الضحى
Ad-Dhuhaa
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلضُّحَىٰ
Open ayah 93:1Na rantse da lokacin hantsi.
وَٱلَّيۡلِ إِذَا سَجَىٰ
Open ayah 93:2Da kuma dare idan ya yi tsit
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ
Open ayah 93:3Ubangijinka bai bar ka ba, kuma bai ƙi ka ba.
وَلَلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لَّكَ مِنَ ٱلۡأُولَىٰ
Open ayah 93:4Kuma lalle lahira ta fi maka alheri a kan duniya.
وَلَسَوۡفَ يُعۡطِيكَ رَبُّكَ فَتَرۡضَىٰٓ
Open ayah 93:5Kuma lalle Ubangijinka zai ba ka har sai ka yarda (da abin da Ya ba ka). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa da lokacin hantsi, wanda shi ne farkon wuni. Ya kuma rantse da dare lokacin da yi tsit ya lulluɓe komai da duhunsa, mutane suka koma mazaunansu don su huta su yi barci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin rantsuwarsa da cewa, bai ƙyale Annabinsa (ﷺ) ba bai kuma yi fushi da shi ba, kamar yadda mushirikai suke zargi, don ganin wahayi ya yanke masa na wani ɗan lokaci ƙanƙani. Sai kuma ya yi masa albishir da cewa, tabbas lahira ta fi masa alheri a kan duniya, domin a can ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa tanadin ni’imomin da ba za su yanke ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Annabi (ﷺ) ya zo gidan ‘yarsa Faɗima (Allah ya kara mata yarda), sai bai shiga ba ya koma, da Aliyyu (Allah ya kara masa yarda) ya dawo sai ta gaya masa. Sai ya je ya tambayi Manzon Allah (ﷺ), sai ya ce masa: “Na ga labule ne mai zane a ƙofarta, ina ni ina duniya?” Sai Aliyyu ya dawo wajen Faɗima (Allah ya kara mata yarda) ya faɗa mata abin da ya ce. Sai ta ce: “Ya ba ni duk umarnin da ya ga dama in yi da shi.” Sai ya ce: “Ta aika wa wane, domin gida ne da suke cikin buƙata.” [Bukhari #2613]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya kwanta ya yi barci a kan wata tabarma har alamunta suka bayyana a gefen jikinsa, sai muka ce: Ya Manzon Allah, da ka sami shimfiɗa mai laushi. Sai ya ce: “Ina ni ina duniya? Ni a duniya ba wani ba ne sai kamar mahayi ne da ya sauka ya sha inuwar wata bishiya sannan ya tashi ya bar ta.” [Tirmizi #2377, da Al-Albani, As-Sahiha #439]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa, lalle zai ba shi gwaggwaɓan sakamako, watau shi da al’ummarsa, har sai ya yarda da abin da aka ba shi aka ba al’ummarsa.
أَلَمۡ يَجِدۡكَ يَتِيمٗا فَـَٔاوَىٰ
Open ayah 93:6Shin bai same ka maraya ba sai Ya haɗa ka (da mai kula da kai)?
وَوَجَدَكَ ضَآلّٗا فَهَدَىٰ
Open ayah 93:7Ya kuma same ka marashin shiriya Ya shiryar (da kai)?
وَوَجَدَكَ عَآئِلٗا فَأَغۡنَىٰ
Open ayah 93:8Ya kuma same ka matalauci Ya wadata (ka)?
فَأَمَّا ٱلۡيَتِيمَ فَلَا تَقۡهَرۡ
Open ayah 93:9Don haka maraya fa kada ka yi masa fin ƙarfi.
وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنۡهَرۡ
Open ayah 93:10Mai tamabya kuma kada ka daka masa tsawa.
وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ
Open ayah 93:11Amma kuma game da ni’imar Ubangijinka sai ka ba da labari. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lissafa wa Manzonsa (ﷺ) wasu ni’imomi da ya yi masa a rayuwarsa, da cewa, ya same shi maraya, domin mahaifinsa ya rasu tun yana ciki, mahaifiyarsa ma ta rasu yana ɗan shekara shida, amma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tanadar masa matsuguni, ya haɗa shi da mai kula da shi, watau kakansa Abdulmuɗɗalib sannan bayansa baffansa Abu Ɗalib. Ya kuma tabbatar masa cewa, ya same shi marashin shiriya, bai san wani littafi ko imani ba, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba shi shiriya, ya karantar da shi abin da bai sani ba. Ya kuma tabbatar masa cewa, ya same shi matalauci ba ya da komai, amma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wadatar da shi, ya ba shi ganimar yaƙi mai yawa, ya kuma ba shi wadatar zuciya bayan ta dukiya. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Yawan kadara ba shi ne wadata ba; wadata ita ce wadatar zuci.” [Bukhari #6446 da Muslim #1051]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya musulunta aka ba shi cin yau da na gobe, Allah ya ba shi wadatar zuci game da abin da ya ba shi, to haƙiƙa ya rabauta.” [Muslim #1054]. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalinsa da cewa, kada ya nuna wa maraya fin ƙarfi, ya yi masa kyakkyawar mu’amala da nuna masa tausayi. Hakanan shi ma mai tambaya saboda buƙata, kada ya yi masa tsawa. Kuma ya riƙa gode wa Allah bisa ni’imomin da ya yi masa, ya kuma riƙa ba da labarinsu.