الشرح
Ash-Sharh
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
أَلَمۡ نَشۡرَحۡ لَكَ صَدۡرَكَ
Open ayah 94:1Shin ba Mu yalwata maka ƙirjinka ba?
وَوَضَعۡنَا عَنكَ وِزۡرَكَ
Open ayah 94:2Muka kuma sauke maka nauye-nauyenka?
ٱلَّذِيٓ أَنقَضَ ظَهۡرَكَ
Open ayah 94:3Wanda ya nauyayi bayanka?
وَرَفَعۡنَا لَكَ ذِكۡرَكَ
Open ayah 94:4Muka kuma ɗaukaka maka ambatonka? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tuna wa Manzon Allah wasu manyan ni’imomi da ya yi masa, da cewa, ya yalwata masa ƙirjinsa, ya hore masa son sauraron wahayin da yake yiwo masa, da kuma juriya game da gallazawar mutanensa gare shi. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mala’iku sun zo min, sai suka kama ni suka nufi Rijiyar Zamzam da ni, sai aka tsaga ƙirjina sannan aka wanke shi da ruwan Zamzam, sannan suka sauko da ni.” [Muslim #260]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo wa Manzon Allah (ﷺ) ya same shi a cikin yara yana wasa, sai ya kama shi, ya kwantar da shi, ya tsaga ƙirjinsa ya fito da zuciyarsa, ya cire wani gudan jini daga jikinta, ya ce: “Wannan rabon Shaiɗan ne a jikinka.” Sannan ya sanya shi a cikin tasa ta zinariya ya wanke shi da ruwan Zamzam, sannan ya liƙe shi, ya mayar da shi wurinsa. Sai yara suka tafi a guje wajen mai renon sa, suka faɗa mata cewa, an kashe Muhammadu. Bayan sun nufo inda yake sai suka gamu da shi launin fatar jikinsa ya canza.” [Muslim #261]. Allah kuma ya tabbatar masa cewa, ya sauke masa duk wani laifinsa wanda ya yi masa nauyi, kamar yana ɗauke da shi a gadon bayansa zai karya masa shi. Watau dai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gafarta masa duk wasu laifuka na baya da suka wuce da na nan gaba idan da za su samu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa, ya ɗaukaka ambatonsa, yayin da ake ambaton sa a cikin kiran salla da iƙama da tahiya da sauransu.
فَإِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرًا
Open ayah 94:5To lalle tsanani yana tare da sauƙi.
إِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرٗا
Open ayah 94:6Lalle tsananin yana tare da sauƙi.
فَإِذَا فَرَغۡتَ فَٱنصَبۡ
Open ayah 94:7Saboda haka idan ka gama (harkokinka) sai ka kafu (wajen bautar Allah).
وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَٱرۡغَب
Open ayah 94:8Sannan kuma ka yi kwaɗayi wajen Ubangijinka kawai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, tare da kowane tsanani da ƙunci, to akwai sauƙi da yalwa, Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma nanata cewa, lalle tare da tsananin da ƙuncin akwai sauƙi da yalwa, domin ya tabbatar masa da cewa, koyaushe yana tare da nasara da rinjaye mai ƙarfi, don haka kada muzgunawar mutanensa ta dame shi har ta hana shi aikinsa na kira zuwa ga Allah (Mai tsarki da daukaka). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da cewa, idan ya gama ayyukansa na yau da gobe to ya sami isasshen lokaci ya ƙara sa ƙaimi wajen bautarsa, ya kuma nuna kwaɗayinsa gare shi (Mai tsarki da daukaka) shi kaɗai.