الأعلى

Al-A'laa

The Most High · Surah 87 · Ayahs: 19 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. سَبِّحِ ٱسۡمَ رَبِّكَ ٱلۡأَعۡلَى

    Open ayah 87:1

    Ka tsarkake sunan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.

  2. ٱلَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰ

    Open ayah 87:2

    Wanda Ya yi halitta sai Ya daidaita (ta).

  3. وَٱلَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰ

    Open ayah 87:3

    Wanda kuma Ya ƙaddara (abubuwa) sannan Ya shiryar (da halittarsa).

  4. وَٱلَّذِيٓ أَخۡرَجَ ٱلۡمَرۡعَىٰ

    Open ayah 87:4

    Wanda kuma Ya fitar da makiyaya.

  5. فَجَعَلَهُۥ غُثَآءً أَحۡوَىٰ

    Open ayah 87:5

    Sai Ya mayar da ita duddugaggiya mai baƙi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Annabi (ﷺ) da ya tsarkake Ubangijinsa mafi ɗaukaka, watau wanda yake sama da dukkan halittunsa, tare da furta sunansa lokacin ambaton sa da girmama shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta kansa da siffofi uku : <b>Na ɗaya, </b>shi ne wanda ya yi halitta ya kuma daidaita halittar. <b>Na biyu, </b> shi ne wanda ya ƙaddara wa kowace halitta jinsinta da nau’inta da siffofinta, ya kuma shiryar da kowane mahaluƙi zuwa ga abin da ya dace da shi. <b>Na uku, </b> shi ne wanda ya fitar da abincin da dabbobi za su ci daga ƙasa, sannan ya mayar da shi duddugagge baƙi bayan da farko yana kore shar.

  6. سَنُقۡرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰٓ

    Open ayah 87:6

    Za Mu karantar da kai (Alƙur’ani) don haka ba za ka manta ba.

  7. إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ وَمَا يَخۡفَىٰ

    Open ayah 87:7

    Sai abin da Allah Ya ga dama, Lalle Shi Yana sane da bayyanannen (abu) da kuma abin da yake ɓuya.

  8. وَنُيَسِّرُكَ لِلۡيُسۡرَىٰ

    Open ayah 87:8

    Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al\'umara) mafiya sauƙi A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) babbar ni’imar da ya yi masa ta saukar masa da Alƙur’ani ya sanar da shi cewa, zai karantar da shi Alƙur’ani, ya tattara masa shi a ƙirjinsa ta yadda ba zai manta da shi ba, don haka ba sai ya yi ta bin bayan Mala’ika Jibrilu da gaggawa ba, lokacin da yake karanta masa shi don gudun kada ya manta. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi togaciyar abin da Manzonsa (ﷺ) zai iya mantawa na Alƙur’ani idan Allah ya ga damar faruwar haka, saboda wata hikima tasa, domin shi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sane da duk abin da ake bayyanawa da abin da ake ɓoyewa, babu abin da yake ɓuya a gare shi. An karɓo daga Abdurrahman ɗan Abza (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya yi wa mutane sallar Asuba, sai ya tsallake wata aya. Yayin da ya gama salla sai ya waiwaya ya tambaya cewa: “A cikin mutanen nan akwai Ubayyu ɗan Ka’ab?” Sai Ubayyu ya ce: “Ya Manzon Allah, shin an shafe aya kaza da kaza ne ko kuma an mantar da kai ita ne?” Sai ya ce: “An mantar da ni ne.” [Ahmad #5365]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Manzonsa (ﷺ) alƙawarin zai sauƙaƙe masa dukkan al\'amuransa na addini da rayuwa, don ya samu damar isar da saƙon Allah cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

  9. فَذَكِّرۡ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكۡرَىٰ

    Open ayah 87:9

    To ka yi wa’azi idan wa’azin zai yi amfani.

  10. سَيَذَّكَّرُ مَن يَخۡشَىٰ 

    Open ayah 87:10

    Wanda yake tsoron Allah zai wa’azantu.

  11. وَيَتَجَنَّبُهَا ٱلۡأَشۡقَى

    Open ayah 87:11

    Mafi shaƙiyanci kuma zai nesance shi.

