النازعات
An-Naazi'aat
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلنَّٰزِعَٰتِ غَرۡقٗا
Open ayah 79:1Na rantse da (mala’iku) masu cizgar (ran kafiri) mummunar cizga.
وَٱلنَّٰشِطَٰتِ نَشۡطٗا
Open ayah 79:2Da kuma (mala’iku) masu zare (ran mumini) sassauƙar zarewa.
وَٱلسَّٰبِحَٰتِ سَبۡحٗا
Open ayah 79:3Da kuma (mala’iku) masu ninƙaya (a sama don sauko da umarni) ninƙaya mai tsananin sauri.
فَٱلسَّٰبِقَٰتِ سَبۡقٗا
Open ayah 79:4Sannan da (mala’iku) masu matuƙar rigegeniya (don zartar da umarnin Allah).
فَٱلۡمُدَبِّرَٰتِ أَمۡرٗا
Open ayah 79:5Sannan da (mala’iku) masu tsara al’amura.
يَوۡمَ تَرۡجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ
Open ayah 79:6Ranar da mai girgizawa za ta yi girgiza (watau busar ƙaho ta farko).
تَتۡبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ
Open ayah 79:7Mai bin ta kuma za ta biyo ta (watau busa ta biyu).
قُلُوبٞ يَوۡمَئِذٖ وَاجِفَةٌ
Open ayah 79:8Wasu zukata a wannan ranar a tsorace suke.
أَبۡصَٰرُهَا خَٰشِعَةٞ
Open ayah 79:9Idanuwansu kuma a ƙasƙance suke.
يَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرۡدُودُونَ فِي ٱلۡحَافِرَةِ
Open ayah 79:10(A duniya) suna cewa: “Yanzu zai yiwu a dawo da mu a raye (bayan mutuwa)?
أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمٗا نَّخِرَةٗ
Open ayah 79:11“Yanzu ko bayan mun zama ƙasusuwa rududdugaggu?”
قَالُواْ تِلۡكَ إِذٗا كَرَّةٌ خَاسِرَةٞ
Open ayah 79:12Suka ce: “Idan ko ya yiwu, to wannan komawa ce mai cike da asara.”
فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٞ وَٰحِدَةٞ
Open ayah 79:13To lalle ita kawai tsawa ce guda ɗaya tal!.
فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ
Open ayah 79:14Sai ga su a bayan ƙasa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantse-rantse guda biyar. Ya rantse da mala’iku masu fizgar rayukan kafirai mummunar fizga yayin da suka zo mutuwa. Ya kuma yi rantsuwa da mala’iku masu zare rayukan muminai cikin sauƙi yayin mutuwarsu. Ya kuma rantse da mala’iku masu ninƙaya daga sama zuwa ƙasa ɗauke da umarnin Allah. Ya kuma yi rantsuwa da mala’iku masu rigegeniya da junansu wajen zartar da umarnin Allah. Ya kuma yi rantsuwa da mala’iku masu zartar da al’amuran da ya tsara ko ya hukunta a cikin bayinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi waɗannan rantse-rantse ne domin ya tabbatar wa mushirikai cewa lalle za a tashe su bayan mutuwarsu domin yi musu hisabi da sakamako. Sai kuma Allah ya bayyana ranar alƙiyama da cewa, ita ce ranar da ƙasa za ta girgiza lokacin busar ƙaho ta farko, sannan busa ta biyu ta biyo bayanta. A wannan ranar zukatan wasu mutane za su cika da tsoro, alamun ƙasƙanci da wulaƙanci su bayyana a idanuwansu. Su ne kuma a duniya cikin izgili da fitsara suke cewa, wai shin bayan sun mutu anya za a sake dawo da su wata rayuwa sabuwa, bayan sun zama rududdugaggun ƙasusuwa rarakakku? Wai ta yaya kuma za a ce za a dawo musu da rayukansu? Wai da kuwa haka zai faru da ya zame musu dawowa mai cike da asara. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, wannan sassauƙan al’amari ne a wurinsa, domin kuwa sake dawo musu da rayukansu al’amari ne na tsawa guda ɗaya tal wadda mala’ika mai busa ƙaho zai yi, sai kawai kowa da kowa ya fito da ransa a bayan ƙasa bayan a da yana matacce a cikinta.
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ
Open ayah 79:15Shin labarin Musa ya zo maka?
إِذۡ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوًى
Open ayah 79:16Lokacin da Ubangijinsa Ya kirawo shi a kwari mai tsarki, (watau) Ɗuwa?
ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ
Open ayah 79:17(Aka ce da shi): Ka tafi zuwa ga Fir’auna, haƙiƙa shi ya yi ɗagawa.
فَقُلۡ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ
Open ayah 79:18Sai ka ce: “Shin zai yiwu gare ka kuwa ka tsarkaka?
وَأَهۡدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخۡشَىٰ
Open ayah 79:19“In kuma shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka, sai ka ji tsoron Sa?
فَأَرَىٰهُ ٱلۡأٓيَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰ
Open ayah 79:20Sai ya nuna masa babbar aya.
فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ
Open ayah 79:21Sai ya ƙaryata ya kuma kangare.
ثُمَّ أَدۡبَرَ يَسۡعَىٰ
Open ayah 79:22Sannan ya ba da baya yana ta gaggawa.
فَحَشَرَ فَنَادَىٰ
Open ayah 79:23Sai ya tattara (jama’arsa) sai ya yi shela.
فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلۡأَعۡلَىٰ
Open ayah 79:24Sai ya ce, “Ni ne ubangijinku mafi girma!”
فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلۡأٓخِرَةِ وَٱلۡأُولَىٰٓ
Open ayah 79:25Saboda haka Allah Ya kama shi da azabar lahira (watau Jahannama) da ta duniya (watau nutse wa a ruwa).
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّمَن يَخۡشَىٰٓ
Open ayah 79:26Lalle a game da wannan tabbas akwai izina ga wanda yake tsoron (Allah). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Manzonsa (ﷺ) labarin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yayin da ya aike shi zuwa ga Fir’auna da jama’arsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi Manzonsa (ﷺ) cewa, shin labarin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo masa tare da babban maƙiyinsa Fir’auna lokacin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kirawo shi ya yi magana da shi a kwarin Ɗuwa mai tsarki? Watau wani wuri ne kusa Dutsen Ɗuri, inda Allah ya ba shi manzanci ya kuma umarce shi da ya tunkari Fir’auna Sarkin Misra, domin kuwa ya ƙetare duk wasu iyakokin Allah, ya kuma shimfiɗa mulki na zalunci a kan Banu Isra’ila. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya yi wa Fir’auna tayin ko zai tsarkaka cikin tausasan kalmomi na hikima, ya yi watsi da aikata kafirci da zalunci ya musulunta, shi kuma Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiryar da shi zuwa sanin Ubangijinsa mahaliccinsa, don ya sami tsoronsa ya aikata abin da zai jawo masa yardarsa ya guji duk abin da zai sa ya yi fushi da shi. Amma sai Fir’auna ya bijire wa tayin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi masa. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) nan take ya nuna wa Fir’auna mafi girman ayoyinsa masu nuna lalle shi Manzon Allah ne, watau ya nuna masa hannunsa mai haske kamar fitila ba tare da wata cuta ba da kuma sandarsa mai rikiɗa ta zama macijiya. Amma Fir’auna bai yi wata-wata ba sai ya ƙaryata waɗannan ayoyin, ya bijire wa yin imani da gaskiyar da Annabi Musa ya zo masa da ita. Bai ma tsaya iya nan ba, sai da ya shiga tattara rundunoninsa don faɗa da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya yi shela cikin jama’arsa da cewa, shi ne ubangijinsu mafi girma, don haka kada su yi wa kowa biyayya sai shi kaɗai. Sai kuwa mutanen Fir’auna suka yarda suka bi shi a kan ɓatansa, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya damƙe shi da uƙubar farko ta nan duniya ya nutsar da shi a cikin ruwa, da kuma uƙubar ƙarshe yayin da zai shigar da shi mafi tsananin azabar wuta a lahira. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a cikin irin wannan uƙuba da ya yi wa Fir’auna da mutanensa akwai izina da wa’azi ga wanda yake tsoron Allah.
ءَأَنتُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُۚ بَنَىٰهَا
Open ayah 79:27Yanzu ku ne halittarku ta fi tsanani ko kuwa sama wadda Shi ne Ya gina ta?
رَفَعَ سَمۡكَهَا فَسَوَّىٰهَا
Open ayah 79:28Ya ɗaukaka rufinta Ya kuma daidaita ta.
وَأَغۡطَشَ لَيۡلَهَا وَأَخۡرَجَ ضُحَىٰهَا
Open ayah 79:29Ya lulluɓe darenta da duhu Ya kuma fitar da hasken hantsinta.
وَٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ
Open ayah 79:30Ƙasa kuma bayan haka Ya shimfiɗa ta.
أَخۡرَجَ مِنۡهَا مَآءَهَا وَمَرۡعَىٰهَا
Open ayah 79:31Ya fitar da ruwanta da makiyayarta daga gare ta.
وَٱلۡجِبَالَ أَرۡسَىٰهَا
Open ayah 79:32Duwatsu kuma Ya kafa su.
مَتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ
Open ayah 79:33Don jin daɗinku da na dabbobinku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kafa wa mushirikai masu ƙaryata tashin alƙiyama wata ƙaƙƙarfar hujja ta hankali, inda ya tambaye su cewa, wai shin halittarsu ce ta fi ba da wahala ko kuma halittar sama wadda Allah ne ya gina ta da cikar Ƙudurarsa? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ɗaukaka rufinta sama sannan ya daidaita ta babu wata ɓaraka ko tsagewa ko wani aibi a tare da ita. Sannan kuma idan rana ta faɗi sai ya sanya darenta ya yi duhu ko’ina a bayan ƙasa, kuma idan rana ta hudo da hantsi sai ko’ina ya yi haske. Kuma bayan ya gama halittar sama sai ya dawo ya shimfiɗa ƙasa ya sanya mata ababan amfaninta waɗanda suka haɗa da ruwa da ya fitar da idanuwansu masu kwarara a bayan ƙasa, ya fitar da tsirrai waɗanda dabbobi suke ci a wuraren kiwonsu. Duwatsu kuwa ya kafa su a cikinta, don kada ta riƙa tangal-tangal da na bayanta. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa mutane cewa, duk waɗannan ababan amfani ne gare su da dabbobinsu. Don haka wanda ya ƙagi irin waɗannan halittu, ai sake dawo musu da ransu bayan sun mutu ba abu ne da zai gagare shi ba.
فَإِذَا جَآءَتِ ٱلطَّآمَّةُ ٱلۡكُبۡرَىٰ
Open ayah 79:34Sannan idan mafi girman busar ƙaho ta zo (watau busa ta biyu).
يَوۡمَ يَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا سَعَىٰ
Open ayah 79:35A ranar da mutum zai tuna abin da ya aikata.
وَبُرِّزَتِ ٱلۡجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ
Open ayah 79:36Aka kuma bayyana (wutar) Jahimu ga kowane mai gani.
فَأَمَّا مَن طَغَىٰ
Open ayah 79:37To (a wannan ranar) duk wanda ya yi ɗagawa.
وَءَاثَرَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا
Open ayah 79:38Ya kuma fifita rayuwar duniya.
فَإِنَّ ٱلۡجَحِيمَ هِيَ ٱلۡمَأۡوَىٰ
Open ayah 79:39To lalle (wutar) Jahimu ita ce makoma.
وَأَمَّا مَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفۡسَ عَنِ ٱلۡهَوَىٰ
Open ayah 79:40Duk wanda kuma ya ji tsoron tsayuwa gaban Ubangijinsa, ya kuma hana zuciya bin abin da take so.
فَإِنَّ ٱلۡجَنَّةَ هِيَ ٱلۡمَأۡوَىٰ
Open ayah 79:41To lalle Aljanna ita ce makoma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi mushirikai masu ƙaryata tashin alƙiyama da su kiyayi ranar da za su yi nadama kuma nadamarsu ba za ta yi musu amfanin komai ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, idan har busar ƙaho ta biyu ta zo wadda tsoron da ke cikinta zai mamaye komai, to alƙiyama ta tsaya ke nan, kuma a ranar ne mutum zai tuna duk abin da ya aikata a duniya mai kyau da mummuna, a kuma bayyanar da wutar Jahannama a sarari don kowa ya gan ta tana jiran ta karɓi ‘ya’yanta. A nan ne mutane za su kasu kashi biyu: Duk wanda ya ƙetare iyakokin Allah da kafirci da saɓo, ya kuma fifita rayuwar duniya mai ƙarewa a kan rayuwar lahira mai wanzuwa, to wannan wutar Jahannama ce makomarsa. Amma kuma wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaban Ubangijinsa, ya hana ransa bin son zuciyarsa, to wannan Aljanna ce makomarsa.
يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرۡسَىٰهَا
Open ayah 79:42Suna tambayar ka game da alƙiyama, yaushe ne lokacinta?
فِيمَ أَنتَ مِن ذِكۡرَىٰهَآ
Open ayah 79:43Me ya gama ka da ambaton lokacinta?
إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَآ
Open ayah 79:44Zuwa ga Ubangijinka ne iyakacin saninta yake.
إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخۡشَىٰهَا
Open ayah 79:45Kai dai kawai mai gargaɗin wanda yake tsoron ta ne.
كَأَنَّهُمۡ يَوۡمَ يَرَوۡنَهَا لَمۡ يَلۡبَثُوٓاْ إِلَّا عَشِيَّةً أَوۡ ضُحَىٰهَا
Open ayah 79:46Kai ka ce su ranar da za su gan ta ba su zauna ba (a duniya) face wani yammaci ko kuma hantsinta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda mushirikai masu ƙaryata zuwan ranar alƙiyama suka matsa wa Manzon Allah (ﷺ) da tambayar ƙwaƙwa game da takamaiman lokacin zuwanta da nufin su ƙure shi, ba wai don su gamsu su yi imani ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa, babu abin da ya haɗa Manzonsa (ﷺ) da sanin takamaiman lokacin alƙiyama, domin ba wannan ne aikin da aka ɗora masa ba; ilimin sanin haka yana ga Allah (Mai tsarki da daukaka) shi kaɗai bai kuma sanar da kowa shi ba. Shi Manzon Allah (ﷺ) aikinsa shi ne kawai ya gargaɗi duk wanda yake tsoron ranar tashin alƙiyama domin shi ne zai amfana da gargaɗinsa. Su kuwa mushirikai masu ƙaryata ta duk ranar da za su gan ta, za su ga kamar ma ba su rayu a duniya ba sai gwargwadon yini ɗaya kacal ko hantsin yini guda, watau farkonsa.