البلد

Al-Balad

The City · Surah 90 · Ayahs: 20 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. لَآ أُقۡسِمُ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ

    Open ayah 90:1

    Na rantse da wannan gari (na Makka).

  2. وَأَنتَ حِلُّۢ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ

    Open ayah 90:2

    Alhali kuwa kai an halatta maka wannan gari.

  3. وَوَالِدٖ وَمَا وَلَدَ

    Open ayah 90:3

    (Na rantse) da mahaifi da abin da ya haifa.

  4. لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِي كَبَدٍ

    Open ayah 90:4

    Haƙiƙa Mun halicci mutum cikin wahala. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa da garin Makka, musamman lokacin da Manzon Allah (ﷺ) yake zaune a cikinsa. Ko kuma yana nufin, alhalin Manzon Allah (ﷺ) an halatta masa abin da zai aikata a cikin garin Makka na kashe duk wanda ya cancanci kisa. Wannan tafsirin shi ne aka ruwaito daga magabata, kamar Abdullahi ɗan Abbas da almajiransa. Ya kuma rantse da mahaifi, watau Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ko kuma duk wani mahaifi. Ya rantse da abin da mahaifi ya haifa, watau zurriyar Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ko kuma duk wani wanda aka haifa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wannan rantsuwa ne don ya tabbatar da cewa, lalle ya halicci ɗan’adam cikin wahala, saboda abin da yake fuskanta na wahalhalun duniya da masifunta.

  5. أَيَحۡسَبُ أَن لَّن يَقۡدِرَ عَلَيۡهِ أَحَدٞ

    Open ayah 90:5

    Yanzu mutum yana tsammanin cewa wani ba zai sami iko a kansa ba?

  6. يَقُولُ أَهۡلَكۡتُ مَالٗا لُّبَدًا

    Open ayah 90:6

    Yana cewa: “Na ɓatar da dukiya mai ɗimbin yawa.”

  7. أَيَحۡسَبُ أَن لَّمۡ يَرَهُۥٓ أَحَدٌ

    Open ayah 90:7

    Shin yana tsammanin cewa ba wanda ya gan shi?

  8. أَلَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ عَيۡنَيۡنِ

    Open ayah 90:8

    Shin ba Mu sanya masa idanuwa biyu ba ne?

  9. وَلِسَانٗا وَشَفَتَيۡنِ

    Open ayah 90:9

    Da harshe da kuma laɓɓa biyu?

  10. وَهَدَيۡنَٰهُ ٱلنَّجۡدَيۡنِ 

    Open ayah 90:10

    Muka kuma bayyana masa hanyoyi biyu? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin ɗan’adam game da girman kai da yake yi yana saɓon Allah, ya nuna masa cewa, yanzu yana tsammani ne cewa, wani ba zai sami iko a kansa ba idan ya aikata laifuka, don haka ya fi ƙarfin a kama shi da laifinsa ko da kuwa Ubangijinsa ne mahaliccinsa? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ɗan’adam yana gadara da cewa, ya kashe maɗuɗuwar dukiya mai yawan gaske. Shin tsammani yake cewa Allah (Mai tsarki da daukaka) ba ya ganin sa, kuma ba zai yi masa hisabi a kan wannan dukiyar tasa ba; ta ina ya same ta, kuma ta ƙaƙa ya kashe ta? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da shi ni’imomin da ya yi masa waɗanda ba zai iya sayen su da kuɗi ba. Ya tabbatar masa cewa, shi ne ya sanya masa idanuwa biyu da yake gani da su. Ya kuma yi masa harshe da laɓɓa biyu waɗanda da su ne yake iya magana. Ya kuma nuna masa hanyoyi biyu; hanyar alheri da hanyar sharri. Duk waɗannan ni’imomi ne da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa ɗan’adam amma sai yake butulce masa, ya ƙi gode masa ta hanyar yi masa biyayya.

  11. فَلَا ٱقۡتَحَمَ ٱلۡعَقَبَةَ

    Open ayah 90:11

    Sai bai ƙetare hanya mai wahala ba?.

