العلق

Al-Alaq

The Clot · Surah 96 · Ayahs: 19 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. ٱقۡرَأۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلَّذِي خَلَقَ

    Open ayah 96:1

    Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, Wanda Ya yi halitta.

  2. خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِنۡ عَلَقٍ

    Open ayah 96:2

    Ya halicci mutum daga gudan jini.

  3. ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ

    Open ayah 96:3

    Ka yi karatu alhali Ubangijinka Shi ne mafi karamci.

  4. ٱلَّذِي عَلَّمَ بِٱلۡقَلَمِ

    Open ayah 96:4

    Wanda Ya koyar ta (hanyar) alƙalami.

  5. عَلَّمَ ٱلۡإِنسَٰنَ مَا لَمۡ يَعۡلَمۡ

    Open ayah 96:5

    Ya koyar da mutum abin da bai sani ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Manzon Allah (ﷺ) ya yi karatu da sunan Ubangijinsa wanda ya halicci dukkan halittu. Ya halicci mutum daga gudan jini bayan a da yana ɗigon maniyyi. Sannan ya sake umartar sa da ya karanta abin da aka yiwo masa wahayinsa na Alƙur’ani, ya kuma sani cewa, Ubangijinsa shi ne mafi karamci da babu wanda ya kai shi, saboda shi mai yawan kyauta ne da kyautatawa. Shi ne wanda ya koyar da ɗan\'adam rubutu ta hanyar amfani da alƙalami, ya kuma sanar da shi abin da bai sani ba.

  6. كَلَّآ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَيَطۡغَىٰٓ

    Open ayah 96:6

    Tabbas! Lalle (jinsin) mutum haƙiƙa yana yin ɗagawa.

  7. أَن رَّءَاهُ ٱسۡتَغۡنَىٰٓ

    Open ayah 96:7

    Don ya ga kansa yana cikin wadata.

  8. إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجۡعَىٰٓ

    Open ayah 96:8

    Lalle kuma zuwa ga Ubangijinka ne makomar (taka) take.

  9. أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يَنۡهَىٰ

    Open ayah 96:9

    Ka ba ni labarin wanda yake hana.

  10. عَبۡدًا إِذَا صَلَّىٰٓ 

    Open ayah 96:10

    Bawa yayin da ya yi salla.

  11. أَرَءَيۡتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلۡهُدَىٰٓ

    Open ayah 96:11

    Ka ba ni labari idan (shi Bawan) ya kasance a kan shiriya.

  12. أَوۡ أَمَرَ بِٱلتَّقۡوَىٰٓ

    Open ayah 96:12

    Ko kuma ya yi umarni da taƙawa.

  13. أَرَءَيۡتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ

    Open ayah 96:13

    Ka ba ni labari idan (shi mai hanawar) ya ƙaryata ya kuma ba da baya.

  14. أَلَمۡ يَعۡلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ

    Open ayah 96:14

    Shin bai sani ba cewa lalle Allah Yana ganin (sa)?

  15. كَلَّا لَئِن لَّمۡ يَنتَهِ لَنَسۡفَعَۢا بِٱلنَّاصِيَةِ

    Open ayah 96:15

    A\'aha! Tabbas idan bai hanu ba to za Mu ja shi ta makwarkwaɗar kai.

  16. نَاصِيَةٖ كَٰذِبَةٍ خَاطِئَةٖ

    Open ayah 96:16

    Makwarkwaɗar kai mai ƙaryatawa, mai aikata laifi.

  17. فَلۡيَدۡعُ نَادِيَهُۥ

    Open ayah 96:17

    To ya kirawo majalisar tasa.

  18. سَنَدۡعُ ٱلزَّبَانِيَةَ

    Open ayah 96:18

    Mu kuma lalle za Mu kirawo (mala’iku) zabaniyawa.

