الفجر
Al-Fajr
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلۡفَجۡرِ
Open ayah 89:1Na rantse da alfijir.
وَلَيَالٍ عَشۡرٖ
Open ayah 89:2Da kuma darare goma.
وَٱلشَّفۡعِ وَٱلۡوَتۡرِ
Open ayah 89:3Da kuma abin da yake cika da kuma mara.
وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَسۡرِ
Open ayah 89:4Da kuma dare lokacin da yake tafiya (cikin duhu).
هَلۡ فِي ذَٰلِكَ قَسَمٞ لِّذِي حِجۡرٍ
Open ayah 89:5Shin a game da waɗannan akwai rantsuwa (mai gamsarwa) ga mai hankali? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa da abubuwa biyar : <b>Na ɗaya, </b> Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rantse da lokacin alfijir, wanda shi ne ƙarshen dare, kuma farkon gabatowar yini. <b>Na biyu, </b> ya rantse da darare goma, watau kwanaki goma na farkon watan Zulhijja, kamar yadda ya zo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) da Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) da Abdullahi ɗan Zubair (Allah ya kara masa yarda) da Mujahid da Masruƙ. [Dubi, Mausu’atut Tafsiril Ma’asur , juzu’i na 23, shafi na 182-184]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wasu kwanaki da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fi son aiki nagari a cikinsu kamar kwanaki goma (na farkon Zulhijja)”. Sai aka ce: “Ya Manzon Allah, ko da jihadi don Allah?” Sai ya ce: “Ko da jihadi don Allah, sai dai mutumin da ya fita jihadi don Allah da dukiyarsa da kansa, amma bai dawo da komai ba.” Watau ya ƙarar da dukiyarsa wajen taimakon addinin Allah, ya kuma yi shahada a fagen daga. [Bukhari #969]. <b>Na uku, </b> Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da abu mai cika, watau abin da yake bibbiyu ko hurhuɗu ko shida-shida da sauransu. <b>Na huɗu, </b> ya rantse da abin da yake mara ne, watau ɗaya ne ko uku ko biyar da sauransu. Rantsuwa da cika da kuma mara, ta ƙunshi rantsuwa da komai cikin halittar Allah wanda yake cikin ɗayan waɗannan abubuwa biyu. Watau ko cika ne shi ko mara ne. <b>Na biyar, </b> ya yi rantsuwa da dare idan ya zo ya wuce da duhunsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da waɗannan abubuwa ne don ya tabbatar da cewa, lalle za a yi wa mutane sakayya a kan ayyukansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tambaya cewa, shin a cikin waɗannan abubuwa akwai wata rantsuwa mai gamsarwa irinta ga duk wani mai hankali? Lalle duk mai hankali zai gamsu da waɗannan rantse-rantse da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi.
أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ
Open ayah 89:6Shin ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ba ga Adawa?
إِرَمَ ذَاتِ ٱلۡعِمَادِ
Open ayah 89:7(Watau ƙabilar) Iramu ma’abociyar tsawo.
ٱلَّتِي لَمۡ يُخۡلَقۡ مِثۡلُهَا فِي ٱلۡبِلَٰدِ
Open ayah 89:8Wadda ba a halicci irinta ba a cikin garuruwa (a tsananin ƙarfi).
وَثَمُودَ ٱلَّذِينَ جَابُواْ ٱلصَّخۡرَ بِٱلۡوَادِ
Open ayah 89:9Da kuma Samudawa waɗanda suka fafe duwatsu a wurin da ake kira Wadil-Ƙura .
وَفِرۡعَوۡنَ ذِي ٱلۡأَوۡتَادِ
Open ayah 89:10Da kuma Fir’auna ma’abocin turaku.
ٱلَّذِينَ طَغَوۡاْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ
Open ayah 89:11Waɗanda suka yi ɗagawa a cikin garuruwa.
فَأَكۡثَرُواْ فِيهَا ٱلۡفَسَادَ
Open ayah 89:12Suka kuma yawaita ɓarna a cikinsu.
فَصَبَّ عَلَيۡهِمۡ رَبُّكَ سَوۡطَ عَذَابٍ
Open ayah 89:13Sai Ubangijinka Ya saukar musu azaba mai tsanani.
