٱلۡجِبَالَ أَوۡتَادٗا

    Open ayah 78:7

    Duwatsu kuma turaku?

  8. وَخَلَقۡنَٰكُمۡ أَزۡوَٰجٗا

    Open ayah 78:8

    Muka kuma halicce ku bibbiyu (watau maza da mata)?

  9. وَجَعَلۡنَا نَوۡمَكُمۡ سُبَاتٗا

    Open ayah 78:9

    Muka kuma sanya baccinku (ya zama) hutu?

  10. وَجَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ لِبَاسٗا 

    Open ayah 78:10

    Muka kuma sanya dare (ya zama) sutura?

  11. وَجَعَلۡنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشٗا

    Open ayah 78:11

    Muka kuma sanya yini don neman abinci?

  12. وَبَنَيۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعٗا شِدَادٗا

    Open ayah 78:12

    Muka kuma gina (sammai) bakwai ƙarfafa a sama da ku?

  13. وَجَعَلۡنَا سِرَاجٗا وَهَّاجٗا

    Open ayah 78:13

    Muka kuma sanya wata fitila mai tsananin haske (watau rana)?

  14. وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡمُعۡصِرَٰتِ مَآءٗ ثَجَّاجٗا

    Open ayah 78:14

    Muka kuma saukar da ruwa mai kwarara daga (hadari) da ya batse da ruwa?

  15. لِّنُخۡرِجَ بِهِۦ حَبّٗا وَنَبَاتٗا

    Open ayah 78:15

    Domin Mu fitar da ƙwayoyi da tsirrai da shi?

  16. وَجَنَّٰتٍ أَلۡفَافًا

    Open ayah 78:16

    Da kuma gonaki masu itatuwa sassarƙe da juna? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tambaya game da mushirikai masu ƙaryata Alƙur’ani cewa, game da mene ne suke yi wa juna tambaya bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aika musu Manzonsa (ﷺ)? Sai kuma ya bayyana kan abin da suke yi wa junansu tambaya da cewa, suna yin tambaya ne game da labari mai girma, watau shi ne Alƙur’ani wanda Allah ya aiko Manzonsa (ﷺ) da shi kuma yake ƙunshe da maganar tashin alƙiyama domin yi wa kowa hisabi. Kafirai suna ta saɓani a kansa cewa, da me ya kamata su kwatanta shi, shin su kira shi da tsafi ko su ce masa waƙa ko bokanci, ko kuma su siffanta shi da tatsuniyoyin mutanen farko? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa, lamarin Alƙur’ani ba duk yadda suke faɗa ba ne, amma da sannu za su san mummunan ƙarshen ƙaryatawarsu gare shi, sannan hakan zai tabbata a gare su ba da jimawa ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalinsu ta hanyar tunatar da wasu ni’imominsa guda tara da ya yi musu waɗanda sun isa su zama ƙwararan hujjoji a kan ingancin manzancin Annabi (ﷺ) da gaskiyar tashin alƙiyama da Alƙur’ani yake faɗa musu. <b>Na farko, </b> Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su cewa, ashe ba shi ne ya sanya musu ƙasa ta zama shimfiɗa a gare su ba, yadda suke rayuwa a kanta cikin nutsuwa? Lalle shi ne ya yi musu wannan ni’imar mai girma. <b>Na biyu, </b> kuma ba shi ne ya kafa musu duwatsu a cikin ƙasa don su hana ta girgiza da tangal-tangal da su ba? <b>Na uku, </b> ya kuma halicce su jinsin namiji da mace, don kowa ya sami nutsuwa da ɗan’uwansa da soyayya da tausayi da samun ƙaruwar zuriya? <b>Na huɗu, </b> ya kuma sanya barcinsu ya zame musu hutu bayan sun gaji da ɗawainiya ta yau-da-gobe? <b>Na biyar, </b> ya sanya musu dare ya zame musu sutura da zai lulluɓe su da duhunsa? <b>Na shida, </b> ya kuma sanya musu rana lokaci ne da za su fita domin neman abincinsu da harkokinsu na rayuwa? <b>Na bakwai, </b> ya kuma gina musu sammai bakwai masu ƙarfi a samansu? <b>Na takwas, </b> ya sanya musu rana mai tsananin haske da suke amfana da haskenta da zafinta? <b>Na tara, </b> ya saukar musu da ruwan sama mai matuƙar yawa daga gizagizai masu tatso ruwa daga cikinsu, domin ya fitar musu da dangogin ƙwaya da dangogin tsirrai da wannan ruwan? Ya kuma fitar musu da gonaki masu cike da itatuwa sassarƙafe da juna saboda yawansu? Lalle Allah ne ya yi musu duk waɗannan ni\'imomin. To don me suke jayayya da abin da ya aiko Annabinsa (ﷺ) da shi, watau Alƙur\'ani har suke ƙaryata rayuwa bayan mutuwa?

