الشمس
Ash-Shams
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلشَّمۡسِ وَضُحَىٰهَا
Open ayah 91:1Na rantse da rana da walaharta.
وَٱلۡقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا
Open ayah 91:2Da kuma wata idan ya bi ta (wato ranar).
وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا
Open ayah 91:3Da kuma wuni idan ya bayyana ta.
وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰهَا
Open ayah 91:4Da kuma dare idan ya lulluɓe ta
وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا
Open ayah 91:5Da kuma sama da gininta
وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا طَحَىٰهَا
Open ayah 91:6Da kuma ƙasa da shimfiɗarta.
وَنَفۡسٖ وَمَا سَوَّىٰهَا
Open ayah 91:7Da kuma rai da daidaitarsa.
فَأَلۡهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقۡوَىٰهَا
Open ayah 91:8Sai Ya kimsa masa (gane) lalacewarsa da taƙawarsa.
قَدۡ أَفۡلَحَ مَن زَكَّىٰهَا
Open ayah 91:9Haƙiƙa wanda ya tsarkake shi (ran) ya rabauta.
وَقَدۡ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا
Open ayah 91:10Haƙiƙa kuma wanda ya binne shi da saɓo ya taɓe. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da rantsuwa har goma sha ɗaya don nuna muhimmancin abin da zai zo da bayaninsa a cikinta. <b>Na ɗaya, </b> Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da rana, domin ita wata babbar halittar Allah ce mai nuna cikar Ƙudurar wanda ya samar da ita. <b>Na biyu, </b> ya yi rantsuwa da lokacin hasken walaharta, watau lokacin rana da ta fara haske bayan ta hudo daga mahudarta. <b>Na uku, </b> ya yi rantsuwa da wata idan ya biyo bayan faɗuwar rana. <b>Na huɗu, </b> ya yi rantsuwa da wuni idan ya bayyana abin da yake kan ƙasa da haskensa. <b>Na biyar, </b> ya rantse da dare idan ya lulluɓe ƙasa da duhunsa. <b>Na shida, </b> ya rantse da sama da ya ɗaga ta ba tare da wasu dirkoki ba. <b>Na bakwai, </b> ya rantse da ginin sama wanda ya kyautata halittarsa, ya daidaita shi. <b>Na takwas, </b> ya yi rantsuwa da ƙasa wadda ya halicce ta, domin rayuwar ɗan’adam a kanta. <b>Na tara, </b> ya rantse da shimfiɗar ƙasa da daidaita ta, don ɗan’adam ya ji daɗin zama da tafiya a kanta. <b>Na goma, </b> ya yi rantsuwa da kowane rai da ya halitta. <b>Na sha ɗaya, </b> ya rantse da yadda ya daidaita halittar kowane rai, sannan ya kimsa masa sanin abu mai kyau, don ya aikata shi da sanin mummuna don ya guje shi. Sai kuma ya bayyana sakamakon wanda ya tsarkake ransa da kyawawan ayyuka da ɗabi’u da cewa ya rabauta, ya sami abin da yake so, sannan wanda ya binne shi da saɓon Allah da laifuka da miyagun ɗabi’u shi kuma ya taɓe ya yi asara. An karɓo daga Imrana ɗan Husain (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wasu mutane biyu daga ƙabilar Muzaina sun zo wurin Manzon Allah (ﷺ) suka ce: Ya Manzon Allah, ka ba mu labari game da abin da mutane suke aikatawa a yau (watau duniya), suke wahala a kansa, shin wani abu ne na ƙaddara da aka riga aka hukunta musu aka kuma zartar musu da shi, ko kuma wani sabon abu ne wanda suke fuskanta daga abin da Annabinsu ya zo musu da shi, hujja kuma ta tabbata a kansu? Sai ya ce: “A\'a, abu ne da aka riga aka hukunta musu aka kuma zartar musu da shi. Abin da yake gaskata wannan a littafin Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne faɗar Allah: ‘Da kuma rai da daidaitarsa. Sai ya kimsa masa (gane) lalacewarsa da taƙawarsa ’....” [Muslim #2650 da Ahmad #19936]. An karɓo daga Zaidu ɗan Arƙam (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana cewa: “Ya Allah, lalle ni ina neman tsarinka daga gazawa da kasala da ragwanci da rowa da tsufa tukub da azabar ƙabari. Ya Allah, ka ba wa raina taƙawarsa, ka tsarkake shi, kai ne fiyayyen mai tsarkake shi, kai ne majiɓincin sa mai taimakon sa....” [Muslim #2722 da Nasa’i #5458].
كَذَّبَتۡ ثَمُودُ بِطَغۡوَىٰهَآ
Open ayah 91:11Samudawa sun ƙaryata saboda ɗagawarsu.
إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشۡقَىٰهَا
Open ayah 91:12Yayin da mafi tsagerancinsu ya zabura.
فَقَالَ لَهُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقۡيَٰهَا
Open ayah 91:13Sai Manzon Allah ya ce da su: “Ku bar taguwar Allah da (ranar) shanta.”
فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمۡدَمَ عَلَيۡهِمۡ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمۡ فَسَوَّىٰهَا
Open ayah 91:14Sai suka ƙaryata shi sannan suka soke ta, sai Ubangijinsu Ya kama su da azaba saboda zunubinsu, sai Ya daidaita ta (watau ƙabilar wajen azaba).
وَلَا يَخَافُ عُقۡبَٰهَا
Open ayah 91:15Kuma ba Ya tsoron abin da zai biyo bayanta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yi wa mushirikan Ƙuraishawa masu ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) kashedi da cewa, Samudawa sun ƙaryata Annabinsu Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) saboda ƙetare iyakarsu da saɓon Allah da miyagun laifuka, lokacin da mafi tsagerancinsu ya zabura ya nufi taguwar Allah da niyyar zai soke ta, yayin da mutanensa suka zuga shi a kan haka. Sai Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya gargaɗe su, ya ja musu kunne a kan su ƙyale taguwar Allah da ranar shan ruwanta, kada su yi ƙoƙarin cutar da ita. To amma sai suka ƙaryata Manzonsu Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), suka yi watsi da nasiharsa dangane da wannan taguwar, sai tsageran cikinsu ya kashe ta, duk sauran kuma suka goyi bayansa, sai suka zama abokan tarayyarsa a wajen laifi. A kan haka ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar musu da azabarsa wadda ta mamaye su gaba ɗaya, ya hallaka su da tsawa saboda mummunan laifinsu, ya kuma daidaita su a wajen uƙuba bai bambance wani daga cikinsu ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu wannan azabar, ya hallaka su gaba ɗaya, ba tare da yana jin tsoron abin da zai biyo bayanta ba.