الإنفطار

Al-Infitaar

The Cleaving · Surah 82 · Ayahs: 19 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتۡ

    Open ayah 82:1

    Idan sama ta tsattsage.

  2. وَإِذَا ٱلۡكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتۡ

    Open ayah 82:2

    Idan kuma taurari suka farfaɗo suka tarwatse.

  3. وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ فُجِّرَتۡ

    Open ayah 82:3

    Idan kuma koguna aka harhaɗe su.

  4. وَإِذَا ٱلۡقُبُورُ بُعۡثِرَتۡ

    Open ayah 82:4

    Idan kuma ƙaburbura aka fito da matattun da ke cikinsu.

  5. عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّا قَدَّمَتۡ وَأَخَّرَتۡ

    Open ayah 82:5

    Kowane rai ya san abin da ya gabatar da wanda ya jirkintar. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da ambaton wasu manyan al’amura huɗu da za su faru kafin tashin alƙiyama : <b>Na farko, </b> idan sama ta tsattsage domin saukar mala’iku. <b>Na biyu, </b> idan taurari suka farfaɗo, suka warwatse, watau haskensu da kyansu suka gushe. <b>Na uku, </b> idan koguna aka harhaɗe su da junansu, suka gauraya suka zama kogi ɗaya. <b>Na huɗu, </b> idan ƙaburbura aka bubbuɗe su aka fito da matattun cikinsu, aka tara su wuri ɗaya a gaban Allah domin yi musu hisabi. To a wannan lokaci kowane rai zai san ayyukan da ya yi a duniya da wanda ya jinkirtar bai aikata ba.

  6. يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡإِنسَٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلۡكَرِيمِ

    Open ayah 82:6

    Ya kai mutum, me ya ruɗe ka ne game da Ubangijinka Mai karamci?

  7. ٱلَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ

    Open ayah 82:7

    Wanda Ya halicce ka Ya kuma daidaita ka Ya miƙar da kai?

  8. فِيٓ أَيِّ صُورَةٖ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ

    Open ayah 82:8

    Ya harhaɗa ka cikin irin surar da Ya ga dama?

  9. كَلَّا بَلۡ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ

    Open ayah 82:9

    A\'a dai, kawai dai kuna ƙaryata ranar sakamako ne.

  10. وَإِنَّ عَلَيۡكُمۡ لَحَٰفِظِينَ 

    Open ayah 82:10

    Kuma lalle akwai masu kula da ku.

  11. كِرَامٗا كَٰتِبِينَ

    Open ayah 82:11

    Masu daraja marubuta.

  12. يَعۡلَمُونَ مَا تَفۡعَلُونَ

    Open ayah 82:12

    Suna sane da abin da kuke aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira ɗan\'adam ya ja hankalinsa game da sakacinsa wajen bautar Ubangijinsa, ya tambaye shi cewa, mene ne ya ruɗe shi game da Ubangijinsa mai karamci, har yake saɓa wa umarninsa, duk kuwa da ya saurara masa bai gaggauto masa da uƙuba ba? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa duk wani mai girman kai da saɓon sa cewa, ya sani Allah ne ya halicce shi bayan a da babu shi, sa’annan ya daidaita masa gaɓoɓinsa, ya miƙar masa da halittarsa ya yi matuƙar kyau. Sannan a duk cikin irin surar da ya ga damar halittar sa hakan ya halicce shi, watau ya lura da babbar ni’imar da ya yi masa yayin da bai yi masa irin halittar jaki ba ko ta biri ko ta kare. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsawatar wa kafirai masu ruɗuwa da duniya cewa, al’amarin ba kamar yadda suka ɗauka ba ne, suna dai kawai ƙaryata ranar sakamako ne, sun ƙi yin imani da zuwanta, amma su sani dole sai ta zo, an kuma yi musu hisabi a kan ayyukansu, domin kuwa koyaushe akwai mala’iku masana marubuta tare da su suna kiyaye dukkan ayyukansu, suna rubuta su ba tare da sun bar komai ba.

  13. إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٖ

    Open ayah 82:13

    Lalle mutanen kirki tabbas suna cikin ni’ima

  14. وَإِنَّ ٱلۡفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٖ

    Open ayah 82:14

    Lalle kuma fajirai tabbas suna cikin (wutar) Jahima.

  15. يَصۡلَوۡنَهَا يَوۡمَ ٱلدِّينِ

    Open ayah 82:15

    Za su ƙonu da ita ranar sakamako.

  16. وَمَا هُمۡ عَنۡهَا بِغَآئِبِينَ

    Open ayah 82:16

    Kuma su ba masu rabuwa ne da ita ba.

  17. وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ

    Open ayah 82:17

    Kuma kai me ya sanar da kai mece ce ranar sakamako?

  18. ثُمَّ مَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ

    Open ayah 82:18

    Sannan me ya sanar da kai mece ce ranar sakamako?

  19. يَوۡمَ لَا تَمۡلِكُ نَفۡسٞ لِّنَفۡسٖ شَيۡـٔٗاۖ وَٱلۡأَمۡرُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ

    Open ayah 82:19

    (Ita ce) ranar da wani rai ba ya mallakar wani amfani ga wani rai; al’amari kuwa (gaba ɗayansa) a wannan ranar yana ga Allah. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana karkasuwar mutane a lahira gida biyu ; mutanen kirki waɗanda suka kula da haƙƙoƙin Allah da haƙƙoƙin bayinsa, suka yawaita ayyukan alheri, to waɗannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar cewa lalle suna cikin ni’ima madawwamiya a ranar alƙiyama. Sai kuma fajirai waɗanda suka yi watsi da haƙƙoƙin Allah da na bayinsa, suka aikata munanan ayyuka, waɗannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, lalle suna cikin wutar Jahima, za su shige ta a ranar sakamako su ɗanɗani matsanancin zafinta; idan kuma sun riga sun shige ta, to ba za su taɓa barin ta ba har abada, za su dawwama ne a cikinta. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Manzonsa (ﷺ) girman wannan rana ta alƙiyama, yana mai nanata masa tambayar cewa, mene ne ya sanar da shi abin da ake kira ranar sakamako? Sai kuma ya amsa masa da kansa cewa, ita ce ranar da wani mutum ba zai iya amfanar da wani da komai ba; al’amura gaba ɗayansu a ranar ga Allah suke shi kaɗai; shi ne zai yi yadda ya ga dama da kowa, babu mai iya hana shi aikata abin da ya so.