إِنَّ رَبَّكَ لَبِٱلۡمِرۡصَادِ
Open ayah 89:14Lalle Ubangijinka tabbas Yana nan a madakata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya labarta wa Manzonsa (ﷺ) mummunan sakamakon da ya auka wa wasu al’ummun da suka gabata bayan sun ƙaryata annabawansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye shi cewa, shin labarin yadda ya aikata ga Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai zo masa ba ne? Lalle labarin ya zo masa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana su da cewa, su ne ƙabilar Iramawa, watau waɗanda aka danganta su da kakansu \'Iramu\', waɗanda kuma Allah ya halicce su ma’abota tsawo da ƙarfi, wadda Allah bai taɓa halittar wata ƙabila mai ƙarfinta a sauran garuruwa ba. Allah kuma ya sake tambayar Ma’aiki (Mai tsarki da daukaka) cewa, shin bai samu labarin Samudawa mutanen Annabi Salihu ba, waɗanda suka fafe duwatsu suka yi gidaje a wani wuri da ake kira Wadil-Ƙura ? Kuma bai samu labarin Fir’auna ba, wanda yake da turaku na ɗaure mutane da gana musu azaba? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, duk waɗannan mutane sun yi taurin kai sun ƙetare iyakokin Allah a garuruwansu, domin sun yawaita ɓarna a cikinsu ta hanyar yaɗa kafirci da saɓon Allah da yaƙar Allah da manzanninsa, sai Allah ya saukar musu da azabarsa mai tsanani, ya kawar da su daga bayan ƙasa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, lalle yana wurin da yake hangen ɗaukacin ayyukan bayinsa yake sa ido a kansu, don ya yi wa duk wanda ya kyautata aikinsa sakamako da Aljanna, ya kuma yi wa wanda ya munana aikinsa sakamako da wutar Jahannama.
فَأَمَّا ٱلۡإِنسَٰنُ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ رَبُّهُۥ فَأَكۡرَمَهُۥ وَنَعَّمَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَكۡرَمَنِ
Open ayah 89:15Amma kuma mutum idan Ubangijinsa Ya jarrabe shi sai Ya karrama shi, Ya kuma yi masa ni’ima, sai ya ce: “Ubangijina Ya karrama ni.”
وَأَمَّآ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ فَقَدَرَ عَلَيۡهِ رِزۡقَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَهَٰنَنِ
Open ayah 89:16Amma kuma idan Ya jarrabe shi sai Ya ƙuntata masa a arzikinsa, sai ya ce: “Ubangijina Ya wulaƙanta ni.”
كَلَّاۖ بَل لَّا تُكۡرِمُونَ ٱلۡيَتِيمَ
Open ayah 89:17Faufau, ba haka ba ne; ku ba kwa karrama maraya ne.
وَلَا تَحَٰٓضُّونَ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ
Open ayah 89:18Kuma ba kwa kwaɗaitar da juna kan ciyar da miskinai.
وَتَأۡكُلُونَ ٱلتُّرَاثَ أَكۡلٗا لَّمّٗا
Open ayah 89:19Kuma kuna cinye dukiyar gadon marayu mummunan ci.
وَتُحِبُّونَ ٱلۡمَالَ حُبّٗا جَمّٗا
Open ayah 89:20Kuma kuna son dukiya so mai yawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani mummunan hali na ɗan’adam da rashin godiyarsa ga Allah idan ya yi masa wata ni’ima, da rashin dangana da haƙuri idan ya rasa wata ni’ima. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lalle shi ɗan’adam idan Ubangijinsa ya jarrabe shi ya karrama shi, ya yi masa dangogin ni’ima ta dukiya da ‘ya’ya da matsayi, sai ya yi zaton wannan wata karama ce Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa don ya cancanci haka, har ya riƙa taƙama yana hura hanci yana cewa, Allah ya yi masa karamci don yana ƙaunar sa. Hakanan kuma idan akasin haka ya faru da shi, watau Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jarrabe shi ya ƙuntata masa arzikinsa, sai ya riƙa zaton Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wulaƙanta shi, sai ya yi ta raki yana ta ƙorafi da haka. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar masa da martani, ya nuna masa kuskuren wannan mummunan zato da yake yi na cewa, samun wadata shi ne alamar ƙaunar Allah gare shi; rashi kuma shi ne alamar Allah ya wulaƙanta shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da haɗamar masu irin wannan mummunan zato, domin ko da ya ba su dukiyar ba sa tallafa wa maraya da dukiyar da ya ba su, ba ma sa kwaɗaitar da junansu a kan ciyar da mabuƙaci wanda ba shi da cin yau balle na gobe. Tare da wannan duka suna yin rub-da-ciki a kan haƙƙoƙin raunana, kamar mata da marayu, suna cinye musu dukiyoyinsu mummunan ci. Ga su kuma da mugun son dukiya, don haka suke rowa ba sa ciyar da dukiyoyinsu don Allah.
كَلَّآۖ إِذَا دُكَّتِ ٱلۡأَرۡضُ دَكّٗا دَكّٗا
Open ayah 89:21Ba haka ne ba, idan aka girgiza ƙasa matuƙar girgiza.
