المطففين
Al-Mutaffifin
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَيۡلٞ لِّلۡمُطَفِّفِينَ
Open ayah 83:1Tsananin azaba ya tabbata ga masu tauye ma’auni.
ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكۡتَالُواْ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسۡتَوۡفُونَ
Open ayah 83:2Waɗanda idan suka auna daga wajen mutane suna cikawa fal.
وَإِذَا كَالُوهُمۡ أَو وَّزَنُوهُمۡ يُخۡسِرُونَ
Open ayah 83:3Idan kuwa su za su aunar, da mudu ne ko da sikeli, to sai su tauye.
أَلَا يَظُنُّ أُوْلَٰٓئِكَ أَنَّهُم مَّبۡعُوثُونَ
Open ayah 83:4Yanzu waɗannan ba sa zaton cewa su lalle za a tashe su?
لِيَوۡمٍ عَظِيمٖ
Open ayah 83:5A wata rana mai girma?
يَوۡمَ يَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 83:6Ranar da mutane za su tsaya gaban Ubangijin talikai? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da kakkausan alƙawarin narko da azaba ga masu tauye ma’auni. Ya bayyana su da cewa, su ne waɗanda idan suka yi awo daga wasu sai sun cika ma’aunai fal, ba sa rage haƙƙinsu ko kaɗan. Amma kuma idan su ne za su auna wa mutane da mudu ko da sikeli sai su tauye musu haƙƙoƙinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin waɗannan mutane tare da tsoratarwa cewa, wai hala ba su tabbatar da cewa, za a tashe su ba a wata rana mai girma, watau ranar alƙiyama, ranar da duk mutane za su tsaya a gaban Ubangijin halittu domin yi musu hisabi da sakamako a kan ayyukansu? An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya umarci Siba’u ɗan Urfu (Allah ya kara masa yarda) ya kula da garin Madina yayin da ya fita zuwa Khaibara, sai Siba’u ya karanta wannan Surar, sai na ce (in ji Abu Huraira): “Wane kuwa ya hallaka, domin yana da sa’i biyu, ɗaya yana aunarwa da shi, ɗayan kuma yana auna da shi.” [Ahmad #8552 da Al-Hakim #2241 da Albazzar #8140]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda), ya karanta wannan ayar sai ya fashe da kuka ya ce: “Shi ne mutumin da zai ɗau wani aiki, ko wani mai yin awo alhalin ya san yana tauye wa mutane kayan awonsu, to laifinsa yana kan wanda ya ba shi aikin.” [Al-Hakim, juzu’i na 2, shafi na 517]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abubuwa biyar sakamako ne na abubuwa biyar.” Sahabbai suka ce: “Me ake nufi da abu biyar sakamakon abu biyar ne?” Sai ya ce: “Babu mutane da za su riƙa warware yarjejeniya sai an bai wa maƙiyansu nasara a kansu. Kuma ba za su koma yin hukunci da abin da ba shi Allah ya saukar ba sai talauci ya yaɗu a tsakaninsu. Kuma alfasha ba za ta bayyana a cikinsu ba sai mace-mace sun yaɗu a cikinsu. Ba kuma za su tauye ma’auni ba sai an hana musu amfanin gona an jarrabe su da fari. Ba za su kuma hana zakka ba sai an hana su ruwan sama.” [Aɗɗabrani #10992]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya karanta faɗar Allah: (Ranar da mutane za su tsaya a gaban Ubangijin talikai ) sai ya ce: “Har sai ɗayansu ya nutse a cikin guminsa wanda zai kai har daidai kunnuwansa.” [Bukhari #4938 da Muslim #2862].
كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٖ
Open ayah 83:7Tabbas, lalle littafin fajirai yana cikin Sijjinu .
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سِجِّينٞ
Open ayah 83:8Me kuma ya sanar da kai me ake ce wa Sijjinu ?.
كِتَٰبٞ مَّرۡقُومٞ
Open ayah 83:9Littafi ne rubutacce.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 83:10Tsananin azaba a wannan ranar ya tabbata ga masu ƙaryatawa.
ٱلَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ
Open ayah 83:11Waɗanda suke ƙaryata ranar sakamako.
وَمَا يُكَذِّبُ بِهِۦٓ إِلَّا كُلُّ مُعۡتَدٍ أَثِيمٍ
Open ayah 83:12Babu kuwa mai ƙaryata ta sai duk wani mai shisshigi mai yawan saɓo.
إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 83:13Idan ana karanta masa ayoyinmu sai ya ce: “Wannan tatsuniyoyi ne na mutanen farko.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa masu ƙaryata ranar alƙiyama cewa, abin ba kamar yadda suke tsammani ne ba, domin kuwa dukkan ayyukan bayi suna nan a rubuce, kuma tabbas littafin fajirai daga cikin kafirai da munafukai yana cikin Sijjinu , watau a can ƙarƙashin ƙasa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi Manzonsa (ﷺ) cewa, mene ne ya sanar da shi abin da ake kira Sijjinu ? Sai ya bayyana masa shi da cewa, wani rubutaccen littafi ne wanda ya ƙunshi cikakkun ayyukan fajirai cif-cif babu daɗi babu ragi.. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle bawa kafiri idan ya zo barin duniya zai fuskanci lahira, sai wasu mala’iku masu baƙaƙen fuskoki su sauko masa daga sama da wata algarara a tare da su, su zauna a gabansa iya ganinsa, sannan Mala’ikan mutuwa ya zo ya zauna daidai kansa sannan ya ce: “Ya kai wannan mummunan rai, ka fito zuwa ga hushin Ubangijinka” sai (ran) ya warwatsu a jikinsa, sai Mala’ikan mutuwa ya fizgo shi kamar yadda ake fizgo da ƙarfen gashin nama daga jiƙaƙƙen gashin dabbobi, sai ya cabke shi; yana cabkar sa, sauran mala\'ikun ba za su bar shi a hannunsa daidai da ƙiftawar ido ba har sai sun saka shi cikin wannan algararar, sai ya fito daga cikinta yana wari kamar mushen da ya fi kowane irin mushe wari a bayan ƙasa, sai su hau sama da shi, duk sanda suka wuce ta gaban wata jama’a ta mala’iku sai sun ce: “Wane mummunan rai ne wannan?” Sai su ce: “Wane ne ɗan wane.” Su kira shi da mafi munin sunan da ake kiran sa da shi a duniya, har sai sun isa sama ta farko da shi, sai a nemi a buɗe masa, sai a ƙi buɗe masa.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya karanta faɗar Allah: “Lalle waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu, kuma suka yi girman kai gare su, ba za a buɗe musu ƙofofin sama ba, ba kuma za su shiga Aljanna ba har sai raƙumi ya shige ta ƙofar allura .” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce: “Ku rubuta littafinsa a cikin Sijjinu , a can ƙasa ta ƙarshe.” Sai a jefo ransa ƙasa da ƙarfi….” [Ahmad #18534]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake jan kunnen masu ƙaryata ranar alƙiyama, ya yi musu alƙawarin narkon azaba da asara a wannan ranar da cewa, babu mai ƙaryata wannan ranar ta alƙiyama sai mutumin da ya zamanto mai yawan ƙetare iyakar Allah, mai yawan aikata laifuka; idan ana yi masa wa’azi ana karanta masa ayoyin Allah da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ) sai ya ƙaryata su, ya ma ce, duk tatsuniyoyin mutanen da ne ba daga Allah suke ba.
كَلَّاۖ بَلۡۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Open ayah 83:14A\'a, abin ai ba haka ba ne; abin da suke aikatawa ne ya yi tsatsa a zukatansu.
كَلَّآ إِنَّهُمۡ عَن رَّبِّهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّمَحۡجُوبُونَ
Open ayah 83:15Tabbas! Lalle su haƙiƙa ababan kangewa ne daga (ganin) Ubangijinsu a wannan rana.
ثُمَّ إِنَّهُمۡ لَصَالُواْ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 83:16Sannan kuma lalle su tabbas masu shiga wutar Jahimu ne.
ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Open ayah 83:17Sannan za a ce: “Wannan ne abin da kuka kasance kuna ƙaryata shi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tsawatar wa masu ƙaryata ranar alƙiyama, ya kuma tabbatar musu cewa, ba wani abu ne ya sanya su ƙaryatawa ba sai yawan laifukan da suke aikatawa, su ne suka toshe musu hankulansu don haka suka kasa ganin gaskiya da zukatansu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Haƙiƙa bawa idan ya yi wani zunubi sai a ɗiga wani baƙin ɗigo a kan zuciyarsa, idan ya tuba ya daina ya nemi gafarar Allah sai a goge masa zuciyarsa tas; idan kuwa ya koma ga wannan laifin sai wannan baƙin ɗigo ya daɗa ƙaruwa har sai ya lulluɓe zuciyarsa. Wannan ita ce tsatsar da Allah ya ambata a Alƙur’ani: “A’a, ba haka abin yake ba, abin da suke aikatawa ne ya yi tsatsa a kan zukatansu .” [Ahmad #7952 da Tirmizi #3624 da Ibn Maja #4244]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, a ranar alƙiyama ba su da wani matsayi a wurinsa, domin kuwa ba za a bari su gan shi ba, kamar yadda suka kasa ganin gaskiya a duniya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, lalle su masu shiga wutar Jahima ne, su ɗanɗani kuɗar zafinta, ana daka musu tsawa da cewa, wannan azabar da suke ɗanɗana ita ce abin da suka kasance a duniya suna ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) a kanta.
كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡأَبۡرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ
Open ayah 83:18Tabbas! Lalle littafin mutanen kirki haƙiƙa yana cikin Illiyyuna .
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ
Open ayah 83:19Me ya sanar da kai mene ne Iliyyuna ?
كِتَٰبٞ مَّرۡقُومٞ
Open ayah 83:20Wani littafi ne rubutacce.
يَشۡهَدُهُ ٱلۡمُقَرَّبُونَ
Open ayah 83:21(Mala’iku) makusanta suke halartar sa.
إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٍ
Open ayah 83:22Lalle masu biyayya tabbas suna cikin ni’ima.
عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ
Open ayah 83:23A kan gadaje suna kallo.
تَعۡرِفُ فِي وُجُوهِهِمۡ نَضۡرَةَ ٱلنَّعِيمِ
Open ayah 83:24Za ka gane hasken ni’ima a fuskokinsu.
يُسۡقَوۡنَ مِن رَّحِيقٖ مَّخۡتُومٍ
Open ayah 83:25Ana shayar da su giyar da aka rufe (bakin mazubinta).
خِتَٰمُهُۥ مِسۡكٞۚ وَفِي ذَٰلِكَ فَلۡيَتَنَافَسِ ٱلۡمُتَنَٰفِسُونَ
Open ayah 83:26(Har) ƙarshensa (ƙamshin) almiski ne. To game da wannan kuwa lalle masu gasa su yi gasa.
وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسۡنِيمٍ
Open ayah 83:27Mahaɗinsa kuma daga ruwan tasnimu yake.
عَيۡنٗا يَشۡرَبُ بِهَا ٱلۡمُقَرَّبُونَ
Open ayah 83:28Wani idon ruwa wanda bayi makusanta ne suke sha daga gare shi. <b> </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon mutanen kirki masu yi wa Allah ɗa’a da cewa, lalle littafin kyawawan ayyukansu yana cikin Illiyyuna , watau wani wuri mai ɗaukaka wanda ko shi Manzon Allah (ﷺ) kansa bai san shi ba, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana masa shi cewa wani rubutaccen littafi ne wanda aka tanada don rubuta kyawawan ayyukan muminai, ba a rage komai daga cikinsa ko a ƙara ba, kuma mala’iku makusanta ga Allah na kowace samaniya su ne suke halartar inda yake. An karɓo daga Bara’u ɗan Azib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Haƙiƙa bawa mumini yayin da ya zo barin duniya yana fuskantar lahira, sai wasu mala’iku masu fararen fuskoki su sauko masa daga sama, fuskokinsu suna haske kamar rana, suna ɗauke da likkafani na Aljanna da turare na Aljanna, sai su zauna a gabansa iya ganinsa, sannan Mala’ikan mutuwa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo ya zauna daidai kansa sai ya ce: “Ya kai wannan rai nutsattse, ka fito zuwa ga gafarar Allah da yardarsa.” Sai (ran) ya kwararo a hankali kamar yadda ruwa yake kwararowa daga bakin gora, sai Mala’ikan mutuwa ya kama shi, daga nan sauran mala’ikun ba za su bar shi a hannunsa daidai da ƙiftawar ido ba sai sun karɓe shi sun sanya shi cikin wannan likkafanin na Aljanna, sun kuma sanya masa wannan turaren. Sai ya fito yana ƙamshin turaren almiskin da ba a taɓa jin irinsa ba a duniya. Sai mala’ikun su hau sama da wannan rai, duk sa’adda suka wuce da shi ta gaban wani taron mala’iku sai su ce: “Wane rai ne mai ƙamshi haka?” Sai mala’ikun nan su ce: “Wane ne ɗan wane.” Su kira shi da mafi kyan sunan da ake kiran sa da shi a duniya, har sai sun isa sama ta farko, sai su nemi a buɗe masa, sai a buɗe musu; sai daga kowace samaniya mala’ikunta makusanta su raka shi zuwa sama ta gaba, har sai ya kai sama ta bakwai, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce: “Ku rubuta littafin bawana a cikin Illiyyuna , ku mayar da shi can ƙasa, domin ni daga ita na halicce su, kuma cikinta ne zan mayar da su, daga cikinta ne kuma zan sake tashin su karo na biyu.” [Ahmad #18534]. An karɓo daga Abu Umama (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Salla a bayan salla waɗanda babu yasasshiyar magana a tsakaninsu ana rubuta ta a cikin Illiyyuna .” [Abu Dawud #1288]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakonsu a ranar alƙiyama da cewa, lalle suna cikin ni’ima dawwamamma ta Aljanna, suna kan gadaje masu ado na alfarma, suna masu kallon Ubangijinsu tare da duk wani abin da zai