الليل
Al-Lail
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰ
Open ayah 92:1Na rantse da dare idan ya lulluɓe (da duhunsa).
وَٱلنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ
Open ayah 92:2Da kuma wuni idan ya bayyana.
وَمَا خَلَقَ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ
Open ayah 92:3Da kuma halittar namiji da mace.
إِنَّ سَعۡيَكُمۡ لَشَتَّىٰ
Open ayah 92:4Lalle aikinku ya sha bamban. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa iri uku: <b>Ta ɗaya, </b> ya rantse da dare yayin da ya lulluɓe komai da duhunsa, kowa ya koma mazauninsa don ya huta daga kujuba-kujuba da ɗawainiyar rana. <b>Ta biyu, </b> ya rantse da wuni idan ya bayyana da haskensa, mutane da dabbobi da tsuntsaye suka fita don neman abincinsu. <b>Ta uku, </b> ya rantse da halittar komai jinsi biyu; namiji da mace, don nuna cikakkiyar Ƙudurarsa da hikimarsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da bambancin ayyukan bayinsa, daga cikinsu akwai kyawawan ayyuka waɗanda su ne sanadiyyar shigar bawa Aljanna; akwai kuma munanan ayyuka waɗanda su ne sanadiyyar shigarsa wuta.
فَأَمَّا مَنۡ أَعۡطَىٰ وَٱتَّقَىٰ
Open ayah 92:5To wanda ya ba da (haƙƙoƙin da ke kansa) ya kuma yi taƙawa.
وَصَدَّقَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ
Open ayah 92:6Ya kuma gaskata (sakamako) mafi kyau.
فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡيُسۡرَىٰ
Open ayah 92:7To lalle ne za Mu sauƙaƙa masa (hanyar) Aljanna.
وَأَمَّا مَنۢ بَخِلَ وَٱسۡتَغۡنَىٰ
Open ayah 92:8Amma kuma wanda ya yi rowa (da haƙƙin Allah) ya kuma wadatu (da neman lada).
وَكَذَّبَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ
Open ayah 92:9Kuma ya ƙaryata (sakamako) mafi kyau.
فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡعُسۡرَىٰ
Open ayah 92:10To lalle ne za Mu hore masa (hanyar) wuta.
وَمَا يُغۡنِي عَنۡهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ
Open ayah 92:11Dukiyarsa kuma ba za ta amfane shi ba idan ya gangara (cikin wuta). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana bambancin ayyukan bayinsa da sakamakon kowane mai aiki, da cewa, duk wanda ya bayar da haƙƙoƙin da suke kansa, ya kuma guji abin da aka hana shi na saɓon Allah, ya kuma gaskata alƙawarin da Allah ya yi masa na ba shi madadin abin da ya ciyar domin shi, ya kuma gaskata alƙawarin gidan Aljanna da aka yi wa mai ciyar da dukiyarsa don Allah, to wannan lalle Allah zai sauƙaƙe masa ayyukan alheri da ciyarwa don Allah, domin ya kai shi ga samun gidan Aljanna. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, duk wanda ya yi rowa da dukiyarsa, bai fitar da haƙƙoƙin da ke cikinta ba, ya ƙanƙame dukiyarsa ya saki Allah (Mai tsarki da daukaka) ba ya neman falalarsa, ya kuma ƙaryata alƙawarin Allah na bayar da madadi ga wanda ya ciyar da dukiyarsa dominsa, da sakamakon Aljanna ga mai bayarwa don Allah, to wannan Allah (Mai tsarki da daukaka) zai hore masa munanan ayyuka, ya tsaurara masa ya hana shi aikata alheri. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, dukiyarsa da yake rowar ta, ya ƙi aikin alheri da ita ba za ta amfana masa komai ba lokacin da ya faɗa cikin hallaka aka jefa shi cikin wutar Jahannama. An karɓo daga Aliyyu ɗan Abu Ɗalibi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mun kasance a wurin wata jana’iza a maƙabartar \'Baƙi’ul Gharƙadi\', sai Manzon Allah (ﷺ) ya zo mana, ya sami wuri ya zauna, mu ma muka zauna kewaye da shi, yana riƙe da kwagirinsa, sai ya sunkuyar da kansa ya riƙa tona ƙasa da kwagirinsa, sannan ya ce: “Babu wani mutum ɗaya mai rai daga cikinku face an rubuta masa mazauninsa a Aljanna da wuta, sai kuma an rubuta ɗan wuta ne shi ko ɗan Aljanna.” Sai wani mutum ya ce: “Ya Manzon Allah, yanzu ba ma dogara da abin da aka riga aka rubuta mana ba mu bar aiki? Wanda cikinmu ya zamanto ɗan Aljanna ne, to zai kama aikin ‘yan Aljanna; wanda yake ɗan wuta ne zai kama aikin ‘yan wuta?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle ‘yan Aljanna za a sauƙaƙe musu aikata aikin ‘yan Aljanna, hakanan ‘yan wuta ma za a sauƙaƙe musu aikata aikin ‘yan wuta.” Sannan ya karanta faɗar Allah: “To amma wanda ya ba da (haƙƙoƙin da ke kansa) ya yi taƙawa ....” har zuwa ƙarshen ayoyi.” [Bukhari #1362 da Muslim #2647].
