البينة
Al-Bayyina
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
لَمۡ يَكُنِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ مُنفَكِّينَ حَتَّىٰ تَأۡتِيَهُمُ ٱلۡبَيِّنَةُ
Open ayah 98:1Waɗanda suka kafirta daga ma’abota littafi da mushirikai ba su zamanto masu barin abin da suke kai (na kafirci) ba har sai hujja bayyananniya ta zo musu.
رَسُولٞ مِّنَ ٱللَّهِ يَتۡلُواْ صُحُفٗا مُّطَهَّرَةٗ
Open ayah 98:2(Watau) Manzo daga Allah da zai riƙa karanta (musu) takardu masu tsarki.
فِيهَا كُتُبٞ قَيِّمَةٞ
Open ayah 98:3(Waɗanda) a cikinsu akwai hukunce-hukunce masu ƙima.
وَمَا تَفَرَّقَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَةُ
Open ayah 98:4Waɗanda kuma aka bai wa littafi ba su rarraba ba sai bayan da hujja bayyananniya ta zo musu.
وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَذَٰلِكَ دِينُ ٱلۡقَيِّمَةِ
Open ayah 98:5Ba a kuma umarce su ba sai don su bauta wa Allah suna masu tsantsanta addini gare Shi, suna masu kauce wa ɓarna, suna kuma tsayar da salla, kuma suna ba da zakka. Wannan kuwa shi ne addinin miƙaƙƙiyar hanya.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمۡ شَرُّ ٱلۡبَرِيَّةِ
Open ayah 98:6Lalle waɗanda suka kafirta daga ma’abota littafi da mushirikai suna cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafiya sharrin halitta.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أُوْلَٰٓئِكَ هُمۡ خَيۡرُ ٱلۡبَرِيَّةِ
Open ayah 98:7Lalle waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, waɗannan su ne mafiya alherin halitta.
جَزَآؤُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُۚ ذَٰلِكَ لِمَنۡ خَشِيَ رَبَّهُۥ
Open ayah 98:8Sakamakonsu a wajen Ubangijinsu gidajen Aljanna ne na dawwama waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu har abada; Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi. Wannan kuma (sakamako ne) ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da bayyana cewa, kafirai daga cikin Yahudawa da Nasara da mushirikan Larabawa, ba su zamanto masu barin kafircinsu da suka haɗu a kai ba har sai wata hujja bayyananniya ta zo musu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wannan hujjar da cewa, wani manzo ne da zai aiko yana karanta musu wasu takardu masu tsarki, watau waɗanda shaiɗanu ba sa iya shafar su sai dai mala’iku masu tsarki. A cikinsu kuma akwai labarai na gaskiya da hukunce-hukunce na adalci waɗanda suke ɗora mutane a kan miƙaƙƙen tafarki na gaskiya. Wannan shi ne halin da suke ciki kafin aiko Manzon Allah (ﷺ), wai suna dakon zuwan sa, domin ya zo su yi imani da shi. Bayan zuwansa kuma sai suka rarrabu, wasu suka yi imani; wasu kuma suka ci gaba da kafircinsu, suka ƙaryata shi da duk abin da ya zo da shi. Wannan ya sa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Yahudawa da aka ba su littafin Attaura da Nasara da aka ba su littafin Linjila ba su rarraba ba sai bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu da Annabinsa (ﷺ), daga cikinsu wasu suka musulunta, wasu kuma suka doge a kan kafircinsu, tare da sun tabbatar shi mai gaskiya ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa, abin da zai ƙara fito da taurin kan ma’abota littafi a fili shi ne cewa, babu wani umarni da aka yi musu a cikin Alƙur’ani wanda ya saɓa irin umarnin da aka yi musu a littattafansu na cewa, su bauta wa Allah shi kaɗai su guje wa shirka, su kuma tsayar da salla su bayar da zakka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, wannan fa shi ne addinin miƙaƙƙiyar hanya wadda babu karkata a cikinta. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan sakamakon waɗanda suka kafirta daga Yahudawa da Nasara da mushirikai, inda ya tabbatar da cewa, za su shiga wutar Jahannama a ranar alƙiyama su kuma dawwama a cikinta har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta ta su da cewa, su ne mafi sharrin halittu, saboda kafircinsu da yadda suka ƙaryata Manzon Allah (ﷺ). Su kuma waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa (ﷺ) suka kuma yi ayyuka nagari, to waɗannan su ne mafiya alherin halittu, domin kuwa sakamakonsu a wajen Ubangijinsu shi ne gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, za su shige su su kuma dawwama a cikinsu har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yarda da su saboda sun yi imani da shi sun yi masa ɗa’a, su ma kuma sun yarda da shi saboda cikakkiyar rahamarsa da suka samu. Wannan rahama ta Allah kuwa, sakamako ne ga duk wanda ya ji tsoron sa ya bi umarninsa ya kuma guje wa haninsa.