عبس
Abasa
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
عَبَسَ وَتَوَلَّىٰٓ
Open ayah 80:1Ya ɗaure fuska, ya kuma ba da baya.
أَن جَآءَهُ ٱلۡأَعۡمَىٰ
Open ayah 80:2Don makaho ya zo masa.
وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّهُۥ يَزَّكَّىٰٓ
Open ayah 80:3Me kuma zai sanar da kai cewa wataƙila shi ne zai tsarkaka?
أَوۡ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ ٱلذِّكۡرَىٰٓ
Open ayah 80:4Ko ya wa’azantu, sai wa’azin ya amfane shi?
أَمَّا مَنِ ٱسۡتَغۡنَىٰ
Open ayah 80:5Amma wanda ya wadatu (daga wa’azinka).
فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ
Open ayah 80:6To kai shi kake fuskanta.
وَمَا عَلَيۡكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ
Open ayah 80:7Babu kuwa komai a kanka don ya ƙi ya tsarkaka
وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسۡعَىٰ
Open ayah 80:8Amma kuma wanda ya zo maka yana sauri.
وَهُوَ يَخۡشَىٰ
Open ayah 80:9Alhali kuma shi yana tsoron (Allah).
فَأَنتَ عَنۡهُ تَلَهَّىٰ
Open ayah 80:10To kai shi kake kawar wa da kai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da labarin Annabi (ﷺ) tare da Abdullahi ɗan Ummu Maktum wanda ya kasance makaho ne kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka shiga Musulunci tun a Makka, suka kuma yi hijira zuwa Madina. Ya zo wurin Manzon Allah (ﷺ) yana yi masa tambaya don ya ƙaru da sanin hukunce-hukuncen addininsa, shi kuma Annabi (ﷺ) hankalinsa yana kan shuwagabannin Ƙuraishawa waɗanda yake ƙoƙarin janyo hankulansu zuwa ga Musulunci. Da Ibnu Ummi Maktum (Allah ya kara masa yarda) ya matsa wa Annabi (ﷺ) da tambaya sai shi kuma ya ɓata fuskarsa ya kawar da kansa daga gare shi, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan Surar yana zargin sa (ﷺ) cewa, ya murtuke fuskarsa ya juya baya domin makaho Abdullahi ɗan Ummu Maktum (Allah ya kara masa yarda) ya zo yana tambayar sa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi Manzonsa (ﷺ) cewa, me ya ya sanar da shi cewa, wala’alla wannan makahon da ya haɗe wa fuska ya juya masa baya zai tsarkaka daga zunubansa a dalilin wa’azinsa da karantarwarsa, ko ya amfana da abin da zai ji na wa’azi nan gaba? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, amma wanda Manzon Allah (ﷺ) yake ganin ya wadatu da dukiyarsa ba ya buƙatar wani wa’azi, me zai sa ya fuskance shi har ya raja’a a kansa? Kuma me zai sami Manzo (ﷺ) idan wannan mutum ya ƙi tsarkaka daga laifukansa ya ƙi ya tuba zuwa ga Allah? Watau babu wata cutuwa da za ta same shi don waɗannan manyan kafiran sun ƙi karɓar Musulunci. To amma dangane da shi Abdullahi ɗan Ummi Maktum (Allah ya kara masa yarda) da ya zo masa yana gaggawa yana son ya ƙaru da wani alheri, kuma yana tsoron Ubangiji, me zai sa shi Manzo (ﷺ) zai shagala da wasu mushirikai ya ƙyale shi?
كَلَّآ إِنَّهَا تَذۡكِرَةٞ
Open ayah 80:11Abin ba haka yake ba, lalle (wannan da\'awar) wa’azi ne.
فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ
Open ayah 80:12Don haka wanda ya ga dama ya wa’azantu.
فِي صُحُفٖ مُّكَرَّمَةٖ
Open ayah 80:13(Wannan Alƙur\'ani) yana cikin takardu ababan girmamawa.
مَّرۡفُوعَةٖ مُّطَهَّرَةِۭ
Open ayah 80:14Maɗaukaka, tsarkaka.
بِأَيۡدِي سَفَرَةٖ
Open ayah 80:15A hannayen jakadu (mala’iku).
