العاديات

Al-Aadiyaat

The Chargers · Surah 100 · Ayahs: 11 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. وَٱلۡعَٰدِيَٰتِ ضَبۡحٗا

    Open ayah 100:1

    Na rantse da (dawaki) masu sukuwa suna kukan ciki.

  2. فَٱلۡمُورِيَٰتِ قَدۡحٗا

    Open ayah 100:2

    Sannan masu bugun ƙyastu da kofatai.

  3. فَٱلۡمُغِيرَٰتِ صُبۡحٗا

    Open ayah 100:3

    Sannan masu kai hari da asuba.

  4. فَأَثَرۡنَ بِهِۦ نَقۡعٗا

    Open ayah 100:4

    Sai suka tayar da ƙura da ita (sukawar tasu).

  5. فَوَسَطۡنَ بِهِۦ جَمۡعًا

    Open ayah 100:5

    Sai kuma suka shiga tsakiyar taro (da mahayansu)

  6. إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٞ

    Open ayah 100:6

    Lalle mutum tabbas mai yawan butulci ne ga Ubangijinsa.

  7. وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٞ

    Open ayah 100:7

    Lalle kuma shi shaida ne a kan haka.

  8. وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلۡخَيۡرِ لَشَدِيدٌ

    Open ayah 100:8

    Lalle shi kuma mai tsananin son alheri ne.

  9. ۞أَفَلَا يَعۡلَمُ إِذَا بُعۡثِرَ مَا فِي ٱلۡقُبُورِ

    Open ayah 100:9

    Shin bai sani ba ne idan aka bankaɗo abubuwan da suke cikin ƙaburbura?

  10. وَحُصِّلَ مَا فِي ٱلصُّدُورِ 

    Open ayah 100:10

    Aka kuma tattaro abubuwan da suke cikin ƙiraza?

  11. إِنَّ رَبَّهُم بِهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّخَبِيرُۢ

    Open ayah 100:11

    Lalle a wannan ranar tabbas Ubangijinsu Masani ne game da su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa da dawakai waɗanda ya siffanta su da cewa masu sukuwa ne suna kukan ciki saboda tsananin gudu. Masu kuma ƙyasta wuta da kofatansu idan suka daki duwatsu da su, saboda tsananin dirarsu. Kuma masu kai wa maƙiya hari lokacin asuba. Da wannan tsananin gudun ne kuma suke tayar da ƙura, sannan su kutsa tsakiyar taron maƙiya da mahayansu, don su tarwatsa su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata mummunar ɗabi’a ta ɗan’adam da cewa, shi mai tsananin butulce wa ni’imomin Ubangijinsa ne, ba ya gode masa, kuma ba ya yi wa wani alheri da abin da Allah ya ba shi, shi kansa kuma shaida ne a kan wannan butulci da rowar tasa, sannan kuma ga shi mai tsananin son dukiya, wanda hakan ne yake sanya shi rowa da mammaƙo. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗe shi inda ya ja hankalinsa da cewa, shin bai sani ba ne idan Allah ya tashi matattun da suke cikin ƙaburbura, ya fito da su domin yi musu hisabi, ya kuma bayyana abin da yake cikin zukata na aƙidu da niyyoyi? To a lokacin ne ɗan\'adam zai gane cewa, lamarin ya fi ƙarfin yadda yake zato, domin zai tabbatar da cewa, lalle Ubangijin bayi a wannan rana masanin komai ne ciki da waje, babu abin da zai ɓuya gare shi, kuma zai yi wa kowa sakayya a kan ayyukansa masu kyau ko munana.