التكوير

At-Takwir

The Overthrowing · Surah 81 · Ayahs: 29 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ

    Open ayah 81:1

    Idan rana aka naɗe ta.

  2. وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتۡ

    Open ayah 81:2

    Idan kuma taurari suka farfaɗo.

  3. وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ سُيِّرَتۡ

    Open ayah 81:3

    Idan kuma duwatsu aka tafiyar da su.

  4. وَإِذَا ٱلۡعِشَارُ عُطِّلَتۡ

    Open ayah 81:4

    Idan kuma raƙuma masu ciki aka bar su ba makiyayi.

  5. وَإِذَا ٱلۡوُحُوشُ حُشِرَتۡ

    Open ayah 81:5

    Idan kuma namun daji aka tattara su.

  6. وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ سُجِّرَتۡ

    Open ayah 81:6

    Idan kuma koguna aka rura su (suka zama wuta).

  7. وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتۡ

    Open ayah 81:7

    Idan kuma rayuka aka haɗa su (da jinsinsu).

  8. وَإِذَا ٱلۡمَوۡءُۥدَةُ سُئِلَتۡ

    Open ayah 81:8

    Idan kuma yarinyar da aka binne da rai aka tambaye ta.

  9. بِأَيِّ ذَنۢبٖ قُتِلَتۡ

    Open ayah 81:9

    Da wane laifi ne aka kashe ta?

  10. وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ 

    Open ayah 81:10

    Idan kuma takardun (ayyuka) aka baza su.

  11. وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتۡ

    Open ayah 81:11

    Idan kuma sama aka ɗaye ta.

  12. وَإِذَا ٱلۡجَحِيمُ سُعِّرَتۡ

    Open ayah 81:12

    Idan kuma wutar Jahimu aka hura ta.

  13. وَإِذَا ٱلۡجَنَّةُ أُزۡلِفَتۡ

    Open ayah 81:13

    Idan kuma Aljanna aka kusanto da ita.

  14. عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّآ أَحۡضَرَتۡ

    Open ayah 81:14

    To kowane rai ya san abin da ya halarto (da shi na ayyuka). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da bayanin wasu manyan abubuwan ban tsoro shida da za su faru gabanin tashin alƙiyama, da kuma wasu shida da za su auku bayan tashinta. <b>Na farko, </b> shi ne lokacin da za a tattara rana da wata wuri guda a tafiyar da haskensu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Rana da wata za a naɗe kowannensu a ranar alƙiyama.” [Bukhari #3200]. <b>Na biyu, </b> su kuma taurari idan suka warwatse haskensu ya bice. <b>Na uku, </b> idan su kuma duwatsu aka matsar da su daga wurarensu, watau aka dandaƙe su suka zama kamar rairayi ko ƙura abar ɗaiɗaitawa. <b>Na huɗu, </b> idan raƙuma masu ciki aka watsar da su babu mai kula da su duk da irin darajarsu a idon makiyaya. <b>Na biyar, </b> idan namun daji aka tattara su wuri guda tare da ‘yan’adam. <b>Na shida, </b> idan koguna aka rura su suka zama wuta. Sannan ya ambaci abubuwa shida waɗanda za su biyo bayan tashin alƙiyama. <b>Na farko, </b>idan aka haɗa rayuka da jinsinsu, watau aka haɗa fajirai wuri guda, mutanen kirki wuri guda. <b>Na biyu, </b>idan yarinyar da aka binne ta da rai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye ta, da wane laifi ne mai kisan ta ya kashe ta ? Su ne yara mata da iyayensu suka riƙa binne su da rai a zamanin jahiliyya kafin zuwan Musulunci, wai don tsoron talauci ko gudun su jawo musu abin kunya. <b>Na uku, </b>idan aka baza takardun ayyukan bayi don kowa ya karanta takardarsa da kansa. <b>Na huɗu, </b>idan aka ɗaye sama kamar yadda ake feɗe fata daga jikin dabba. <b>Na biyar, </b>idan aka rura wutar Jahima ruruwar da ba ta taɓa yin irinta ba. <b>Na shida, </b> idan aka matso da Aljanna dab da masu taƙawa. To idan waɗannan abubuwan guda goma sha biyu suka faru, a lokacin kowane rai zai san ayyukan da ya gabatar a baya domin wannan ranar.

  15. فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلۡخُنَّسِ

    Open ayah 81:15

    To ina rantsuwa da taurari masu ɓuya.

  16. ٱلۡجَوَارِ ٱلۡكُنَّسِ

    Open ayah 81:16

    Masu gudu zuwa masaukansu.

  17. وَٱلَّيۡلِ إِذَا عَسۡعَسَ

    Open ayah 81:17

    Da kuma dare idan ya yi duhu.