إِنَّ عَلَيۡنَا لَلۡهُدَىٰ
Open ayah 92:12Lalle bayyana hanyar shiriya a kanmu yake.
وَإِنَّ لَنَا لَلۡأٓخِرَةَ وَٱلۡأُولَىٰ
Open ayah 92:13Kuma lalle lahira da duniya namu ne.
فَأَنذَرۡتُكُمۡ نَارٗا تَلَظَّىٰ
Open ayah 92:14Don haka ina yi muku gargaɗin wata wuta mai ruruwa.
لَا يَصۡلَىٰهَآ إِلَّا ٱلۡأَشۡقَى
Open ayah 92:15Ba mai shigar ta sai mafi tsiyacewa.
ٱلَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
Open ayah 92:16Wanda ya ƙaryata ya kuma ba da baya.
وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلۡأَتۡقَى
Open ayah 92:17Kuma lalle za a nesantar da mafi taƙawa daga gare ta.
ٱلَّذِي يُؤۡتِي مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ
Open ayah 92:18Wanda yake ba da dukiyarsa yana neman tsarkaka.
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعۡمَةٖ تُجۡزَىٰٓ
Open ayah 92:19Ba kuwa wani da ya yi masa wata ni\'ima da za a saka masa (a kanta)
إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِ ٱلۡأَعۡلَىٰ
Open ayah 92:20Sai dai don neman Fuskar Ubangijinsa Maɗaukaki.
وَلَسَوۡفَ يَرۡضَىٰ
Open ayah 92:21Kuma lalle zai yarda (da sakamakon da za a ba shi). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yanke wa kowa hanzari, domin kuwa ya wajabta wa kansa bayanin hanyar shiriya da ta ɓata da abin da yake biyayya ne gare shi da wanda yake saɓo ne. Ya kuma tabbatar da cewa, rayuwar lahira da ta duniya duk nasa ne; shi ne yake yin abin da ya ga dama a cikinsu babu mai tilasta masa ko ya hana shi. Sai kuma Allah ya gargaɗi bayinsa da azabar wuta mai tsananin ruruwa idan suka saɓa masa. Kuma babu wanda zai shiga wannan wutar ya ɗanɗani tsananin zafinta sai mafi tsiyacewa, watau kafiri, wanda ya ƙaryata Ubangijinsa da saƙon da ya aiko Manzonsa da shi, ya kuma juya baya, ya bijire wa bin Allah da Manzonsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wanda zai nesantar daga shiga wannan wuta, watau wanda yake mai matuƙar kiyaye dokokinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta shi da cewa, shi ne wanda yake ciyar da dukiyarsa a ayyukan alheri, domin ya tsarkake kansa daga zunubai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa shaida da cewa, ba yana ciyar da dukiyarsa ne don ya saka wa wani a kan wata ni’ima da ya yi masa ba. Ba ya nufin komai da ba da dukiyarsa sai don neman fuskar Ubangijinsa Maɗaukaki, kuma da sannu zai yarda da sakamakon da Allah zai ba shi a lahira na gidan Aljanna. Da dama daga cikin malaman tafsiri sun bayyana cewa, waɗannan ayoyi sun sauka ne a kan Abubakar As-Siddiƙ (Allah ya kara masa yarda), wasu ma sun ce ijma’in malamai ne a kan haka. Haƙiƙa babu wanda ya fi cancanta da wannan ayar kamar Sayyidina Abubakar (Allah ya kara masa yarda), domin shi ne kan gaba a cikin wannan al’umma wajen siffantuwa da waɗannan siffofi da aka ambata a waɗannan ayoyi, domin shi mutum ne mai yawan gaskiya da tsoron Allah da bin dokokinsa sau-da-ƙafa da ciyar da dukiyarsa, don taimakon addinin Allah da Manzon Allah (ﷺ). Ya bayar da ilahirin dukiyarsa domin Allah da neman yardarsa, ba wai don yana biyan wani mutum wani alheri da ya taɓa yi masa ba, bai kuma taɓa neman wani ya yi masa sakayya a kan haka in ba Allah (Mai tsarki da daukaka) ba. Don haka shi ya fi kowa cancantar wannan falala. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya ciyar da dangogi biyu na dukiyarsa (watau kamar dirhami biyu ko dinari biyu) don Allah, za a kira shi ta ƙofofin Aljanna da cewa: Ya bawan Allah, (taho) ga alheri. Duk wanda ya kasance cikin ma’abota salla, to za a kira shi ta ƙofar salla; wanda kuma ya zamanto daga ma’abota jihadi, za a kira shi ta ƙofar jihadi; wanda ya kasance cikin ma’abota azumi, to za a kira shi ta ƙofar Rayyan; wanda ya kasance cikin ma’abota sadaka, to za a kira shi ta ƙofar sadaka.” Sai Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ya Manzon Allah, mahaifina da mahaifiyata fansa ne a gare ka, babu wata cutuwa tare da duk wanda za a kira shi ta waɗannan ƙofofi, to shin akwai wanda za a kira shi ta ƙofofin nan gaba ɗayansu?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Na’am, ina fatan kana cikinsu.” [Bukhari #1897 da Muslim #1027].