faranta musu rai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da a ce Manzon Allah (ﷺ) zai gan su to da ya ga fuskokinsu suna sheƙi da annuri alamar jin daɗin da suke ciki. Sannan a gefe guda kuma ga hadimansu suna shayar da su cikakken kofi na giya wanda aka rufe bakinsa, ƙamshin turaren almiski yana fita daga gare shi har zuwa ƙarshensa ba zai daina ƙamshi ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zaburar da bayinsa da cewa, game da irin wannan babban sakamako ne ya wajaba masu gasa su yi gasa ta hanyar aikata abin da Allah yake so da barin abin da ba ya so. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara bayanin wannan rufaffen abin sha na ‘yan Aljanna da cewa, ana gauraya shi da wani ruwan marmaro da ake kira ‘Tasnim’ , shi kuma wani marmaro da yake can ƙololuwar Aljanna wanda bayin Allah mafiya kusanci da Allah suke shan sa tsantsa garai-garai babu haɗin komai a cikinsa, sauran muminai kuwa suna shan sa ne bayan an gauraya shi da wani abin shan daban.
إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْ كَانُواْ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يَضۡحَكُونَ
Open ayah 83:29Lalle waɗanda suka yi manyan laifuka sun kasance suna yi wa waɗanda suka yi imani dariya (a duniya).
وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمۡ يَتَغَامَزُونَ
Open ayah 83:30Kuma idan suka wuce ta wajensu sai su riƙa zunɗen su.
وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓاْ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمُ ٱنقَلَبُواْ فَكِهِينَ
Open ayah 83:31Idan kuma sun koma wurin iyalinsu sai su komo suna masu farin ciki.
وَإِذَا رَأَوۡهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ
Open ayah 83:32Kuma idan sun gan su sai su ce: “Lalle waɗannan ɓatattu ne.”
وَمَآ أُرۡسِلُواْ عَلَيۡهِمۡ حَٰفِظِينَ
Open ayah 83:33Ba a kuwa aiko su don su zama masu tsaron su ba.
فَٱلۡيَوۡمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنَ ٱلۡكُفَّارِ يَضۡحَكُونَ
Open ayah 83:34To a wannan rana ne waɗanda suka yi imani za su yi wa kafirai dariya.
عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ
Open ayah 83:35Daga kan gadaje suna kallo.
هَلۡ ثُوِّبَ ٱلۡكُفَّارُ مَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ
Open ayah 83:36Shin an saka wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafirai suka riƙa yi wa muminai izgili a duniya da yadda reshe zai juye da mujiya a lahira, watau su ma muminai su rama abin da kafirai suke yi musu a duniya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, lalle masu manyan laifuka, watau kafirai sun kasance suna yi wa muminai dariya da izgilanci a duniya, idan muminai suka zo wucewa ta gabansu sai su riƙa zunɗen su, suna nuna wa junansu su da idanu, idan suka koma gidajensu wurin iyalansu sai su koma cike da farin ciki game da izgili da dariya da suka yi wa muminai, suna ganin sun yi wata bajinta, suna kuma ganin su ne masu gaskiya a kan shiriya, don haka duk sanda suka ga Musulmi sai su ce ga ɓatattu nan, watau waɗanda suka saki addinin iyaye da kakanni suka kama wani sabon addini. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan shisshigi ne kawai kafirai suke yi masa da suke yin hukunci a kan wasu ba tare da wani ilimi ba, domin ba a aiko su don su zama masu tsaron ayyukan Musulmi ba har da za su riƙa faɗar wannan maganar. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakonsu a lahira lokacin da su kuma muminai za su riƙa yi musu dariya kamar yadda su suka yi wa muminai dariya a duniya. A lokacin muminai za su hango kafirai suna ɗanɗanar matsananciyar azaba a wutar Jahannama su kuma suna kishingiɗe a kan gadaje na alfarma suna kallon abin da Allah ya tanadar musu na ni’ima ta har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, an yi wa kafirai sakayya da azaba ta wulaƙanci game da abin da suka kasance suna aikatawa a duniya.