الإنشقاق

Al-Inshiqaaq

The Splitting Open · Surah 84 · Ayahs: 25 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتۡ

    Open ayah 84:1

    Idan sama ta tsattsage.

  2. وَأَذِنَتۡ لِرَبِّهَا وَحُقَّتۡ

    Open ayah 84:2

    Ta kuma saurari Ubangijinta, kuma ya wajaba (ta saurara).

  3. وَإِذَا ٱلۡأَرۡضُ مُدَّتۡ

    Open ayah 84:3

    Kuma idan ƙasa aka miƙe ta.

  4. وَأَلۡقَتۡ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتۡ

    Open ayah 84:4

    Ta kuma jefar da abin da yake cikinta ta wofinta.

  5. وَأَذِنَتۡ لِرَبِّهَا وَحُقَّتۡ

    Open ayah 84:5

    Ta kuma saurari Ubangijinta kuma ya wajaba (ta saurara).

  6. يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡإِنسَٰنُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدۡحٗا فَمُلَٰقِيهِ

    Open ayah 84:6

    Ya kai mutum, lalle kai mai yin aiki ne tuƙuru zuwa ga Ubangijinka, to mai haɗuwa da Shi ne

  7. فَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ

    Open ayah 84:7

    To amma duk wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na dama.

  8. فَسَوۡفَ يُحَاسَبُ حِسَابٗا يَسِيرٗا

    Open ayah 84:8

    To za a yi masa hisabi mai sauƙi.

  9. وَيَنقَلِبُ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ مَسۡرُورٗا

    Open ayah 84:9

    Ya kuma juyo zuwa ga iyalinsa yana farin ciki.

  10. وَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ وَرَآءَ ظَهۡرِهِۦ 

    Open ayah 84:10

    Amma wanda kuwa aka bai wa littafinsa ta bayan bayansa.

  11. فَسَوۡفَ يَدۡعُواْ ثُبُورٗا

    Open ayah 84:11

    To zai yi kiran halaka.

  12. وَيَصۡلَىٰ سَعِيرًا

    Open ayah 84:12

    Zai kuma shiga (wutar) Sa’ira.

  13. إِنَّهُۥ كَانَ فِيٓ أَهۡلِهِۦ مَسۡرُورًا

    Open ayah 84:13

    Lalle a da shi ya kasance mai farin ciki ne cikin iyalinsa.

  14. إِنَّهُۥ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ

    Open ayah 84:14

    Lalle ya yi zaton ba zai koma (ga Allah) ba.

  15. بَلَىٰٓۚ إِنَّ رَبَّهُۥ كَانَ بِهِۦ بَصِيرٗا

    Open ayah 84:15

    Haka yake, (zai koma), lalle Ubangijinsa Ya kasance Mai ganin sa ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da bayanin manyan abubuwan da za su auku lokacin tashin alƙiyama, yayin da sama za ta tsattsage mala’iku su yi ta saukowa, domin ta saurari umarnin Ubangijinta ta kuma miƙa wuya gare shi, kuma haka ne ya cancanci ta yi, domin a ƙarƙashin ikonsa take, shi ne wanda ba a saɓa wa umarninsa. Ita kuma ƙasa idan Allah ya miƙar da ita kamar yadda ake miƙar da fata; taskokin da ke cikinta da matattun da suke ƙarƙashinta duka ta fito da su waje, ta rabu da su, cikinta ya koma fayau babu sauran wani abu. A wannan lokaci ne ɗan’adam zai haɗu da Ubangijinsa domin yi masa hisabi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira ɗan’adam domin ya tabbatar masa da cewa, lalle shi mai aiki ne tuƙuru a nan duniya, ko dai aikin alheri ko nkuma a sharri, don haka shi mai haɗuwa ne da Ubangijinsa, don ya yi masa sakayya a kan ayyukansa masu kyau da munana. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon mutane a ranar alƙiyama gwargwadon ayyukansu da cewa, duk wanda aka ba shi littafin ayyukansa a hannunsa na dama, to wannan ya rabauta, kuma da sannu za a yi masa hisabi mai sauƙi ta hanyar bijiro ayyukansa a dunƙule ba tare da binciken ƙwaƙwaf ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya suturta masa laifukansa bayan ya yi iƙirari a gabansa, sai ya juya zuwa iyalansa a Aljanna yana mai farin ciki, domin ya kuɓuta daga azabar Allah ya samu babban rabo. Wanda kuwa aka ba shi littafin ayyukansa a hannunsa na hagu, ta bayan bayansa, to wannan zai dinga kira wa kansa hallaka, domin munin abin da ya gani rubuce a cikin littafinsa na miyagun laifukan da ya aikata a duniya bai tuba ba, kuma a ƙarshe zai shiga wutar Jahannama ya ɗanɗani matsanancin zafinta, domin kuwa tun a duniya sanda yake cikin iyalansa yana farin ciki da kafircinsa da saɓon Allah da yake aikatawa, ya kuma yi zaton ba za a dawo da shi da ransa bayan mutuwa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, lalle zai mayar da shi da ransa bayan mutuwarsa kamar yadda ya halicce shi da farko, domin Ubangijinsa yana ganin duk halin da yake ciki babu abin da yake ɓuya gare shi, zai kuma yi masa sakayya a kan aikinsa. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wanda za a yi wa hisabi ne ƙeƙe-da-ƙeƙe sai ya hallaka.” Sai na ce: “Shin ba Allah ne yake cewa ba: (To duk wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na dama, to za a yi masa hisabi mai sauƙi )?” Sai ya ce: “Wannan ba shi ne hisabin ba, wannan bijiro da ayyuka ne kawai, duk wanda za a yi masa hisabi na ƙwaƙwafi to ya hallaka.” [Bukhari #103 da Muslim #2876].