  18. وَٱلصُّبۡحِ إِذَا تَنَفَّسَ

    Open ayah 81:18

    Da kuma asuba idan ta keto.

  19. إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ

    Open ayah 81:19

    Lalle shi (Alƙur’ani) magana ce ta Manzo mai karamci.

  20. ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي ٱلۡعَرۡشِ مَكِينٖ 

    Open ayah 81:20

    Ma’abocin ƙarfi a wurin Mai Al’arshi, kuma mai babban matsayi.

  21. مُّطَاعٖ ثَمَّ أَمِينٖ

    Open ayah 81:21

    Wanda ake yi wa biyayya ne a can (sama), amintacce.

  22. وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجۡنُونٖ

    Open ayah 81:22

    Mutumin naku kuma (watau Ma’aiki) ba mahaukaci ba ne.

  23. وَلَقَدۡ رَءَاهُ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡمُبِينِ

    Open ayah 81:23

    Haƙiƙa kuma ya gan shi a sararin sama mabayyani.

  24. وَمَا هُوَ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ بِضَنِينٖ

    Open ayah 81:24

    Shi kuma ba mai rowa ba ne game da wahayi.

  25. وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٖ

    Open ayah 81:25

    Kuma shi (Alƙur’ani) ba zancen Shaiɗan ne la’ananne ba.

  26. فَأَيۡنَ تَذۡهَبُونَ

    Open ayah 81:26

    To ina za ku dosa ne?

  27. إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 81:27

    Shi ba wani abu ba ne sai wa’azi ga talikai.

  28. لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَسۡتَقِيمَ

    Open ayah 81:28

    Ga wanda ya ga dama daga cikinku ya bi hanya madaidaiciya.

  29. وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 81:29

    Ku kuma ba za ku iya ganin dama ba sai Allah Ubangijin talikai Ya ga dama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, Alƙur’ani maganarsa ce wadda ya yiwo wahayinta ga Annabi Muhammadu (ﷺ). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da taurari masu ɓuya kafin su bayyana da daddare, masu gudu a cikin falaƙinsu suna ɓuya lokacin hudowar hasken asuba, kamar yadda gada take ɓoyewa a cikin gidanta. Ya kuma yi rantsuwa da farkon dare lokacin da ya fuskanto, da ƙarshensa lokacin da ya ba da baya. Ya kuma yi rantsuwa da asuba yayin da haskensa ya bayyana. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi waɗannan rantse-rantse ne domin ya tabbatar da cewa, lalle Alƙur’ani da aka saukar wa Annabi Muhammadu (ﷺ) maganar Allah ce da wani amintaccen mala’ika ya isar masa da ita, watau Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amince masa ya isar wa da Manzonsa (ﷺ) zancensa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa, ma’abocin ƙarfi ne, kuma mai babban matsayi ne a wurin Ubangijin Al’arshi, watau Allah (Mai tsarki da daukaka). Kuma mala’iku a sama suna yi masa ɗa’a, kuma an aminta da shi game da saƙon wahayi da yake saukowa da shi ga Annabi (ﷺ). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffar Annabi (ﷺ) da aka saukar wa Alƙur’ani, ya tabbatar wa mushirikai cewa, shi Manzon Allah (ﷺ) ne ba mahaukaci ba ne kamar yadda suke riyawa, domin sun san shi sarai sun kuma san hankalinsa da nutsuwarsa da gaskiyarsa da amanarsa. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ga Mala\'ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a sararin samaniya mabayyani, kuma a cikin surarsa da Allah ya halicce shi da ita, don haka ya san mai kawo masa wahayi sarai babu wanda zai yi masa basaja. Kuma shi Manzon Allah (ﷺ) ba mai yi musu rowar abin da aka yiwo masa wahayinsa ba ne, yana isar musu da saƙon da aka umarce shi ya isar musu, kuma ba ya karɓar wani lada a wurinsu kamar yadda bokaye suke karɓa. Sannan Allah ya sake tabbatar musu cewa, Alƙur’ani ba zancen Shaiɗani ne la’ananne ba wanda aka riga aka kore shi daga rahamar Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi mushirikai cewa, ina kuma suka dosa ne wajen ci gaba da ƙaryata cewa Alƙur’ani daga Allah ne bayan sun ji wannan ƙwararan hujjoji? Ya sake tabbatar musu cewa, Alƙur’ani ba wani abu ba ne sai wa’azi da tunatarwa ga talikai, mutane da aljannu, ga wanda ya ga dama daga cikinsu ya bi hanya madaidaiciya, ya rungumi gaskiya. To amma su sani cewa ba duk abin da suka ga dama mai kyau ko mummuna ne zai auku ba sai Allah Ubangijin talikai ya ga damar aukuwarsa sannan zai auku.