التين

At-Tin

The Fig · Surah 95 · Ayahs: 8 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. وَٱلتِّينِ وَٱلزَّيۡتُونِ

    Open ayah 95:1

    Na rantse da ɓaure da zaitun.

  2. وَطُورِ سِينِينَ

    Open ayah 95:2

    Da (dutsen) Ɗuri Sinina .

  3. وَهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ ٱلۡأَمِينِ

    Open ayah 95:3

    Da wannan garin amintacce (watau Makka).

  4. لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِيٓ أَحۡسَنِ تَقۡوِيمٖ

    Open ayah 95:4

    Haƙiƙa Mun halicci mutum a kan mafi kyan diri.

  5. ثُمَّ رَدَدۡنَٰهُ أَسۡفَلَ سَٰفِلِينَ

    Open ayah 95:5

    Sannan Muka mayar da shi mafi ƙasƙancin ƙasƙantattu.

  6. إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَلَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونٖ

    Open ayah 95:6

    Sai fa waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, to su kam suna da lada ba mai yankewa ba.

  7. فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعۡدُ بِٱلدِّينِ

    Open ayah 95:7

    To (kai kafiri) me ya sa kake ƙaryata ranar sakamako bayan haka?

  8. أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَحۡكَمِ ٱلۡحَٰكِمِينَ

    Open ayah 95:8

    Ashe Allah ba Shi ne Mafi iya hukuncin masu hukunci ba? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa da wasu abubuwa guda huɗu: <b>Na farko, </b> ya yi rantsuwa da bishiyar ɓaure, watau da wuraren tsurowarta. <b>Na biyu, </b> ya yi rantsuwa da bishiyar zaitun, watau da wuraren tsurowarta. <b>Na uku, </b> ya yi rantsuwa da Dutsen \'Ɗuri Sinina\' inda Allah ya yi magana da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). <b>Na huɗu, </b> ya yi rantsuwa da garin Makka mai alfarma, wanda duk wanda ya shige shi ya aminta daga duk wani tsoro. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin waɗannan rantse-rantse da cewa, lalle ya halicci ɗan’adam a kan mafi kyan diri da kamanni, sannan daga baya sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar da shi tsoho tukuf a duniya har ya kasa amfana da gangar jikinsa, kamar yadda ba zai iya amfana da shi ba idan kyakkyawar halittarsa ta asali, watau fiɗira ta lalace, ya zamanto ɗan wuta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya togace wasu bayinsa waɗanda suka yi imani da shi da Manzonsa (ﷺ) suka yi kyawawan ayyuka, to waɗannan ko da sun tsufa tukuf, sun kasa ci gaba da aikata kyawawan ayyukan da suka saba, to suna da wani lada wanda ba ya yankewa har abada, shi ne gidan Aljanna, domin sun tsarkake asalin halittarsu ba su gurɓata shi da miyagun ayyuka ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna butulcin ɗan’adam kafiri yana tambayar sa dalilin da ya sanya yake ƙaryata ranar sakamakon ayyuka bayan duk wasu ƙwararan alamu masu nuna cikar Ƙudurar Allah a kan komai sun bayyana a gare shi. Shin bai san cewa kasancewar ranar alƙiyama ita ce ranar sakamako shi ya tabbatar da cewa, Allah shi ne ya fi duk wasu masu hukunci iya hukunci da tsayar da adalci ba? Don haka ta yaya wani zai yi tsammanin Allah (Mai tsarki da daukaka) zai ƙyale bayinsa hakanan sakaka ba tare da ya yi hukunci a tsakaninsu, ya saka wa wanda ya kyautata da kyakkyawan sakamako, wanda kuma ya munana ya haɗa shi da mummunan sakamako ba?