  12. وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡعَقَبَةُ

    Open ayah 90:12

    Me kuma ya sanar da kai mece ce hanya mai wahala?

  13. فَكُّ رَقَبَةٍ

    Open ayah 90:13

    (Watau) ‘yanta wuyaye (bawa ko baiwa).

  14. أَوۡ إِطۡعَٰمٞ فِي يَوۡمٖ ذِي مَسۡغَبَةٖ

    Open ayah 90:14

    Ko kuma ciyarwa a wata rana ta yunwa.

  15. يَتِيمٗا ذَا مَقۡرَبَةٍ

    Open ayah 90:15

    Ga maraya ma\'abocin kusanci.

  16. أَوۡ مِسۡكِينٗا ذَا مَتۡرَبَةٖ

    Open ayah 90:16

    Ko miskini ma\'abocin talauci.

  17. ثُمَّ كَانَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلصَّبۡرِ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلۡمَرۡحَمَةِ

    Open ayah 90:17

    Sannan kuma ya zama daga waɗanda suka yi imani, suka yi wa junansu wasiyya da yin haƙuri kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayawa.

  18. أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ

    Open ayah 90:18

    Waɗannan su ne ma’abota dama.

  19. وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ

    Open ayah 90:19

    Waɗanda kuwa suka kafirce wa ayoyinmu, su ne ma’abota hagu.

  20. عَلَيۡهِمۡ نَارٞ مُّؤۡصَدَةُۢ 

    Open ayah 90:20

    A kansu akwai wuta abar kullewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa ɗan’adam cewa, ana buƙatar sa da ya ƙetare hanya mai wahala wadda ta raba tsakaninsa da gidan Aljanna, domin ya samu damar bin hanyar alheri, to amma sai bai ƙetare ta ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Manzonsa (ﷺ) wannan mawuyaciyar hanya da cewa su ne: <b>Na ɗaya, </b> ‘yanta bawa ko baiwa domin Allah. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya ‘yanta baiwa ko bawa mumini, to a madadin kowace gaɓa ɗaya ta wannan bawan Allah zai ‘yanta masa gaɓarsa daga shiga wuta.” [Bukhari #2517 da Muslim #1509]. <b>Na biyu, </b> ciyar da marayan da ya rasa ubansa sannan kuma yana da dangantaka ta zumunci da shi. Ko kuma ciyar da mabuƙaci wanda bai mallaki abin da zai ishe shi ba. Ya ciyar da su a lokacin da ake fama da yunwa saboda ƙarancin abinci. An karɓo daga Salmanu ɗan Amir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Sadaka ga mabuƙaci sadaka ce kawai, amma ga makusanci abu biyu ne; sadaka ce, kuma sada zumunci ne.” [Ahmad #16227 da Tirmizi #658 da Nasa’i #2582]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, bayan waɗannan kyawawan ayyukan kuma ya kasance daga cikin waɗanda suka yi imani, suka kuma yi wa junansu wasiyya da yin haƙuri a kan bin Allah da kauce wa saɓa masa da kuma yin haƙuri a kan abin da zai same su na ƙaddara marar daɗi, suka kuma yi wa juna wasiyya da tausaya wa bayin Allah (Mai tsarki da daukaka). An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Masu tausayi, Allah mai rahama yana tausaya musu. Ku tausaya wa mutane a ƙasa sai Allah a sama ya tausaya muku ku ma.” [Abu Dawud #4941 da Tirmizi #1924 da Ahmad #6494]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, masu irin waɗannan siffofi su ne ma’abota dama, domin sun biya haƙƙin Allah da haƙƙoƙin bayinsa, sun kuma guji abin da ya hana. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗanda suka kafirce wa ayoyinsa da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ), to waɗannan su ne ma’abota hagu, za su kuma shiga wutar Jahannama a ranar alƙiyama inda za a kulle su a cikinta, a yi ta yi musu azaba babu ranar fita daga cikinta.