البروج
Al-Burooj
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلۡبُرُوجِ
Open ayah 85:1Na rantse da sama ma’abociyar manziloli.
وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡمَوۡعُودِ
Open ayah 85:2Da ranar da aka yi alƙawarin zuwanta.
وَشَاهِدٖ وَمَشۡهُودٖ
Open ayah 85:3Da mai shaida da kuma abin yi wa shaida.
قُتِلَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأُخۡدُودِ
Open ayah 85:4An la’anci ma’abota rami (na azabtar da muminai).
ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلۡوَقُودِ
Open ayah 85:5Na wuta mai ruruwa.
إِذۡ هُمۡ عَلَيۡهَا قُعُودٞ
Open ayah 85:6Yayin da suke zaune a gefenta.
وَهُمۡ عَلَىٰ مَا يَفۡعَلُونَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ شُهُودٞ
Open ayah 85:7Alhali su suna kallon abin da suke aikata wa muminai.
وَمَا نَقَمُواْ مِنۡهُمۡ إِلَّآ أَن يُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ
Open ayah 85:8Babu kuwa abin da suke tuhumar su da shi sai don kawai sun yi imani da Allah Mabuwayi, Sha-yabo.
ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ
Open ayah 85:9Wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa. Allah kuma Mai ganin komai ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa da sama ma’abociyar manzilolin rana da wata da taurari. Ya kuma rantse da ranar alƙiyama wadda ya yi alƙawarin tattara halittu a cikinta. Sannan ya rantse da duk wani mai shaida, kamar Annabi da zai ba da shaida game da al’ummarsa, da kuma duk wani abin halarta ko abin yi wa shaida. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya la’anci ma’abota wani wawakeken rami, wanda suka haƙa suka hura wuta a cikinsa ganga-ganga, suka riƙa jefa muminai a cikinsa da ransu, yayin da suke zaune a gefen ramin suna kallon yadda suke azabtar da muminai. Ba don wani laifi da suke tuhumar su da aikatawa ba, sai don kawai sun yi imani da Allah Mabuwayi, Sha-yabo, wanda shi ne kaɗai mai mulkin sammai da ƙasa, kuma mai ganin komai. Annabi (ﷺ) ya ba da labarin waɗannan muminai da aka yi wa wannan azaba ta jefa su cikin ramin wuta, kamar yadda ya zo a hadisin da Muslim [#3005] ya ruwaito daga Suhaibu ɗan Sinan (Allah ya kara masa yarda). A taƙaice hadisin ya bayyana cewa: “A da can an yi wani sarki kafiri, yana da mai yi masa aikin sihiri. To lokacin da mai sihirin ya tsufa sai ya buƙaci Sarki ya zaɓo wani matashi daga jama’arsa don ya koya masa sihiri, domin ya ci gaba da wannan aiki nasa ko bayan mutuwarsa. Sarki ya amsa masa, ya tura masa wani saurayi wanda zai riƙa koyon sihiri a wurinsa. A hanyar saurayin ta zuwa wurin malaminsa mai sihiri sai yake gamuwa da wani malami mai ibada, ya riƙa sauraron wa’azinsa, har wa\'azin ya shige shi, daga ƙarshe ya yi imani da Allah ya watsar da bautar gumakan Sarki. Lokacin da Sarki ya gano haka, sai ya sa aka kamo masa wannan malami mai ibada ya sa aka kashe shi. Ya kuma yi yunƙurin kashe wannan saurayi amma Allah bai ba shi sa’a ba. Ya bi duk hanyoyin da zai bi don hallaka shi bai yi nasara ba. Sai saurayin ya nuna masa hanya ɗaya tak wadda zai bi ya samu nasarar hallaka shi. Ita ce ya tattara mutanen gari wuri guda ya ɗauki kibiya daga cikin kwarinsa ya yi Bismilla ya ambaci sunan Allah ya harbe shi da ita. Sarki ya amince da haka. Ai kuwa yana harbin wannan yaro sai kibiyar nan ta same shi, nan take ya faɗi ya mutu. Mutanen gari na ganin haka kuwa sai duk suka fashe da sowa suna cewa: \"Mun yi imani da Ubangijin yaro!\" Ganin haka shi kuma Sarki sai ya sa aka haƙa wani wawakeken rami, aka hura wuta ganga-ganga a cikinsa, ya riƙa kamo muminai waɗanda suka yi imani da Allah yana jefa duk wani wanda ya ƙi ya dawo zuwa ga addininsa na bautar gumakan Sarki. To wannan labari ne Allah (Mai tsarki da daukaka) yake ba wa Ƙuraishawa don su wa’azantu su daina cutar da Musulmi a kan addininsu.
إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُواْ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ ثُمَّ لَمۡ يَتُوبُواْ فَلَهُمۡ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمۡ عَذَابُ ٱلۡحَرِيقِ
Open ayah 85:10Lalle waɗanda suka azabtar da muminai maza da muminai mata sannan ba su tuba ba, to suna da azabar Jahannama, suna kuma da azabar ƙuna.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمۡ جَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡكَبِيرُ
Open ayah 85:11Lalle waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari suna da gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. Wannan kuwa shi ne babban rabo. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsawatar wa azzalumai masu cutar da bayinsa muminai da cewa, lalle waɗanda suka fitini muminai maza da mata, suka riƙa gana musu azaba da wuta don su raba su da imaninsu, sannan ba su tuba daga zunubansu ba, to a ranar lahira suna da azabar wutar Jahannama wadda za ta ƙona su sakamakon irin azabtarwar da suka yi wa muminai ta ƙona su da wuta a duniya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana gwaggwaɓar ni’imar da zai yi wa muminai waɗanda suka yi imani da shi suka yi kyawawan ayyuka, ya tabbatar da cewa, suna da gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. Wannan sakamako da ya tanadar musu kuwa shi ne babban rabo.
إِنَّ بَطۡشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ
Open ayah 85:12Lalle damƙar Ubangijinka tabbas mai tsanani ce.
إِنَّهُۥ هُوَ يُبۡدِئُ وَيُعِيدُ
Open ayah 85:13Lalle Shi ne Yake farar (da komai) Yake kuma dawo (da shi).
وَهُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلۡوَدُودُ
Open ayah 85:14Shi ne kuma Mai gafara, Mai ƙaunar (bayinsa na ƙwarai).
ذُو ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡمَجِيدُ
Open ayah 85:15Ma’abocin Al’arshi Mai girma.
فَعَّالٞ لِّمَا يُرِيدُ
Open ayah 85:16Mai aikata abin da Yake nufi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, lalle damƙar da yake yi wa azzalumi mai tsanani ce ko da kuwa ya saurara masa na ɗan lokaci, to amma ba zai bar shi ba, domin kuwa shi ne yake farar da komai, kamar halitta da azabtar da masu laifi, sannan shi ne zai dawo da wannan halittar bayan mutuwarta, ko ya dawo da azaba a lahira ga wanda ya yi wa azaba a duniya saboda laifinsa. Kuma shi mai gafara ne ga zunuban bayinsa idan sun tuba, mai ƙaunar masoyansa ne masu tsoron sa, kuma ma’abocin Al’arshi ne mai girma ne da karamci; yana aikata duk abin da yake nufi na ya gafarta wa wanda ya ga dama daga cikin bayinsa, ko ya azabtar da wanda ya ga dama, babu mai tilasta shi a kan aikinsa (Mai tsarki da daukaka).
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡجُنُودِ
Open ayah 85:17Shin labarin runduna ya zo maka?
فِرۡعَوۡنَ وَثَمُودَ
Open ayah 85:18(Su ne) Fir’auna da Samudawa.
بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي تَكۡذِيبٖ
Open ayah 85:19A\'a, su dai waɗanda suka kafirta suna cikin ƙaryatawa ne.
وَٱللَّهُ مِن وَرَآئِهِم مُّحِيطُۢ
Open ayah 85:20Allah kuwa Yana kewaye da su (da iliminsa).
بَلۡ هُوَ قُرۡءَانٞ مَّجِيدٞ
Open ayah 85:21A\'a, shi dai Alƙur’ani ne mai girma.
فِي لَوۡحٖ مَّحۡفُوظِۭ
Open ayah 85:22A cikin Lauhul-Mahafuzu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ya karya rundunonin da suka haɗu don yaƙar gaskiya a can baya, inda ya tambayi Manzonsa (ﷺ) cewa, shin ko labarin rundunoni ya zo masa, watau Fir’auna da jama’arsa da Samudawa mutanen Annabi Salihu, waɗanda suka yi ganganko don faɗa da gaskiya da hana mutane karɓar ta, amma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su gaba ɗayansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba rashin samun labarin waɗancan al’ummu ne ya hana waɗannan su yi imani ba; su dai kawai suna ƙaryata abin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo musu da shi ne, don bin son zuciya, Allah kuwa yana kewaye da sanin duk ayyukansu, babu abin da zai ɓuya gare shi, kuma zai yi musu sakayya a kai. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya mayar musu da martani a kan da’awarsu ta cewa Alƙur’ani waƙa ce ko bokanci, da cewa, shi Alƙur’ani ne mai girma da ke cike da manyan batutuwa da alherai masu tarin yawa da ilimi mai zurfi wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsare shi a cikin Lauhul Mahfuzu wanda babu mai iya canja shi ko shigar da ƙari ko ragi a cikinsa.