  17. إِنَّ يَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ كَانَ مِيقَٰتٗا

    Open ayah 78:17

    Lalle ranar hukunci ta kasance (rana ce) mai tsayayyen lokaci.

  18. يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِ فَتَأۡتُونَ أَفۡوَاجٗا

    Open ayah 78:18

    Ranar da za a busa ƙaho sai ku zo jama’a-jama’a.

  19. وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ أَبۡوَٰبٗا

    Open ayah 78:19

    Aka kuma buɗe sama sai ta zama ƙofofi.

  20. وَسُيِّرَتِ ٱلۡجِبَالُ فَكَانَتۡ سَرَابًا 

    Open ayah 78:20

    Aka kuma tafiyar da duwatsu sai suka zama kawalwalniya.

  21. إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتۡ مِرۡصَادٗا

    Open ayah 78:21

    Lalle Jahannama ta kasance madakata ce.

  22. لِّلطَّٰغِينَ مَـَٔابٗا

    Open ayah 78:22

    Makoma ce ga masu ɗagawa.

  23. لَّٰبِثِينَ فِيهَآ أَحۡقَابٗا

    Open ayah 78:23

    Masu zama ne a cikinta shekaru aru-aru.

  24. لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرۡدٗا وَلَا شَرَابًا

    Open ayah 78:24

    Ba sa ɗanɗanar wani sanyi a cikinta ko wani abin sha.

  25. إِلَّا حَمِيمٗا وَغَسَّاقٗا

    Open ayah 78:25

    Sai tafasasshen ruwa da ruwan mugunya.

  26. جَزَآءٗ وِفَاقًا

    Open ayah 78:26

    Don sakayya da ta dace.

  27. إِنَّهُمۡ كَانُواْ لَا يَرۡجُونَ حِسَابٗا

    Open ayah 78:27

    Lalle su sun kasance ba sa tsoron hisabi.

  28. وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كِذَّابٗا

    Open ayah 78:28

    Suka kuma ƙaryata ayoyinmu iyakar ƙaryatawa.

  29. وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ كِتَٰبٗا

    Open ayah 78:29

    Kuma kowane abu Mun ƙididdige shi a rubuce.

  30. فَذُوقُواْ فَلَن نَّزِيدَكُمۡ إِلَّا عَذَابًا 

    Open ayah 78:30

    (Sai a ce da su): To ku ɗanɗana, don ba za Mu ƙara muku ba sai dai wata azaba.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, alƙiyama lokaci ne na tashin matattu, kuma rana ce mai ƙayyadajjen lokaci, don haka tana nan tafe ba makawa, a cikinta ne Allah zai yi hukunci tsakanin halittu gaba ɗaya. Rana ce da mala’ika zai yi busa ta biyu a cikin ƙaho, daga nan duk mutane za su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu daga cikin ƙaburburansu ƙungiya-ƙungiya. A ranar za a buɗe rufin sama ta zama mai buɗaɗɗun ƙofofi, inda mala’iku za su yi ta sauka da umarnin Allah. An kuma dandaƙe duwatsu sun bi iska kamar ƙura, sun koma tamkar kawalwalniya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan sakamakon masu ƙaryata gaskiya a wannan ranar, lokacin da Jahannama ce za ta zama makoma ga masu ɗagawa, masu wuce iyakokin Allah. Idan an jefa su a cikinta za su yi ta zama cikinta shekaru aru-aru har abada babu ranar fita. Su yi rayuwa ta azaba da ƙunci a cikinta, domin kuwa ba za su taɓa shaƙar wata iska mai sanyi ba a cikinta, ba kuma za su sha wani daddaɗan abin sha ba, sai dai wani tafasasshen ruwa da mugunyar ‘yan wuta mai matsanancin wari. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan mummunan sakamako da ya yi musu shi ne sakayyar da ta dace da su, saboda kafircinsu da ɓatansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin da ya ja suka cancanci wannan matsananciyar azabar da cewa, lalle sun kasance a duniya ba sa tsoron hisabin Allah a lahira, domin ba su yi imani da tashi bayan mutuwa ba, saboda da a ce suna jin tsoron ranar lahira da sun yi imani da ita, sun kuma yi ayyuka nagari. Kuma suka ƙaryata ayoyin da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ) iya ƙaryatawa, ba su san cewa, Allah ya ƙididdige duk ayyukansu a rubuce a cikin littattafan ayyukansu ba? Don haka bayan an jefa su wutar Jahannama sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce musu su ɗanɗani azaba ta dindindin, babu abin da za a ƙara musu sai azaba a kan azaba.

