الزلزلة

Az-Zalzala

The Earthquake · Surah 99 · Ayahs: 8 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. إِذَا زُلۡزِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ زِلۡزَالَهَا

    Open ayah 99:1

    Idan aka girgiza ƙasa matuƙar girgiza ta.

  2. وَأَخۡرَجَتِ ٱلۡأَرۡضُ أَثۡقَالَهَا

    Open ayah 99:2

    Ƙasar kuma ta fitar da nauyaye-nauyayenta.

  3. وَقَالَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا لَهَا

    Open ayah 99:3

    Mutum kuma ya ce: “Me ya same ta?”

  4. يَوۡمَئِذٖ تُحَدِّثُ أَخۡبَارَهَا

    Open ayah 99:4

    A wannan ranar ne za ta ba da labaranta.

  5. بِأَنَّ رَبَّكَ أَوۡحَىٰ لَهَا

    Open ayah 99:5

    Don Ubangijinka Ya umarce ta (da yin haka).

  6. يَوۡمَئِذٖ يَصۡدُرُ ٱلنَّاسُ أَشۡتَاتٗا لِّيُرَوۡاْ أَعۡمَٰلَهُمۡ

    Open ayah 99:6

    A wannan ranar mutane za su fito a warwatse, don a nuna musu ayyukansu.

  7. فَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٍ خَيۡرٗا يَرَهُۥ

    Open ayah 99:7

    To duk wanda ya yi aikin alheri daidai da zarra zai gan shi.

  8. وَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ شَرّٗا يَرَهُۥ

    Open ayah 99:8

    Wanda kuma duk ya yi aikin sharri daidai da zarra zai gan shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da ba da labarin lokacin tashin alƙiyama, watau yayin da ƙasa za ta yi matuƙar girgiza ta fitar da matattun da suke cikinta da sauran ma’adanan ƙarƙashinta. A lokacin mutum zai ɗimauce ya riƙa cewa, me ya same ta ne take wannan girgiza mai tsanani? An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ƙasa za ta amayo ‘ya’yan cikinta (manya-manya) kamar dirkoki na zinari da azurfa, sai wanda ya yi kisa ya zo ya ce: ‘A kan wannan ne na yi kisa’; sai mai yanke zumunci ya zo yana cewa: ‘A kan wannan ne na yanke zumuncina’; sai ɓarawo shi ma ya zo ya ce: ‘A kan wannan ne aka yanke mini hannuna’. Sannan sai su duka su bar wannan dukiya ba tare da sun ɗauki komai daga cikinta ba.” [Muslim #1013 da Tirmizi #2208]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a wannan rana ce ƙasa za ta ba da labaran ayyukan da aka aikata a kanta na alheri ko na sharri, domin Allah Ubangijinta ya umarce ta da yin haka, don haka ba za ta saɓa umarninsa ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a wannan rana ce mai tsanani da abin tsoro, mutane za su fito zuwa wurin hisabi ƙungiya-ƙungiya, domin a nuna musu ayyukansu masu kyau da munana, waɗanda suka aikata a duniya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon kowa da cewa, duk wanda ya yi wani aikin alheri gwargwadon \'zarra\', watau daidai da nauyin jaririyar tururuwa, to zai ga aikinsa a gabansa. Hakanan duk wanda ya yi wani aikin sharri gwargwadon \'zarra\', watau daidai da nauyin jaririyar tururuwa, to zai gan shi a gabansa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa: Ya Manzon Allah, mene ne hukuncin zakkar jakai? Sai ya ce: “Ba a saukar mini da komai ba dangane da jakai, sai wannan gamammiyar ayar cewa: “Wanda ya yi aikin alheri daidai da zarra zai gan shi. Wanda kuma duk ya yi aikin sharri daidai da zarra zai gan shi .” [Bukhari #2371 da Muslim #987].