  19. كَلَّا لَا تُطِعۡهُ وَٱسۡجُدۡۤ وَٱقۡتَرِب۩

    Open ayah 96:19

    Faufau! Kada ka bi shi, ka kuma yi salla, ka kusanta (ga Allah). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da abin da yake jefa ɗan’adam cikin girman kai da ɗagawa, watau lokacin da zai samu kansa cikin wadata ta dukiya ko matsayi ko mulki, sai ya manta cewa, makomarsa zuwa ga Ubangijinsa take a ranar alƙiyama inda zai ga sakamakon ayyukansa masu kyau da munana. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ɗagawar mutum takan kai shi har ya nemi hana wani yin salla, watau bautar Ubangijinsa ko da kuwa wanda yake hanawar yana kan shiriya daga Allah (Mai tsarki da daukaka), yana ibadarsa da hujja da ilimi. Ko kuma ya zamanto yana yi wa mutane umarni da taƙawa, watau bin umarnin Allah da guje wa haninsa. Yanzu mutum irin wannan ya dace a hana shi abin da yake yi? Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, yanzu ba abin mamaki ba ne a ce, shi mai hana a bauta wa Allah ya zamanto ya ƙaryata abin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo da shi, ya bijire masa? Shin wannan ba zai ji tsoron Allah ba? Kuma har wa lau shi bai san cewa Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ganin abin da yake aikatawa ba ne? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da shi cewa, al’amarin ba fa kamar yadda yake zato ne ba, tabbas har idan bai daina abin da yake yi ba, watau ƙaryata mai kira zuwa gaskiya da hana shi bautar Allah, to lalle Allah zai damƙi makwarkwaɗar kansa ya ja shi da ƙarfi zuwa wutar Jahannama, domin kuwa mai wannan makwarkwaɗar kai mutum ne maƙaryaci a maganganunsa, mai aikata laifuffuka, don haka ya cancanci azabar Allah wadda babu mai iya kare shi; idan kuwa yana tantama, to sai ya kirawo ‘yan majalisarsa su zo su kuɓutar da shi daga shiga wuta, shi kuma Allah ya tabbatar masa cewa, zai kirawo nasa mala’ikun zabaniyawa masu tsaron wutar Jahannama, ƙarfafa masu kaushin hali halayya, waɗanda ba sa saɓa wa umarnin Allah, masu cika aiki ne, don haka sai ya ga wane ɓangare ne a cikin ɓangarori biyun ya fi ƙarfi da tsanani? An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya kasance yana salla, sai Abu Jahl ya zo ya ce masa: “Ba na hana ka wannan ba? Ba na hana ka ba?” Sai Annabi (ﷺ) ya juya ya daka masa tsawa. Sai Abu Jahl ya ce: “Kai ka san kuwa babu mai yawan ‘yan majalisata?” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “To ya kirawo majalisar tasa, mu kuma za mu kirawo zabaniyawa .” Sai Ibnu Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wallahi da a ce ya kirawo majalisar tasa, da kuwa zabaniyawan Allah sun cafke shi.” [Tirmizi #3349 da Ahmad #2321, 3044]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsawatar masa da cewa al’amarin ba yadda yake zato ne ba, ba zai iya cutar da wanda yake hana wa yin ibada da komai ba, don haka kada Manzon Allah (ﷺ) ya yi masa biyayya, ya ƙyale shi ya ci gaba da ibadarsa, ya yi ta sujjada ga Allah kuma ya kusance shi da ayyukan ɗa’a. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Abu Jahl ya tambayi jama’arsa cewa: “Shin Muhammadu yana zuwa gabanku ya riƙa dungura fuskarsa a cikin ƙasa?” Sai aka ce masa: E, yana yi. Sai ya ce: “Na rantse da gunkin Lata da Uzza idan ya kuskura na gan shi yana haka, to sai na tattaka wuyansa, ko na turbuɗe fuskarsa a cikin rairayi!” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya zo ya shiga salla, sai ko Abu Jahal ya miƙe ya nufi inda yake da niyyar zai tattaka wuyan Manzon Allah (ﷺ), mutane ba su ankara ba sai suka gan shi ya juya da baya a guje yana kakkarewa da hannayensa. Sai aka tambaye shi: “Me ya faru da kai ne haka?” Sai ya amsa da cewa: “Ai abin da na gani tsakanina da shi wani gwalalo ne da wani abin tsoro mai wasu fukafukai.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Da ya kuskura ya matso kusa da ni, da mala’iku sun yi masa gunduwa-gunduwa.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyi har zuwa ƙarshen Sura. [Muslim #2797 da Ahmad #8831]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lokacin da bawa ya fi kusa da Ubangijinsa shi ne lokacin da yake sujjada, don haka ku yawaita yin addu’a.” [Muslim #482].