  31. إِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ مَفَازًا

    Open ayah 78:31

    Lalle masu taƙawa suna da babban rabo.

  32. حَدَآئِقَ وَأَعۡنَٰبٗا

    Open ayah 78:32

    (Su ne) gonaki da inabai.

  33. وَكَوَاعِبَ أَتۡرَابٗا

    Open ayah 78:33

    Da ‘yan mata tsaraiku.

  34. وَكَأۡسٗا دِهَاقٗا

    Open ayah 78:34

    Da kofin giya cikakke.

  35. لَّا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا كِذَّٰبٗا

    Open ayah 78:35

    Ba sa jin maganar banza a cikinta ko kuma ƙarya.

  36. جَزَآءٗ مِّن رَّبِّكَ عَطَآءً حِسَابٗا

    Open ayah 78:36

    Sakamako ne daga Ubangijinka, kyauta ce a lissafe (gwargwadon aikin kowa) . A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kyakkyawan sakamako na masu taƙawa, watau waɗanda suke bin umarnin Allah, suke kuma guje wa haninsa, inda ya tabbatar da cewa, suna da babban rabo, watau gidan Aljanna da samun kuɓuta daga shiga wuta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu tanadin gonaki masu cike da dangogin kayan itatuwan marmari iri-iri da inabai mai yawa. Suna da kuma ‘yan mata tsareku a shekarunsu ga kuma cikakkun kofunan giya mai daɗin kwankwaɗa. Kuma ‘yan Aljanna a cikinta ba sa jin wata magana ta banza ko ta ƙarya, kuma sashinsu ba ya ƙaryata sashi. Duk wannan sakamako da ya ba su kyauta ce isasshiya, kuma a lissafe kowa gwargwadon aikinsa nagari.

  37. رَّبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا ٱلرَّحۡمَٰنِۖ لَا يَمۡلِكُونَ مِنۡهُ خِطَابٗا

    Open ayah 78:37

    Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu (watau Allah) Mai rahama; (halittu) ba sa samun ikon yi masa magana daga gare Shi.

  38. يَوۡمَ يَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ صَفّٗاۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَقَالَ صَوَابٗا

    Open ayah 78:38

    Ranar da Jibrilu da mala’iku za su tsaya sahu-sahu; (halittu) ba sa iya magana sai fa wanda (Allah) Mai rahama Ya yi wa izini, ya kuma faɗi abin da ya dace.

  39. ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلۡحَقُّۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا

    Open ayah 78:39

    Wannan rana ce tabbatacciya; saboda haka wanda ya ga dama sai ya riƙi kyakkyawar makoma zuwa ga Ubangijinsa.

  40. إِنَّآ أَنذَرۡنَٰكُمۡ عَذَابٗا قَرِيبٗا يَوۡمَ يَنظُرُ ٱلۡمَرۡءُ مَا قَدَّمَتۡ يَدَاهُ وَيَقُولُ ٱلۡكَافِرُ يَٰلَيۡتَنِي كُنتُ تُرَٰبَۢا 

    Open ayah 78:40

    Lalle Mun yi muku gargaɗin azaba ta kurkusa, a ranar da mutum zai ga abin da hannayensa suka gabatar (na alheri ko na sharri), kafiri kuma ya riƙa cewa: “Ina ma da na zama turɓaya!” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kansa da cewa, shi ne wanda ya yi wa masu taƙawa sakamakon da aka ambata, shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu, mai rahama ga kowa a duniya mai jin ƙan muminai kaɗai a lahira, wanda duk halittu ba su mallaki ikon yi masa wata magana ba har sai ya yi izini. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a ranar ne Mala’ika Jibrilu da sauran mala’iku za su tsaya sahu-sahu, babu mai iya buɗe baki ya ceci wani sai wanda Allah mai rahama ya yi masa izinin ya yi ceto, ya kuma faɗi magana ta daidai, watau kalmar Tauhidi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, wannan ranar da ya yi bayanin siffofinta rana ce tabbatacciya sai ta auku babu makawa, don haka duk wanda ya so ya tsira a wannan ranar daga azabar Allah, to ya kama kyakkyawar hanyar da za ta sada shi da haka, watau yin ayyuka nagari da barin munana. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da kafirai ya tabbatar musu cewa, lalle ya gargaɗe su da wata azaba ta kurkusa, ranar da mutum zai ga aikin da ya yi a duniya, kafiri kuma ya riƙa burin ina ma ya zama turɓaya, kamar sauran dabbobi da za a ce musu su zama turɓaya.