القارعة
Al-Qaari'a
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلۡقَارِعَةُ
Open ayah 101:1Mai ƙwanƙwasa (zukata da tsoro).
مَا ٱلۡقَارِعَةُ
Open ayah 101:2Mece ce mai ƙwanƙwsa (zukata da tsoro)?
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡقَارِعَةُ
Open ayah 101:3Kuma me ya sanar da kai mece ce mai ƙwanƙwasa (zukata da tsoro)?
يَوۡمَ يَكُونُ ٱلنَّاسُ كَٱلۡفَرَاشِ ٱلۡمَبۡثُوثِ
Open ayah 101:4(Ita ce) ranar da mutane za su zama kamar ɗangon fari masu bazuwa.
وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ ٱلۡمَنفُوشِ
Open ayah 101:5Duwatsu kuma su zama kamar kaɗaɗɗiyar auduga.
فَأَمَّا مَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ
Open ayah 101:6To amma wanda ma’aunan ayyukansa suka yi nauyi.
فَهُوَ فِي عِيشَةٖ رَّاضِيَةٖ
Open ayah 101:7To shi kam yana cikin rayuwa mai gamsarwa.
وَأَمَّا مَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ
Open ayah 101:8Amma kuma duk wanda ma’aunan ayyukansa suka yi shafal.
فَأُمُّهُۥ هَاوِيَةٞ
Open ayah 101:9To shi makomarsa (wutar) Hawiya ce.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا هِيَهۡ
Open ayah 101:10Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?.
نَارٌ حَامِيَةُۢ
Open ayah 101:11Wuta ce mai tsananin zafi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da kiran ranar alƙiyama da wani suna, watau ‘al-Ƙari’a’ wanda yake nufin mai ƙwanƙwasa zukata da tsoro. Sai kuma ya nuna girman sha’aninta inda ya yi tambaya cewa, mece ce mai ƙwanƙwasa zukata da tsoro? Ya kuma tambayi Manzonsa (ﷺ) cewa, mene ne ya sanar da shi me ake kira da mai ƙwanƙwasa zukata da tsoro? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ranar da cewa, ita ce ranar da mutane za su zama kamar ɗangon fara masu bazuwa a ko’ina. Duwatsu kuma su zama kamar kaɗaɗɗiyar auduga saboda rashin nauyinsu da watsewarsu a cikin sararin sama. To kamar haka ne mutane za su tarwatse a wannan rana, saboda tsananin tsoro da firgici su warwatsu a ko’ina da ina, kowa yana ta kansa. Sai kuma Allah ya bayyana sakamakon mutane a wannan rana yayin da za su kasu kashi biyu: <b>Kashi na farko </b>, su ne waɗanda kyawawan ayyukansu za su rinjayi munana, to waɗannan suna cikin rayuwa mai gamsarwa a gidan Aljanna. <b>Kashi na biyu </b>, su ne waɗanda idan aka auna ayyukansu za su yi shafal ba nauyi, watau munanan ayyukansu za su rinjayi kyawawa; to waɗannan makomarsu a wannan rana ita ce wutar Hawiya , watau Jahannama, ita kuwa wuta ce mai tsananin zafi. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wutar da ɗan’adam yake hurawa kaso ɗaya ce daga cikin kaso saba’in na wutar Jahannama.” Sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah, ai ko ta duniya ma ta isa azaba.” Sai ya ce: “Ta lahira ta fi ta da kaso sittin da tara.” [Bukhari #3265 da Muslim #2843].