الطارق
At-Taariq
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ
Open ayah 86:1Na rantse da sama da (tauraro) mai zuwa cikin dare.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلطَّارِقُ
Open ayah 86:2Me ya sanar da kai mai zuwa cikin dare?
ٱلنَّجۡمُ ٱلثَّاقِبُ
Open ayah 86:3Tauraro ne mai keta (duhu) da haskensa.
إِن كُلُّ نَفۡسٖ لَّمَّا عَلَيۡهَا حَافِظٞ
Open ayah 86:4Ba wani rai face akwai mai tsaron sa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da yin rantsuwa da sama da kuma tauraro mai zuwa da daddare. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, bai san mene ne mai zuwa da daddare ba, sai ya bayyana masa shi da cewa, shi ne tauraron nan mai keta duhu da haskensa mai tsananin ƙarfi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wannan rantsuwa ne domin ya tabbatar da cewa, babu wani rai face Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wakilta masa mala’ikan da yake tsaron ayyukansa, domin yi masa hisabi a kansu a ranar alƙiyama.
فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ مِمَّ خُلِقَ
Open ayah 86:5To mutum ya duba mana, daga me aka halicce shi?
خُلِقَ مِن مَّآءٖ دَافِقٖ
Open ayah 86:6An halicce shi ne daga wani ruwa mai ingizar juna.
يَخۡرُجُ مِنۢ بَيۡنِ ٱلصُّلۡبِ وَٱلتَّرَآئِبِ
Open ayah 86:7Mai fita daga tsakanin tsatso da karankarma.
إِنَّهُۥ عَلَىٰ رَجۡعِهِۦ لَقَادِرٞ
Open ayah 86:8Lalle Shi (Allah) Mai iko ne a kan dawo da shi.
يَوۡمَ تُبۡلَى ٱلسَّرَآئِرُ
Open ayah 86:9A ranar da za a bayyana asirai.
فَمَا لَهُۥ مِن قُوَّةٖ وَلَا نَاصِرٖ
Open ayah 86:10To ba shi da wani ƙarfi ko wani mataimaki. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mutum da ya duba ya ga daga wane abu ne Allah ya halicce shi, don ya gane girman Ƙudurar Allah da gajiyawar ɗan’adam. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana masa cewa, ya halicce shi ne daga wani ruwa mai ingizar juna da ake zuba shi a cikin mahaifar mace, watau maniyyi. Wannan ruwa yana fita ne daga tsatson ɗa namiji da karankarmarsa, watau ƙashin gadon bayansa da ƙasusuwan ƙirjinsa. Sai kuma Allah ya bayyana cewa, ashe wanda ya samar da mutum daga ruwa mai ingizar juna, lalle yana da ikon ya dawo da shi da rai bayan mutuwarsa a ranar alƙiyama, ranar da ake tona asiri, a bayyana abubuwan da suke cikin zukata na niyyoyi da aƙidu da sauransu, a tantance mai kyau da mumuna. Don haka a wannan ranar mutum ba ya da wani kataɓus ko ƙarfi da zai kare kansa da shi daga azabar Allah, kuma ba shi da wani mataimaki da zai taimake shi.
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلرَّجۡعِ
Open ayah 86:11Na rantse da sama ma’abociyar dawo (da ruwa).
وَٱلۡأَرۡضِ ذَاتِ ٱلصَّدۡعِ
Open ayah 86:12Da kuma ƙasa ma’abociyar tsagewa (shuka ta fito).
إِنَّهُۥ لَقَوۡلٞ فَصۡلٞ
Open ayah 86:13Lalle shi (Alƙur’ani) magana ce mai tsage gaskiya.
وَمَا هُوَ بِٱلۡهَزۡلِ
Open ayah 86:14Kuma shi ba zancen banza ba ne.
إِنَّهُمۡ يَكِيدُونَ كَيۡدٗا
Open ayah 86:15Lalle su (kafirai) suna ƙulla mummunan makirci.
وَأَكِيدُ كَيۡدٗا
Open ayah 86:16Ni kuma ina shirya musu mummunan sakamako.
فَمَهِّلِ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَمۡهِلۡهُمۡ رُوَيۡدَۢا
Open ayah 86:17To sai ka saurara wa kafirai, ka saurara musu kaɗan. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake yin rantsuwa da sama ma’abociyar ruwa, domin ta nan yake sauka, ya sake kuma sauka. Ya kuma yi rantsuwa da ƙasa wadda take tsagewa tsirrai su fito da ‘ya’yan itatuwa da bishiyoyi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wannan rantsuwa ne domin ya tabbatar da cewa, Alƙur’ani da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ) tabbas magana ce mai tsage gaskiya da bambance tsakaninta da ƙarya. Kuma ba wasa ko zancen banza ba ne; gaskiya ce tsantsa. To amma kafirai masu ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) da abin da ya zo musu da shi, suna yawan shirya masa makirci domin su rusa masa da’awarsa, sai dai ba su sani ba shi ma Allah yana yi musu nasa shiri don rushe mugun nufinsu da bayyanar da gaskiya. Don haka sai ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya ɗan saurara musu ɗan lokaci kaɗan kada ya gaggauto musu da azaba ko hallaka, da sannu ba da jimawa ba za su ga mummunan ƙarshen makircinsu, Allah kuma ya bai wa Manzonsa (ﷺ) nasara a kansu.