القدر

Al-Qadr

The Power, Fate · Surah 97 · Ayahs: 5 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ فِي لَيۡلَةِ ٱلۡقَدۡرِ

    Open ayah 97:1

    Lalle Mu Muka saukar da shi (Alƙur’ani) a daren Lailatul-Ƙadari (dare mai daraja).

  2. وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا لَيۡلَةُ ٱلۡقَدۡرِ

    Open ayah 97:2

    Mene ne ya sanar da kai mece ce Lailatul-Ƙadari?

  3. لَيۡلَةُ ٱلۡقَدۡرِ خَيۡرٞ مِّنۡ أَلۡفِ شَهۡرٖ

    Open ayah 97:3

    (Daren) Lailatul-Ƙadari ya fi wata dubu alheri.

  4. تَنَزَّلُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ فِيهَا بِإِذۡنِ رَبِّهِم مِّن كُلِّ أَمۡرٖ

    Open ayah 97:4

    Mala’iku da Jibrilu suna ta saukowa da dukkanin al’amura a cikinsa da izinin Ubangijinsu.

  5. سَلَٰمٌ هِيَ حَتَّىٰ مَطۡلَعِ ٱلۡفَجۡرِ

    Open ayah 97:5

    Aminci ne shi (daren dukkansa) har zuwa hudowar alfijir. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tabbatar da cewa, ya saukar da Alƙur’ani a daren Lailatul-Ƙadari cikin watan Ramadana, watau ya saukar da jimillarsa a sama ta kusa a cikin wannan daren, kamar yadda a cikinsa ne ya fara saukar da shi ga Manzon Allah (ﷺ) a Kogon Hira. Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “An saukar da Alƙur’ani a dunƙule lokaci guda daga Lauhul Mahfuzu zuwa Baitul-Izza a sama ta kusa, sannan ya sauka ga Annabi (ﷺ) guntu-guntu gwargwadon buƙata a cikin shekara ashirin da uku.” [Al-Hakim #4216, Ibn Abi Shaiba #30190]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi Manzonsa (ﷺ) cewa, ko ya san irin yawan albarka da tarin alheri da ya sanya a cikin daren Lailatul-Ƙadari? Sai ya bayyana masa cewa, wannan dare babban dare ne, domin kuwa ya fi wata dubu alheri, watau ga wanda zai yi sallolin dare a cikinta yana mai neman lada a wurin Allah. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: \"Duk wanda ya yi tsayuwar dare a cikin Lailatul-Ƙadari yana mai imani da neman lada, to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa\". [Bukhari #1910 da Muslim #760]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mala’iku tare da Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suna saukowa a cikinsa da duk wani abu da Allah ya ƙaddara na arziki da mutuwa da haihuwa da duk wani abu da zai faru a wannan shekarar. Suna kuma saukowa ne da izinin Ubangijinsu. Sannan ya bayyana cewa, shi wannan dare dukkansa mai albarka ne da aminci tun farkonsa har zuwa ƙarshensa, watau lokacin huduwar alfijir. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Na ga dukkan mafarkanku sun haɗu a kan goman ƙarshe, don haka ku nemi wannan dare a cikin kwanaki mara na wannan goman.” [Muslim #1165]. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku lalubi daren Lailatul-Ƙadari a kwanakin mara na goman ƙarshe na watan Ramadana.” [Bukhari #2017 da Muslim #1169].