  12. ٱلَّذِي يَصۡلَى ٱلنَّارَ ٱلۡكُبۡرَىٰ

    Open ayah 87:12

    Wanda zai shiga wuta mafi girma.

  13. ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحۡيَىٰ

    Open ayah 87:13

    Sannan ba zai mutu a cikinta ba kuma ba zai rayu (rayuwa mai daɗi) ba. A waɗannan ayoyi, bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Manzonsa (ﷺ) albishir da cewa, zai sauƙaƙa masa ayyukan addini waɗanda za su kai shi ga samun gidan Aljanna, sai kuma ya umarce shi da ya yi wa mutane wa’azi da Alƙur’ani, ya tunatar da su matuƙar za su saurari tunatarwarsa ta kuma amfane su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa duk wani mai jin tsoron Allah to zai wa’azantu da wa’azinsa, amma kafiri taɓaɓɓe zai guji wa’azinsa, domin ya fi kowa tsiyacewa a ranar lahira, don kuwa zai shiga wuta mafi girma ya ɗanɗani zafinta da ƙunarta, kuma ya dawwama a cikinta, ta yadda ba zai mutu ba ya huta da shan azaba, ba kuma zai yi rayuwar da zai ji daɗinta ba. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Amma ‘yan wuta waɗanda su ne ‘ya’yanta, to su ba za su mutu ba, ba kuma za su rayu ba. Sai dai akwai wasu mutane da aka sanya su wuta saboda zunubansu, sai Allah ya kashe su har su zama kamar baƙin gawayi, sai a yi izinin a yi ceto, sai a zo da su ƙungiya-ƙungiya, a baza su a kan ƙoramun Aljanna, sannan a ce: “Ya ku ‘yan Aljanna, ku kwararo musu ruwan Aljanna\". Sai su sake tsirowa kamar yadda ƙwayar magudanar ruwa take tsirowa.” [Muslim #165].

  14. قَدۡ أَفۡلَحَ مَن تَزَكَّىٰ

    Open ayah 87:14

    Haƙiƙa wanda ya tsarkaka ya rabauta.

  15. وَذَكَرَ ٱسۡمَ رَبِّهِۦ فَصَلَّىٰ

    Open ayah 87:15

    Ya kuma ambaci sunan Ubangijinsa sannan ya yi salla.

  16. بَلۡ تُؤۡثِرُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا

    Open ayah 87:16

    Ba haka ba, ku dai kuna fifita rayuwar duniya ne.

  17. وَٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰٓ

    Open ayah 87:17

    Lahira kuwa ita ta fi alheri ta kuma fi wanzuwa.

  18. إِنَّ هَٰذَا لَفِي ٱلصُّحُفِ ٱلۡأُولَىٰ

    Open ayah 87:18

    Lalle wannan (batu) tabbas yana cikin littattafan farko.

  19. صُحُفِ إِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ

    Open ayah 87:19

    Littattafan Ibrahimu da Musa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda ya tsarkake zuciyarsa daga shirka, ya tsarkake gaɓoɓinsa daga saɓon Allah da miyagun ɗabi’u, ya kuma ambaci sunan Ubangijinsa da yin nau’ukan zikiri waɗanda Allah ya shar’anta masa, ya kuma yi salla kamar yadda aka umarce shi, to lalle wannan ya rabauta da samun gidan Aljanna da kuɓuta daga azabar lahira. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar da martani ga waɗanda suka ƙi tsarkake zukatansu, suka shagaltar da kansu da bin soye-soyen zukatansu, da cewa, ba wani abu ne ya kai su ga haka ba, sai fifita rayuwar duniya a kan rayuwar lahira, tare da cewa akwai babbar tazara a tsakaninsu, domin rayuwar lahira ta fi duniya da duk abin da ke cikinta na jin daɗi, ta kuma fi ta wanzuwa, domin ni’imomin lahira ba sa yankewa har abada. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, waɗannan abubuwa da yake yi musu wa’azi da su da umarni da hani da yake yi musu, tabbas suna cikin littattafan farko da ya saukar gabanin Alƙur’ani, su ne littattafan da ya saukar wa Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Don haka Manzon Allah (ﷺ) bai zo musu da wani sabon abu ba wanda ya zama farau a kansa.