كِرَامِۭ بَرَرَةٖ
Open ayah 80:16Manya masu biyayya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wa’azin da ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya yi wa bayinsa tunatarwa ce kawai ba wani abu ne daban ba, don haka wanda ya so sai ya wa’azantu da wannan tunatarwar ya yi aiki da abin da Alƙur’ani ya zo masa da shi, domin Alƙur’ani littafi ne mai girman daraja, wanda yake cikin takardu masu daraja a wurin wasu mala’iku maɗaukaka a kuma wani wuri maɗaukaki, abin tsarkakewa, duk wata najasa ba za ta taɓa su ba, kuma wannan Alƙura\'ani yana hannun wasu mala’iku jakadun Allah masu girma a wurin Ubangijinsu, masu yawan aikata alheri da biyayya ga Allah. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda duk ya zamanto gwani ne wajen karatun Alƙur’ani to yana tare da mala’iku jakadu masu girma, masu biyayya. Wanda kuwa yake shan wahala wajen karatun Alƙur’ani, to yana da lada biyu.” [Bukhari #4937 da Muslim #798].
قُتِلَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَآ أَكۡفَرَهُۥ
Open ayah 80:17An la’anci mutum, me ya kai tsananin kafircinsa!
مِنۡ أَيِّ شَيۡءٍ خَلَقَهُۥ
Open ayah 80:18Shin daga wane abu ne (Allah) Ya halicce shi?
مِن نُّطۡفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ
Open ayah 80:19Daga maniyyi ne Ya halicce shi, sannan Ya ƙaddara shi (matakai a halitta).
ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ
Open ayah 80:20Sannan tafarki (na rayuwa) Ya hore masa shi.
ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقۡبَرَهُۥ
Open ayah 80:21Sannan Ya kashe shi, sai Ya sa shi cikin ƙabarinsa.
ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ
Open ayah 80:22Sannan in Ya ga dama Ya tashe shi.
كَلَّا لَمَّا يَقۡضِ مَآ أَمَرَهُۥ
Open ayah 80:23Fafau (zaton mutum) ba haka ne ba, har yanzu bai aikata abin da (Allah) Ya umarce shi ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi ɗan’adam wanda dukiyarsa da ruɗin duniya suka ruɗe shi suka sanya shi girman kai, har ya butulce wa Allah mahaliccinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya la’anci kafiri, wanda saboda tsananin kafircinsa ga Allah ya zama wani abin mamaki, domin ya manta da wane abu ne Allah ya halicce shi har yake yi masa girman kai a bayan ƙasa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da shi cewa, ya halicce shi ne fa daga wani wulaƙantaccen ruwa, watau ɗigon maniyyi wanda aka sanya shi a cikin mahaifiyarsa Allah kuma ya ƙaddara halittarsa mataki-mataki har ya gama cika masa halittarsa, sannan ya hore masa hanyar fitowa daga cikin mahaifiyarsa zuwa duniya, ya ƙayyade masa iya rayuwar da zai yi a duniya, da zarar ajalinsa ya zo kuma ya karɓi ransa, ya sanya shi a ƙabarinsa wanda zai yi ta zama a cikinsa har zuwa lokacin tashinsa, domin yi masa hisabi da sakamako a bisa yadda Allah mahaliccinsa ya ga dama. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da kafiri cewa, al’amarin ba kamar yadda yake zato ne ba na ganin kamar ya sauke haƙƙoƙin Allah da suke kansa, ko kusa, sam bai aikata abin da Allah ya wajabta masa ba na farillai. Har yanzu nauyi yana nan a kansa, sai kuma an tambaye shi a kai ranar alƙiyama.
فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ
Open ayah 80:24To mutum ya yi duba zuwa ga abincinsa mana?
أَنَّا صَبَبۡنَا ٱلۡمَآءَ صَبّٗا
Open ayah 80:25Cewa lalle Mu Muka zubo da ruwan sama zubowa.
ثُمَّ شَقَقۡنَا ٱلۡأَرۡضَ شَقّٗا
Open ayah 80:26Sannan Muka tsaga ƙasa tsagawa.
فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا حَبّٗا
Open ayah 80:27Sai Muka tsiro da ƙwaya daga cikinta.
وَعِنَبٗا وَقَضۡبٗا
Open ayah 80:28Da inabai da ciyayi.
وَزَيۡتُونٗا وَنَخۡلٗا
Open ayah 80:29Da zaitun da dabino.
وَحَدَآئِقَ غُلۡبٗا
Open ayah 80:30Da gonaki cike da itatuwa.
وَفَٰكِهَةٗ وَأَبّٗا
Open ayah 80:31Da kayan marmari da makiyaya.
مَّتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ
Open ayah 80:32Don jin daɗinku da na dabbobinku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin ɗan’adam ne a kan ya duba ni’imomin da ya yi masa waɗanda suke nuna cikar Ƙudurarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mutum da ya dubi abincinsa da yake ci, ƙaƙa ya samu? Ya tabbatar masa cewa, asalinsa daga ruwan sama ne mai zuba da yawa da ƙarfi, sannan Allah ya tsaga ƙasa ya fito da tsirran cikinta, waɗanda suka haɗa da masu ƙwaya kamar alkama da masara da danginsu, ya kuma fitar da inabi da abincin dabbobi da zaitun da dabino, ya fitar da gonaki masu cike da bishiyoyi iri-iri da kayan marmari da abin da dabbobinsu za su ci yayin kiwonsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu duk waɗannan ni’imomi ne domin jin daɗinsu da na dabbobinsu waɗanda su ma ya halicce su ne ya hore musu su don amfaninsu.
فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ
Open ayah 80:33Sannan idan mai sa kurunta ta zo (watau busa ta farko).
يَوۡمَ يَفِرُّ ٱلۡمَرۡءُ مِنۡ أَخِيهِ
Open ayah 80:34A ranar da mutum yake guje wa ɗan’uwansa.
وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ
Open ayah 80:35Da uwarsa da ubansa.
وَصَٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ
Open ayah 80:36Da matarsa da ‘ya’yansa.
لِكُلِّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ يَوۡمَئِذٖ شَأۡنٞ يُغۡنِيهِ
Open ayah 80:37Kowane mutum daga cikinsu a wannan ranar yana da lamarin da ya sha kansa.
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ مُّسۡفِرَةٞ
Open ayah 80:38Wasu fuskoki a wannan ranar masu haske ne.
ضَاحِكَةٞ مُّسۡتَبۡشِرَةٞ
Open ayah 80:39Masu dariya, masu farin ciki.
وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ عَلَيۡهَا غَبَرَةٞ
Open ayah 80:40Wasu fuskokin kuma a ranar akwai ƙura a kansu.
تَرۡهَقُهَا قَتَرَةٌ
Open ayah 80:41Baƙin ciki zai lulluɓe su.
أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَفَرَةُ ٱلۡفَجَرَةُ
Open ayah 80:42Waɗannan su ne kafirai maɓarnata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar da cewa, ba makawa sai an tashi aƙliyama, don haka idan aka yi busa ta biyu mai tsananin ƙarfi da za ta kurumtar da kunnuwa saboda tsananin ƙararta, to a wannan ranar ne mutum zai guje wa ɗan’uwansa da mahaifinsa da mahaifiyarsa da matarsa da ‘ya’yansa, domin kowa a wannan ranar al’amarinsa ya ishe shi, saboda tsananin tsoro da firgici. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Za a tattara ku (ranar alƙiyama) babu takalmi, tsirara, masu loɓa.” Sai wata daga cikin matansa ta ce: “Shin muna kallon al’aurar junanmu?” Sai ya ce: “Ya wance, (Kowane mutum daga cikinsu a wannan ranar yana da lamarin da ya ishe shi .)” [Tirmizi #3622]. An karɓo daga Saudatu ‘yar Zam’ah (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Za a tashi mutane marasa takalma, tsirara masu loɓa, gumi zai zo musu iya wuya, ya kai har fatun kunnuwansu.” Sai ta ce: Sai na ce: Ya Manzon Allah, na shiga uku! Za mu riƙa kallon junanmu? Sai ya ce: “Mutane ba ta wannan suke yi ba.” Sai ya karanta faɗar Allah: “Kowane mutum daga cikinsu a wannan ranar yana da lamarin da ya ishe shi .” [Alhakim #3898]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mutane a ranar za su kasu kashi biyu: <b>Kashi na farko, </b> ‘yan <b> </b>Aljanna waɗanda fuskokinsu za su yi ta haske suna masu dariya, cike da farin ciki saboda ganin tanadin rahama da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu. <b>Na biyu, </b> su ne ‘yan wuta waɗanda fuskokinsu za su yi ɓutu-ɓutu da ƙura, duhu ya lulluɓe su ta ko’ina, sun ɗebe ƙaunar samun rahamar Allah (Mai tsarki da daukaka). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan su ne suka haɗa siffar kafirci da fajirci, watau suka kafirce wa Allah da ni’imominsa, suka kuma keta iyakokinsa da ayyukan saɓonsa.