  16. فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلشَّفَقِ

    Open ayah 84:16

    To ina rantsuwa da shafaƙi.

  17. وَٱلَّيۡلِ وَمَا وَسَقَ

    Open ayah 84:17

    Da kuma dare da abin da ya tattara.

  18. وَٱلۡقَمَرِ إِذَا ٱتَّسَقَ

    Open ayah 84:18

    Da kuma wata idan ya cika.

  19. لَتَرۡكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٖ

    Open ayah 84:19

    Tabbas za ku hau wani mataki bayan wani mataki.

  20. فَمَا لَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ 

    Open ayah 84:20

    To me ya same su ne ba sa yin imani?

  21. وَإِذَا قُرِئَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقُرۡءَانُ لَا يَسۡجُدُونَۤ۩

    Open ayah 84:21

    Idan kuma an karanta musu Alƙur’ani ba sa yin sujjada?

  22. بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُكَذِّبُونَ

    Open ayah 84:22

    A’a, su dai waɗanda suka kafirce suna ƙaryatawa ne.

  23. وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا يُوعُونَ

    Open ayah 84:23

    Allah kuwa (Shi) Ya fi sanin abin da suke ɓoyewa (a zukatansu).

  24. فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

    Open ayah 84:24

    To ka yi musu albishir da azaba mai raɗaɗi.

  25. إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونِۭ

    Open ayah 84:25

    Sai dai waɗanda suka yi imani, suka kuma yi ayyuka nagari, to suna da lada marar yankewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da shafaƙi, watau jan da ke bayyana a sararin samaniya bayan faɗuwar rana kafin duhu ya yi. Ya kuma rantse da dare da abin da ya tattara a cikinsa, da wata idan ya cika girmansa ya yi haske. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da waɗannan manyan halittu nasa ne don ya tabbatar wa mutane cewa, tabbas sai sun hau wani mataki bayan mataki, watau na halittarsu, sai sun kasance ɗigon maniyyi sannan su zama gudan jini sannan gudar tsoka har zuwa cikar halittarsu sannan su zo duniya su rayu har kuma zuwa mutuwarsu, daga nan kuma a tashe su don yi musu hisabi. To wannan yanayi bayan yanayi da ɗan’adam yake shiga wata babbar hujja ce ta tabbatar da Kaɗaitakar Allah da isar Ƙudurarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai. To amma me ya samu kafirai ba sa yin imani da Kaɗaitakar Allah da ranar lahira, idan kuma aka karanta musu Alƙur’ani ba sa faɗuwa su yi wa Allah sujjada, su miƙa wuya ga umarninsa da haninsa? Maimakon haka sai dai su riƙa ƙaryata abin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo musu da shi. To su sani Allah ne mafi sanin abin da suke ɓoyewa a zukatansu, babu abin da bai sani ba na ayyukansu, don haka ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi musu albishir da azaba mai raɗaɗi da take tsumayin su a ranar lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, amma akwai waɗanda suka yi imani da shi suka yi aiki nagari, to waɗannan suna da wani babban sakamako marar yankewa, shi ne gidan Aljanna.