وَجَآءَ رَبُّكَ وَٱلۡمَلَكُ صَفّٗا صَفّٗا
Open ayah 89:22Ubangijinka kuma Ya zo tare da mala’iku sahu-sahu.
وَجِاْيٓءَ يَوۡمَئِذِۭ بِجَهَنَّمَۚ يَوۡمَئِذٖ يَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَٰنُ وَأَنَّىٰ لَهُ ٱلذِّكۡرَىٰ
Open ayah 89:23Aka kuma zo da Jahannama a wannan ranar. To fa a wannan ranar ne mutum zai tuna (sakacinsa), ta yaya wannan tunawar za ta yi masa amfani?
يَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي قَدَّمۡتُ لِحَيَاتِي
Open ayah 89:24Zai ce: “Kaitona, ina ma da na gabatar (da ayyukan alheri) a rayuwata!”
فَيَوۡمَئِذٖ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُۥٓ أَحَدٞ
Open ayah 89:25To a wannan ranar ba wani ɗaya da zai yi azaba irin azabarsa (watau Allah).
وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُۥٓ أَحَدٞ
Open ayah 89:26Ba kuma ɗaya da zai yi ɗauri irin ɗaurinsa.
يَٰٓأَيَّتُهَا ٱلنَّفۡسُ ٱلۡمُطۡمَئِنَّةُ
Open ayah 89:27(Za a ce): Ya kai wannan rai mai nutsuwa.
ٱرۡجِعِيٓ إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةٗ مَّرۡضِيَّةٗ
Open ayah 89:28Ka koma zuwa ga Ubangijinka kana mai yarda (da sakamako), abin yarda.
فَٱدۡخُلِي فِي عِبَٰدِي
Open ayah 89:29Don haka ka shiga cikin bayina.
وَٱدۡخُلِي جَنَّتِي
Open ayah 89:30Ka kuma shiga Aljannata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin mutane game da ranar alƙiyama wadda yin tanadi dominta shi ne abu mafi amfani a gare su ba wai tara dukiya ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsawatar musu da cewa, ba haka ya kamata aikinsu ya kasance ba, su tuna lokacin da za a girgiza ƙasa matuƙar girgiza, Allah kuma ya zo don yin hukunci tsakanin bayinsa, da mala’iku sahu-sahu. Aka kuma zo da wutar Jahannama a ranar da linzamanta har dubu saba’in, kowane linzami mala’ika dubu saba’in ne suke jan sa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A ranar alƙiyama za a zo da Jahannama tana da linzami dubu saba’in, tare da kowane linzami mala’ika dubu saba’in ne suke janye da shi.” [Muslim #2842]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a ranar ne mutum zai tuna sakacin da ya yi wajen bin Allah, amma ina wannan tunawar za ta amfane shi a wannan ranar, domin wannan ranar sakamako ce ba ranar aiki ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a wannan ranar ɗan’adam cikin nadama zai riƙa faɗin ina ma da ya yi wani kyakkyawan aiki domin rayuwarsa ta lahira. An karɓo daga Muhammad ɗan Abu Umaira (Allah ya kara masa yarda), ɗaya daga cikin sahabban Annabi (ﷺ) ya ce: “Da a ce bawa tun sanda aka haife shi har zuwa mutuwarsa ya faɗi a kan fuskarsa (watau ya yi sujjada) har ya tsufa a cikin yi wa Allah (Mai tsarki da daukaka) ɗa’a, to da lalle ya raina aikinsa a wannan ranar, da ya yi burin a mayar da shi duniya domin ya ƙara aikin lada.” [Ahmad #17650]. A wannan ranar babu wanda zai iya yin azaba kamar azabar Allah, domin azabarsa ta fi tsanani ta kuma fi wanzuwa. Kuma babu wanda zai iya yin ɗauri da sarƙoƙi kamar ɗaurinsa ga kafirai, domin za a ɗaure su da sarƙoƙi na wuta, a ja su a kan fuskokinsu zuwa wuta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon mumini wanda tun lokacin mutuwarsa da kuma a ranar alƙiyama za a kira shi da sunan ‘rai mai nutsuwa’, watau wanda ya nutsu da imani da kyawawan ayyuka. Sai a umarce shi da ya koma zuwa ga Ubangijinsa yana mai yarda da sakamakon da za a ba shi, yana kuma yardajje a wurin Ubangijinsa saboda imaninsa da kyawawan ayyukansa. Sai kuma Allah ya umarce shi da ya shiga cikin ayarin bayinsa nagari, ya shiga Aljannar da Allah ya tanadar musu.