الغاشية
Al-Ghaashiya
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡغَٰشِيَةِ
Open ayah 88:1Shin labarin mai lulluɓewa da (tsoro) ya zo maka?
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ خَٰشِعَةٌ
Open ayah 88:2Wasu fuskoki a wannan ranar ƙasƙantattu ne.
عَامِلَةٞ نَّاصِبَةٞ
Open ayah 88:3Masu aiki ne (tuƙuru) masu shan wahala.
تَصۡلَىٰ نَارًا حَامِيَةٗ
Open ayah 88:4Za su shiga wuta mai tsananin ƙuna.
تُسۡقَىٰ مِنۡ عَيۡنٍ ءَانِيَةٖ
Open ayah 88:5Za a shayar da su daga idon ruwa mai tsananin zafi.
لَّيۡسَ لَهُمۡ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٖ
Open ayah 88:6Ba su da wani abinci sai na ƙayar tsidau.
لَّا يُسۡمِنُ وَلَا يُغۡنِي مِن جُوعٖ
Open ayah 88:7Ba ya sa ƙiba kuma ba ya maganin yunwa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tunatar da Manzon Allah (ﷺ) labarin ranar alƙiyama wadda take tafe babu makawa, kuma ya siffanta ta da cewa, rana ce mai lulluɓe mutane da tsoro da firgici. A wannan ranar za a tantance mutane a kasa su gida biyu, ‘yan wuta da ‘yan Aljanna. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta fuskokin ‘yan wuta a ranar da cewa ƙasƙantattu ne, masu aiki ne tuƙuru a wutar Jahannama masu shan wahala ne matuƙa, domin za a riƙa jan su da sarƙoƙi da ƙuƙumai a wuyoyinsu har zuwa wuta mai tsananin ƙuna. Idan kuma sun buƙaci abin sha a cikinta saboda tsananin ƙishirwa sai a shayar da su wani idon ruwa mai tsananin zafi. Idan sun buƙaci abinci kuwa ba za su sami wani abinci mai ɗanɗano ba sai dai a ba su abincin da ya fi kowanne muni da azaba, watau na ƙayar tsidau, wanda ba ya sa ƙiba ba kuma ya maganin yunwa.
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاعِمَةٞ
Open ayah 88:8Waɗansu fuskokin kuwa a wannan ranar ni’imtattu ne.
لِّسَعۡيِهَا رَاضِيَةٞ
Open ayah 88:9Masu gamsuwa ne da (sakamakon) ayyukansu.
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٖ
Open ayah 88:10(Suna) cikin Aljanna maɗaukakiya.
لَّا تَسۡمَعُ فِيهَا لَٰغِيَةٗ
Open ayah 88:11Ba a jin zancen banza a cikinta.
فِيهَا عَيۡنٞ جَارِيَةٞ
Open ayah 88:12A cikinta akwai marmaro mai gudana.
فِيهَا سُرُرٞ مَّرۡفُوعَةٞ
Open ayah 88:13A cikinta akwai gadaje maɗaukaka.
وَأَكۡوَابٞ مَّوۡضُوعَةٞ
Open ayah 88:14Da kofuna a ajijjiye.
وَنَمَارِقُ مَصۡفُوفَةٞ
Open ayah 88:15Da matasan kai a jejjere.
وَزَرَابِيُّ مَبۡثُوثَةٌ
Open ayah 88:16Da dardumai a shisshimfiɗe. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon ‘yan Aljanna, waɗanda ya siffanta fuskokinsu da cewa masu ni’ima ne da farin ciki, saboda yalwar ni’imar da suka samu kansu a ciki, suna masu yarda da kyawawan ayyukan da suka aikata a duniya, domin su samu sakamakonsu a ninninka musu shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta gidajensu na Aljanna da siffofi bakwai: <b>Na ɗaya, </b> Aljanna ce maɗaukakiya, watau a wurin da yake da ɗaukaka ta mahalli da ɗaukaka ta daraja da matsayi, domin gidajen Aljanna benaye ne wasu kan wasu. <b>Na biyu, </b> ba sa jin wata maganar banza a cikin Aljanna ballantana su ji wata haramtacciyar magana. <b>Na uku, </b> a cikinta akwai idanuwan marmaro na ruwa masu gudana waɗanda \'yan Aljanna ne da kansu suke sarrafa su bisa son ransu, ganin su kuma yake faranta musu rai. <b>Na huɗu, </b> akwai gadaje maɗaukaka a cikinta, idan mumini ya zauna a kai zai riƙa hango duk ni’imomin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tanadar musu. <b>Na biyar, </b> akwai kofuna da aka ajiye don amfani da su wajen shaye-shaye, don haka ɗauka kawai za su yi yayin da suka buƙata. <b>Na shida, </b> akwai matasan kai waɗanda aka jejjera a jikin juna, idan sun ga dama su zauna a kansu, idan kuma sun ga dama su jingina da su, idan sun ga dama su zauna a kan wasu su jingina da wasu. <b>Na bakwai, </b> akwai shimfiɗu na alfarma da aka shimfiɗa a ko’ina don zama da hutawa.
أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى ٱلۡإِبِلِ كَيۡفَ خُلِقَتۡ
Open ayah 88:17Shin ba sa duban raƙumi yadda aka halicce shi?
وَإِلَى ٱلسَّمَآءِ كَيۡفَ رُفِعَتۡ
Open ayah 88:18Da kuma sama yadda aka ɗaga ta?
وَإِلَى ٱلۡجِبَالِ كَيۡفَ نُصِبَتۡ
Open ayah 88:19Da kuma duwatsu yadda aka kakkafa su?
وَإِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَيۡفَ سُطِحَتۡ
Open ayah 88:20Da kuma ƙasa yadda aka shimfiɗa ta? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin kafirai masu ƙaryata ranar alƙiyama da cewa, me ya sa ba za su dubi raƙuma su ga yadda aka halicce su ba, aka hore amfani da su ga ‘yan’adam? Su kuma dubi sama su ga yadda Allah ya ɗaga ta a kansu, ta zama kamar rufi ba tare da ta faɗo a kansu ba? Su kuma dubi duwatsu su ga yadda Allah ya kafa su a cikin ƙasa, don ya hana ta tangal-tangal da mutanen da ke bayanta? Su kuma dubi ƙasa su ga yadda ya shimfiɗa ta ya sanya ta daidai da rayuwar mutane a bayanta? Watau da sun yi dubi na tsanaki zuwa ga waɗannan halittu, to da sun tabbatar da cewa, ba za su taɓa samuwa ba ba tare da mai samar da su ba, ba za su taɓa tsare kansu ba ba tare da mai tsaron su ba, da kuma lalle sun fahimci cewa, duk wanda ya yi wannan aiki yana da cikakken iko a kan dawo da matattu bayan mutuwarsu don yi musu hisabi.
فَذَكِّرۡ إِنَّمَآ أَنتَ مُذَكِّرٞ
Open ayah 88:21To ka yi wa’azi, lalle kai mai wa’azi ne kawai.
لَّسۡتَ عَلَيۡهِم بِمُصَيۡطِرٍ
Open ayah 88:22Kai ba mai tilasta su ba ne.
إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ
Open ayah 88:23Sai dai wanda ya ba da baya ya kuma kafirce.
فَيُعَذِّبُهُ ٱللَّهُ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَكۡبَرَ
Open ayah 88:24To Allah zai azabtar da shi azaba mafi girma.
إِنَّ إِلَيۡنَآ إِيَابَهُمۡ
Open ayah 88:25Lalle zuwa gare Mu ne makomarsu take.
ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا حِسَابَهُم
Open ayah 88:26Sannan kuma a kanmu ne hisabinsu yake. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) game da ƙaryata shi da mushirikai suke yi, ya umarce shi da ya yi musu wa’azi ya tsoratar da su azabar Allah da take jiran su idan ba su yi imani ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa, wannan ne kaɗai aikin da aka ɗora masa, watau ya yi musu wa’azi da tunatarwa kawai, amma ba a umarce shi sai ya tilasta su sai sun yi imani ba, wannan aikin Allah ne ba nasa ba ne. Don haka duk wanda ya ba da baya ya bijire wa yin imani, ya kafirce wa Allah da Manzonsa (ﷺ), to wannan a ranar alƙiyama Allah (Mai tsarki da daukaka) zai azabtar da shi azaba mai girman gaske, domin kuwa zai shigar da shi wutar Jahannama inda zai dawwama a cikinta har abada. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, duk halittu gaba ɗaya makomarsu zuwa gare shi ne shi kaɗai bayan mutuwarsu, sannan shi kaɗai ne wanda ya ɗauki nauyin yi musu hisabi a kan ayyukansu da suka aikata a duniya masu kyau ko munana, babu wanda zai yi tarayya da shi a kan haka.